Mabudin Kunnuwa
Kasancewar wayoyin salula kayayyakin fasaha ne da aka kera su da na’urori da sinadaran fasaha da kimiyyar lantarki, ya zama wajibi mu san irin tsarin da suke gudanuwa a kai. Wannan zai sawwake mana lalurori da dama. Misali, idan muka san tsarin babbar manhajar da waya ke amfani da ita, zamu san yadda ake sarrafa waya mai irin wannan manhaja. Idan muka san tsari da nau’in batirin da take amfani dashi, hakan zai taimaka mana wajen fahimtar tsarin caji da zamu rika yi. Idan muka san dabi’ar waya ta hanyar yanayi da kirarta, hakan zai sawwake mana matsaloli da dama. Wannan tasa yau muka dauko wannan bangare don gabatar da bayanai iya gwargwado, kan bangarorin wayar salula. A yau mai karatu zai san dukkan karikitan da wayar salula ke dauke dasu; masu motsi da marasa motsi; wadanda ake gani da wadanda ba a ganinsu sai dai a hankalci tasirinsu kawai. Kafin mu kutsa cikin wannan bayani, zai dace mu yi ‘yar gajeriyar gabatarwa kan dukkan wadannan karikitai.
Ita dai wayar salula na dauke ne da muhimman bangarori guda biyu; bangaren gangar-jiki da kuma bangaren ruhi ko rai. Wannan shine tsarin da dukkan kayayyakin sadarwa ke gudanuwa a kai, irinsu Kwamfuta, da na’urar daukan hoto, da talabijin irin na zamani da sauransu. Kowannesu na dauke ne da gangar-jiki da kuma bangaren ruhi. Bangaren gangar-jiki shine ake kira Hardware, ko kuma kwarangwal a Hausar zamani. Shine bangaren da mai karatu ke gani, kuma yake iya tabawa. Sai bangaren ruhi ko masarrafa, wanda a turance ake kira Software ko Firmware a turancin sadarwa ta zamani. Wannan bangare ya kumshi ruhin da wayar ke gudanuwa a kansu, wanda mai mu’amala ke iya gani a fuskar wayar ko masu gudanuwa a karkashin kasa. A halin yanzu ga bayanai nan dalla-dalla kan wadannan bangarori. Sai a kasance tare damu.
Gangar-jikin Wayar Salula
Gangar-jikin wayar salula, kamar yadda bayani ya gabata a sama, shine “kwarangwal” ko kuma dukkan wani abinda zaka iya tabawa a jikinta. A turance su ake kira Hardware. Su ne bangare na biyu da ke da muhimmanci a wayar wajen sadarwa. Abu na farko cikin wannan bangare shine inji, wanda ke dauke da sauran bangarorin ta hanyoyi dabam-daban. Wannan bangare dai shine kashin bayan wayar baki daya. Yana dauke ne da karafa, da robobi, da batir, da kuma cibiyoyi masu muhimmanci ga rayuwar wayar; irinsu Cibiyar Sadarwa (Network Point), da Cibiyar Wutar Lantarki (Circuit), da Cibiyar Samar da Caji (Charging Point) da dai sauransu. Har wa yau, wannan bangare na dauke ne da ramuka kanana, da layukan wutar lantarki masu nuna hanyar da kowace waya ke bi don isar da wutar lantarki ko sinadaran sadarwa a yayin da ake amfani da wayar ko take zaman dirshan.
Abu na biyu bayan gangar-injin shine Cibiyar Sadarwa, watau Network Point. Kamar yadda mai karatu yaji sunan, aikin wannan bangare shine samar da sinadaran sadarwa ko kuma tsarin sadarwa (watau Network). Idan mai karatu ya dubi fuskar wayarsa zai ga alama ko tambarin da ke nuna halin sadarwar da ke tsakanin wayarsa da kamfanin sadarwar da yake amfani da katin SIM dinsu. Wannan cibiya ce ke daidaita sahu tsakanin wayar da tsarin sadarwar da ke bigiren da mai wayar ke zaune. Wasu lokuta yanayin sadarwa yayi sama, wasu lokuta kuma yayi kasa. Har wa yau, karfin wannan cibiya wajen jawo yanayin sadarwa ga mai amfani da wayar ya danganci nau’in wayar da yake amfani da ita. Misali, wayoyin Nokia sun yi suna a duniya wajen karfin jawo yanayin sadarwa a waya fiye da sauran wayoyi. Ire-iren wayoyin da ke fitowa daga kasar Sin a halin yanzu (masu arha da matukar kara wajen kidi), galibinsu basu da karfin inganci wajen jawo yanayin sadarwa a waya. Shi yasa idan kana waje daya da mai wayar salula ‘yar kasar Sin, kai kuma kana rike da ta asali irinsu Nokia ko Motorola, sai ka fi su samun yanayin sadarwa a lokaci guda. Duk da yake hakan ya danganci wurin da kake ne, da kuma karfin na’urar kamfanin da ke baka sadarwa. Wannan cibiya ta sadarwa dai a karshe, tana jone ne da kunnen sadarwar wayar salula, watau Antenna, wacce ke gine cikin galibin wayoyin salula na zamani.
Bangare mai muhimmanci na uku shine Cibiyar Wutar Lantarki, ko Circuit a turance. Wannan bangare ne ke samar da wutar lantarkin da wayar ke amfani dashi wajen sarrafa sauran gabobinta. Bangaren na like ne da ramin samar da caji, ko Charging Port a turance. Cibiyar Wutar Lantarki na like ne a jikin inji, kamar yadda Cibiyar Sadarwa take. Kuma ita ce ke samar da wutar lantarki ga injin wayar, ta hanyar batir. Kamar Cibiyar Sadarwa, Cibiyar Wutar Lantarki ita ma tana da alama ko tambari a fuskar wayar, wanda ke nuna yanayin caji ko karfin wutar lantarkin da ke dauke da wayar a kowane lokaci. Idan caji yayi kasa, sai alamar ta gangara, kamar yadda muka saba gani a fuskar wayoyinmu.
Bangare na hudu kuma shine batir, wanda na san masu karatu sun sanshi. Yana daya daga cikin shahararrun bangarorin wayar salula; saboda tasiri da kuma amfaninsa wajen baiwa wayar rayuwa a dukkan lokuta. Shi batir na dauke ne da sinadaran lantarki nau’uka dabam-daban, dangane da yanayin aikinsa. Galibin batiran da kamfanonin kera wayoyin salula ke kerawa suna dauke ne da sinadaran Lithium-ion Phosphate. Wadannan sinadarai aikinsu shine taskance karfin lantarki (Electric Current) da ke shigowa ta kogon lantarkin (Charging Port) mai mu’amala da na’urar caji, watau Charger. Idan wadannan sinadarai na lantarki sun shigo sai a taskance su tsibi-tsibi. Da zarar sun cika, sai wayar taci gaba da amfani dasu. Wadannan batira dai sun sha bamban da batiran rediyo da muka saba amfani dasu. Su batiran rediyo (kanana da manya) da zarar an gama zagwanyar da karfinsu, sai su mace. Amfaninsu ya kare kenan. Sai dai a siyo wasu. Amma su nau’in Lithium-ion Phosphate taskance sinadaran lantarkin suke yi, idan suka samu iya gwargwadon da suke bukata, sai su daina karban sinadaran lantarkin. Daga nan sai a ci gaba da amfani da su har zuwa lokacin da zasu zagwanye. Idan suka zagwanye, sai a sake jona su cikin lantarki don su kara taskance wadannan sinadaran lantarki kamar yadda aka yi a baya. Akan dauki a kalla shekara guda ana amfani dasu kafin tagomashinsu ya kare.
Sai bangare na biyar, watau Allon Shigar da Bayanai, ko Keypad a Turance. Kamar yadda kowa ya sani, aikin wannan bangare shine taimaka wa mai mu’amala da wayar salula don shigar da lamban da yake son kira, ko amsa kira, ko rubuta sakon tes, ko karanta su, da kuma dukkan hanyoyin mu’amala da fasahohin da ke cikin wayar – irinsu daukan hoto, da daukan bidiyo, da kallon talabijin, da mu’amala da fasahar Intanet ko Bluetooth ko Infra-red, da dai sauransu. Hakan ya faru ne saboda yana dauke ne da dukkan haruffa da lambobin da ake bukata don mu’amala da wayar. Shi allon shigar da bayanai nau’i-nau’i ne. Ya danganci tsari da kimtsin wayar. Galibin wayoyin salula suna dauke ne da allon shigar da bayanai guda daya. Akwai wasu wayoyin salula na musamman masu dauke da alluna guda biyu. Da wanda ke saman marfin wayar, da kuma wanda ke ciki idan an bude. Sannan shi kanshi allon shigar da bayanai din ya sha bamban wajen tsari. Akwai wanda tsarinsa iri daya ne da na kwamfutocin tafi-da-gidanka, watau Laptop. Ire-iren wadannan su ake kira Standard Keypad, kuma suna dauke ne a manyan wayoyin salula na musamman nau’in Smartphones ko Blackberry a takaice. Allon shigar da bayanai dai na manne ne da asalin injin wayar, mai dauke da gurabun da kowane harafi ko lamba ko alama/tambari ke zaune. Duk lambar da ka matsa, zata doshi gurbinta ne, don sanar da wayar irin harafi ko lambar da za ta nuna a fuskarta nan take.
Bayan Allon shigar da bayanai, bangare na gaba mai muhimmanci ga kowace wayar salula duk kankantarta, shine Ma’adanar Bayanai, watau Memory, a takaice. Wannan ma’adana ne ke dauke da dukkan manhajojin da ke cikin wayar, wadanda take amfani dasu don baiwa mai mu’amala damar gudanar da abinda yake so, a lokaci ko yanayin da yake so. Wannan ma’adana kuwa ta kasu kashi uku ne: akwai tabbatacciyar ma’adana, wacce ke dauke da babbar manhajar wayar. Wannan bangaren ma’adana shi ake kira Read Only Memory (ROM). Dukkan wata manhaja da ke cikin wayar na dauke ne cikin wannan ma’adana. Da zarar ka kira kowace irin manhaja ce, sai manhajar ta shigo cikin ma’adanar wucin-gadi, watau bangaren ma’adana ta biyu kenan. Wannan bangare kuma shi ake kira Random Access Memory (RAM). Idan wayar tana kashe, wannan ma’adanar na zama holoko ce, wofintacciya; babu komai ciki. Da zarar ka kunna wayarka, sai masarrafan da ke fuskar wayar (irinsu agogo da alamar yanayin sadarwa, da na cajin batir da sauran bayanai) su shigo cikin RAM, don fara gudanar da aikinsu. Duk masarrafar da ka budo, cikin wannan ma’adana na RAM take zuwa. Da zarar ka gama amfani da ita, ka rufe, sai bayananta su koma can cikin tabbatacciyar ma’adanar, watau Read Only Memory (ROM). Sai bangaren ma’adana ta uku, wacce sanyawa ake yi, ba wai tare ake gina shi da wayar ba. Ma’ana, kana iya sanya mata a kowane lokaci, sannan a kowane lokaci kana iya cirewa, ko da kuwa wayar na kunne ne. Wannan bangare shi ake kira Removable Storage. Wannan nau’in kuwa ya kumshi Ma’adanar Katin Waya na musamman da ake iya saya a sanya mata, mai suna Memory Card (MMC). Wadannan su ne nau’ukan ma’adanai da galibin wayoyin salula ke mu’amala da su. Kowace wayar salula na zuwa ne da ginanniyar ma’adanar bayanai – da nau’in ROM da na RAM. Amma ba kowace waya bace ke zuwa da nau’in Removable Storage. Har wa yau, tsawon rayuwar wadannan ma’adanai ya ta’allaka ne da irin nau’ukan bayanai da ake sanyawa cikinsu, da kuma tsabta ko ingancin bayanan, da kuma dacewarsu da muhallin ma’adanar. Idan aka shigar musu da bayanai masu dauke da kwayoyin cuta, watau Virus, suna iya kamuwa nan take, har su lalata asalin manhajojin da ke dauke cikin wayar, ta kowane irin hali. Bayanai kan haka na nan tafe in Allah Yaso.
Sai bangare na karshe da zamu dakata a kansa, ba don sun kare ba. Wannan bangare kuwa shine marafan wayar; da na gaba da na baya da wanda ke tsakiya – ya danganci yanayin kirar wayar. Kowa ya san amfani murfi ga wayoyin salula. Kariya ne ga kura da datti da dauda da dukkan abinda zai iya zama barazana ga lafiyarta. Haka kariya ne ga lafiyar mai amfani da wayar, a yayin da take kunne. Domin akwai abubuwan da ka iya cutar da shi idan babu murfi, musamman ta bangaren wutar lantarki. Bayan nan, su kansu marafan ado ne ga wayar, wajen bata kima da kwarjini da kuma kamannin da ya dace da ita. Tsari da kimtsin marafan wayar salula sun sha bamban wajen kira, dangane da kamfanin da ya kera wayar. Akwai marafan da tsabar ado ne su. Babu wahala sun fashe ko tsage idan aka mu’amalance su da tsauri. Akwai wadanda kuma su a matsayin kariya kawai suke. Galibinsu zaka samu basu da wani kwarjini a ido, amma kuma suna da inganci wajen baiwa wayar kariya ga lafiyarta da na manhajojin da take dauke dasu. Wayoyin salular da galibi aka kera su don ado (irin na mata misali), zaka samu basu da aminci sosai. Bayan haka, akwai wayoyin da ke zuwa da marafa har guda biyu. Daya na tare da ita, dayan kuma na ajiye. Idan kana bukatar sauyi, sai ka tube ta ka sanya mata sabon. Galibin wayoyin salula ana iya samun marafansu a saya a kasuwa. Duk da yake akwai daidaiku wadanda baka samun murfinsu, muddin wanda ke tare da su ya lalace. Misali, wayoyin salula irin su Nokia 5320 XpressMusic tana zuwa ne da murfinta na asali, kuma kamfanin Nokia bai kera mata makwafi ba. Idan suka lalace, sai dai ka saya mata jabu, wadanda ake kera su ba-kai-ba-gindi. Wanda kuma galibinsu basu cika zama daram a jikin wayar ba. In ma baka yi sa’a ba, su lalata maka wayar; musamman wajen amfani da allon shigar da bayanai.
Kafin mu shiga bayani kan Manhaja ko Ruhin Wayar Salula, akwai abinda na kira “Makale-makalen Wayar Salula”, ko kuma Mobile Phone Accessories. Wadannan su ne ire-iren kayayyakin amfani da ake iya makala wa wayar salula don sauraron bayanai, ko kallon hotuna – masu motsi ko daskararru – ko mu’amala da fasahar Intanet, ko kuma shigarwa ko fitar da bayanai daga ma’adanar wayar. Daga cikin wadannan kayayyaki akwai na’urar caji, ko Charger a turance. Wanda ake amfani dashi wajen caja wayar, da kara mata karfi ta hanyar karfin sinadaran lantarki. Sai lasifikar kunne (Head Phone), da lasifikar amsa kira (Hands-free), masu taimakawa wajen sauraron kade-kade da wake-wake, da kallace-kallace. Har wa yau akwai Wayar Karba ko Shigar da Bayanai, watau Data Cable, ko USB Cable. Da wannan waya zaka iya shigar da bayanai na sauti ko hotuna ko bidiyo, daga kwamfutarka zuwa wayar salula, ko kuma daga wayarka zuwa kwamfuta – ta kan tebur ce ko ta tafi-da-gidanka. Wannan tsari na shigar da bayanai ta hanyar USB Cable na amfani ne da kogon shigar bayanai mai suna Universal Serial Bus (USB), kuma yana cikin hanyoyin zamani da ake amfani dasu a kayayyakin sadarwa na zamani. Abu na karshe da zamu dakata a kai shine abinda har wa yau na sanya wa suna da “Tsinken Ligidi”, ko kuma Joy Stick, a tsarin sadarwa ta zamani. Wannan tsinke ana amfani dashi ne wajen shigar da bayanai ko lodo su ko kuma shiga wurare a cikin wayar salula. Galibin wayoyin salular zamani na musamman, suna zuwa ne da wannan tsinke mai matukar tasiri wajen sadarwa. Saboda sawwake sadarwa da mu’amala da wayar salula musamman a lokutan da mai mu’amala da wayar ke cikin natsuwa ko nishadi. Wadannan, a takaice, su ne kadan cikin karikitan da ake iya makala wa wayar salula da sawwake mu’amala a lokuta dabam-daban.
No comments:
Post a Comment