Thursday, January 14, 2010

Sakonninku Daga Jakar Imel

Neman Afuwa

Mun samu wasiku ta hanyar Wasikar Hanyar Sadarwa ta Intanet, watau Imel, masu dimbin yawa. Da dama cikinsu duk na bayar da jawabinsu, musamman wadanda ke bukatar amsoshi na musamman da suka kebanci tambayoyin da aka aiko. Akwai kuma wadanda ke bukatar bincike mai dan zurfi da bazan iya amsa su nan take ba, na jinkirta sai wani lokaci. Ga kadan cikin wadanda aka rubuto masu nasaba da yanayin shafinmu wajen rashin tsawo. Ina kuma sanar da Malam Abbass Ameen da ya taimaka ya aiko da jadawalin da ya taba aiko min watannin baya, mai dauke da kalmomi da yake neman a fassara masa su. A wancan lokacin na shagaltu da aiki ne, kuma wasikar na bukatar daukan lokaci don tantance kalmomin tare da ware musu ma’anonin da suka cancance su a harshen Hausa. Na duba wannan wasika sama ko kasa a cikin Jakar Wasikar Imel dinmu, amma na kasa gani. A gafarce ni a sake aikowa.

Haka ma ina sanar da Malam Aliyu Mukhtar Sa’idu (IT) da ke Kano, cewa sakonnin tes masu dauke da tambayoyin da ya aiko mani cikin watan da ya gabata, sun salwance a lokacin da na bayar da wayar salula ta aka farfado da ita (flashing) sanadiyyar kwayoyin cuta (virus) da suka kama ta. Kamar yadda aka sani ne, da zarar an sumar da waya aka sake farfado da ita, to duk bayanan da ke ciki an rasa su kenan. Don haka dukkan sakonnin da ya aiko, da wasu ma da bazan iya tuna wadanda suka aiko su ba, duk sun salwance. A yi hakuri a sake aiko min su. A halin yanzu ga wadannan sakonni nan.

Gaisuwa daga Jumhoriyar Nijer

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Na hadu da kasidun da kake rubutawa ne a Internet, hakan ya sa ni in bayyana ma gamsuwa na. A gaskiya na fa'idantu da wannan kokari naka. Kuma Allah ya taimakeku. Sai an jima. ---  Isma'il Adam, Jumhoriyar Nijer: samaila_ada@yahoo.com

Malam Ismaila mun gode da wannan wasika taka kuma Allah saka da alheri, ya kuma bar zumunci. Kai ne mutum na uku da ya taba rubuto mana wasika daga wajen Nijeriya. Don haka mun gode. Kuma kamar yadda na sanar da kai kwanakin baya, da fatan zaka ci gaba da ziyartar wanann shafi namu da ke Intanet don samun kasidun da ake fitarwa a duk mako.

Loda Bayanai Cikin Mudawwana

Assalaamu Alaikum, bayan gaisuwa ta addinin Musulunci, Malam ya aiki ya kokarin ilmantar da al'umma? Bayan haka Malam ina da tambayoyi kamar haka: ina kokarin gina mudawwana ce tawa, amma da Blogger. A yanzu ina son in fara tura sakonni cikin mudawwanar ta hanyar amfani da WordPad, to Malam ya zan yi in tura rubuntun cikin mudawwana? Saboda ba na son in bi ta hanyar Blogger wajen tura sakonnin, don ina son in yi amfani da hanyoyin “Web Design” ne, ta amafani da  “vertical table” da “radio button”. Kuma ance (za a iya amfani da) WordPad ko kuma Notepad, to shine na ke son Malam ya gaya min yadda zan yi wajen tura sakonnin. Sai kuma idan ina son in sanya adireshin wani gidan yanar sadarwa a ciki shi ma yaya zan yi? A huta lafiya. --- Aliyu Abdullahi, Kano: malakhum@yahoo.com

Malam Aliyu na samu sakonka, kuma ina neman a min afuwa saboda tsawon lokacin da na dauka ba tare da na aiko maka da jawabin da kake nema ba. Na karanta sakonka kuma na fahimci wasu cikin tambayoyin, kamar yadda zaka gani, ba dukkan wasikar na kalato mana ba. Na yago iya inda na fahimta ne, kuma a kan haka zan baka amsa. Da farko dai kamar yadda ka sani, manhajar gina Mudawwanai na Blogger na dauke ne da dukkan hanyoyin da ake bi wajen zuba bayanai da gyatta su, da kuma canza musu launuka ko launin da ake so, da kuma hanyar tsara alamomi a Mudawwanar a gefen da ya dace da dai sauransu. Yin amfani da masarrafar “Wordpad” ko “Notepad” bai dace ba saboda dalilai biyu: na farko dai shine, Manhajar Blogger bata bayar da damar shigar da bayanai ta amfani da wadannan masarrafai; domin ko ka tsara bayanai a cikinsu ka kuma gyatta su, da zarar ka debo su zuwa Blogger, tsarin da kayi zai watse gaba daya. Na biyu kuma shine, yin amfani dasu bata lokaci ne. Sai idan kana nufin zaka killace wata kwamfuta ce mai zaman kanta, a gidanka ko ofishinka, ya zama kayi amfani da Blogger ne kadai don samun adireshi, to kana iya tsara shafuka ta hanyar amfani da wadannan masarrafai, ka loda su cikin kwamfutar, ta yadda duk wanda ya shiga shafin, zai ci karo da bayanan da suke dauke dasu. Kamar dai gidan yanar sadarwa kenan ka bude. Amma in har a Blogger zaka ajiye shafinka, to ban ga dalilin da zai sa ka yi amfani dasu ba. Ina dada nanata mana, amfaninsu wajen gina gidan yanar sadarwa ne kadai, ko gyara bayanan da ke gidan yanar sadarwa da sake loda su. Amma basu da alaka da abinda ya shafi amfani dasu wajen shigar da bayanai a Blogger. Amma idan wanda ya sanar da kai na da wata sabuwar hanya ko fasahar yin hakan a aikace, to ka iya sanar damu don mu karu.

Kawai idan kana da bayanan da kake son dorawa ko shigarwa a cikin Mudawwanar, ka kwafe su (copy), ka zuba (paste) a cikin allon Mudawwanar. A inda ka zuba bayanan, kana iya gyatta su. Idan so kake ka sanya musu launi, a nan zaka zaba. Idan so kake ka mayar dasu ta bangaren hagu, akwai inda zaka yi. Idan a tsakiyar shafin kake son ajiye su, duk akwai inda zaka zaba. Maganar amfani da masarrafar “Notepad” ko “Wordpad” ma duk bai taso ba, sam ko kadan. Duk abinda ka zuba cikin mudawwana, a nan zaka gyatta musu zama ta kowane yanayi ko hali kake so.

A karshe, masarrafan “Wordpad” da “Notepad” ana amfani dasu ne kawai idan kana gina gidan yanar sadarwa na musamman, kamar yadda bayani ya gabata. A ciki zaka shigar da bayanan, ka yi amfani da ka’idojin gyatta su, kamar yanayin launi, ko bigiren da kake son gyatta su da dai sauran hanyoyi. Hakan kuma na samuwa ne ta amfani da fasahar Hypertext Markup Language (HTML tags), wadda muka asha ambato a lokutan baya. Amma a manhajar Blogger duk baka bukatar haka. Domin manhajar na dauke ne da wannan fasaha ta HTML tags; zuba bayananka kawai zaka yi, manhajar za ta gyatta maka su. Sannan idan kana son sanya adireshin wasu gidajen yanar sadarwa a shafin Mudawwanarka, duk babu wahala. Idan ka je “Settings”, sai ka karasa “Layout”, a can zaka kirkiri inda zaka sanya adireshin, tare da lakabin gidan yanar, da adireshinsa gaba daya. Da fatan ka gamsu.

Neman Kasidun Baya

Salam Baban Sadik ina maka fatan alkairi a cikin wannan dare. Nine El-bashir daga kano, kuma ni ma'abocin wannan makaranta ce tun lokacin kafa ta kusan shekaru biyu kenan, ban taba turo maka sako bane. Ina so dan Allah ka turo min bayanin da kayi a kan “‘Yan Dandatsa”, saboda ina so in yi amfani da bayanan da kayi ne don fitar da wasu bayanai. Wassalam, ka huta lafiya. – El-basheer, Kano: ashareef@yuurok.com

Malam El-Bashir mun gode da wannan wasika taka, kuma Allah saka da alheri. Kuma na tura maka dukkan bayanai ko kasidun da muka rubuta ko fitar kan “’Yan Dandatsa” a wannan shafi. Da fatan ka same su. Idan akwai abinda baka fahimta ba, ko kana iya neman karin bayani kan wani bangare na musamman da bamu tabo a cikin kasidun ba, kana iya sanar dani sai in tanada maka. Saboda gaba, duk kasidun da kake nema idan kaje Mudawwanar wannan shafi da ke http://fasahar-intanet.blogspot.com ko http://kimiyyah.blogspot.com, zaka same su in Allah Ya yarda. Allah sa mu dace, kuma mun gode.

Sauraron Labarun BBC ta Wayar Salula

Assalamu alaikum, da fatan Baban Sadik ya wuni lafiya. Bayan haka, gidan rediyon Sashen Hausa na BBC suna ta sanarwa cewa za'a iya sauraronsu ta hanyar Intanet ta amfani da wayar hannu, amma na shiga na rasa yadda zan saurare su. Yaya abin yake ne Malam? Daga dalibinka Danlami Muhammad Doya, Bauchi: danlamindoya@gmail.com

Malam Danlami sannu da kokari kuma da fatan kana cikin koshin lafiya. Watau abinda ke faruwa shine, sauraron labaru ta hanyar wayar salula ya danganci tsari da kuma nau’in wayar salular, ba kowace iri ake iya yin hakan da ita ba. Da farko dai kamar yadda muka sani, dole ne ya zama wayar na da ka’idar mu’amala da fasahar Intanet, watau “WAP”. Na biyu kuma ya zama akwai kudi a cikin katin wayarka, ba wai da holoko ake yin lilo ba. Domin da zarar ka shiga Intanet ta wayar, to nan take kamfanin wayarka zai fara zaftare kudin da ke ciki; iya gwargwadon yawan kalmomi ko haruffa ko kuma bayanan da wayar ke nuna maka. Kuma kasancewar tsarin “sauti” ko “hoto mai motsi” ko “daskararre” da wayar zata budo maka daga Intanet yafi cin kudi fiye da tsantsar bayanai na labaru da zaka karanta, ta sa dole ka zuba kudi mai yawa a wayar kafin ka fara sauraro. Abu na uku kuma shine ya zama wayar tana da masarrafan da ke taimakawa wajen budo maka jakunkunan bayanan sauti da ke dauke da labarun da kake son sauraro.

Ba kowace wayar salula mai iya shiga Intanet ne ke da ire-iren wadannan masarrafa na kwamfuta ba. Shahararrun cikinsu dai sune: “Real Player” da kuma “Windows Media Player”. Idan wayar salularka bata da wadannan masarrafai, to baza ka iya sauraron labaru ba, ko da kuwa ka shiga gidan yanar sadarwar BBC. Abu na karshe kuma shine ya zama kayi rajistar layin wayarka da kamfanin wayarka, don baka damar mu’amala da fasahar Intanet a wayar. Wasu kamfanonin wayar (irinsu “Etisalat’ da “MTN” – a layukansu masu 0803) nan take suke maka rajista da zarar ka sanya Katin SIM dinka a wayar da ke da ka’idar mu’amala da Intanet. Zaka ji nan take an turo maka sakon tes don sanar da kai hakan. Amma wasu kamfanonin wayar kuma sai ka aika musu da sakon tes na bukatar yin hakan sannan zasu turo maka.

Idan kuma aka dace kana da dukkan wadannan, to sai ka zarce gidan yanar a www.bbc.co.uk/hausa. Da zarar ka shigo, sai ka zarce bangaren dama, inda aka rubuta “Saurari Shirye-shiryenmu”, a kasa zaka ga nau’ukan shirye-shiryen; da na safe, da na hantsi, da na rana da kuma na yamma. Sai ka matsa wanda kake son sauraro. Shafi zai budo, dauke da wadannan masarrafan jin sauti da bayaninsu ya gabata, watau “Real Player” da kuma “Windows Media Player”. Idan ka zabi wanda kake son amfani dashi wajen sauraro ko kuma wanda wayarka ke dauke dashi, sai ka gangara kasa daga hannun dama inda aka rubuta “Ok”, ka matsa. Da zarar ka matsa sai kawai ka kishingida ka fara sauraron labaru radau-radau; kai kace a tafin hannunka gidan rediyon BBC da ke Landan yake. Kada a mance Malam Danlami, a zuba kudi da yawa cikin wayar, idan kuwa ba haka ba, kana cikin sauraron zaka ji shiru. Ba sadarwar wayar salula bace balle na’urar tace maka “kudinka ya kare”. Sai dai kawai kaji shiru! Da fatan ka gamsu.

No comments:

Post a Comment