Thursday, January 14, 2010

Yaduwar Wayar Salula a Duniya

Shimfida

Kamar kowane mako, ina fatan mai karatu na tare da mu cikin wannan silsila da muka faro cikin makonnin baya kan wayar salula da tsari da kimtsin amfani da ita a dukkan lokuta da zamunna. A makon da ya gabata mun kawo bayanai ne kan shahararrun kamfanonin da ke kera wayar salula a duniya. A yau kuma gamu nan tafe da bayani kan dalilan da suke haddasa yaduwar wayar salula a duniya, tun zamanin farko da aka fara kera su, shekaru kusan dari da suka gabata kenan.

Cikin makon da ya gabata ne Hukumar ITU ta fitar da wani rahoto da ke nuna cewa an samu Karin yaduwar wayoyin salula a kasashen Afirka daga kashi biyar cikin dari (5%) zuwa kashi talatin cikin dari (30%). A halin yanzu, kamar yadda wannan rahoto ya tabbatar, akwai a kalla wayoyin salula guda miliyan dari biyu da hamsin da biyar (255 million) da ake amfani dasu a kasashen Afirka. Wannan ke nuna cewa akwai dalilai masu karfi da ke haddasa wannan yaduwa da wayoyin salula ke yi cikin gaugawa a nahiyar Afirka.

Sanin dalilan da suka haddasa yaduwar wannan kayan sadarwa mai matukar tasiri yana da muhimmanci, zai kuma taimaka wa mai karatu wajen fahimtar tsarin da kowace irin wayar salula ke gudanuwa a kai, kamar yadda sanin tsarin da kowane kamfani ke bi wajen kera wayar yake da muhimmanci. Bayan nan, ga daliban ilimi a fannin sadarwa ko fannin zamantakewa, hakan na da muhimmanci har wa yau wajen fahimtar dasu yadda zamani ke saurin canzawa, tare da sanin manyan dalilan da ke haddasa ko kawo sauyi a rayuwar al’umma ta fannin sadarwa.

Dalilan da ke haddasa yaduwar wayar salula a duniya suna da yawa. Amma duk wanda ya dube su, zai ga akwai kamaiceceniya a tsakaninsu. Wannan tasa na dunkule su zuwa gida ko dalilai shida, manya. Wannan kuma shi zai sawwake wa mai karatu fahimtarsu cikin sauki ba tare da bin kowane dalili daya-bayan-daya ba. A halin yanzu ga wadannan dalilan nan.

Saukin Mu’amala

Dalilin farko na abinda ke haddasa yaduwar wayar salula a duniya shine saukin mu’amala. Wannan shine mizanin da malaman kimiyya da fasahar sadarwa na zamani ke amfani dashi wajen gane yaduwa ko tasirin kayan sadarwa cikin sauki a cikin kowane al’umma. A bayyane yake cewa kowa na son sauki. Son sauki dabi’a ce ta kowane dan Adam mai hankali. Idan muka yi la’akari da yaduwar wayoyin salular zamanin farko, da na biyu da wanda ke biye dasu, zamu ga cewa akwai bambancin yawa a tsakanin zamunnan. Su kansu masu tsara wadannan kayayyakin sadarwa a kan takarda, watau injiniyoyin kimiyyar sadarwa da ke zana hoton kowane kayan sadarwa ne, suna la’akari da abinda zai sawwake wa mai mu’amala da fasahar rayuwarsa ne. A galibin kasashen duniya mizanin da masu sayan kayayyakin fasaha ke amfani da ita kenan su ma, duk sadda suka tashi sayan kowane irin abin mu’amala ne na fasaha. Haka idan muka koma kan sauran kayayyakin mu’amala wajen taskancewa da yada bayanai, irinsu kwamfuta da sauransu, haka zamu gani. Kwamfutocin zamanin farko, wadanda a Turancin kimiyyar sadarwa ake kira Main Frame Computers, suna da wahalar mu’amala fiye da na yau. A wannan zamanin ma haka abin yake. Akwai kwamfutoci masu amfani da babbar manhajar sadarwar Linux, galibinsu suna da wuyan sha’ani. Ko a yanzu ba kowa ke iya sarrafa su ta sauki ba tsakanin masu amfani da kwamfuta. Wannan tasa zaka samu basu yadu ba sosai; domin ba kowa ke iya sarrafa su ba. Amma idan muka dubi tsarin babbar manhajar kamfanin Microsoft, watau Windows Operating System, sai mu ga tafi yawa da saurin yaduwa a duniya. Me yasa? Saboda saukin mu’amala da aka yi la’akari da shi wajen gina manhajar. Haka idan muka yi la’akari da wayoyin salular zamanin farko, da wadanda muke amfani dasu yanzu, haka zamu gani. Duk sadda wayoyin salula suka ci gaba da zama masu saukin mu’amala, to zasu ci gaba da yaduwa babu kakkautawa. Saboda kowa na iya amfani dasu; da wanda ya iya karatu, da ma wanda bai iya ba; da mai gani, da wanda baya gani.

Saukin Farashi/Rahusa

Dalili na biyu shine saukin farashi. Tabbas Allah bai yi mutane a kan daraja ko martabar rayuwa iri daya ba. Akwai talakka, da mai kudi, da mai mulki da mai son mulki. Haka muka bambanta, kuma su ma wayoyin salular haka suke. Akwai na masu kudi, da masu karancin kudi, da kuma na masu karancin kudi. Lokacin da wayoyin salula suka fara yaduwa zuwa kasashe masu tasowa irin Nijeriya da sauran kasashen Afirka, galibin wayoyin salular da suka fara zuwa duk zaka samu masu dan karen tsada ne. Wannan tasa ba kowa ke iya sayensu ba, sai wane da wane. Amma daga baya su kansu masu shigowa da wayoyin sun lura da wannan, sai suka nemo nau’uka dabam-daban, kuma masu araha ko masu matsakaicin farashi. Ai nan take sai kasuwa ta fara ja. Ko shakka babu idan muka kwatanta yawan masu wayar salula a yanzu da lokutan baya, zai bayyana cewa yanzu wayoyin salula sun fi yawa, da saurin yaduwa – duk wannan ya faru ne sanadiyyar saukin farashi. Daga naira dubu biyu zuwa dubu dari, kana iya samun wayar salula sabuwa, mai dauke da katin SIM, ka saya. Daga naira dari biyar zuwa dubu goma misali, kana iya samun wayar salula ta hannu ka saya, ka ci gaba da amfani da ita.

Samuwar Nau’uka Dabam-daban

Bayan tasirin saukin mu’amala da rahusa kuma, dalili na uku mai haddasa yaduwar wayar salula a duniya shine samun nau’ukan wayoyin salula dabam-daban a halin yanzu. Bayani kan nau’ukan wayoyin salula ya gabata makonni uku da suka gabata. Samun nau’ukan wayoyin salula na da tasiri wajen nau’unta masu amfani da wayoyin a duniya. Abinda wannan ke nufi shine, kana iya samun wayar salula mai araha, da mai tsada, da mai shafaffen fuska, da mai rufaffiyar fuska, da karama wajen kira, da babba wajen kira, da karama wajen tsari, da babba wajen tsari, da masu launuka daban-daban, da masu launin fari da baki kadai, da masu talabijin, da masu na’urar daukan hoto, da masu na’urar bidiyo da na daukan sauti, da masu tsarin fasahar Intanet, da masu dauke da fasahar Bluetooth, da masu dauke da fasahar Infra-red, da masu dauke da rediyo, da masu dauke da sauran kayayyakin mu’amala da masu kayatarwa. Wadannan siffofi da suka gabata sun yi tasiri sosai wajen yaduwar wayar salula a duniya, a musamman kasashe masu tasowa. Saboda sun baiwa mai saye ko mu’amala da wayar salula damar yin hakan cikin sauki, da kuma samun abinda yake so a yanayin da ya kamace shi. Iya yawaitan wadannan siffofi masu jawo hankula da sawwake matsaloli, iya yawaitan wayoyin salula a hannun mutane.

Yawaitan Kamfanonin Sadarwa

Daga cikin dalilan da ke saurin yada wayoyin salula cikin al’umma akwai yawaitan kamfanonin sadarwa, ko Telecommunication Operators, a Turancin sadarwa. Idan mai karatu ya lura, lokacin da tsarin sadarwar wayar tarho ta GSM ta shigo kasar nan, shekaru kusan goma da suka gabata, kamfanonin sadarwa guda uku ne kadai. Da kamfanin MTN, da Econet, sai kuma na hukumar Sadarwa ta Kasa (NITEL), watau Mtel. A lokacin nan, ba kowa ke iya rike wayar salula mai dauke da katin SIM ba, saboda tsadar wayoyin da kuma takaituwansu ga daidaikun mutane kadai. Amma daga baya aka samu kamfanoni irin su Globacom, da Starcoms, da Etisalat, da Visafone, da dai sauran kamfanonin sadarwa da muke dasu a halin yanzu. Samuwarsu ya haifar da yawaitan wayoyin salula a cikin al’ummar Nijeriya. Domin kusan kowanne cikinsu kan zo da wayoyin salula na musamman masu dauke da katin SIM dinsa, da wadanda sayarwa suke yi kadai. Da haka sai ka samu mutum daya da wayoyin salula wajen nau’uka uku ko hudu ko biyu. A wasu gidajen zaka samu kusan duk daki akwai wayar salula a ajiye, ko duk falo akwai wayar salula, a sama ne ko a kasa. Duk wannan yayi tasiri wajen yaduwar wayoyin salula a Nijeriya da sauran kasashen duniya.

Zumunci Tsakanin Kayayyakin Sadarwa

Saboda tasirin kayayyaki da hanyoyin sadarwa a duniya, an samu wata gamayya da ta samar da kwakkwarar zumunci a tsakanin wadannan kayayyakin ko hanyoyin sadarwa. Wannan tsari, a ilimin fasahar sadarwa ta zamani, shi ake kira Network Convergence. Shi kanshi wannan tsari na zumunci a tsakanin kayayyakin sadarwa ya haddasa yaduwar wayoyin salula a duniya baki daya. Domin akwai zumunci mai kwari a tsakanin kwamfuta da wayar salula. Akwai zumunci a tsakanin wayar salula da wayar salula ‘yar uwarta. Akwai zumunci tsakanin wayar salula da na’urar kyamara. Akwai zumunci tsakanin wayar salula da na’urorin jin wake na MP3. Akwai zumunci a tsakanin wayar salula da fasahar Intanet da hanyoyin mu’amala da ita. Akwai zumunci mai danko a tsakanin na’urar buga bayanai (Printer) da wayar salula. Akwai zumunci a tsakanin na’urar talabijin ta zamani da wayar salula. Manyan sinadaran da ke hada wannan alaka a tsakanin wadannan kayayyakin sadarwa dai sune: fasahar Infra-red, da fasahar Bluetooth, sai kuma ka’idar sadarwa a tsakanin kwamfutoci, watau Internet Protocols (IP), wadanda ke gine cikin fasahar Wireless Application Protocol (WAP) da ke like da galibin wayoyin salula na zamanin yau. Da wadannan ne duniya ta dada hadewa da rikediwa zuwa abu daya. Daga kasar Sin mutum na iya karban sako yana birnin Arizona da ke Amurka, cikin kasa da dakika daya. Birnin Jidda kana iya kiran dan uwanka da ke birnin Quebec na kasar Kanada, ku zanta. Kana iya aika wa matarka da sakon tes daga birnin Islam Abad na kasar Pakistan, alhalin tana zaune a garin Free Town a kasar Seraliyon, nan da dakiku uku. Kamar yadda zaka iya aikawa da sakon bayanai ko murya, haka kana iya aikawa da sakonnin hotuna da na bidiyo. Wannan tasa hanyoyin yada ilimi suka yawaita, sanadiyyar yawaitar wadannan kayayyakin sadarwa da kuma zumunci mai danko da ke a tsakaninsu.

Bunkasar Bincike kan Hanyoyin Sadarwa

Wannan shine abu na karshe, wanda tasirinsa ne ya haifar da sauran dalilan da suka gabata, wajen yada wayoyin salula a duniya. Wannan kuwa shine tasirin bincike kan sawwake hanyoyin sadarwa da tsarinsu a duniya. misali, binciken malaman sadarwa ne ya gano alakar da ke tsakanin saukin farashi da yawan wayoyin salular da kowane mutum zai iya saya. Bincike ne ya binciko tabbatuwar alaka a tsakanin tsarin saukin mu’amala da kuma dabi’ar duk wani mai so ko sayen wayar salula. Bincike ne ya samo alaka a tsakanin yawaita kamfanonin sadarwa, mai haifar da arahar farashin buga waya, tare da sawwake shigo da sabbin wayoyin salula cikin al’umma a ko ina ne a duniya. Wannan shine dalili na karshe da zamu dakata a kansa, don kauce wa tsawaitawa.

No comments:

Post a Comment