Monday, May 28, 2007

Ziyartan Gidajen Yanan Sadarwa #2

KANOONLINE.COM (http://www.kanoonline.com)

A yau ga mu tsundum cikin birnin Kano; Ta-Dabo Ci-gari; gari ba Kano ba dajin Allah; Yaro ko da me ka zo an fi ka! Cikin ziyaran da mu ka fara kaiwa wasu gidajen yanan sadarwa da ke giza-gizan sadarwa ta Intanet, a yau za mu kashe yini ne a zauren KANOONLINE.COM, shahararren gidan yanan sadarwan da aka tanada musamman, don taimaka ma dukkan mai neman sanin wani abu dangane da birnin Kano da ke arewacin Nijeriya.

Gidan Yanar, Kacokan

Wannan gidan yanan sadarwa na Kanoonline, kayataccen gida ne irin na yanar sadarwa, wanda aka gina shi da kwarewa irin ta fasahar gina gidan yanan sadawa na zamani, watau Web Progamming Techniques. Daga cikin fasahar da aka yi amfani dasu akwai Java Script, wanda ya taimaka wajen kawata haruffa da hotunan da mai ziyara zai ta cin karo dasu. Idan ka matsa rariyar likau (Web Link) a Kanoonline, zaka ga haruffa na wani laushi da laudi, suna canza kama, kamar sa maka Magana ko dariya. Wannan shi ake kira Mouse Over, kuma duk da fasahar Java Script ake tsara su. Sai kuma fasahar Cascading Style Sheets, ko kace CSS a takaice. Shi ma wani gajeren dabara ne da ake amfani da shi wajen gyatta zaman bayanai a gidan yanan sadarwa, musamman wajen abinda ya shafi tsarawa da shirya launin haruffa da ajiye bayanai a irin bigiren da ake so, a ko ina ne cikin daki ko zauren gidan yanan sadarwa. Har wa yau, maginin wannan gidan yanan sadarwa na Kanoonline yayi amfani da hanyoyin saukaka ma mai ziyara fita ko shiga wani shafi daga wani. Duk shafi ko dakin gidan yanan da ka shiga a cikin gidan, zaka samu alamar da zata riskar da kai zuwa wani dakin ko kuma ka dawo zauren gidan gaba daya. Sannan, da zaran ka shigo zauren (Home Page), abinda za ka fara cin karo da shi shine wani kafcecen tambarin KANO, tare da taswiran jihar gaba daya (Map), daga hannun hagu a sama. A kasan tambarin ne zaka ci karo da agogon da ke sanar da kai ko karfe nawa ne yanzu a birnin Kano! Tirkashi! Wani aikin sai Kanawa. Zaka ga lokaci da kuma kwanan wata duk a nan (Date and Time). Daga can kuryan dama kuma, zaka sake cin karo da bayanai kan layin bigiren da Kano ke kai, a taswiran duniya (Longitude and Latitude). Daga nan sai maginin gidan ya raba gidan zuwa kashi uku, daga sama zuwa kasa. Daga bangaren farko daga hannun hagu, sai tsakiya, da kuma bangaren karshe daga dama. To me ke zube cikin wannan gida ne?

Me Ke Ciki?

Kamar gidan yanan sadarwa ta Gamji, Kanoonline na makare ne da bayanai da hotuna masu motsi da marasa motsi da sauti da kuma taswirori. Bayanan sun hada da kasidu da mujallu da makaloli da littafai da kuma manhajojin da ke taimaka ma mai ziyara aiwatar da wasu ayyuka. Akwai kuma hotunan birnin Kano, da hotunan Dogarawan Kano da kuma hotunan Badala/Ganuwa da dai sauransu. Sai dai galibin wadannan hotuna a makale suke a matsayin tambari (banners) da ke shafuka daban-daban a dakunan gidan gaba daya. Akwai kuma sauti na karatuttukan tafsirin Malam Isah Waziri, Marigayi Malam Lawal Kalarawi, Marigayi Malam Nasiru Kabara, Marigayi Malam Bashir Dandago, da kuma wakokin Imfiraji da wata baiwar Allah ta wake su. Akwai kuma Marigayi Malam Bala Mai Yafe, in da yake wake Al-Burdah. Kana shigowa zauren Kanoonline, a tsakiya za ka ci karo da: AS SALAAMU ALAIKUM! A kasan sa kuma akwai sanarwa da ke sanar da masu ziyara cewa wannan gidan yanan sadarwa da bayanan da ke jibge ciki ba mallakin gwamnatin Jihar Kano bane. Kana kara gangarawa kuma zaka cin ma takaitaccen bayani kan Birnin Kano. Wannan bangaren tsakiya kenan, na gidan yanan sadarwan. Idan ka yi bangaren hagu kuma, zaka fara cin karo ne da Tools, manhajoji ne a wajen. Idan kana son aikawa da adireshin Imel dinka, don a rinka aiko maka bayanai kai tsaye, sai ka mika a Join Our Mailing List. A wannan bangare zaka samu bayanai kan wasu garuruwa ko ince takwarorin Kano, a kasashe irin su Rasha, Congo Democratic Republic, Japan, Nijer, Hungari, Chadi. Akwai garuruwa masu suna “Kano” a dukkan wadannan kasashe. Daga nan zaka samu manhajar da za ta taimaka maka wajen auna mizani ko kimar kudade tsakanin Nairan Nijeriya da sauran kudade (Currency Converter). Kasa da shi kuma sai tambarin Kungiyar Inuwar Jama’ar Kano (Kano Forum), wacce ke daukan nauyin tafiyar da gidan yanan. Daga nan kuma sai bayanai kan Gidan Makama, watau gidan tarihi da ke Kano, sai bayanai kan Ganuwar Kano. Daga nan sai aka jero rariyar likau na wasu gidajen yanan sadarwan, irinsu Gamji, Dandali, Gwamnatin Jihar Jigawa, Arewaonline, Association of Nigerian Authors (ANA) da kuma British Council. Wadannan su ne ababen da ke bangaren hagu a zauren gidan yanan. A bangare na karshe kuma, wanda ke hannun dama, nau’ukan bayanan da ke ciki sun hada da kasidu (articles), littafai, mujallu, zauren hira da tattaunawa (Discussion Forum), wakoki na kafiya (poems) da kuma jakunkunan sauti na tafisiri da wakokin Imfiraji (kamar yadda bayani ya gabata a sama). Har wa yau, a wannan bangare ne ake da cikakken bayani kan adadin jama’ar da ke Kano, da adadin Bankunan da ke Kano, da adadin asibitocin da ke Kano, da adadin hadarurrukan jirgin sama da aka yi a Kano, da kuma adadin wadanda suka shugabanci Kano a matsayin Gwamnoni, da kuma adadin Kananan Hukumomin da ke Jihar gaba daya. A kasa da wadannan kuma akwai kasidu da aka tara, wadanda kuma galibinsu sun ta’allaka ne da jihar Kano gaba daya, kan abinda ya shafi hanyoyin sadarwa, ilimi da sauransu. Dukkan wadannan bayanai zaka same su a bangaren hannun dama, da zaran ka shigo zauren. To wa ke tafiyar da wannan gidan ne?

Uban Gidan Gaba Daya

Wannan gidan yanan sadarwa an gina shi ne a shekarar 2001, ranar 23 ga watan Agusta. Kuma duk da cewa wasu mutane hudu ne suka hada kai wajen wannan aiki na alheri, daya daga cikin su ne ya gina gidan gaba daya, a aikace nake nufi. Wadannan mutane kuwa su ne: Farfesa Abdallah Uba Adamu (Jami’ar Bayero, Kano), Malam Salisu Danyaro Soron-Dinki (Amurka), Malam Ibrahim Ado Kurawa (Cibiyar Binciken Ilimi, Kano), da kuma Malam Adamu Yusuf. Wadannan mutane shahararru ne, ba a Nijeriya ko arewancinta kadai ba, har a sauran kasashen duniya. Farfesa Abdallah Uba Adamu ne mai Majalisar Fina-finan Hausa da ke Intanet, da ma sauran majalisu. Kusan duk wanda ya riski fasahar Intanet a arewacin Nijeriya, ina da yakinin cewa da hannunsa a ciki, hatta masu karanta wannan shafi, da shi kanshi abinda ke rubuce a wannan shafi. Duk sanadiyyar sa ne muka samu riskuwa da wannan bakuwar hanyar sadarwa. Malam Salisu Dan Yaro kuma mutumin Soron-Dinki ne da ke Birnin Kano, yana kuma zaune ne a kasar Amurka. Shi ne ya gina wannan gidan yanan sadarwa na Kanoonline, domin masanin kwamfuta ne da manhajarta, na gaske kuwa. Shi ne mai gidan yanan sadarwan Dandali.com, mai dauke da al’adun Hausa kai kace a kasar Hausa kake. Wadannan bayin Allah hudu ne ke tafiyar da wannan gidan yanan sadarwa, duk da yake suna samun agaji daga Inuwar Jama’ar Kano (Kano Forum), wajen hakan. Mutane ne masu son ci gaban al’umma ta hanyar ilimi. Duk wanda Allah Ya hada ka dashi daga cikinsu, zai yi wahala ka yi nadama, muddin agaji kake nema ta hanyar ilimi da abinda ya shafe shi. Ina da shaida mai karfi a kan haka.

Manufa

Duk da cewa mai ziyara ba zai ga in da aka sanar dashi manufar gina wannan gidan sadarwa ba, manufar a fili take; ilimantar da duniya kan kasar Kano da jama’arta da kuma kasan Hausa gaba daya. Har wa yau, daga cikin manufarsu akwai karuwa da juna ta hanyar ilimi. Sai ka shiga Majalisar Tattaunawarsu zaka fahimci hakan. Wadannan manufofi sun isa a matsayin hujja wajen nuna damuwarsu kan halin da al’umma take ciki. Suna ganin babu al’ummar da zata ci gaba, muddin ta mance al’adunta da addininta, har abada. Allah saka musu da alheri, amin.

Shawarwari

Kafin mu karkare, yana da kyau mu mika shawarwarinmu ga masu lura da wannan gida, don kamar yadda Hausawa ne ke fadi – kogi bai kin dadi. Akwai wasu dakuna (Web Pages), da ke da ‘yan matsaloli, kasancewar suna dauke ne da makaloli masu amfani, ya kamata a duba su, don taimaka ma masu ziyara samun saukin isa garesu. Na samu Error 404, yayin da nayi kokarin shiga dakunan da ke dauke da wadannan kasidu: 1) Telecommunication in Kano, 2)Sharia Law and Western Reaction, 3) Sickle Cell Desease. Bayan nan, zai dace a rinka dora sabbin wakoki a sashen ANA, ganin cewa duk karshen wata suna fid da sabbin wakoki kan al’amura daban-daban masu amfani. Domin wakokin da ke nan duk na baya ne, a iya zuba su a rumbu, a mayar da makwafinsu. Akwai kuma matsala wajen sauraron jakunkunan sautin karatuttukan da aka sanya da wakokin Imfiraji. Basu budowa, kuma ga alama ina ganin Broken Links ne. zai dace a gyara musu zama don amfanin masu ziyara. Shawara ta karshe kuma ita ce, in da hali (na san ba abu ne mai sauki ba, musamman ga mai lura da gidan yanan sadarwa irin wannan) a budo wani sashe na labaru zalla, kan Kasar Kano, in da mai ziyara zai samu sabbin labaru kan abinda ke faruwa a wannan gawurtaccen birni mai cike da dimbin albarka. Allah kara taimakawa, Ya kuma sa wannan aiki a mizanin ayyukanmu baki daya, amin.

Sabbin Mudawwanai

Kamar yadda muka sanar, wasu sun fara aiko da adireshin Mudawwanan da suka gina, kuma har sun ma fara watsa ra’ayoyinsu tuni. Akwai Malam Shehu Mustapha Chaji, za a same shi a http://shehuchaji.blogspot.com. Sai kuma Malam Muntaka Abdul-Hadi, wani Bazazzagi, shima za a sameshi a http://anguwarfatikaonline.blogspot.com. Na san akwai ‘yan uwa da ke hankoron ginawa, kada a mance, a aiko za mu sanar da yardan Allah. Daga karshe, ina mika godiyata ga dukkan masu bugo waya ko aiko da sakon text ko Imel. Na gode!

Friday, May 18, 2007

Ziyartan Gidajen Yanan Sadarwa #1

Kasidar Makon Jiya:

Ga dukkan alamu kasidar makon da ya gabata tayi tasiri matuka, kamar kasidun sauran makonni. Na gane hakan ne daga yanayin sakonnin waya da Imel da kuma kira da wasu daga cikin masu karatu suka yi ta yi. Hakan har wa yau na dauke ne da bukatun neman Karin bayani ko godiya, kamar dai yadda aka saba. Don haka na ce bari mu dan killace rabin shafi don jawabi kan biyu rak daga cikin wadannan bukatu, kafin mu shiga sabon babin wannan mako.

Yanayin Girman Wayar Salula


Da akwai tambaya kan ko zai iya yiwuwa mutum ya aika da jakan sako (attached file) daga akwatin Imel dinsa, ta hanyar wayar salula? Wannan, kamar yadda na shaida ma mai neman Karin bayani, ya danganta ne kacokan da irin girman mizanin wayar salular. Sai kuma girman sakon da za a aika. Da farko dai abinda zamu lura da shi shine, wayar salula ta sha banban da kwamfuta, wajen girman mizani da yawan karikitan da ke taimaka mata sadar da sako. Don haka idan kana son wayar da zata rinka taimaka maka wajen aikawa da jakunkunan bayanai ta hanyar Imel, idan ka tashi saya sai ka yi ma masu sayarwa bayanin irin abinda kake bukata. Wayoyi irin wadannan na da matukar tsada, kuma zaka samu suna da girman jiki.

Tafi Sannu Kwana Nesa

Idan ka fara amfani da fasahar Intanet da hanyar wayar salularka, zaka ga banbanci wajen budowan shafi da rufewa da dai sauransu, kasa da yadda ka saba gani idan a kan kwamfuta kake lilo. Wannan na faruwa ne saboda mizanin wayar ba daya yake da na kwamfuta ba. Sannan ka tuna cewa kana amfani da wayarka ne a matsayin makalutun sadarwa (modem), wanda ke zuko sigina daga jikin Uwar Garke (Server), don shigar maka da shi a matsayin harrufa da hotuna ko makamantansu. Don haka dole ne a samu tsaiko. Amma a galibin lokuta, zaka samu masu mashakatar tsallake-tsallake (cyber café) na samun sigina ne daga tauraron dan Adam ko kuma Broadband, a takaice. Wanda shi ya fi sauri da hanzari wajen zuko sigina. Don haka sai a yi hakuri.
………………………………………………………………………………….................

GAMJI.COM (
http://www.gamji.com)

A wannan mako zamu fara kai ziyara ne zuwa wasu gidajen yanan sadarwa a giza-gizan sadarwa ta duniya, don samun wuraren yawo da kuma sawwake ma kawunanmu jigilar neman gurabun shakatawa ba tare da dogon yawo maras ma’ana ba. Idan mai karatu bai mance ba, a kasidar Waiwaye Adon Tafiya, mun nuna muhimmancin sanin wuri da abinda mutum yaje yi a duniyar gizo. Domin wuri ne mai matukar fadi, cike da abubuwa masu kama da juna amma asalinsu da nau’in dabi’arsu ta sha banban. In kuwa haka ne, kenan akwai bukatar sanin inda mutum zai je, me zai yi, kuma me yake ko yaje nema, don guje ma bacewa ko walagigi. Wannan tasa zamu samu makonni uku nan gaba, don kawo bayanai da samfurin wasu gidajen yanan sadarwa da mai karatu zai so a ce can yake kashe dare ko rana, wajen amfanin kudinshi da lokacinshi. A yau zamu fara da gidan yanan sadarwan GAMJI.COM, in Allah Ya yarda.

Gidan Yanar, Kacokan:

Wannan gidan yanan sadarwa ginanne ne, kayatacce, wanda kuma aka gina da kwarewa irin ta ilimin manhajar kwamfuta, watau Computer Programming Skills. Duk da yake akwai ilimin gina gidan yanan sadarwa na musamman, ta amfani da fasahar Hypertext Markup Language (HTML), a yanzu masana kan ilimin manhajar kwamfuta (Computer Programmers) sun kwace fagen. Don yanzu galibin gidajen yanan sadarwan da ke giza-gizan sadarwa ta duniya da wannan fasaha ko ilimi aka gina su. Domin masu wannan ilimi ne suka kirikiro masarrafa irinsu Dreamweaver, Frontpage da dai sauransu. Gidan yanan sadarwan Gamji na dauke ne da Frames a matsayin babban fuskan da ke zauren gidan. Shi Frame wani kwarangwal ne da ake ginawa a makala shi a saman zauren gidan yanan sadarwa, ta inda duk dakin da ka shiga a gidan, ba zai bace maka ba, zaka ci gaba da ganinsa. Da zaran ka shigo Gamji, abin da za ka fara cin karo dashi shine tambarin Bismillaahir-Rahmaanir-Rahim, wanda aka lika cikin harshen larabci. A kasan basmalan ne zaka ga Home a tsakiya, Disclaimer daga dama, sai kuma Chatroom daga hagu. Dukkan wadannan a saman Frames suke. Don haka duk shafin da ka budo a gidan yanan, zaka ga wannan bayani yana binka. Frames kenan. A dore yake a saman shafin zauren gidan gaba daya, don haka duk inda ka bude, zai kasance a kasansa. Daga nan kuma sai aka kasa zauren, wanda ke kasan Frames, zuwa bangare hudu, daga sama zuwa kasa, kuma wadannan bangarori ne suka kunshi dukkan abubuwan da ke cikin gidan yanan sadarwan gaba daya.

Me Ke Ciki?

Akwai tarin bayanai wadanda suka shafi makaloli (Articles), da hotuna, da sauti da kuma rariyar likau (links). Bangaren farko daga hagu, zaka samu tarin bayanai na makaloli da mutane ke aikowa ana dorawa don masu karatu da nazari. Wadannan kasidu ko makaloli na samuwa ne daga hanyoyi biyu; hanya ta farko ita ce ta masu aikowa gama-gari, irinka iri na. Idan kana son duniya taji ra’ayoyinka, sai ka aika ma Uban Gidan Yanan a
webmaster@gamji.com. Ka tabbata ka aika da cikakken adireshinka. Zasu buga, don a karanta. Hanya ta biyu kuma ita ce, ta hanyar marubutan Gamji, watau Gamji Writers. Gamji na da marubuta da dama; wasu na raye, wasu kuma sun riga mu gidan gaskiya. Akwai Muhammad Haruna (shahararren dan jarida), marigayi Wada Nas, Marigayi Abubakar Jika, Mr. Mobolaji Aluko, Mr. Paul Mamza (Malami a ABU), Malam Aminu Magashi, Dr. Aliyu Tilde da dai sauran marubuta da dama. Wadannan marubuta ne na musamman da Gamji ke da su. Kuma kasidunsu ne ake watsawa a bangaren hagu da ke zauren gidan yanan. A bangaren da ke biye kuma, takaitattun labarai ne da suka shafi Nijeriya gaba daya. Wadannan labarai sun hada da babban labari (Editorial) na jaridun Nijeriya, da muhimman labaran cikin gida, na kasa, da labarai daga jihohin Nijeriya, da labarai musamman kan siyasa, sai labarai kan wasanni (sports). A wannan bangare, ba labarum karara zaka gani ba, a a, rariyar likau ne, wadanda zasu kai ka inda zaka samu labaru cikakku. Sai bangaren da ke biye da wannan, wanda ke dauke da rariyar likau na takaitattun labarai kan duniya gaba daya. A wannan bangare, an nau’anta labaran ne ta la’akari da gidajen yanan sadarwan su. Akwai labaru daga gidan yanan sadarwan BBC, da na Al-Jazeera sashen turanci, da CNN, sai kuma sauran gidajen yanan sadarwa da ba wadannan ba. Dukkan labaran na samuwa ne ta hanyar bin rariyar likau, wanda zai sadar da kai inda kake son zuwa. Sai kuma bangare na karshe, wanda ke hannun dama, daga sama zuwa kasa. Shi wannan bangare ne na musamman, inda aka tanada ma masu ziyara musamman daga wasu kasashe, don samun bayanai kan hanyoyin kasuwanci a Nijeriya ta hanyar jaridun Nijeriya irinsu Daily Champion, Daily Independent, Daily Sun, Leadership, Newswatch, Punch, Guardian, The News, Triumph, Vanguard, Weekly Trust, da Al-Mizan. Har wa yau, a kasa an tanadi wasu gidajen yanan sadarwa na musamman irinsu EFCC, Gumel, Kanoonline, NigerDelter, Amanaonline, da Arewa Online. Wadannan su ne abubuwan da ke tattare a Gamji.com.

Manufa:

Ga duk wanda ya saba shiga wannan gidan yanan sadarwa ta Gamji, zai fahimci cewa duk wannan jigila da suke yi, manufarsu shine baiwa mai karatu daman samun bayanai ko labaru cikin sauki, a tattare a wuri daya, ba tare da kayi ta yawace-yawace ba wajen neman labaru. Idan ka shiga Gamji, zaka samu dukkan labarun da kake bukata. Idan ma bincike kake son yi, na tabbata sai ka gaji da kasidu wadanda zasu taimaka maka wajen kafa hujjoji kan abinda kake bincike a kai. Za ka samu kasidu kan siyasar Nijeriya, tattalin arzikin kasa, addini, al’adu, zamantakewa, shakatawa, shugabanci da dai sauransu. Wadanda suka fi kowa amfana da Gamji su ne galibin ‘yan Nijeriya da ke kasashen waje. Domin a nan suke samun dukkan bayanai duk safiya ko yammaci. Na sha buga waya ko aika ma wasu abokanai na da ke turai waya ko sako don sanar da su wani sabon abu da ke faruwa a gida Nijeriya, sai su ce mani ai sun karanta labarin a Gamji. Sau tari ire-iren kasidu ko labarun Gamji ne za ka ta cin karo da su a majalisun tattaunawa ana yadawa.

Shahara:

Alal hakika gidan yanan sadarwan Gamji ta shahara fiye da yadda mai karatu ke zato, daga Nijeriya har wajenta. Wannan a fili yake. Biyu daga cikin abubuwan da suka haddasa haka kuwa su ne; nau’in bayanan da ke ciki (labaru, kasidu, makalu da sauransu), da kuma Zauren Hira da Tattaunawa (Chat Room), in da galibin masu ziyara kan yi rajista don zuwa hira da tattaunawa da sauran maziyarta ‘yan uwansu. Saboda yawan masu ziyara a kullum da wannan gidan yanan sadarwa ke samu, babban gidan yanan sadarwa ta kasuwancin Intanet ta duniya, watau AMAZON.COM (
http://www.amazon.com), ta baiwa Gamji lambar yabo na kasancewarta na daya a sahun gidajen yanan sadarwan da ke Nijeriya, wajen samun mafiya yawan maziyarta a kullum. Har wa yau, idan mai karatu ya shiga gidan yanan sadarwan sashen Hausa na BBC (http://www.bbc.com/hausa), zai ga cewa bayan Gamji, babu wata gidan yanar da suka lika gidan yanansu da ita, sam sam. Sannan idan aka zo kan gidan yanan sadarwan da ke makare da tarin bayanai na gida Nijeriya zalla, wadanda ‘yan Nijeriya ne suka rubuta (a ko ina su ke), watau Local Content a takaice, a nan kuma Gamji ce ta zo ta biyu, a dukkan gidajen yanan sadarwan da ke Nijeriya. Wannan ke nuna irin karbuwan da Gamji ta samu a duniya gaba daya.

Uban Gidan Gamji:

Bayan duk mai karatu ya ji wannan, watakil zai so jin ko wa ke da Gamji? To a takaice dai ba wata kungiya bace ko wata jiha daga jihohin Nijeriya ta kafa wannan gidan yanan ba. Mai wannan gidan yanan sadarwa wani bawan Allah ne, mai suna Dr. Ismaila Iro (PhD), masanin kwamfuta da manhajojinta (Computer Programmer). Yana zaune ne a kasar Amurka, duk da cewa yana nan Nijeriya a halin yanzu. Shi ya gina gidan gaba daya, ya kuma dora a giza-gizan sadarwa ta duniya, don amfanin al’umma. Kuma shi ne Uban Gidan (Webmaster). A kullum shi ke lura da gyatta kasidu da labaru da makalu, don kayatar da masu ziyara. Wanda ke taimaka masa a nan gida Nijeriya kuma shine Malam Magaji Galadima, shi ma wani mahiri ne a fagen kwamfuta da manhajojinta. Malam Magaji ne ke lura da tafiyar da dukkan wani abinda ya shafi Gamji ta bangaren Nijeriya. Kuma duk wannan aiki suna yinsa ne a matsayin kyauta ga jama’a, ba mai biyansu ko sisi. Wannan na daya daga cikin abinda ya kamata mu rinka dabbaka shi; duk lokacin da Allah Ya hore maka wata kwarewa kan ko mene ne, yana da kyau ka ciyar da al’umma don ita ma ta karu. Allah saka musu da alheri, amin.

Shawarwari:

Kafin mu karkare zan so sanar da mai karatu wani abinda ke da muhimmanci dangane da wannan gidan yanan sadarwa ta Gamji. Tarin kasidu ko makalolin da ke makare a ciki, ba kadan bane, gaskiya. Ina da yakinin cewa idan aka tattaro su, aka buga su a matsayin littafi, zasu gina babban dakin karatu mai zaman kansa, tabbas. Don haka na ke son ba masu wannan gidan yanan shawara wajen karfafa tsaro (security) musamman a banganren rumbum kasidu (archives). Domin na san wani dan ta’adda (hacker/cracker) ya so rushe rumbun gaba daya, wajen shekarar 2002 in ban mance ba. Don haka a kara tsaro ta wannan bangare. Shawara ta biyu kuma ita ce, a yi kokarin sanya manhajar Matambayi Ba Ya Bata (Search Engine Programme), wanda zai rinka taimaka ma mai neman bayanai (musamman kasidu) ba tare da bata lokaci ba. Duk da yake an shirya kasidun baya ne a tsarin shekara-shekara, amma samun tabbataccen rumbu da kuma manhajan da zai taimaka wajen zakulo kasidu masu nasaba da abinda ake nema zai dada taimakawa. Allah sa mu dace baki daya, amin.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)
Off Lagos Crescent, Garki II
Abuja. 080 34592444
absad143@yahoo.com salihuabdu@yahoo.comhttp://fasahar-intanet.blogspot.com, http://babansadiq.blogspot.com

Friday, May 11, 2007

Sa-in-sa Tsakanin Google Inc. da Hukumar Kasar Thailand

Kamfanin Google Inc. mai gidan yanan sadarwan Google da Youtube, ta mayar da jawabi kan cajin da Hukumomi a kasar Thailand suke mata na rashin girmama sarkin kasar, sanadiyyar wasu bayanai na bidiyo da gidan yanan sadarwanta na Youtube) ya watsa masu nuna cin mutunci ga gwamnati da kuma sarkin kasar Thailand gaba daya. Wannan tasa kasar Thailand ta rufe wannan gidan yanan sadarwa, babu mai iya shiga daga kasar, sanadiyyar wannan abu da ta kira "cin mutumci da rashin lura da hakkin sarkinsu." A cikin jawabin da ta fitar wannan mako, kamfanin Google Inc. tace ai ba dukkan faya-fayan bidiyon da aka watsa bane suka keta hurumin mai martaba ba. Cikin goma sha biyu da aka watsa, hudu daga ciki ne, a cewar Google Inc. suka nuna cin mutunci ga sarki. Sauran na shagube ne ga gwamnati kan abinda ya shafi mu'amala da bakin wasu kasashe da ke zaune a kasar.

Kasar Thailand dai a halin yanzu ta rufe wannan gidan yanan sadarwa na Youtube, kuma ta bukaci da a sanar da ita wanda ya zuba wadannan faya-fayai a gidan yanan. Gwamnatin sojan kasar Thailand dai ta kwace karagan mulki ne daga tsohon shugaban kasan, wanda tayi ikirarin cewa ba ya girmama mai martaba sarki, a shekarar da ta gabata. Za a samu karin bayani a nan.

Fasahar Intanet a Wayar Saluala!

Musabbabi:

Duk da cewa wannan shafi an killace shi ne musamman don kayayyaki da hanyoyin fasahar sadarwa na zamani, a tabbace yake cewa fasahar sadarwar da tafi samun shuhura ita ce Fasahar Intanet. Sai dai kuma wannan ba laifi bane, musamman idan mai karatu ya koma ya kakkabe kurar da ke saman tsoffin bugun jaridar AMINIYA da ya karanta a baya, musamman wanda kasidar farko mai taken “FASAHAR INTANET (1)” ta fito a ciki, zai ga inda muka sanar da cewa kasidun da zasu bayyana a wannan shafi zasu yi ta bayanai ne kan alakar da ke tsakanin dukkan fasahan sadarwan zamani, musamman tsakanin Intanet da sauran iyaye da yayyai da kuma kakanninsa, irinsu Radiyo, Talabijin, Jaridu, Mujallu da sauran danginsu. Da wannan dalili, a bangare daya, da kuma sakonnin text da da Imel da waya da ake bugo mani ta hanyar Salula, a daya bangaren, ya sa na ga dacewar assasa kasidar wannan mako kacokan kan alakar da ke tsakanin wayoyin salula ko tafi-da-gidanka masu tsarin Global System of Mobile Communications (GSM), da Fasahar Intanet; yadda ake shiga a yi lilo da tsallake-tsallake da sauran bayanai da ke da nasaba da wannan alaka.

Wayar Salula da Karikitanta

Idan masu karatu basu mance ba, a kasidarmu mai taken “Kwamfuta da Manhajojinta”, mun sanar da cewa “kwamfuta na tattare ne da manyan bangarori guda biyu; bangaren gangar jiki, wanda aka fi sani da Hardware, a turance. Sai kuma bangaren ruhi ko rai, wanda ake kira Software, shi ma a turance. To haka ma wayar salula take. Gangar jikin shine wanda muke gani, kwarangwal din, wanda ya kunshi batir, da injin da kuma gangar marfin wayar. Wannan bangare shine wanda ke rike da bangare na biyu, watau ruhin, wanda kuma ke da bangarori biyu, daya ya ta’allaka ne da daya. Na farkon shine babban ruhinta, wanda ke samuwa idan aka sanya mata batir, aka kuma kunna ta. Da zaran ka kunna, zata umarce ka da ka sanya mata ruhinta na biyu, watau katin SIM (insert SIM). Idan ka sanya mata katin SIM, wanda shine bangare na biyu, daga nan zaka iya samun isa cikin wayar don yin duk abinda zaka iya yi, na kiran waya, amsa kira daga wasu, shigar da lambobin wayan wasu, da sauran ayyuka.

Idan ka sanya ma wayar salula katin SIM, ka kunna, to nan kuma za a sake samun bangarori biyu a cikin ruhin da ya samu tsakanin ruhin wayar da wanda katin SIM ke dauke dashi. Zamu bayar da misali da wayar tafi-da-gidanka na kamfanin Nokia, don tafi shahara. (masu Samsung da SonyErricsson da Siemens, ku gafarce ni). Bangare na farko ya kunshi abinda ake kira “Network Services”, a turance, watau hanyoyin amfani da waya, wadanda kamfanin Sadarwa ne ke bayar da su, a kunshe cikin katin SIM. Idan ka shiga Menu zaka same su. Wasu daga cikin su sune: Messages (hanyoyin karba da kuma aika gajerun sakonni), Call Register (rajistan lambobi ko sunayen masu bugo waya ko ka buga musu), Settings (Wajen tsara dukkan hanyoyin mu’amala da wayar), Web (hanyar shiga yanar gizo ta duniya, ko Intanet, a takaice), MTN Services ko Magic Plus (hanyoyin samun labarai takaitattu ta hanyar kamfanin waya). Wadannan a takaice sune hanyoyin da yanayin amfani da su ya danganta ne da kamfanin da kake amfani da katinsu. Bangare na biyu kuma sune hanyoyin da kana iya amfani dasu ba tare da taimakon kamfanin waya sun taimaka ko kuma sun caje ka ba. Su kuma sun hada da: Contacts (wajen ajiye sunaye da lambobin abokan hulda), Settings (wani bangarenshi, irinsu: themes, tones, display, time and date, my shortcuts, call settings, phone settings, enhancements, configurations, da kuma security), Gallery (wajen adana jakunkunan sauti, hotuna, wakoki, sautin karban kira da sakonni – tones), Media (wajen Radio, da kemara, rekoda da sauransu), Organiser (wajen kalanda, jakar tafi-da-gidanka – wallet – da kuma alarm), da kuma Application (wajen manhajojin lissafi ko raskwana – calculator – manhajan wasan kwamfuta – games – da agogon kididdiga ko kiyasi, watau stop watch/timer). Wadannan su ne ababen da ke tattare da wayar salula ta Nokia ‘yar madaidaiciya, ba mai dan Karen kudin tsiya ba. To mene ne damuwanmu a yanzu?

Wireless Application Protocol (WAP)

WAP, ko kace Wireless Application Protocol, ita ce ka’idar da ke lura ko sadar da sakonni (na murya ko bayanai) ga na’urorin fasahar sadarwa na tafi-da-gidanka (Wireless Mobile Communication). Idan mai karatu bai mance ba, a kasidarmu mai taken “Hada Intanet”, mun yi bayanin cewa daya daga cikin kayayyakin da ake bukata wajen sadar da kwamfuta da kwamfuta ‘yar uwanta, shine wayan kebul (cable), a gajeren zangon sadarwa (Local Area network – LAN). To amma a tsarin Wide Area Network (WAN), wanda shine tsarin da ke sadar da sakonni tsakanin na’urorin fasahar sadarwa a dogon zango, ka’idar WAP ce ke da hakki. Ita WAP ka’ida ce ba na’ura bace kamar kwamfuta da muke gani. Ka’ida ce ta sadarwa tsakanin kayayyakin sadarwa na tafi-da-gidanka irinsu wayar salula, kwamfutar tafi-da-gidanka (Laptop/Notebook) da manyan na’urorin sadarwa makamantansu. Tun ran gina irin wadannan na’urori ake shigar da wannan ka’ida cikin gangar jikin su. Wannan ka’ida ta WAP na cikin dukkan wayoyin salula na tafi-da-gidanka. Kuma tana da bangarori biyar ne wadanda dukkan wani sako na sauti/murya (voice) ko bayanai (text) ke bi, don saduwa da na’urar da aka tunkuda shi. Bangarori hudu ke isar da sakon, daya bangaren kuma ke taimakawa wajen budowa. Bangarorin su ne: WAP Datagram Protocol (WDP), wanda ke aikawa da sakonnin text (SMS) da na GPRS; Wireless Transport Layer Security (WTLS), mai taimakawa wajen tsare sakonnin da ake aikawa, don kada wani dan ta’adda ya tsare su a hanya; WAP Transaction Protocol (WTP), wanda ke jaddada aikin WDP, wajen isar da sakon kamar yadda aka aiko su; WAP Session Protocol (WSP), wanda ke taimakawa wajen isar da sakon da ake karba ko aikawa ta hanyar sadar da manhajojin da zasu karbi sakon, a na’urar mai aikawa da na mai karba. Na karshe kuma shine Hypertext Transfer Protocol Interface (HTTP Interface), wanda ke budo sakon da aka aiko, ta hanyar masarrafan lilo da tsallake-tsallake (Browser). Dukkan wadannan ka’idoji a jikin na’urar sadarwa na tafi-da-gidanka ake gina su, kamar yadda bayani ya gabata. Don haka mai karatu ba zai gansu ba, karara, amma su ne manyan jami’ai. Wannan, a takaice, ita ce tsarin da ke kunshe cikin WAP. Su kuma ka’idojin WAP na aiki ne cikin wayar salula ko kwamfutar tafi-da-gidanka mai dauke da hanyoyin rubutawa da aikawa da sakonni na murya da bayanai, ta hanyar fasahar sadarwa ta Intanet. Wadannan hanyoyi su ne: General Packet Radio Services (GPRS), wanda hanya ce ta aikawa da sakonni cikin gaggawa. Sakonnin sun hada da murya/sauti, rubutu/bayanai da hotuna masu motsi da ma marasa motsi. Wannan tsari na GPRS na samuwa a galibin wayoyin salula na zamani da kuma dukkan kwamfutar tafi-da-gidanka (Laptop). Wannan hanya ta kunshi hanyoyi irinsu USB Port/Cable da Bluetooth da kuma Infrared. Sai kuma Short Message Service (SMS), tsarin da ke taimakawa wajen aikawa da gajerun sakonni na wayar salula, masu amfani da tsarin Global System for Mobile Communications (GSM). A wannan tsari mai wayar salula na iya aikawa da sako daga wayar salularsa zuwa na dan uwansa ko matarsa, iya fadin nisan da transmitter din kamfanin sadarwan ya kai. Misali, duk inda ake da sabis na MTN, kana iya aikawa da sakon SMS har can, a karba, a bude, a karanta, sannan a aiko maka da jawabi kai ma. Wadannan su ne masu nasaba da abinda muke tattaunawa a kai. Don haka zamu tsaya a nan.

Shiga Intanet ta Wayar Salula

Da farko dai, kamar yadda muka sanar, zamu yi misali da wayar kamfanin Nokia ne, wacce ta fi shahara. A Nokian ma zamu dauki Nokia 6230i, don kawo misali. Idan ka tashi shiga Intanet ta hanyar wayar salula, abu na farko da zaka tabbatar shine ko wayar tana da ”Web”, don ba dukkan wayoyi bane ke da wannan tsari. Don tabbatarwa, sai kaje Menu, ka gangara, sai ka ci karo da ”Web”, ko “WAP”, ko “GPRS Services” ko “Login”. Duk wadannan kalmomi ne da wasu kamfanoni ke amfani dashi. Amma kamfanin Nokia na amfani ne da kalmar “Web” a dukkan wayoyinta. Don haka idan ka iso “Web” a Nokia 6230i, sai ka matsa shi, zaka fara cin karo da “Home”, wanda idan ka matsa zai kai ka zauren gidan yanan sadarwan Nokia ne, kai tsaye; sai “Bookmarks”, inda zaka iya adana adireshin gidajen yanan da ka ziyarta kuma suka burgeka; sai “Downloads”, inda zaka samu rariyar likau zuwa wuraren da zaka iya samun muryoyi (Tones) da labulen fuskar wayar salula (Themes) dsr; sai kuma “Last Web Address”, wanda shine zai kai ka gidan yanan sadarwan da ka ziyarta na karshe, a baya, idan ka yi hakan; sai “Service Inbox”, wanda bamu bukatarsa cikin bayaninmu; sai “Settings”, inda zaka tsara hanyoyin yawo ko lilo da tsallake-tsallake a wayarka; sai kuma “Go to Address”, inda zaka shigar da adireshin gidan yanan sadarwan da kake son shiga - shi zamu kira “address bar” a nan; sai na karshe, watau “Clear Cache”, ita “cache” jaka ce da ke adana dukkan aikin da kayi a wannan bangare na “Web” – duk inda ka ziyarta, da yawan shafukan da ka shiga. Sai dai ba za ka iya ganin komai ba, don ita “clear cache” aiki daya kawai take yi, shine share wannan jaka gaba daya. Da zaran ka gama dubawa ka tabbatar da cewa kana da alamar “Web” a Menu dinka, to sai mataki na biyu, shine samun kamfanin sadarwan da ke da tsarin Intanet a Network dinsu. Wannan shine abinda galibin masu bugo mani waya basu fahimta ba sosai; kasancewar kana da wayar salula mai “WAP” ko “Web” a cikin jerin Menu dinta, ba shi ke nuna zaka iya lilo da tsallake-tsallake a ciki ba. Sai kamfanin sadarwanka na da tsarin Intanet. A Nijeriya ina ganin kamfanin MTN da Globacom ne kadai ke da wannan tsari. Idan ka sayi katin SIM din MTN, misali, ka sanya ma wayarka, sai kaje ofishinsu kuma su tsara (configure) maka wayar. Idan suka tsara wayar, zasu aiko maka da sakonnin text guda biyu; na farko zai sanar da kai ne cewa ka adana (save) sakon da za a aiko maka nan ba da dadewa ba; na biyun kuma za a sanar da kai ne cewa an gama hada maka, kuma kana iya amfana da hanoyin mikawa da karban sakonni na MTN a ko ina kaje. Amma akwai sabbin layukan MTN da ake sayarwa yanzu masu 0803, idan ka samu irinsu, to baka bukatan zuwa ofishinsu don su jona ka, muddin wayar salularka na da tsarin “WAP” ko “Web”. Kana sanya katin SIM din kawai zaka ji sakonni sun shigo guda biyu, masu dauke da bayanan da na sanar a sama. Sai ka adana su a cikin wayarka (ka aika dasu Saved Messages, don kada ka mance ka share su idan suna Inbox). Amma idan layin Globacom kake dashi, zaka iya kiransu a layin “customer care”, ko kuma kaje ofishinsu. Da zaran an gama tsara maka wayarka shikenan. Sai lilo da tsallake-tsallake kawai.

Shawarwari

Kafin mu karkare, yana da kyau mai karatu ya fahimci wasu abubuwa dangane da abinda ya shafi yin lilo da tsallake-tsallake a wayar salula. Da farko dai suna cajin kudi, ba kyauta suke bayarwa ba. Duk da yake idan layinka na MTN sabon layi ne, ka iya sa’a cikin dare ka jima kana lilo ba a cire maka ko kwabo ba (na taba sa’an haka na kusan tsawon awa daya a layin Maman Sadiq). Suna caji ne dangane da yawan haruffan da ka karanta ko ka bude, ba wai da yawan mintuna ko awannin da kayi kana lilo ba. Idan ka budo shafuka masu hotuna ne, to za a caje ka sosai, domin hotuna sun fi haruffa yawa da nauyi, a ka’idar na’urar sadarwa. Don haka idan baka bukatar wayarka ta rinka budo maka hotuna a shafukan da kake yawo a ciki, sai kaje “Settings” a layin “Web”, don canzawa (Web = Settings = Appearance Settings = Show Images = No). Idan ba wani tsananin bukata kake dashi ba wajen yin lilo a wayar salularka, ya zama sakonnin Imel kawai zaka rinka dubawa ta nan, don kada cajin ya yawaita. Idan kana son yin awa daya ko sama da haka, zan ba ka shawara da kaje mashakatar tsallake-tsallake kawai, watau “Internet Café”. Bayan haka, duk sanda kayi lilo da tsallake-tsallake (browsing) ta wayar salularka, to sai ka gyatta saitin agogon wayar, idan ba haka ba, zaka ga ta cilla gaba da awa daya. Me yasa? Oho! Daga karshe kuma, sai ka yawaita caja batirinka, domin duk lokacin da ka shiga “Web” ka fara yawo a duniyar gizo, wayarka na daukan kaso mai yawa wajen aiwatar da wani aiki da ya sha karfin mizanin batirin da take zuka a yanayin da ba wannan ba. Sai a kiyaye.

Kammalawa

Wannan shine bayani a takaice. Da fatan masu karatu sun gamsu. Idan da akwai inda ba a fahimta ba, to a rubuto ta text ko Imel, don samun cikakken bayani. Ina mika godiyata ga dukkan masu bugowa don gaisawa ko neman Karin bayani, musamman Malam Rabi’u Ayagi daga Kano, da Malam Muhammad Abbas Jos, da Malam Muntaka Dabo Zaria, da kuma Malam AbdusSalam, shi ma mazaunin Jos. Na gode. Na gode!

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)

Off Lagos Crescent,

Garki II – Abuja.

080 34592444 salihuabdu@yahoo.com, absad143@yahoo.com

http://fasahar-intanet.blogspot.com, http://babansadiq.blogspot.com

Monday, May 7, 2007

Mudawwana (WebLog) #2

Makon Da Ya Gabata:

Idan mai karatu bai mance ba, a makon da ya gabata mun kawo bayanai ne kan Mudawwanar Intanet, watau Web Log, a turance, da tarihinta da kuma yadda ake mallakar mudawwana ga duk mai son yada nasa ra’yin don wasu su karanta a giza-gizan sadarwa ta duniya. Na san da dama cikin masu karatu sun fara himma wajen gina nasu mudawwanar, sakamakon sakonnin da nai ta samu ta Imel da wayar salula da kuma bugowa ma da wasu suka yi, don neman Karin bayani. Haka ake so daman. Wannan na daga cikin abinda nai ta jaddada mana cikin kasidar Waiwaye Adon Tafiya, watau kwatanta abinda aka koya ko karanta, a aikace. Da haka harkan ilimi ya ci gaba a duniya gaba daya. Don haka duk wanda ya fara ginawa, to ya natsu ya karasa. Wanda bai fara ba, ya fara. Wanda kuma ya gama ginawa, ya aiko mana da adireshin don mu ziyarce shi, mu ga abinda yake tallata ma duniya a tsarin tunaninsa. A yau zamu ci gaba da bayanai kan Mudawwana har wa yau, sai dai zamu dan maimaita wasu gabobin bayanan da muka yi, kafin mu zarce, don na fahimci wasu na samun matsala.

Matashiya:

Bayan dogon bayani da muka kawo kan ma’ana da tarihi da kuma bunkasar wannan kebantacciyar hanyar sadarwa, mun nuna ma mai karatu yadda zai iya bude nasa shafin cikin sauki, ba tare da mishkila ba. To amma saboda dabi’ar koyo ta gaji ‘yan kurakurai, wasu basu fahimci tsarin sosai ba. Da farko dai muka ce akwai gidajen yanan sadarwa masu bayar da daman bude Mudawwana kyauta, kamar su LiveJournal (http://www.livejournal.com), Xanga.com (http://www.xanga.com), NewBlog.com (http://newblog.com), Blog.com (http://blog.com), da Blogger.com (http://www.blogger.com/start) na kamfanin Google kenan. Kowanne tsarinsa daban. Mun kuma kawo misali ne da Blogger.com, wanda gidan yanan sadarwan Google ce ke dashi. Muka kuma sanar da mai karatu cewa ba zai iya bude Mudawwana ba sai yana da adireshin Imel, amma in so samu ne ya zama Imel din na Gmail ne. Idan bashi da Gmail, sai ya je http://mail.google.com. Da zaran shafin ya budo, sai ya dubi can kasa daga hannun dama, zai ga inda aka rubuta “Sign Up for Gmail”, sai ya matsa, ya bi ka’idojin da ke tafe a fam din, don samun adireshin Imel na Gmail. Da zaran ka samu, sai ka shigo Zauren Blogger da ke http://www.blogger.com/start, ka shigar da suna (username) da kalmar iznin shiganka (password), ka matsa “Sign In”. Za a kai ka shafin da zaka zabi suna da adireshin Mudawwanarka, wanda da shi za a iya shiga don karanta abinda ka zuba a ciki. Kana gama zaba, sai ka zarce shafin gaba, inda zaka zabi irin kala da kuma tsarin da kake son Mudawwanarka ta kasance da shi. Akwai ginannun kwarangwal (Templates) wajen goma, sai ka zabi daya daga cikinsu. Ka gama kenan, sai kawai ka fara zuba bayanai don wasu su karanta. Amma ka tabbata ka bayar da bayanai kan karan kanka (Biodata), don masu ziyara su san ko waye kai. Nan gaba zamu kawo bayanai kan yadda ake canza ma shafin yanayi gaba daya, zuwa irin tsarin da kake so. Sai dai hakan na bukatar wasu yan dabaru na gina gidan yanan sadarwa. A yanzu dai wadannan sune hanyoyin da ake bi wajen bude mudawwana. Sai ka haddace adireshin Mudawwanarka, kuma ka san cewa duk lokacin da kake son zuba bayanai a ciki, zaka je Zauren Blogger.com ne (http://www.blogger.com/start), ka shigar da suna (username) da kalmar iznin shiganka (password). Za ka iya shiga ma ta Mudawwanarka; sai ka dubi can sama daga hannun dama, zaka ga inda aka rubuta “Sign In”, da ka matsa za a kai ka zauren. Kuma a lura da cewa, adireshin Mudawwana bashi da haruffan “www”, kamar cikakkun gidajen yanan sadarwa. Ga yanda yake zuwa http://sunan-mudawwanarka.sunan-manhajar-mudawwanar.com. Mu kaddara ka bude da sunan “tunanin-zuci, a Blogger.com. Ga yadda adireshin zai kasance: http://tunanin-zuci.blogspot.com. Da fatan an gamsu.

Matambayi Ba Ya Bata

Wani abinda masu karatu zasu so ji shine dukkan Mudawwanan da aka gina su a yanzu (wanda sun zarce Milayan Saba’in da Biyar, kamar yadda muka sanar makon da ya gabata), su na da gidan yanan sadarwan Matambayi Ba Ya Bata (Search Engine Web Site) na musamman da ake neman su ta nan. Idan ba a manta ba, a baya mun yi ta’arifin Matambayi Ba Ya Bata da cewa “gidan yanan sadarwa ne mai dauke da manhajar neman bayanai, wanda ke yawo rariya-rariya don cafko bayanai daga gidajen yanan sadarwan da ke giza-gizan sadarwa ta duniya, yana zubawa a runbun bayanan gidan yanansa, don amsa tambayoyin masu neman bayanai.” Wasu daga cikin ire-iren wadannan gidajen yanan sadarwa ba boyayyu bane. Akwai irin su Google (http://www.google.com), Yahoo (http://www.yahoo.com) da dai sauransu. Ta la’akari da cewa Mudawwana wani kebantaccen gidan yanan sadarwa ne mai dauke da kebantaccen sakon da ya sha banban da na galibin gidajen yanan sadarwan da ke Intanet, wasu masu kwazo sun yi kokarin kirkiro masa nasa gidan yanan sadarwa na Matambayi Ba Ya Bata na kashin kansa, don ba masu sha’awan yawo ko bincike a ire-iren wadannan mudawwanai daman yin haka. A kasidar da ta gabata, mun kawo cewa galibin bayanan da ke cikin Mudawwanan mutane duk ra’ayoyi ne na kashin kai (personal opinions), duk kuwa da cewa galibin gwamnatocin duniya na da Mudawwanai su ma, amma wannan bai banbanta kalan ra’ayin da ke ciki da na talakka iri na. A takaice dai Mudawwana wata kafa ce da mai ita ke fitar da ra’ayinsa karara don kowa ya karanta, hakan na iya faruwa ba tare da bin ka’idojin ilimi ba wajen muhawara ko tattauna mas’ala. Don haka masana fasahar Intanet ke shawartan duk mai son jin ra’ayin mutane tsagwaronsa, to ya shiga Mudawwanai, sai ya gaji dasu. Wannan tasa aka samu gidajen yanan sadarwa na Matambayi Ba Ya Bata da ke taimaka ma mai yawo a giza-gizan sadarwa nemo bayanai ko nau’ukan bayanan da ke Mudawwanai. Manya daga cikinsu su ne Technorati.com (http://www.technorati.com), da kuma Blogdigger.com (http://www.blogdigger.com). Idan ka shiga wadannan gidajen, zaka samu gamsassun bayanai kan nau’ukan Mudawwanan da ke Intanet. Wannan zai taimaka ma masu son budewa, idan sun kasa tsayar da hankalinsu kan abinda zasu zuba cikin Mudawwanansu. Idan suka gabatar da dan gajeren bincike ta amfani da kalmomin da ke da nasaba da abinda suke sos a Blogdigger.com ko kuma Technorati.com, zasu samu waraka in Allah Ya yarda.

Ingancin Bayanai

Kamar yadda bayani ya gabata a sama, Mudawwana wuri ne da ake zuba bayanai na son zuciya da ra’ayi; shin ra’ayin mai kyau ne ko akasinsa. Abinda zai tabbatar da hakan kuwa shine abinda mai ziyara ke son ji. Domin galibin bayanan da ke cikinsu ba a gina su kan tabbatattun mizanin ilimi ba. Wannan tasa a farkon al’amari wasu ke ganin cewa idan dalibi ne kai mai neman bayanai na ilimi, to kada ka kuskura ka tattaro bayanai daga Mudawwanai, sam sam. To amma a yanzu al’amura sun fara canzawa. Ana samun kasidu da makaloli masu muhimmanci da amfani da aka rubuta su cikin insafi da bin ka’idojin ilimi wajen tabbatar da hujja. Misali, idan ka shiga Mudawwanar Farfesa Abdallah Uba Adamu da ke Jami’ar Bayero, Kano (http://arewanci.blogspot.com), zaka samu kasida da ya rubuta, doguwa mai cike da hujjoji kan batun cire rubutun Ajami da aka yi a kudaden Nijeriya. Wannan ke nuna cewa a yanzu akan samu bayanai ingantattu masu amfani a Mudawannai, ba kamar da ba. Abinda mai neman bayanai zai kiyaye kawai shine, ka tabbata ka samu cikakken bayanai kan wuraren da marubuci ya ciro bayanai da hujjojinsa (references), ba da ka ya rubuta ba. Kada kyale-kyale da tsarin Mudawwanansa su razana ka. Idan ka samu wannan, ba ka bukatan daukan adireshin Mudawwanarsa don ishara.

Fadin Albarkacin Baki da Haddinsa

Duk da yake Mudawwana wuri ne da mai shi zai zage dantse wajen fadin albarkacin bakinsa, a wasu lokuta hakan na bukatan nazari, musamman ta la’akari da yadda hankalin Gwamnatoci da kungiyoyi ya fara komawa kan su don samun ra’ayoyin masu rubuce-rubuce, musamman ma ‘yan jaridu. Domin galibin ‘yan jaridu sun fi zagewa su fadi gaskiyar yadda abu yake ko kuma hakikanin ra’ayinsu kan wani al’amari da ya shafi kasarsu ko siyasar duniya, fiye da yadda suke yi a shafukan jaridunsu da ake bugawa kuma ake yadawa a kan titi. Galibin ‘yan jaridun da ke lura da al’amuran da ke faruwa a kasar Iraki (wanda galibinsu Amurkawa ne ko Turawan Turai), kan mike kafa wajen fadin hakikanin abinda ke faruwa a birnin Bagadaza. Wannan bai yi ma kasar Amurka dadi, sam! Har wa yau, galibin matasan da ke kasashen Larabawa su ma ta haka su ke baza “hakikanin” abinda ke faruwa a kasashensu (akwai Mudawwanai cikin harshen Larabci a http://www.maktoob.com) . Wannan tasa hankalin gwamnatoci, musamman a Gabas-ta-Tsakiya, ya koma kan ire-iren wadannan Mudawannai na yan jaridu marasa-boda (Freelance Journalists). Don haka ba abin mamaki bane kaji an kama dan jarida haka kawai, saboda irin ra’ayin da ya zuba a cikin Mudawwanarsa. Cikin watan Maris hukumar kasar Masar (Egypt) ta cafke wani saurayi da tace ya fadi wasu maganganu da a cewarta cin mutuncin addinin Musulunci ne. Ba na tunanin an sake shi a yanzu. Makamancin wannan ya sha faruwa a kasashe da dama. Wannan ke nuna ma mai karatu cewa yancin fadin albarkacin baki na da iyaka, musamman a kasashen da ke ganin sun ci gaba wajen yanci da ilimi, a farkon al’amari. Don haka, sai a yi taka-tsantsan da abinda za a zuba cikin Mudawwana, duk da yake mu ba mu fara samun irin wannan karan tsayen ba a kasashenmu.

Kammalawa

A nan za mu dakata, sai wani mako. Duk kuma wanda ya bude Mudawwanarsa sai ya aiko mana da adireshin don mu sanar da sauran masu karatu, su leka su ga abinda ya rubuta ko yake tsarawa. Ni ma na bude nawa Mudawwanar na kashin kai na, za a kuma same ta a http://babansadiq.blogspot.com. Har wa yau, da zaran na gama rubuta littafin Intanet da nake kai, zan zuba shi dungurun cikin Mudawwana ta musamman da na bude don masu son karantawa su karanta; Babi Babi. Daga karshe, kada a mance a shigo Mudawannar Fasahar-Intanet in da za a samu dukkan kasidun da aka buga a wannan shafi. Mudawwanar na http://fasahar-intanet.blogspot.com. Dubun gaisuwa da fatan alheri ga ma’aikatan Media Trust masu buga AMINIYA, musamman Hajiya Aishah Umar Yusuf, da kuma Malam Abubakar AbdurRahman. Sai mun sadu mako mai zuwa.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)

Off Lagos Crescent,

Anguwar Hausawa, Garki Village

Abuja.

080 34592444 salihuabdu@yahoo.com, absad143@yahoo.com

http://fasahar-intanet.blogpsot.com, http://babansadiq.blogspot.com