Friday, May 18, 2007

Ziyartan Gidajen Yanan Sadarwa #1

Kasidar Makon Jiya:

Ga dukkan alamu kasidar makon da ya gabata tayi tasiri matuka, kamar kasidun sauran makonni. Na gane hakan ne daga yanayin sakonnin waya da Imel da kuma kira da wasu daga cikin masu karatu suka yi ta yi. Hakan har wa yau na dauke ne da bukatun neman Karin bayani ko godiya, kamar dai yadda aka saba. Don haka na ce bari mu dan killace rabin shafi don jawabi kan biyu rak daga cikin wadannan bukatu, kafin mu shiga sabon babin wannan mako.

Yanayin Girman Wayar Salula


Da akwai tambaya kan ko zai iya yiwuwa mutum ya aika da jakan sako (attached file) daga akwatin Imel dinsa, ta hanyar wayar salula? Wannan, kamar yadda na shaida ma mai neman Karin bayani, ya danganta ne kacokan da irin girman mizanin wayar salular. Sai kuma girman sakon da za a aika. Da farko dai abinda zamu lura da shi shine, wayar salula ta sha banban da kwamfuta, wajen girman mizani da yawan karikitan da ke taimaka mata sadar da sako. Don haka idan kana son wayar da zata rinka taimaka maka wajen aikawa da jakunkunan bayanai ta hanyar Imel, idan ka tashi saya sai ka yi ma masu sayarwa bayanin irin abinda kake bukata. Wayoyi irin wadannan na da matukar tsada, kuma zaka samu suna da girman jiki.

Tafi Sannu Kwana Nesa

Idan ka fara amfani da fasahar Intanet da hanyar wayar salularka, zaka ga banbanci wajen budowan shafi da rufewa da dai sauransu, kasa da yadda ka saba gani idan a kan kwamfuta kake lilo. Wannan na faruwa ne saboda mizanin wayar ba daya yake da na kwamfuta ba. Sannan ka tuna cewa kana amfani da wayarka ne a matsayin makalutun sadarwa (modem), wanda ke zuko sigina daga jikin Uwar Garke (Server), don shigar maka da shi a matsayin harrufa da hotuna ko makamantansu. Don haka dole ne a samu tsaiko. Amma a galibin lokuta, zaka samu masu mashakatar tsallake-tsallake (cyber café) na samun sigina ne daga tauraron dan Adam ko kuma Broadband, a takaice. Wanda shi ya fi sauri da hanzari wajen zuko sigina. Don haka sai a yi hakuri.
………………………………………………………………………………….................

GAMJI.COM (
http://www.gamji.com)

A wannan mako zamu fara kai ziyara ne zuwa wasu gidajen yanan sadarwa a giza-gizan sadarwa ta duniya, don samun wuraren yawo da kuma sawwake ma kawunanmu jigilar neman gurabun shakatawa ba tare da dogon yawo maras ma’ana ba. Idan mai karatu bai mance ba, a kasidar Waiwaye Adon Tafiya, mun nuna muhimmancin sanin wuri da abinda mutum yaje yi a duniyar gizo. Domin wuri ne mai matukar fadi, cike da abubuwa masu kama da juna amma asalinsu da nau’in dabi’arsu ta sha banban. In kuwa haka ne, kenan akwai bukatar sanin inda mutum zai je, me zai yi, kuma me yake ko yaje nema, don guje ma bacewa ko walagigi. Wannan tasa zamu samu makonni uku nan gaba, don kawo bayanai da samfurin wasu gidajen yanan sadarwa da mai karatu zai so a ce can yake kashe dare ko rana, wajen amfanin kudinshi da lokacinshi. A yau zamu fara da gidan yanan sadarwan GAMJI.COM, in Allah Ya yarda.

Gidan Yanar, Kacokan:

Wannan gidan yanan sadarwa ginanne ne, kayatacce, wanda kuma aka gina da kwarewa irin ta ilimin manhajar kwamfuta, watau Computer Programming Skills. Duk da yake akwai ilimin gina gidan yanan sadarwa na musamman, ta amfani da fasahar Hypertext Markup Language (HTML), a yanzu masana kan ilimin manhajar kwamfuta (Computer Programmers) sun kwace fagen. Don yanzu galibin gidajen yanan sadarwan da ke giza-gizan sadarwa ta duniya da wannan fasaha ko ilimi aka gina su. Domin masu wannan ilimi ne suka kirikiro masarrafa irinsu Dreamweaver, Frontpage da dai sauransu. Gidan yanan sadarwan Gamji na dauke ne da Frames a matsayin babban fuskan da ke zauren gidan. Shi Frame wani kwarangwal ne da ake ginawa a makala shi a saman zauren gidan yanan sadarwa, ta inda duk dakin da ka shiga a gidan, ba zai bace maka ba, zaka ci gaba da ganinsa. Da zaran ka shigo Gamji, abin da za ka fara cin karo dashi shine tambarin Bismillaahir-Rahmaanir-Rahim, wanda aka lika cikin harshen larabci. A kasan basmalan ne zaka ga Home a tsakiya, Disclaimer daga dama, sai kuma Chatroom daga hagu. Dukkan wadannan a saman Frames suke. Don haka duk shafin da ka budo a gidan yanan, zaka ga wannan bayani yana binka. Frames kenan. A dore yake a saman shafin zauren gidan gaba daya, don haka duk inda ka bude, zai kasance a kasansa. Daga nan kuma sai aka kasa zauren, wanda ke kasan Frames, zuwa bangare hudu, daga sama zuwa kasa, kuma wadannan bangarori ne suka kunshi dukkan abubuwan da ke cikin gidan yanan sadarwan gaba daya.

Me Ke Ciki?

Akwai tarin bayanai wadanda suka shafi makaloli (Articles), da hotuna, da sauti da kuma rariyar likau (links). Bangaren farko daga hagu, zaka samu tarin bayanai na makaloli da mutane ke aikowa ana dorawa don masu karatu da nazari. Wadannan kasidu ko makaloli na samuwa ne daga hanyoyi biyu; hanya ta farko ita ce ta masu aikowa gama-gari, irinka iri na. Idan kana son duniya taji ra’ayoyinka, sai ka aika ma Uban Gidan Yanan a
webmaster@gamji.com. Ka tabbata ka aika da cikakken adireshinka. Zasu buga, don a karanta. Hanya ta biyu kuma ita ce, ta hanyar marubutan Gamji, watau Gamji Writers. Gamji na da marubuta da dama; wasu na raye, wasu kuma sun riga mu gidan gaskiya. Akwai Muhammad Haruna (shahararren dan jarida), marigayi Wada Nas, Marigayi Abubakar Jika, Mr. Mobolaji Aluko, Mr. Paul Mamza (Malami a ABU), Malam Aminu Magashi, Dr. Aliyu Tilde da dai sauran marubuta da dama. Wadannan marubuta ne na musamman da Gamji ke da su. Kuma kasidunsu ne ake watsawa a bangaren hagu da ke zauren gidan yanan. A bangaren da ke biye kuma, takaitattun labarai ne da suka shafi Nijeriya gaba daya. Wadannan labarai sun hada da babban labari (Editorial) na jaridun Nijeriya, da muhimman labaran cikin gida, na kasa, da labarai daga jihohin Nijeriya, da labarai musamman kan siyasa, sai labarai kan wasanni (sports). A wannan bangare, ba labarum karara zaka gani ba, a a, rariyar likau ne, wadanda zasu kai ka inda zaka samu labaru cikakku. Sai bangaren da ke biye da wannan, wanda ke dauke da rariyar likau na takaitattun labarai kan duniya gaba daya. A wannan bangare, an nau’anta labaran ne ta la’akari da gidajen yanan sadarwan su. Akwai labaru daga gidan yanan sadarwan BBC, da na Al-Jazeera sashen turanci, da CNN, sai kuma sauran gidajen yanan sadarwa da ba wadannan ba. Dukkan labaran na samuwa ne ta hanyar bin rariyar likau, wanda zai sadar da kai inda kake son zuwa. Sai kuma bangare na karshe, wanda ke hannun dama, daga sama zuwa kasa. Shi wannan bangare ne na musamman, inda aka tanada ma masu ziyara musamman daga wasu kasashe, don samun bayanai kan hanyoyin kasuwanci a Nijeriya ta hanyar jaridun Nijeriya irinsu Daily Champion, Daily Independent, Daily Sun, Leadership, Newswatch, Punch, Guardian, The News, Triumph, Vanguard, Weekly Trust, da Al-Mizan. Har wa yau, a kasa an tanadi wasu gidajen yanan sadarwa na musamman irinsu EFCC, Gumel, Kanoonline, NigerDelter, Amanaonline, da Arewa Online. Wadannan su ne abubuwan da ke tattare a Gamji.com.

Manufa:

Ga duk wanda ya saba shiga wannan gidan yanan sadarwa ta Gamji, zai fahimci cewa duk wannan jigila da suke yi, manufarsu shine baiwa mai karatu daman samun bayanai ko labaru cikin sauki, a tattare a wuri daya, ba tare da kayi ta yawace-yawace ba wajen neman labaru. Idan ka shiga Gamji, zaka samu dukkan labarun da kake bukata. Idan ma bincike kake son yi, na tabbata sai ka gaji da kasidu wadanda zasu taimaka maka wajen kafa hujjoji kan abinda kake bincike a kai. Za ka samu kasidu kan siyasar Nijeriya, tattalin arzikin kasa, addini, al’adu, zamantakewa, shakatawa, shugabanci da dai sauransu. Wadanda suka fi kowa amfana da Gamji su ne galibin ‘yan Nijeriya da ke kasashen waje. Domin a nan suke samun dukkan bayanai duk safiya ko yammaci. Na sha buga waya ko aika ma wasu abokanai na da ke turai waya ko sako don sanar da su wani sabon abu da ke faruwa a gida Nijeriya, sai su ce mani ai sun karanta labarin a Gamji. Sau tari ire-iren kasidu ko labarun Gamji ne za ka ta cin karo da su a majalisun tattaunawa ana yadawa.

Shahara:

Alal hakika gidan yanan sadarwan Gamji ta shahara fiye da yadda mai karatu ke zato, daga Nijeriya har wajenta. Wannan a fili yake. Biyu daga cikin abubuwan da suka haddasa haka kuwa su ne; nau’in bayanan da ke ciki (labaru, kasidu, makalu da sauransu), da kuma Zauren Hira da Tattaunawa (Chat Room), in da galibin masu ziyara kan yi rajista don zuwa hira da tattaunawa da sauran maziyarta ‘yan uwansu. Saboda yawan masu ziyara a kullum da wannan gidan yanan sadarwa ke samu, babban gidan yanan sadarwa ta kasuwancin Intanet ta duniya, watau AMAZON.COM (
http://www.amazon.com), ta baiwa Gamji lambar yabo na kasancewarta na daya a sahun gidajen yanan sadarwan da ke Nijeriya, wajen samun mafiya yawan maziyarta a kullum. Har wa yau, idan mai karatu ya shiga gidan yanan sadarwan sashen Hausa na BBC (http://www.bbc.com/hausa), zai ga cewa bayan Gamji, babu wata gidan yanar da suka lika gidan yanansu da ita, sam sam. Sannan idan aka zo kan gidan yanan sadarwan da ke makare da tarin bayanai na gida Nijeriya zalla, wadanda ‘yan Nijeriya ne suka rubuta (a ko ina su ke), watau Local Content a takaice, a nan kuma Gamji ce ta zo ta biyu, a dukkan gidajen yanan sadarwan da ke Nijeriya. Wannan ke nuna irin karbuwan da Gamji ta samu a duniya gaba daya.

Uban Gidan Gamji:

Bayan duk mai karatu ya ji wannan, watakil zai so jin ko wa ke da Gamji? To a takaice dai ba wata kungiya bace ko wata jiha daga jihohin Nijeriya ta kafa wannan gidan yanan ba. Mai wannan gidan yanan sadarwa wani bawan Allah ne, mai suna Dr. Ismaila Iro (PhD), masanin kwamfuta da manhajojinta (Computer Programmer). Yana zaune ne a kasar Amurka, duk da cewa yana nan Nijeriya a halin yanzu. Shi ya gina gidan gaba daya, ya kuma dora a giza-gizan sadarwa ta duniya, don amfanin al’umma. Kuma shi ne Uban Gidan (Webmaster). A kullum shi ke lura da gyatta kasidu da labaru da makalu, don kayatar da masu ziyara. Wanda ke taimaka masa a nan gida Nijeriya kuma shine Malam Magaji Galadima, shi ma wani mahiri ne a fagen kwamfuta da manhajojinta. Malam Magaji ne ke lura da tafiyar da dukkan wani abinda ya shafi Gamji ta bangaren Nijeriya. Kuma duk wannan aiki suna yinsa ne a matsayin kyauta ga jama’a, ba mai biyansu ko sisi. Wannan na daya daga cikin abinda ya kamata mu rinka dabbaka shi; duk lokacin da Allah Ya hore maka wata kwarewa kan ko mene ne, yana da kyau ka ciyar da al’umma don ita ma ta karu. Allah saka musu da alheri, amin.

Shawarwari:

Kafin mu karkare zan so sanar da mai karatu wani abinda ke da muhimmanci dangane da wannan gidan yanan sadarwa ta Gamji. Tarin kasidu ko makalolin da ke makare a ciki, ba kadan bane, gaskiya. Ina da yakinin cewa idan aka tattaro su, aka buga su a matsayin littafi, zasu gina babban dakin karatu mai zaman kansa, tabbas. Don haka na ke son ba masu wannan gidan yanan shawara wajen karfafa tsaro (security) musamman a banganren rumbum kasidu (archives). Domin na san wani dan ta’adda (hacker/cracker) ya so rushe rumbun gaba daya, wajen shekarar 2002 in ban mance ba. Don haka a kara tsaro ta wannan bangare. Shawara ta biyu kuma ita ce, a yi kokarin sanya manhajar Matambayi Ba Ya Bata (Search Engine Programme), wanda zai rinka taimaka ma mai neman bayanai (musamman kasidu) ba tare da bata lokaci ba. Duk da yake an shirya kasidun baya ne a tsarin shekara-shekara, amma samun tabbataccen rumbu da kuma manhajan da zai taimaka wajen zakulo kasidu masu nasaba da abinda ake nema zai dada taimakawa. Allah sa mu dace baki daya, amin.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)
Off Lagos Crescent, Garki II
Abuja. 080 34592444
absad143@yahoo.com salihuabdu@yahoo.comhttp://fasahar-intanet.blogspot.com, http://babansadiq.blogspot.com

No comments:

Post a Comment