Friday, December 9, 2011

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu Ta tes da Imel (6)


Wannan shi ne kashin karshe na Amsoshin Tambayoyi a wannan marhala.  Ina mika gaisuwa da godiyata ga dukkan masu karatu, musamman masu aiko da addu'o'i kan gamsuwarsu, da masu aiko tsokaci ko gyara kan kurakuran da ake tafkawa.  Allah saka da alheri, amin.  
...................................................
Salam, a bisa bayanin da kayi kan ATM da kuma yadda yake aiki  da shi, ina so ka yi mini bayanin yadda zan sayi wani abu ta intanet kuma na biya kudin ta hanyar amfani da katin ATM di na.  Ina amfani da katin masta ne (Mastercard).  Ina maka fatan alheri.   Na gode, Bashiru Musa, Zaria.

Malam Bashiru ban san bankin da kake amfani da katinsa ba, ina kyautata zaton GTBank ne.  In haka ne, lallai za ka iya cinikayya da katin ta hanyar Intanet.  Sai dai ya danganci shafin da za ka yi cinikayyan a cikinsa.  Domin wasu kamfanonin sayar da kayayyaki a Intanet ba su yarda da 'yan Najeriya wajen cinikayya a Intanet. Wannan ke sa idan kaje shafin don aiwatar da kasuwanci, akwai inda za ka zabi kasarka, idan ka duba za ka ga babu Najeriya a ciki.  Wannan kuwa ba sai na gaya maka dalilin ba.  Amma dai a takaice za ka iya.  Na farko, ka tabbata akwai isassun kudi a cikin taskar ajiyarka ta banki.  Na biyu kuma, za ka je shafin da kake son sayan hajar ne, ka zabi hajar da kake bukata (za ka ga an rubuta "Add to cart" a kasar hajar, ko a gefen hajar, ko ka ga an rubuta "buy" ko wata kalma makamanciyarta).  Idan ka matsa za a budo maka bayanai kan hajar.  Abu na uku, za a bukaci ka yi rajista a shafin, inda za ka shigar da bayanan da suka dangance ka, da adireshin gidanka, da jahar da kake, da lambar katinka na ATM, da adireshin da kake son a kawo maka hajar (gida ko ofishinka misali), da nau'in katin da kake amfani da shi (Mastercard, ko Visacard), da tsawon lokacin da kake son hajar ta riske ka, da kuma kamfanin aika wasiku (Courier Service Provider – irin su Fedex, ko DHL dsr) da kake son ayi amfani da shi wajen aiko maka.  Daga nan za a zarce da kai shafin da zai kididdige maka dukkan kudaden da za ka biya; da kudin haja, da kudin aikowa. Daga nan sai ka tura.  Za a turo maka sako ta adireshin Imel dinka ana sanar da kai cewa an tura sakonka, kuma rana kaza zai iso.  Idan masarrafar kwamfuta ce, ko littafin da ke yanayin masarrafar kwamfuta (eBook), wadannan ba ka bukatar kamfanin aikawa, nan take za a  tura maka rariyar da za ka bi don saukar da ita kai tsaye.  Amma kafin nan, sai kamfanin kati sun daidaita da bankin da kake ajiya da su, a cire musu nasu kason, sannan banki ya turo maka sako don sanar da kai kan haka.  Wadannan, a takaice, su ne 'yan bayanan da suka sawwaka.  Da fatan ka gamsu.

Assalamu Alaikum Baban Sadiq, da fatan kana lafiya. Tambayata itace. Ina neman karin bayani game da yadda ake amfani da Blog, kuma ya ake yin register da shi kuma ya ake zuba labaru a cikin shafin mutum. Na gode. Daga Ismail Bello (IT Student Katsina University), Katsina.

Malam Ismail barka da warhaka.  Idan kana bukatar bude shafin Mudawwana na Blogspot, sai ka je zauren gidan yanar da ke www.blogspot.com/start ka matsa inda aka rubuta "Sign Up" don mallakar akwatin Imel na Gmail, sannan ka matsa inda aka rubuta "Create a Blog."  Bayanan da za a bukata ba su da yawa, kuma ba su da wahalar bayarwa.  Sunan shafin ne, da adireshin shafin, yadda kake so ya kasance, da kuma tsare-tsaren da kake son shafin ya sifatu da su.  Idan ka gama, za a kai ka inda za ka iya kirkirar bayanai don lodawa a shafin.  A saman shafin daga hannun dama akwai inda aka rubuta "Create a New Post," da zarar ka matsa zai zarce da kai shafin da za ka rubuta bayanan da kake son shigarwa, kana gamawa akwai inda aka rubuta "Publish" daga saman shafin da kake a hannun dama shi ma, sai ka matsa don lodawa a shafinka.  Lamarin ba wahala.  Idan ka shiga, akwai abubuwa da yawa da za ka iya yinsu da kanka, ba sai ka tambaye ni ba.  Abin sauki ne dashi, kamar cire wando ta ka!  Da fatan malam Ismail ya gamsu.

Salamu alaikum, Baban Sadiq muna godiya da karuwa da muke yi da kai a shafukanka da ke Intanet,  da kuma gidajen radiyo. Allah kara taimako da ilmi mai amfani amin. Na ga ka yi bayani kan na'urar ATM, amma na fahimci ka fi ba da karfi wajen aikinta na fitar da kudi, alhali ka ce akwai wasu ayyukan da take yi kamar na biyan kudin wuta, ko na katin waya da dai sauransu.  Ina fata in hali ya yiwu za a yi mana bayani a kansu nan gaba. Na gode. Lawal B Yusuf 08020636825

Malam Lawal wannan bayani naka haka yake.  Abin da yasa na takaita bayani kan wadannan abubuwa kadai shi ne don su ne suka fi shahara, kuma su ne asalin dalilan da suka sa aka kera wannan na'ura.  Duk sauran abubuwa daga baya ne suka samu.  Dalili na biyu kuma shi ne, duk da cewa biyan kudin wuta da sayan katin waya (watau "Quick Teller" kenan) ba wasu abubuwa bane masu wahala wajen aiwatarwa, sai dai ga mutumin da bai saba yinsu ba, akwai rikitarwa, kuma karamin kuskure na iya sa mutum ya kidime.  Idan ya kidime a muhalli irin wannan, ba kowane mai zuwa wurin bane zai iya agaza masa.  Domin cikin kashi dari na masu amfani da wannan na'ura, za ka samu kashi goma ne ko kasa da haka suke aiwatar da ayyuka irin wadannan. A takaice dai abu ne da ke bukatar kwarewa da kuru.  Wannan yasa na takaita bayani kan abin da yake mafi sauki, wanda kuma ake samun agaji a kansa cikin sauki. Da fatan an gamsu.

Salam Baban Sadik, gidan yanar Yahoo! ne yanzu ba na iya shiga.  Ban san dalili ba.  Sai a ce mini:  "Page not found". Shin, su ne da matsala? Nagode daga Sharif
Liman Giwa: 08090547770

Malam Sharif duk sadda ka samu sako irin wannan wajen mu'amala da wani shafi a Intanet, dayan biyu ne: ko dai baka shigar da adireshin gidan yanar sadarwar daidai ba, ko kuma akwai matsalar sadarwar Intanet tsakanin wayar salularka ko kwamfutarka, da kamfanin da ke ba ka sabis na Intanet.  Abu na farko sai ka duba adireshin ka gani.  Idan daidai ka shigar, sai kuma ka duba tsarin sadarwa ta Intanet da ke wayar, watakila yanayin sadarwa ya yanke, watau "Network" kenan, ko kuma a lokacin da kake kokarin shiga shafin, wani kira ya shigo, ko wani tes ya shigo.  Idan kana mu'amala da shafin Intanet a waya sai aka kira ka, to nan take yanayin sadarwar intanet din zai yanke, sai ka gama zancenka sannan ya dawo.  Da fatan ka gamsu.

Salamu alaikum Baban Sadik, Tambayata ita ce;  dangane da na'urar hangen nesa, watau Telescope; ya yake ne? Kuma iri nawa ne? Har yanzu ma ana aiki da shi sosai kuwa?. Daga Aliyu Mukhtar Saidu (I.T) Kano, aliitpro2020@yahoo.com 08034332200 / 08099109200

Malam Aliyu barka da warhaka.  Lallai har yanzu akwai wannan na'ura ta hangen nesa da ake kira "Telescope" a harshen Turanci.  Wannan na'ura ana amfani da ita ne wajen hango abubuwan da ke cikin sama, wadanda suka sha karfin idon dan adam, don ganin hakikaninsu, da girmansu, da kuma yadda suke.  Wannan na'ura ta hangen nesa dai an fara kirkirarta ne a kasar Nedalands da ke nahiyar Turai, cikin karni na 17.  Shekara guda bayan kirkirar wannan na'ura ne shahararren masanin kimiyyar nan mai suna Galileo ya fara amfani da ita wajen gano wasu daga cikin duniyoyin da ke makwabtaka da wannan duniyar tamu.  A haka ya gano wasu taurari da ke shawagi a gewaye da wadannan sababbin duniyoyi na Jofita da Benus da ya gano.  Wannan bincike da Galileo yayi ne ya haska wa duniya fa'idar da ke tattare da na'urar hangen nesa a wancan zamani.  Wannan ne ma yasa har wasu ke ganin cewa ko shi ne ya fara kirkirar na'urar.  Ba shi bane.  Wannan na'ura ta hangen nesa dai tana amfani ne da haske da ke darsanuwa a jikin gilashin da ke cikin na'urar, don jawo shi kusa, da bayyana hakikaninsa.  Akwai nau'in da ke janyo hoton abu daga nesa ta amfani da haske, sai ta cillo shi cikin na'urar, inda gilashin da ke ciki daga tsakiya yake cafke hasken, sannan ya cilla shi zuwa kasa, daidai inda idon mai nazari ke kallo.  Wannan nau'i shi ake kira "Reflective Telescope."  Sai kuma nau'i na biyu da ke amfani da gilashi mai rage kaifin haske (watau Lens), don jawo hasken da ke dauke da hoton abin da ta hasko, sai wannan gilashi na farko ya cilla hasken zuwa wani dan karamin gilashin rage kaifin haske da ke gab da idon mai nazari, don ba shi damar ganin hoton abin da ke kunshe cikin hasken ba tare da wata matsala ba. Wannan nau'i shi ake kira "Rafractive Telescope."  Dangane da girma kuma, sun kasu kashi kashi. Akwai kanana wadanda ake iya rikewa da hannu a hango abin da ake son hangowa.  Akwai wadanda ake girkewa a kan sanda, a cilla su zuwa inda ake son hangowa. Akwai kuma manya wadanda ke saman farantin tauraron dan adam.  Mafi girma cikin nau'ukan na'urar hangen nesa shi ne wanda masana ke amfani da shi wajen hango sirrin da ke sararin samaniyar halittar duniya baki daya, ba wannan duniyar da muke ciki ba kadai.  Wanann nau'i shi ake kira "The Hubble Space Telescope."  Dangane da tambayarka ta karshe, lallai har yanzu ana amfani da wannan na'ura ta hangen nesa, sai ma abin da yayi gaba.  Da fatan malam Aliyu ya gamsu.

Assalamu alaikum. Baban Sadik, Barka da aiki. Da fatar kana lafiya. Baban Sadak  don Allah a taimaka min da bayani a kan wace hanya ce bankuna da kamfanoni ke bi wajen tura wa Jama'a sako ta layukansu (Sim), sannan ko kamfanin Yahoo yana da irin wannan hanyar? Sannan shi ma dandalin sada zumunta na Facebook yana da irin wannan hanyar? Sannan wai idan ma akwai wannan, to me yasa jama'a ba sa amfani da wannan hanyar? Na gode. Daga:- Hassan Muh'd Binanci.  A Jihar Sakkwato/ h.muhammad30@yahoo.com

Wannan tsarin aikawa da sakonni dai shi ake kira "Bulk Messaging."  Idan na sakonnin waya ne, akan kira shi "Bulk SMS", idan kuma na Imel ne "Bulk Messaging" ma ya isa.  Tsari ne da ake amfani da shi wajen aikawa da sakonni masu dimbin yawa, iri daya, zuwa ga jama'a masu yawa, cikin lokaci daya.  Wannan tsari dai yana da masarrafa ce ta musamman, duk da cewa za a iya gudanar da ita ta hanyar wayar salula ma, ma'ana kana iya aika wa dukkan wadanda kake da lambarsu sako iri daya kai tsaye, a lokaci guda.  To amma idan kamar mutane miliyan daya ne fa?  Ya za ka yi?  Kamfanonin wayar salula suna da wannan tsari a cikin na'urorinsu.  Idan ka je za su gaya maka nawa za ka biya, sai ka basu nassin sakon da kake son a aika, kamar na gayyatar biki misali ko wani taro, duk sai ka bayar.  Nan take za su tura wa kowa da kowa.  Haka ma idan ta Imel ne, akwai masarrafar da ake amfani da ita don aikawa.  Kamfanin Yahoo! Ba su rasa wannan tsari, don kamfanin sadarwa ne, kuma suna da kwararru kan haka.  A tsarin Facebook ma ba za a rasa ba, sai dai kuma wannan ya kebanci masu kamfanin ne ko ma'aikatansu.  Suna iya aika wa kowa da kowa sako nan take, amma masu amfani da shafuka damarsu wajen yin hakan takaitacciya ce. Za su iya aika wa dukkan abokanansu sako iri daya a lokaci daya, amma ba dukkan mai amfani da dandalin Facebook ba.  Da fatan ka gamsu.

Salamu alaikum Baban Sadik, don Allah ina da tambaya.  Na aje memory card kimanin kwanaki 40, kuma akwai abubuwa da yawa saboda babba ne.  Wallahi saboda shi na sayi waya mai tsada, amma na yi ta fama ya ki ya nuna komai.  To yanzu yaya zan yi? Ina son abubuwan da ke ciki. Salisu Bare, Dikko, Suleja Naija 08065275983
 
Babbar magana, wai dan sanda ya gawar soja!  Malam Salisu ban san me ya samu wannan kati naka ba mai matukar muhimmanci ba.  Zan so in san irin matsalar da wayar ke nunawa a sadda ka tsofa mata katin.  Shin, tana cewa a shigar da "Password" ne?  In haka ne, to watakila sadda kake amfani da katin a baya ka sanya masa makullan tsaro ne, sai ka lalubo so don shigarwa.  Idan kuma ta ki karba ne gaba daya, to watakila akwai matsala a baya, tun sadda kake shigar mata da bayanan.  Domin idan kana shigar mata da bayanai, sai ka cire tun bayanan basu gama shiga ba, to ko ka bukaci amfani da ita ba za ka samu komai ba, domin dukkan bayanan da ke ciki za su gurbace. Ko kuma ruwa ya taba, ko tsananin sanyi, ko kuma kura sun cike ta, ko kuma kwayar cutar wayar salula, watau "Virus" ta shige ta.  Duk wadannan na iya zama musabbabai.  A takaice dai, in da hali ka kai wa masu gyaran wayar salula don su duba maka.  Idan matsala ce da za su iya gyarawa ba tare da an yi hasarar bayanan da ke ciki ba, za su taimaka.  Idan kuma bayanan da ke ciki sun gurbace (watau "Corrupted"), to a nan fa sai dai a yi hakuri.  Haka rayuwa ta gada.  Allah sa a dace, amin.

Friday, November 25, 2011

Amsoshin Wasikun Masu Karatu ta Tes da Imel (1 - 5)


Matashiya

Kamar yadda na sanar a makon da ya gabata, a yau ga mu dauke da amsoshin sakonninku da kuka aiko ta tes, da wadanda kuka aiko ta jakar Imel dinmu.  Kamar yadda na saba, wasu daga cikin sakonnin na amsa su ta hanyar tes ko ta Imel inda aka aiko su.  Ire-iren wadannan sakonni ban kawo su tunda na amsa su tuni.  Bayan haka, akwai wadanda ke bugo waya har yanzu – duk da cewa na roki a daina bugo waya.  A haka dai nakan saurare su, har in ba da amsa iya gwargwadon hali.  Wasu kuma in ce su yi hakuri sai na rubuto musu. Akwai wadanda kuma ke cewa kada in buga sakonsu a shafin jarida, su ma nakan yi iya kokari wajen ganin ban buga ba, ta hanyar ba su jawabin tambayarsu.  Bayan haka, har yanzu akwai masu damu na da filashin.  Ire-iren wadannan mutane ina rokonsu da su ji tsoron Allah su daina.  Ba na ganinsu, amma Allah na ganinsu kuma ya sansu, ya kuma san abin da suke yi, zai kuma yi musu sakamakon da ya dace da ayyukansu, ba ruwana.

Har wa yau, akwai wanda ya rubuto yana neman fassarar wasu kalmomi a gaggauce, saboda an bashi aikin gida ne (watau Assignment) a makaranta, kuma lokacin da ya aiko ya nuna yana son amsar a ranar don idan gari ya waye zai gabatar a makaranta.  A gaskiya ban samu damar bashi amsa ba, saboda sakonsa ya same ni cikin yanayin zirga-zirga ne.  Ire-iren wadannan bukatu yana da kyau a rika gabatar da su cikin lokaci, don nima in samu damar bincike – idan sakon na bukatar bincike – kafin in san amsar da zan bayar.  Don haka ina neman afuwa daga wurin wanda ya turo wancan bukata da ban samu damar amsawa ba. A gafarce ni, sai wani jikon idan Allah ya sake hada mu.

A karshe kuma akwai wadanda suka rubuto tsokaci mai tsawo, ban san inda zan sa ba – shin tambaya ce, ko nasiha suke mini, ko gargadi, wallaahu a'alamu -  kan batun yadda ruwa ke samuwa.  Da cewa su sunyi imani da abin da Allah ya fada a Kur'ani cewa ruwa daga sama yake, ba tare da wani dogon bayani ba. Da dai sauran bayanai makamantan wannan.  To, ni dai iya abin da na sani kenan na rubuta.  Kuma ba da ka nayi rubutun ba, sai da na gudanar da bincike a kimiyyance, sannan na gudanar da bincike a addinance, ta hanyar nassoshin Kur'ani da na duba, da sharhin malaman tafsiri, da hadisai, da dai sauran hanyoyi.  Na kuma sanar da masu karatu dukkan ayoyin da na ciro, da hujjojin da suke kokarin tabbatarwa.  To amma akwai alamar wasu basu gamsu ba, ko basu fahimci inda na dosa ba, ko kuma ra'ayinsu ya sha bamban da nawa kan wancan lamari, ko kuma basu samu karanta dukkan kasidun ba.  Abin da na so su yi shi ne, su nuna mini inda na yi kuskure, da hujjojinsu, da kuma abin da yake shi ne daidai, don nan gaba in gyara.  To amma hakan bai samu ba.  Wannan nake sauraro.  In kuwa bai samu ba, to duk wani sakon da aka aiko mai alaka da haka, wanda kuma ba tambaya bace ta neman sani, zan ajiye ta.  Allah mana jagora.

A yanzu dai ga amsoshin tambayoyinku nan.  Duk abin da ba a fahimta ba, don Allah, a nemi karin bayani. In Allah ya so zan fadada bayani iya gwargwadon iko.  Allah shi ne masani, mai cikakken sani da fahimta, wacce babu nakasa a tare da ita.  Allah sa mu dace:

…………………………………………………………

Assalamu Alaikum, Baban Sadik, shawara ta gareka ita ce, ina ganin cewar kalmar 'tes' da 'Imel' ba kalmomin Hausa bane. Ya kamata kayi amfani da ainihin fasarar da za'a fahimci manufar sakonnin. Huta lafiya. Musa Ningi, No.22 Prison Road, Ningi, Jihar Bauchi.

Malam Musa muna godiya da wannan tsokaci da kayi, Allah saka da alheri.  Watau abin da ya sa nake amfani da kalmar "tes" da "Imel" shi ne, don su ne kalmomin da mutane suka fi fahimta, sabanin yadda kake zato.  Duk bahaushen da kace masa "tes" ko "Imel" a wannan zamani, zai fi saurin fahimta nesa ba kusa ba, da kace masa "gejeren sakon waya" ko "wasikar hanyar sadarwa ta Intanet."  Dalili na biyu kuma shi ne, wadannan kalmomi sun fi sauki ta wajen gajarta, bayan saukin fahimta.  Sannan kuma duk da cewa kalmomin Turanci ne, ba wani laifi, domin aron kalma a ilmance ba laifi bane.  A takaice ma dai, duk harshen da ba ya aron kalmomi daga wasu harsuna, to ba zai taba ci gaba ba. Hatta kai kanka sai da kayi amfani da wannan tsari sannan na fahimci sakonka.  Domin ka yi amfani da "kalma" da kuma "fasara", wadanda kuma duk ba Hausa bane a asalinsu.  Kalmomin larabci ne.  A tsarin aron kalma kuwa ba a bambancewa tsakanin wani harshe da wani.  Aron kalma dai aron kalma ne; daga harshen Larabci ne ko Turanci.  Don haka, dangane da yadda malamai suka tabbatar, ba laifi bane don na yi amfani da wadannan kalmomi. Na kuma tabbata masu karatu na fahimta.  Da ba su fahimta da tuni an dame ni da neman karin bayani.  Tunda na bude wannan shafi shekaru biyar da suka wuce, kai ne mutum na farko da ka yi inkarin wannan tsari, duk da cewa kaima ka fahimci abin da nake nufi.  Da fatan dai ka gamsu da wannan jawabi nawa.

Assalamu alaikum Baban Sadiq, Allah ya kara maka basira amin.  Ina son ka yi mini cikakken bayani ne a kan na'uran nan ta "iPad 2"; yaya tsarin sadarwarta take?  Daga Hambali Azare: 08036966225.

Malam Hambali, iPad 2 dai wata na'urar sadarwa ce da kamfanin Apple Inc ya fara kerawa shekaru kusan uku da suka wuce.  Akwai "iPad Wi-Fi", da "iPad 3G", da kuma "iPad 2 Wi-Fi."  Wannan na'urar sadarwa dai ana amfani da ita ne wajen taskance bayanai rubutattu – musamman littattafai -  da bidiyo, da kuma bayanan sauti.  Haka kuma, akwai masarrafai da dama da ke sawwake mu'amala da wadannan bayanai.  Akwai tsarin sadarwa mai inganci, wanda ke sawwake mu'amala da Fasahar Intanet, watau "Wireless Frequency."  Fasahar iPad na cikin sababbin kirkirarun kayayyakin fasahar sadarwa masu inganci da tsada da tasiri a duniyar yau.  Sai dai ba wayar salula bace, don ba ta da inda aka sanya katin SIM.  An yi ta ne don mu'amala da bayanai da bidiyo da bayanan sauti da kuma littattafan da suke a tsarin na'urar sadarwar zamani.  Idan ka saya, ba za ka iya mu'amala da fasahar Intanet ba sai ka sa mata makalutun sadarwa.  Kana iya zuwa kamfanin waya na MTN, ko GLO, ko Etisalat, don su jona ka da tsarin sadarwarsu.  Idan suka jona ka, za ka rika biyan kudin layi a duk wata ko yadda tsarinsu ya kama.  Wannan na'urar sadarwa dai tana da kafar da ake shigar da katin SIM, sannan tana amfani da tsarin sadarwar zamani na GSM.  Mafi karancinta a mizani, watau iPad 2 (16GB), ta kai naira dubu dari da ashirin a nairan Najeriya.  Da fatan ka gamsu.

Me yasa wayoyi kirar CDMA suke daukar zafi kuma cajin batirinsu yake saurin karewa a wurin da babu tsarin sadarwar na katin SIM din da ke kansu? Abubakar Wada Kadi.

Alal hakika ban da masaniya kan cewa wannan matsala ta takaita ne kadai ga wayoyin salula masu amfani da tsarin sadarwa ta CDMA.  Abin da na sani shi ne wayoyin salula kan yi zafi, kuma daga cikin dalilan da ke haddasa musu wannan zafi akwai matsalar batir; ko dai saboda jabun batir, ko kuma batirin da ke cikinsu ya samu matsatsi daga mummunar yanayin zafin rana ko muhallin da wayar ke ajiye.  Cikin shekarar 2003 da 2004 an samu rahotannin wayoyin da suka yi ta fashewa da wuta sanadiyyar zafi da suka yi a kasar Amurka da sauran kasashen Turai.  An kuma danganta dukkan wadannan matsaloli ne ga jabun batira ko kuma zafin yanayi da muhalli.  Daga karshe ma dai an gano cewa ko da ingantattun batira ne suna iya fashewa idan akwai yanayin da suke ciki ya dumama.  Daga cikin dalilan har wa yau daukan tsawon lokaci ana amfani da waya ko wata masarrafa da ke cikinta.  Wannan shi ma yakan janyo zafi ga wayar salula.  Amma zafin da waya ke yi sanadiyyar rashin yanayin sadarwa a inda waya take, babu wani alaka a tsakaninsu.  Ta yiwu dai batirin da ke wayar ya lalace, ko kuma jabu ne, ba ingantacce ba. A takaice dai, jabun batira sun fi haddasa zafi ga wayar salula fiye da kowace irin matsala.  Don haka ne ma kamfanonin waya a yanzu suka dauki matakin sanya wasu hanyoyin kariya a cikin batiran masu nuna tantance ingantaccen batir da jabunsa. Kuma hakan bai takaitu ga wayoyin salula masu amfani da tsarin sadarwa nau'in CDMA ba.  Wannan shi ne dan abin da na sani.  Da fatan an gamsu.

Baban Sadiq da fatan an tashi lafiya, tambayata ita ce, na bude shafin Facebook, ya yi, amma da na sake budewa jiya sai aka ce mini "Pls be patient while testing the connection for the first time."  Idan ya dan jima, can sai ya ce: "Connection failed.  Check Your internet setting."  Ina neman karin bayani.  A. Sadiq

Abin da wannan sako ke nufi shi ne, akwai matsala da tsarin sadarwar Intanet da ke wayar.  Don haka sai a duba a gani.  Idan akwai "Internet Settings" sama da guda daya ne a wayar, sai a zabi guda daya a mayar da shi "Default."  Idan kuma babu ne gaba daya, sai a aika wa kamfanin waya sako don su turo.  Allah sa a dace.

Assalamu alaikum, da fatan kana lafiya? Dan Allah meye amfanin WLAN Service? Kuma yaya zan yi amfani da shi? Na ga kasidarka game da IPv4 da IPv6, zan iya canzawa daga IPv4 zuwa IPv6?  Dan Allah meye bambamcin tura sako ta imel da tes? Kuma me yasa idan na tura sako ta imel ba ya tafiya? Waya ta {C3 Nokia} ce ko akwai wani abin da ya kamata na yi ne wanda ban yi ba? Wasalam nine Ibrahim Muhammad, Toro, Bauchi; 08065750790

Amfanin "Wireless LAN Service" shi ne aiwatar da sadarwar Intanet ta hanyar yanayin sadarwar wayar iska.  Galibin wayoyin salular zamani suna amfani da wannan tsari ne.  Amma ba za ka iya amfani da shi ba sai a wurin da ake da tsari irin wannan. Idan ka kunna shi, wayar za ta sanar da kai cewa "Akwai yanayin sadarwar wayar iska a nan."  Bayan haka, za ka iya amfani da wannan tsari don shiga Intanet iya gwargwadon yadda tsarin yake.  Akwai tsarin WLAN da ke kulle, watau "Secured WLAN" kenan.  Irin wannan tsari ba ka iya mu'amala da shi sai an tsara maka, ta hanyar shigar da kalmomin sirrin da aka tsare tsarin da su.  Akwai kuma budadden tsarin sadarwar wayar iska, watau "Unsecured WLAN."  Shi wannan da zarar ka jona wayarka da shi kawai shikenan, sai ka ta kwasan garabasa kyauta.  Tsarin IPv4 dai shi ne wanda ake amfani da shi har yanzu.  Ba a riga aka yi hijira zuwa IPv6 ba.  Idan lokacin yayi, ba sai ka yi hijira da kanka ba, wayar da kake amfani da ita za ta iya yin haka nan take.  Domin galibin wayoyin salula da kayayyakin sadarwa na zamani a yanzu suna zuwa ne da dukkan tsare-tsaren guda biyu.  Amsar tambayarka ta gaba kuma ita ce, akwai bambanci tsakanin Imel da sakonnin Tes.  Imel dai hanyar aikawa da sakonni ne ta Intanet, wacce ke da tsari da kintsi da hanyarta na musamman, da kuma ka'idojin sadarwa masu taimakawa don yin hakan; a wayar salula ne ko a kwamfuta.  Amma tsarin Tes kuwa hanyar aikawa da sakonni ne ta amfani da yanayin sadarwar kamfanin wayar tarho, ta wayar iska.  Tsarin Imel a wayar salula da kwamfuta duk yana bukatar sai an tsara shi, watau "Configuring" kenan, a turancin kimiyyar sadarwa. Na kuma tabbata rashin tsarin ne ya sa idan ka yi kokarin aikawa da sakonnin Imel sai ya kasa tafiya.  Ka duba kundin da wayar ta zo dashi, za ka ga yadda ake saitawa.  Amma tsarin Tes a wayar salula ba ya bukatar wani saiti; da zarar ka sayi waya, ka sa mata katin SIM, nan take kana iya rubuta sakonnin tes ka aika.  Domin dukkan tsare-tsarenta na cikin katin SIM, wanda ke aiwatar da sadarwa ta kai tsaye da yanayin sadarwar kamfanin waya.  Da fatan an gamsu.

Salam, Baban Sadik barka dai.  Na ga wata waya nau'in BlackBerry 8.0 kirar china, ko ya take da wacce kake bamu labarinta?  Daga S.S Dala

Akwai bambanci a tsakaninsu sosai kuwa.  Wayoyin salula nau'in Blackberry da ke zuwa daga kasar China sun kasu kashi biyu ne.  Akwai ingantattun wayoyin Blackberry da ake gwanjonsu, wadanda wasu suka gama amfani da su.  Ire-iren wadannan ingantatu ne, babu matsala tare da su, kuma kana iya saya, ka je kamfanin waya a saita maka su ka kama mu'amala da tsarin da suke gudanuwa a kai wajen sadarwa.  Kuma duk irinsu ne muka yi bayani akansu, kuma kamfanin Research in Motion ne ke kera su.  Amma wadanda ke zuwa daga kasar Sin masu lambobi (kamar wadanda kake magana akai), jabun Blackberry ne, kuma ba su da wadannan sifofi da muka yi bayaninsu a baya.  Akwai wadanda ke zuwa ma da katin SIM biyu. Duk jabu ne.  Da fatan an gamsu.

Wato inason ka bani shawara ne, a hakika ina son fara "Online business," kuma a yanzu na tanadi hanyoyi masu inganci, masu yawa, kai har littafi na rubuta don koya wa mutane, amma matsalata kawai itace ta tsarin aiwatar da biyan kudade. Wato Mastercard da sauransu. Ta yaya zan mallaki wadancan katuna?  Daga Sadiq Tukur, gwarzan gwaraza. Gwarzo

Malam Sadiq lallai ka cancanci jinjina.  Idan kana bukatar katin ai samunsa ba wahala.  Ka je bankin GTBank, ko Fidelity, ko Zenith, sai ka musu bayani, za su bude maka taskar ajiya mai dauke da katin.  Amma kafin nan, ka tabbata ka yi rajistan kamfaninka, da hajojin da kake son sayarwa.  In kuwa ba haka ba, to zai yi wahala su bude maka taskar.  Allah sa a dace.

Salam Baban Sadik dan allah wai da gaske ne Katin ATM yana daukan magana, kamar yadda blackberry take daukar sirri zuwa wani waje.  Daga M. J. Jos

A gaskiya ban taba karantawa ba, ban kuma taba ji ba.  Abin da na sani dai shi ne dan abin da na gabatar a kasidun baya.  Da fatan ka gamsu.

Barka da war haka Baban Sadiq, ga 'yan tambayoyi na; 1) Me ake nufi da ICT a harshen Hausa? 2) wace irin gudunmuwa ICT ke ba wa harshen hausa?  3) A fada mini gidajen yanar sadarwa guda 10 da ke bayani da harshen Hausa kamar gumel.com da sauransu: shamoo04@yahoo.com

Cikin yardar Allah na aika maka makalar da Farfesa Abdallah Uba Adamu ya rubuta kan wannan haka a shekarar 2004, mai take: Hausa and Information Communication Technologies (ICTs).  A ciki za ka samu amsar dukkan wadannan tambayoyi naka. Makalar tana da tsawo, don shafuka 24 ne. Sai ka saukar za ka iya bugawa ko karantawa a shafin kwamfuta; duk wanda ka so yi.  Allah sa mu dace, amin.

Salamu alaikum Baban Sadiq, ni ne Haruna Katsina da na kira ka dazun da safe.  Da ma abin da nake son tambaya shi ne:  akan Gmail ne; yaya yake?  Kuma ya ake amfani da shi? Nayi rejista dinsa amma na dauka duk tare suke da Imail; amfaninsu daya kuma, amma sai naga sabanin haka. Shi ne nake son ayi man bayani akan shi Gmail din tare da kuma shi Imail din baki daya.  Wannan shi ne username din Gmail din da nayi rejista: Ibrahimharuna1@gmail.com. Sannan inda dama ka ba ni adireshin da zan iya samun Imai din, domin waya ta ba ta da Imail. Na gode

Malam Haruna akwai alamar ba ka taba amfani da masarrafar Imel ba.  Ai kalmar Imel gamammen suna ne da ke ishara ga dukkan hanyar wasikar sadarwa ta Intanet, da wacce ake amfani da ita a tsarin sadarwa tsakanin kwamfutoci a gajere da dogon zango.  Da Yahoo Mail, da Hotmail, da Gmail (ko Google Mail), duk nau'ukan Imel ne.  babu wani bambanci tsakanin Imel da Gmail sai na suna.  Idan kana da jakar wasikar Gmail, to ka mallaki Imel a rayuwarka.  Abin da kalmar "Email" ke nufi shi ne, "Electronic Mail."  Don haka kada ka damu, ka riga ka samu Imel, tunda kana da Gmail.  Gmail wani nau'in Imel ne da kamfanin Google da ya bude ba jimawa ba.  Haka Yahoo Mail, nau'in Imel ne na kamfanin Yahoo!  Haka ma Hotmail, nau'in Imel ne na kamfanin Microsoft.  Dangane da wayarka kuma, ban san wace iri bace, amma ina kyautata zaton cewa lallai tana da Imel.  Idan kana son gane haka, ka je "Menu", sai ka shiga "Message", daga nan ka matsa wajen "Create Message", za a budo maka nau'ukan sakonnin da za ka iya rubutawa ka aika.  A misali, za ka ga: "Text Message, Multimedia Message, Audio Message, Email", a jere.  Sai dai shi tsarin Imel da ke cikin wayoyin salula ya sha bamban da wanda ke jikin Intanet kuma ake shiga ta kwamfuta.  Wanda ke cikin wayar salula na bukatar a saita shi, kuma hakan na bukatar kwarewa, a gaskiya.  Don haka idan kana bukatar mu'amala da Imel ta wayar salula cikin sauki, ka shiga gidan yanar sadarwar Google ko Gmail ta wayarka kawai (da ke http://mail.google.com), sai ka shigar da bayananka.

Salamu alaikum Baban sadik, Tambayata itace ko mutum zai iya tafiya akan doron Wata (Moon) domin wani bincike a kansa? Daga Aliyu Mukhtar Sa'idu (I.T) Kano, aliitpro2020@.com 08034332200

Malam Aliyu ai tuni har an yi kuwa.  Abu ne mai yiwuwa, kamar yadda tarihi ya nuna lokacin tafiyar su Neil Armstrong a shekarar 1969.  Sun taka saman Wata, inda suka gudanar da binciken da suke son yi.  A karshe suka debo samfurin kasar wurin, don shigowa da shi duniya da ci gaba da gudanar da bincike kan yanayin wurin.  Sai dai kuma ya kamata mu sani, muhallin da ke saman Wata ya sha bamban da irin muhallinmu.  Domin a yayin da muke da iska mai kadawa da muke shakarta a nan, a can babu irin wannan iska.  Don haka masu zuwa duniyar Wata ke sanya wasu tufafi masu dauke da na'urar shakar iska, wacce ke taimaka musu wajen numfasawa yadda ta kamata.  Sannan a can babu tsarin Janyo nauyi kasa, watau "Force of Gravity" kamar yadda muke da shi a sararin wannan duniya tamu.  Wannan tasa za ka gansu kamar suna tafiya ne a saman iska, ba su daidaituwa wuri daya a lokaci daya, saboda karancin tasirin wannan tsari a can.  Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum Abu Sadik, don Allah ina son karin bayani akan intanet da Network. Muh'd L Igabi al-igabaawy1986@yahoo.com

Kalmar Intanet dai na nufin hade-haden da ke tsakanin kwamfutoci ko sauran kayayyakin sadarwar zamani, da ke taimaka musu wajen aiwatar da sadarwa ba tare da wata matsala ba, a ko ina suke a duniya.  A daya bangaren kuma, kalmar "Network" na nufin hade-haden da ke tsakanin kwamfutoci ne a a wani wuri na musamman.  Misali, ana iya hada kwamfutoci kamar goma a gida daya, su rika aiwatar da sadarwa a tsakaninsu. Haka ana iya hada alaka a tsakanin kwamfutocin da ke wani gida da wani gida da ke unguwa guda, ko gari guda, ko jiha guda.  Duk wadannan tsare-tsare ana kiransu "Networking".  Idan a gida daya ne, sai a kira su "Locak Area Network" (LAN).  Idan a tsakanin gari da gari ne, ko unguwa da unguwa, sai a kira shi "Wide Area Network" (WAN).  Bambancin da ke tsakaninsu shi ne, Intanet ta fi fadi sama da "Network."  A takaice ka iya cewa, Intanet hadaka ce ta nau'ukan "Network" a duniya.  A yayin da tsarin Network ke da iya haddi da tsaro da kuma mai lura da tsarin (watau Network Administrator), a tsarin Intanet babu wannan.  Ita Intanet muhalli ne ko wata duniya ce mara iyaka.  Ta ko ina kana iya shiga.  Ta ko ina kana iya fita.  A kowane lokaci kana iya shiga.  A kowane lokaci kana iya fita.  Amma a tsarin Network dole sai an baka iznin shiga, da lokaci, da kuma inda za ka tsaya; baka isa ka wuce ba.  Dukkan wadannan kaidoji ba su a tsarin Intanet.  Da fatan ka gamsu.

Salam ya aiki? Ina da kwamfuta amma ban san yadda zan yi rejistan intanet ba, ko a waya ma ban iya ba. Don Allah yaya zan yi?

Wannan abu ne mai sauki. Ka je ofishin kowanne daga cikin kamfanonin wayar salula da muke da su, ka sanar da su cewa kana son "Internet Modem", watau makalutun sadarwa ta Intanet.  Za su sayar maka, sannan su jona maka kwamfutar nan take.  Sai dai zaka rika loda kati a duk sadda kudinka yak are, don ci gaba da samun sadarwa a kwamfutar. Ko a duk sadda iya adadin kwanakin da suka yanke wa kudin.  Ma'ana, idan ka loda kudi, akwai iya adadin bayanan da za a baka; kamar 200MB, ko 500MB misali.  Idan wata guda ya kare baka gama cinye wadannan adadin bayanai ba, za a kulle sai ka sa kudi sannan a kara maka wasu a kan wadanda suka rage.  Dangane da wayar salula kuma, ka aika sakon tes ga kamfanin wayar da kake amfani da layinsu, ko kaje ofishinsu kawai zai fi sauki, ka sanar da su cewa kana son a saita maka wayar don ka rika mu'amala da fasahar Intanet, za su saita maka, kyauta.  Da fatan an gamsu.

Assalamu alaikum, Baban Sadiq ina yi maka fatan alheri. Dan Allah mene ne banbancin MMS da kuma SMS a wajen tura sakwanni? Daga Yusuf Muhammad Gagarawa, Jihar Jigawa, Najeriya. 08061123657, 08154627050

Malam Yusuf muna godiya da addu'a. Haruffan MMS na nufin "Multimedia Message" ne, watau tsarin aika sakonni na murya ko hotuna ko bidiyo.  A daya bangaren kuma, haruffan SMS na nufin "Short Message Service" ne, watau tsarin aika gajerun sakonni rubutattu ta wayar salula. Bambancin da ke tsakaninsu dai na yanayi ne, da kuma hanyar da suke bi wajen aikawa.  MMS dai ta kunshi sauti ne da hotuna masu motsi da daskararru, a yayin da SMS ta kunshi rubutattun sakonni kadai.  Tsarin MMS na bin tafarkin yanayin sadarwar wayar salula mai amfani da fasahar Intanet ne, a yayin da tsarin SMS ke amfani da tsarin yanayin sadarwar wayar salula kadai.  Don haka ko babu tsarin Intanet a wayar salula za ka iya aika sakon SMS, amma tsarin MMS dole sai da tsarin Intanet a tare da ita.  Da fatan an gamsu.

Assalamu alaikum Baban Sadik, a fasahar kere-kere kamar akwai dan tsafi wajen kera wani abu, ko dai zunzurutun ilmi ne?  Don wani malami ya ce mana duk inda fasaha tayi yawa, akwai sihiri. Ka huta lafiya, daga Kabiru Ahmad Gombe 08182374782 uribak.ahmad@yahoo.com

Malam Kabiru ai tun wajen Malaminku ka bar amsar tambayarka.  Domin ban san wani bangaren fasahar kere-kere bane ke kunshe da sihiri ko tsafi.  Sihiri dai shi ne juya hakikanin wani abu zuwa wani abu daban, ta hanyar da ta sha karfin tunanin dan adam a al'adance, tare da taimakon shedan ko kangararrun aljanu.  Da yace idan fasaha ta yi yawa akwai sihiri a ciki, abin da zan iya cewa kawai shi ne; sihiri nau'i biyu ne, kamar yadda wasu malamai ke bayani.  Akwai hakikanin sihiri da tsafi, wanda kowa ya sani, wanda kuma ke tasiri wajen warware imanin duk wani musulmi. Akwai kuma sihiri ta dabi'a, watau dan adam ya yi wani abin da zai kama hankali da tunanin mutane, saboda kwarewa ko tasirin abin, ba tare da taimakon wani aljani ko shedani ba.  Irin wannan sihiri shi ne wanda Manzon Allah (SAW) ke magana a kansa a cikin wani hadisi da yake cewa, "Lallai a cikin zance hakika akwai sihiri…" duk malamai sun tafi a kan cewa ba hakikanin sihirin da ke warware imani ba yake nufi.  Domin sahabbai sun sha kulla baitukan wake a gabanshi, wasu lokuta ma waken shi ake yabo a ciki, kuma bai hana ba.  Kamar su Hassaan bn Thaabit, da Abdullahi bn Rawaaha, duk mawakansa ne masu yabonsa.  Abin da yake nufi shi ne, lallai wake na cikin abin da ke tasiri a zukatan mutane, irin tasirin da kusan sihiri ke yi wajen kama zuciya da dabi'a.  Wannan kuwa wani abu ne sananne ga duk wanda ya san rayuwar Larabawa musamman kafin zuwan Musulunci.  To, idan wannan malami na nufin irin wannan nau'in tasiri ne ko sihiri, sai mu ce eh, akwai.  Domin duk wanda ya ga inda ake abubuwa da dama na kere-kere, musamman inda ake kera jiragen sama, da yadda kwamfutoci ke sarrafa injina ko na'urorin da ke gudanar da wadannan ayyuka, zai ga kamar akwai sihiri a ciki, amma ina; tsantsar ilmi ne da kwarewa.  Wasu kan ce wai Turawan kanfani kan yi tsafi a yayin da suke kokarin gina gadoji a cikin teku, da wasu gidaje da ke wasu wuraren da ake tunanin akwai kwankwamai a ciki, wai shi yasa ma idan suna haka, sai leburori ma'aikata su ta fadawa cikin teku, ko su yi ta hadari, don aljanu na shan jininsu ne sanadiyyar tsafin. Duk wadannan wasu abubuwa ne ko zantuka da babu hakika a cikinsu.  Ban ce karya bane kai tsaye, ban kuma ce turawa ba su yin sihiri ko tsafi ba, a a, suna yi.  Amma abin da ya bayyana mana da shi muke hukunci. Wannan shi ne abin da zan iya cewa.  Idan malam yana kusa, sai ya taimaka maka da karin bayani.  Allah shi ne masanin hakikanin abubuwa. Da fatan an gamsu.

Salam, tambaya ta kan ATM ne. Kamar ina da kudi a Current yaya zan juya su su koma cikin Savings ga na'urar ATM?

Eh to, abin da na sani shi ne, bankuna na iya jona miki taskar ajiyarka guda biyu (Savings da Current) su rika amfani da katin ATM guda daya.  Ma'ana kina iya shiga kowanne daga cikinsu don cire kudi.  Dangane da juye adadin kudaden da kike da su daga Current zuwa Savings kuwa, wannan sai dai ki bi tsarin "Transfer" don yin hakan.  Wannan ne zai baki damar shiga da kudaden da kike da su a Current su koma Savings.  Idan kika sanya katin, za ki ga inda aka rubuta "Transfer", idan kika matsa akwai inda za ki shigar da adadin kudin da kike son fitarwa, da nau'in taskar da kike son mayar da kudin, da sauran bayanai.  Babu wahala tsarin inshallah.  Da fatan kin gamsu.

Assalamu alaikum Baban Sadiq, barka da warhaka. Ina fatan kana lafiya, Allah yasa haka, amin. Tambaya ta ita ce: Me yasa idan mutum yana kallon bidiyo a intanet sai ya rika tafiya lakakai-lakakai, sannan ya dan tsaya, sai kuma ya ci gaba? Ba kamar yadda muka saba kallo a bidiyo CD/DVD ba? Wassalam! Daga Uncle Bash, J/Yola 07037133338, unclebbash@yahoo.com

A gaida Uncle Bash namu.  Wannan tsari na kallon hoto mai motsi ta Intanet shi ake kira "Streaming."  Idan kai tsaye (Live) kake kallo a lokacin da abin ke gudanuwa, ana kiransa "Live Streaming."  Dalilin da yasa kake ganin abin ba ya tafiya da sauri kamar ya kamata, shi ne babu inganci cikin tsarin Intanet din da kake amfani da shi.  Da a ce muna amfani da tsarin "Broadband" ne, da garau za ka gani, babu wani saibi balle tangarda.  Wannan shi ne kokarin da ake ta yi wajen ganin an inganta tsarin sadarwar Intanet a Najeriya.  A wasu kasashe ba ka iya bambance tashar talabijin ta gama-gari, da tashar talabijin ta Intanet (Internet TV), saboda ingancin sadarwar Intanet a kasashen. Da fatan ka gamsu.

Salam, barka Baban Sadiq. Ga tambaya ta: wacce irin gudunmawa kake ganin fasahar ICT za ta iya bayarwa ga nazarin Hausa? Ga adireshin Imail dina nan. ismailaliyu@gmail.com Daga Waziri

Malam Ismaila sai ka duba akwatin Imel dinka, tuni na tura maka kasidar Farfesa Abdallah Uba Adamu.  Sai ka saukar ka buga.  Allah sa  mu dace.

Assalamu alaikum, shin akwai yadda za a yi mutum ya samu makalolinka na aminiya wadanda ka gabatar a baya ta hanyar Imail? Bissalam

Eh kana iya samu, sosai kuwa. Sai dai kuma ganin cewa suna da yawa, ba za ka ji dadin karbarsu a lokaci daya ba.  Domin sun kai wajen 28MB, ma'ana mizaninsu ya kai wajen miliyan ashirin da takwas. Sai dai a turo maka su kadan-kadan.  Ko kuma ka je shafinmu da ke http://fasahar-intanet.blogspot.com don daukansu daya bayan daya, a duk sadda kake so.  idan kuma ka fi sha'awansu samunsu ta Imel din, sai ka turo adireshinka a turo maka.

Assalamu alaikum, ka yi bayani dalla-dalla kan makalarka ta na'urar ATM, amma ban ga ka ambaci na'urar daukar hoto ba, ko babu ita?  Allah ya kara maka basira da lafiya. Alh. Ado Damaturu

Alhaji Ado mun gode da wannan tsokaci naka. Hakika akwai na'urar daukar hoto (Camera) a jikin wannan mashin.  Mancewa na yi ban ambace ta ba.  mun gode.  Allah sa mu dace.

Baban Sadiq, ina gaisheka da kokari. In na fahimceka, shi kamfanin Interswitch ke da ma'aikatan da ke rarraba kudaden ga bankunan da abin ya shafa kenan kullum in gari ya waye? Kuma ladansu shi ne Naira 100 nan? Bashir Ibrahim, Port Harcourt

Malam Ibrahim wannan wani abu ne da ba zan iya ce maka eh ko a a ba. Sai dai ta la'akari da yadda ake gudanar da wannan abu a kullum; dare da rana safe da yamma, zai yi wahala ace ma'aikaci ake turawa a duk safiya ya biya bankuna.  Abin da ke faruwa shi ne, akwai cibiya ta musamman wacce ke tantance adadin kudaden da kowane bangare ke samu, da kuma hanyar da ake bi wajen biya.  Wannan shi ake kira Electronic Clearing System.  Da fatan ka gamsu.

Salam, zanso baban sadik yayima 'yan uwa yadda ake yin "money tranfer ta hanyar na'urar ATM zuwa wani bankin. Daga Baban Mus'ab, Kaduna

An gaida Baban Mus'ab. Aiwayatar da wannan tsari na "Money Transfer" bai da wata wahala ko kadan.  Idan ka je inda na'urar take, ka sa katinka, sai ka shigar da kalmomin sirrinka (watau "Password"), za a budo maka inda za ka zabi "Funds Transfer."  Sai ka matsa, ka zarce inda za ka shigar da lambar asusun wanda kake son aika masa, da bankin da yake ajiya, da kuma adadin kudaden da kake son aika masa.  Wadannan su ne abubuwan da ake bukata. Tsarin bai da wahala ko kadan.  Abin da za ka kiyaye kawai shi ne, wajen shigar da lambar asusun wanda kake son aika masa, ka tabbata ka shigar daidai, don kada a jefa kudaden zuwa asusun wani.  Idan haka ta faru kuwa, kafin a mayar maka da kudadenka zai dan dauki lokaci.  Don sai sun yi amfani da kundin adana bayanan da na'urar ke taskancewa, don tababtar da da'awarka.  Sai a kiyaye.

Salam, Baban Sadiq muna matukar farin ciki da rubutunka. Munji dadin bayanin yadda ake mu'amala da katin ATM, wanda daman mafi yawanmu mata bamu fahimce shi sosai ba. Allah ya yawaita mana irinka a cikin al'umma musulma, amin. Daga Maman Abdulsamad Gombe.

Allah saka da alheri da wannan jinjina mara iyaka.  Bai kamata albarka da rahamar da ke cikin wannan addu'a su shafe ni ni kadai ba.  Ina rokon Allah ya sadar da su ga dukkan masu karatu, da masu lura da wannan shafi a ofishin AMINIYA,  da editan jaridar baki daya, kai, da ma kamfanin Media Trust baki daya.  Allah tara mu cikin alheri, ya sa mu cikin sahun masu ciyar da al'umma gaba baki daya, amin. Mun gode.

Salam, barka da kokari Baban Sadik. Dan gyara ne akan makalar da ka yi a Aminiya ta 23 ga watan Satumba, inda kace "Marigayi Mudi Sipikin."  Yana nan da ransa. A huta lafiya.  Bashir Gwale, Kano

To, malam Bashir na gode. Kafin wannan sako naka ma akwai wadanda suka bugo waya suka mini gyara kan haka.  Gaskiya ba gani nayi a rubuce ba, illa dai na dade ban ji duriyarsa ba tsawon shekaru, sai na dauka ya rasu.  Don ina da mantuwa sosai; akwai wadanda Allah ya musu rasuwa, amma saboda tsawon zamani sai in dauka suna raye.  Wannan nakasa ce daga gare ni.  Allah sa mu cika da imani.  Na gode.

Shin, me ke haifar da rikicewar sauti idan aka yi amfani da wayar salula a kusa da rediyo ko talabijin? Daga Ashiru Dan'azumi Gwarzo.

Malam Ashiru ai kuwa mun sha yin bayani a wannan shafi a baya.  Watakila ba ka riski bugun da ke dauke da bayanin da nayi ba.  Abin da ke haddasa haka shi ne, da sauti, da haske, da iska, duk kowanne daga cikinsu yana da hanyarsa daban ne a sararin wannan duniya ta mu.  Duk sadda wani ya shiga hanyar wani, nan take ake samun tangarda.  Kamar ruwa ne da muke sha da kuma iskar da muke shaka; kowanne hanyarsa daban.  Idan wani ya shiga tafarkin wani, dole a samu matsala.  In abin ma yazo da karen kwana, shikenan.  Tsarin yanayin sadarwar rediyo ta sha bamban da na wayar salula.  Idan aka samu cin karo a tsakaninsu dole a samu matsala.  Haka tsarin sadarwa idan ya ci karo da hanyar wutar lantarki, a kan samu matsala.  Shi yasa idan ka kusanci dirkan wutar lantarki da rediyonka, za ka ji tashoshin sun rikice.  Da fatan ka gamsu.

Salam Baban Sadik, ya aiki? Kullum idan na shiga shafin Blog di na na google, sai na ga sako cewa "zan iya samun kudi ta hanyar Adsense." Shin ya abin yake ne? Bashir Ahmad

Malam Bashir kenan!  Ai wannan wata sabuwar hanya ce da kanfanin Google ya kirkira don samun abin masarufi ga masu gidajen yanar sadarwa ko shafukan Mudawwanai (Blogs).  Idan ka je kayi rajista, za ka basu adireshin gidanka, da lambar taskar ajiyarka, da adireshin gidan wayarka, da kuma adireshin gidan yanar sadarwarka.  Bayan wasu 'yan kwanaki za su turo maka wasu shafuka da za ka shigar a shafinka, masu dauke da tallace-tallace kan abin da ke da nasaba da bayanan da ke shafinka.  Duk wanda ya ziyarci shafinka, idan ya matsa wadannan bayanai na tallace-tallace masu dauke da bayanai da ke shafinka, akwai masarrafar da ke kididdige yawan matsawar da masu ziyara ke yi.  A karshen wata sai a duba yawan shafukan da aka matsa na tallace-tallace, sannan a kirga maka kudinka.  Kowane matsawa akwai adadin kudinsa.  Wannan shi ake kira "Pay Per Click."  Idan a karshen wata kudinka ya kama dala dari biyar ne, sai su aiko maka da "Money Order."  Takardar kudi ce mai dauke da adadin kudinka.  Kana iya zuwa banki ka sanya cikin taskarka, idan kana da taska mai daukan daloli (Dormiciliary Account).  Amma dole mu sani cewa, Google na da masarrafar da ke lura da wadanda ke matsawa. Haramun ne a gareka a matsayinka na mai shafin, ka matsa kowanne daga cikin wadannan bayanai na tallace-tallace. Idan ka matsa, sun sani.  Domin wasunmu sai su dauka ko Google wawaye ne, sai su ta matsawa. Wannan zamba cikin aminci ne, kuma suna iya ganewa, kuma ba za su kirga da irin wadannan matse-matse na cuta ba.  Haka idan ka umarci wasu su rika matsawa don dabara, duk suna lura. Domin suna da bayani kan inda kake zama, don haka idan yawan masu matsawan suna wuri guda ne da kai, duk baka tsira ba.  Abin da ake so shi ne, ka bar abin yadda yake, duk wanda ya matsa, za a kididdige maka.  Ko a musulunci bai kamata ka matsa ba, bai kuma kamata ka umarci wani ya matsa maka ba. Ka hakura da abin da ka samu na halal, shi yafi mai yawa na haram.  Da fatan ka gamsu.

Allah ya kara lafiya da ilimi da nisan kwana. Allah ya raya iyali. Allah ya sa mu dace, amin.  Abba Ibrahim Gwan-Gwan, Mai bibiyar rubutunka a kodayaushe.

Malam Abba mun gode da addu'ar fatan alheri, kuma Allah biya mana bukatunmu gaba daya, baki daya, amin.  Duk matsalolin da muke fama da su a al'ummance, Allah mana maganinsu, amin.

Assalamu alaikum Baban Sadiq, dan Allah a taimaka mini; duk sadda na shiga masarrafar Google Maths don aiwatar da wani lissafi, amsar ba ta fitowa, sai dai a kawo mini wasu misalai daban.  Daga Sadiq Usman, Bauchi

Malam Sadiq yana da kyau ka san cewa masarrafar "Google Maths" masarrafa ce mai dauke da tsarin mu'amala.  Duk sadda ka zo amfani da ita don neman amsar wata ka'ida ta lissafi (maths formular solution), dole ne ka shigar da ka'idojin da suka kamata.  In kuwa ba haka ba, ba za ka samu amsar da kake so ba.  Sai dai ta yi ta rubuto maka misalai, don ka samu misali kan abin da ya kamata ko yadda ya kamata ka shirya tambayarka.  A tunanina wannan shi ne abin da yasa suke ta aiko maka da  wasu misalan.  Ka tabbata ka shigar da ka'idar lissafi (maths formular) sananniya, kafin neman a baka amsa. Sai a kiyaye nan gaba.

Salam, Baban Sadiq ina karuwa da kuma samun annashiwa game da rubuce-rubucen kimiyyarka a cikin jaridar Aminiya. Sai dai na so in san tazarar Tauraron binciken daga duniya a zamanin shawaginsa a kololuwar sama da kuma irin nasarar da ya cimma a lokacin rayuwarsa.  Ibrahim Zubairu, Kufena College Zaria

Malam Ibrahim bayanai makamantan wannan sai dai a je gidan yanar sadarwar NASA, watau Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta kasar Amurka.  Gidan yanar sadarwarta na www.nasa.gov in Allah ya yarda za a samu dukkan wadannan bayanai.  Kada a mance, sunan wannan Tauraron dan adam dai shi ne: Upper Atmosphere Research Satellite (UARS).  Da fatan an gamsu.

Assalamu alaikum. Yanzu na gama karanta makalarka. Allah Ya saka da hairan, kuma Ya taimaka. Nadabo Idris Dabi, Ringim.

To amin, Malam Nadabo.  Muna godiya har kullum.  Allah saka da alherinsa, amin.

Assalamu Alaikum, Baban Sadik Allah ya saka ma da alheri akan wannan karantarwa da kake yi a jaridar Aminiya, a filin Kimiyya. Da fatan Allah ya kara maka fahimta da ilmi mai amfani, domin anfanarwa, Allah kuma ya yi jagora, amin.  Daga Muhammad, Kyari, Aumtco.

To ni ma ina godiya sosai Malam Muhammad.  Allah mana jagora baki daya, ya kuma sa mu zama haske ga al'umma ba duhu ba, amin.

Salam Baban Sadik, barka ya aiki. Don Allah ina so ka turomin mukalolin da ka rubuta a AMINIYA kan Facebook, Twitter, Youtube, Wikileaks da Wikepedia, ta auwalabdulqadirsani@yahoo.com. Wassalam

Malam Auwal duk cikin wadannan ina kyautata zaton "Wikileaks" ne kadai muka yi rubutu kansu.  Sauran duk sai dai amsoshin tambayoyi da suka dangance su. Amma a hankali za mu yi bayani musamman kansu.  Idan ka ga haka, sai ka tuna mini, don ba lalai bane in tuna; kwakwalwar tawa ba ta ja sosai wajen halarto abubuwan baya.  Na tura maka wanda muka rubuta kan "Wikileaks" inshallah.  Da fatan an gamsu.