Sunday, July 29, 2007

Tasirin Fasahar Intanet ga Kwakwalwan Dan Adam (2)

Makon Jiya

A makon da ya gabata ne idan masu karatu ba su mance ba, mu ka fara jero bayanai kan irin tasirin da Fasahar Intanet ke yi ga kwakwalwan dan Adam, saboda irin mu’amalar da ya ke yi da wannan fasaha. Mun yi bayanin irin dalilan da ke haddasa tasirin, da kuma cewa lallai akwai alaka tabbatacciya mai kama da kawalwalniya, wacce ke samuwa tsakanin kwakwalwan dan Adam da kuma asalin duniyar da yake ciki. Mun nuna cewa wannan alaka na samuwa ne sanadiyyar tasirin wannan fasaha da kwakwalwan mai mu’amala. Daga karshe mu ka yi alkawarin kawo abin da hakan ke haifarwa, da yadda za a iya magance wata matsala idan akwai. Saboda yanayin tsarin da bayanan su ka zo, mun ce mai karatu ba zai fahimci in da aka dosa gaba daya ba, sai a wannan mako. Mu na kuma fatan hakan. Don haka yanzu za mu ci gaba.

Sakamakon Alaka

A hankalce duk abinda aka ce yana da wata tasiri kebantacciya sanadiyyar alakantuwansa da wani abu, to dole ne a samu sakamakon da ke haifuwa sanadiyyar alakar, bayan an ji dalilan da ke haddasa hakan kenan. In kuwa haka ne, to mene ne sakamakon tsananin shakuwa da fasahar intanet, mai tabbatar da wata duniya kwakwalwantacciya a cikin tunanin mai yin alakar? A takaice, mutumin da ya mayar da duniyar Intanet a matsayin wata makaranta wacce yake ji da ganin ta a cikin kogon zuciyarsa, kuma ta ke sake a bishiyar kwakwalwansa; da wanda budurwarsa ko abokiyar hirarsa ko abokanansa na samuwa ne kawai ta wannan fasaha; da wanda Intanet ce kasuwarsa, ba kuma ya tuna wata kasuwa ko da kuwa a kofar gidan sa take; da wanda a duk lokacin da yake jin nishadi, bai da wata matattara sai gidan yanar sadarwan wasannin kwamfuta ko Catoons; da mai Lilon Shirme, wajen lasa ma zuciyarsa irin zuman da take bukata duk da dacin da wannan zuma ke tattare da shi a hankali da tunani lafiyayye (ina nufin masu shiga caca da tambola da gidajen yanar sadarwan zinace-zinace da ashararanci), duk wadannan, me ye sakamakon yin hakan ga kwakwalwa da lafiyarsu? Mai karatu kana ina? In kana kusa, to mu dukufa!

Gaggawar Zuci: Tabbas, duk wanda ya saba mu’amala da fasahar Intanet, musamman ma wajen amfani da Imel da kuma Zauren Hira da Tattaunawa, lokacin da zai dabi’antu da Gaggawar Zuci, ba zai sani ba. Za ka wayi gari, duk wani sakon da za ka aika ko karba, idan ba ta wannan hanya bane, sai ka ga nawarsa. Wannan ya faru ne saboda a tunaninka (sabon tunanin Intanet), bai kamata a ce duk wani sako, ta kowace hanya za ka aika ko karba, ya gaza irin gaugawan karba da aikawa irin ta Intanet ba. Duk wani abin da zai sanar da kai cewa “ai komai da muhallinsa; wannan Intanet ne, kuma haka aka tsara shi. Wannan hanyar gidan waya ce, kuma haka aka tsara ta”, zai bace bat daga kwakwalwanka. Don haka komai aka ce za a aiko maka, sai kace sai ta Imel. Duk wata tattaunawa da aka ce za a yi da kai, kace sai ta Chat Room. Haka dai, ka zama wani Walkiya Sarkin gaggawa. Kwanakin baya wata ‘yar uwa ke tamabaya na “Baban Sadiq, wai me yasa aka kasa yin hanyar aikowa da abinci ne ta Intanet?” Sai na bushe dariya. Kin kamu! Watakil wasu lokaci ta kan so ta rinka aika ma aboki ko abokiyar hirarta ne dukkan abinda ta mallaka. Me ya jawo haka? Gaggawar Zuci. Shin wannan abin zargi ne? Za mu ji bayani nan gaba.

Tabbatacciyar Kadaici: Sosai kuwa! Duk wanda ya zama likau ga fasahar Intanet, sai ya lazimci Tabbatacciyar Kadaici. Shi ba hulwa ya shiga ba balle ya yi tsammanin kashfi ko samun lada! Masu karatu su lura da kalmomin: ba kadaici kadai na ce ba, a a, tabbatacciyar kadaici. Wannan ya fi kama masu yin awanni su na gabatar da wani aiki ko hira a kan Kwamfuta, musamman masu gina gidajen yanar sadarwa da kuma masana manhajojin kwamfuta, Computer Programmers. Wani kan yi awanni sama da goma yana kwankwashe-kwankwashe a kan kwamfuta. Ba ya son jin wata sauti, ko da kuwa ta faduwar allura ce. Me yasa? Saboda a cewarsa wannan na iya kawar masa da hankalinsa daga abin da ya ke yi. Bai san cewa wata kyakkyawar budurwa ce mai suna Kadaici ta aure shi ba. Galibin wanda ya saba mu’amala da kayayyakin wasannin kwamfuta ko Cartoons, da masu zuwa musamman don yi hira ko zance da ‘yan mata ko abokanansu, suna kamuwa da wannan cuta ta Tabbatacciyar Kadaici. Sai dai galibi ba su sani. Allah Sarki! Idan a cikin mutane milayan su ke zaune ana gudanar da wani abu, muddin ba su bane ke gudanarwa kai tsaye, yan saurare ne su, to gani suke kamar bata lokacin su kawai su ke. Za su kosa da barin wurin, don ji suke kamar a cikin kwalba su ke. Me yasa? Don duniyar da ke surance a kwakwalwansu kadai su ke kallo. Kuma idan ba a Intanet ba, ba ka da inda zaka samo musu gamsuwa ta hakika. Amma idan su kadai ne da kwamfuta a daki ko mashakatar tsallake-tsallake, wayyo, sai ka shigo har ka gama abinda ya kawo ka (muddin ka iya taku), ba su ma san wani ya shigo ba. Domin a nan kadai su ke samun natsuwa da debe kewa. Ba komai ya kama su ba illa zazzabin kadaici, wanda sauron da ke fitowa daga giza-gizan sadarwa ta Intanet ya cije su, ya kuma zuba musu guban sa cikin kogin jininsu. Ko shi ma wannan abin zargi ne? Za mu ji bayani nan gaba.

Shauki: Shauki fa! Ko ka ce tsananin bege. Ban san wace kalma ce ta fi dacewa ba. Jama’a ku agaza mini; ni Bahaushen (ko Gwarin) Abuja ne. Mene ne banbancin shauki da bege? Ni duk daya na dauke su, illa in ce ya danganta da abinda mutun ke yin abin don shi. Idan mutum ne, nake ganin zai fi dacewa mu ce “bege” - “Ai yana matukar begenta.” Misali. Amma shauki na iya shiga kowane irin abu. Kenan shauki shi ya fi fadi bisa kalmar bege. To shauki din, mu dauke shi. Wannan shi ne mafi girma da hadari daga cikin lalurorin da ke haifuwa sanadiyyar tsananin shakuwa ko sabo da Fasahar Intanet. Larabawa kan kira shi “Al-ishqu”. Amma a turancin Intanet, mu kan kira shi Internet Addiction. Watau tsananin alakantuwa da sabo ko jarabtuwa da Fasahar Intanet. Tabbas, lalurori biyun da su ka gabata duk nau’i ne na wannan addiction din, amma shauki shi yafi dacewa da a kira shi da kalmar. Domin ya kunshi dukkan biyun da ke sama. Shauki ne zai sa mutum ya dabi’antu da gaggawar zuci, don gani ko jin muryan wanda ko abinda yake so. Haka kuma, shi zai sa mutum ya ji cewa idan ba kadaituwa ya yi da abinda yake shauki ba, to ba zai samu cikakkiyar natsuwa tsakaninsa da abin bege ko shaukinsa ba. Ina fatan mun fahimta yanzu. Shi shauki na samuwa ne sanadiyyar tabbatacciyar dadewa ana amfani ko mu’amala da Fasahar Intanet. Ba wai ta yawan shekaru ake nufi ba, a a, yawan kasancewa tare da fasahar sanadiyyar himma da kuma muhimmancin abin da ake gudanarwa a kansa ne ke haddasa wannan illa. Wanda ya kamu da wannan matsala na iya kamuwa da hakikanin zazzabi idan bai samu mu’amala da Intanet ba. Kai wasu ma har sumewa suna yi, saboda tsaban shakuwa. A halin yanzu akwai mutane da dama da su ka samu matsololi irin na tunani da shauki saboda tsananin alakantuwa da wannan fasaha ta Intanet. Wasu sun haukace, wasu sun susuce, wasu kuma ga su nan dai; ba yabo ba fallasa. Ba dukkan masu shauki ne ke kamuwa da wannan matsala a lokaci guda ba; daraja-daraja ne abin. Akwai sabon-shiga, wadanda saboda Allah-Allah da su ke yi a ce sun saba da wannan Fasaha, sai su kasa mallakar hankalinsu. Duk safiyar Allah, su na kan kwamfuta. Duk yinin Allah, su na kan kwamfuta. Duk yammacin Ubangiji, su na kan kwamfuta. A kullum jin su suke a zabure, sai kace dawakan yaki. Duk in da su ka ga wani adireshin Imel ko gidan yanar sadarwa, sai sun kwafa, sun kuma yi mu’amala da mai su. Idan su ka mallaki kansu daga baya, za su rage, musamman idan su ka fahimci abinda su ke son fahimta. Amma idan su ka kasa mallakan hankalinsu waje daya kuma fa? To za su zarce mataki na biyu, wanda ke kunshe da tabbatacciyar kadaici. Mun yi bayanin sa a sama. A wannan mataki, su na baina-baina ne, in ji Larabawa. Tsakanin Gizo da Koki! Idan har yanzu ba su mallaki tunaninsu ba su ka tsara abin da su ke son yi da wanda ba su bukata, to sai matakin karshe, watau tozon shauki kenan. A wannan mataki kam, ko da sun fahimci abinda su ke son fahimta, daga baya ne, wai sadaka da bazawara. Rabuwa da Intanet zai musu wahala. Lokacin da na fara mu’amala da wannan fasaha shekaru kusan bakwai da su ka gabata, na kai mataki na biyu, amma Allah yai min gyadan dogo; kasa ‘yaya sama ‘yaya. A mataki na uku ne mu’amala da fasahar Intanet ke zama ma mutum farilla irin ta dabi’a; idan bai yi ba, gani yake kamar Allah zai tambaye gobe kiyama. Wannan shi ne matakin tsananin shauki da bege, wanda babu mai iya goge tasirinsa a zuciyar wanda ya kamu, sai a hankali. Wannan, ba sai mun je kasa ba, abin zargi ne kai tsaye. Domin da farko dai ya shafi lafiyarka kai tsaye, tun da har an fara kawowa ga sumewa. Yana kuma iya hana ka gabatar da duk abinda zai amfane ka, a wajen Intanet; musulmi ne kai ko ba musulmi ba. Bayan duk mun ji wannan, to ina mafita?

Mafita

Kamar yadda kowa ya sani ne, ba a kaddara cuta ba, sai da aka halicci maganinta. Ma’ana duk lakacin da ka ji an ce ga wata cuta, to maganinta ya riga ta isowa. Illa kawai ya danganta da darajar ilimin masu wannan zamani; sun gano maganin ko ba su gano ta ko ba. To wannan matsala da ke samuwa sanadiyyar zazzabin ciwon sauron giza-gizan sadarwa ta Intanet, na da na ta maganin. Ga wasu hanyoyi nan shahararru:

Tsara Lokaci: A gaskiya duk wanda ka ga ya kai mataki na karshe, musamman a wannan bangaren da muke ciki na duniya, to ba karamin sakaci yayi ba musamman wajen amfani da damar da ya samu, ya kume cinye lokacinsa a haka. A turai samun wannan ba abin mamaki bane, domin su na da ababe da ka iya jawo musu sha’awarsa sosai. Don kusan komai a Intanet a ke gabatar da shi. Shi ya sa a can wajensu su ke da likitoci masu bayar da shawarwari kan wannan cuta na musamman, masu suna: Cyber Counselors. Idan mutum ya iya tsara lokacin da yake dashi, ko da yana da kwamfuta a gidan sa mai hade da fasahar Intanet, ba zai samu kan sa cikin wannan matsala ba. Amma idan bai da tsari, komai nisan da mashakatar tsallake-tsallake ke da shi da gidansa, sai ya tafi. Lokacin da na fara kamuwa, sai in yi tafiyar kusan kilomita goma don yin lilo. Idan kuwa na yi tafiya doguwa zuwa Legas ko Bauchi ko Kano da makamantansu, abin farko da nake fara yi da zaran na sauka masauki shi ne, neman in da mashakatar tsallake-tsallake ta ke. A tsara lokacin shiga Intanet, jama’a.

Kyautata Manufa: Kyautata manufa a nan ba yana nufin zuwa da manufa mai kayau bane kadai, a a, me kake yi wanda zai amfane ka? Wannan zai sa ka shirya su iya gwargwadon lokutan da za ka amfana da su, ba tare da matsala ba. Misali, idan darasi ka ke dauka, ka sanya ma kanka lokaci, idan ba da malami kake ba. Idan gina gidan yanar sadarwa kake, ka sanya ma kanka lokaci iya yadda ka tsara aikin. Idan hira zaka je yi, ka san in da ka dosa. Karatun jarida kake zuwa yi, nan ma ka san ina ne zaka iya samun labaran a tare wuri daya? Domin iya gwargwadon yawonka wajen neman labarai, iya gwargwadon yawaitan tunaninka kan abin da ka gani. Shi yasa kwanakin baya muka kawo bayanai kan wasu gidajen yanar sadarwa kan haka. Mu kyauta manufa tare da tsara abin yi cikin lokacin da muke da shi. Sai mu tsira.

Kankanta Kaskantacce: Wata babbar matsala da masu yin lilo da tsallake-tsallake ba su cika lura da ita ba, ita ce: suna samun kansu cikin kambama wata matsala ko al’amari, wacce a zahirin hankali ba ta cancanci hakan ba. Misali, bai sai wuri ba wajen masifar Intanet, ka ji ana kiran sallah, ko a ce ana kiranka a gida ko wani wuri, wanda zuwanka ke da amfani ga al’umma ko karan kanka, amma saboda kana da wasu ‘yan mintoci kamar talatin da suka rage maka, ko wani abokin hira ya rike ka, kace “a a, bari in gama.” Lokacin da ka zarce, kana iya haduwa da wani ko wata, ko kuma wani abu ya darsu a cikin zuciyarka, wanda bai ma kai mintunan da za ka rufe ba balle abin da ake kiran ka a kai, sai kawai kaji kana bukatar kara lokaci, ba tare da ka tuna da abin da ake kiran ka kan sa ba, da farko. Ka ga nan, ba ka kaskantar da abin da ya cancanci kaskanci ba. Akasin sa ka yi. Ko kuma sai kawai kaji kana sha’awar shiga wuraren tsiyataku da shirme, ga wasu wurare masu amfani ba ka damu da su ba. Karshen ta ka na zuwa can, sai kawai a aure ka ba tare da ka sani ba. Wannan zai sa kusan kullum ka shigo, sai ka dangana da wajen. Alhali wannan wuri bai cancanci wannan muhimmanci da ka bashi ba. Dukkan wannan na cikin ababen da ke haddasa kamuwa da zazzabin cizon sauron giza-gizan sadarwa ta Intanet. Don me ba ka kankanta kaskantacce ba?

Shawarwari: Daga karshe, idan ya zama ka kai matakin karshe na shauki (Addiction), to sai addu’a da neman shawarwari. A wannan bangare na duniya ba mu da kwararrun da su ka wuce Malaman Addini da Dibbu (Likitoci). Domin duk abin da ya shafi kwakwalwa, to zancen ya wuce na shan kwaya ko kuma tsara lokaci. A turai su na da masu bayar da shawara ta hanyar Intanet. To amma a nan idan mutum ya kai matakin sumewa da zazzabi don kawai bai shiga Intanet ba, al’amarin yayi nisa kenan. Don haka sai neman shawarwari daga kwararrun masa kan dabi’a da halittan dan Adam. Allah Ya sawwake, amin.

Kammalawa

A yanzu kam na tabbata mai karatu ya fahimci in da na dosa a makon jiya, matukar fahimta, in ma bai fara tuhumar kan sa ba dangane da irin dabi’ar sa ta mu’amala da fasahar Intanet. Kamar yadda na sanar a makon jiya har wa yau, ina da tabbacin mun fahimci cewa, ba shiga Intanet din ba ne matsala (da an samu tufka-da-warwara kenan), a a, irin tsari da dabi’ar mai shiga ko mu’amalan ne ke sa ya kai wannan mummunan mataki. Don haka Intanet wata ala ce mai matukar muhimmanci, amma a matsayinta na abin aiki, dole ne tana da ka’ido’jin mu’amala. Haka kawai ba ka zuwa ka hau jirgin sama, don kawai ka karanta littafin kera jirgin, sai ka koyi yadda ake komai, tare da tarbiyyar da ke kumshe cikin sana’ar. A nan za mu dakata, sai zuwa wani mako. Duk abinda ba a fahimta ba, to a rubuto. Ina kuma mika godiya ta ga dukkan masu bugo waya ko rubuto sakonnin gaisuwa. A nan zan mika gaisuwa ta musamman ga Malama Habeebah Haroon da ke Jami’ar Jas, mace ta farko da ta fara nuna farin ciki da gamsuwanta ga wannan shafi. Na gode, Allah bar zumunci!

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)
Off Lagos Crescent, Unguwar Hausawa,
Garki II, Abuja. 080 34592444
Fasaha2007@yahoo.com
http://babansadiq.blogspot.com, http://fasahar-intanet.blogspot.com


Saturday, July 21, 2007

Tasirin Fasahar Intanet ga Kwakwalwan Dan Adam (1)

Matashiya:

A cikin kasidar “Amfanin Intanet” da na “Waiwaye Adon Tafiya (1)”, mun gabatar da hanyoyin da mai karatu zai iya taimaka ma kan sa wajen mu’amala da na’urar kwamfuta wacce ke hade da Intanet, don samun saukin lilo da tsallake-tsallake da kuma saukin rayuwa, musamman wajen mu’amala da abokan da yake hulda da su. Sai dai wani abin da ba mu tabo ba tun fara kwararo wadannan kasidu a wannan shafi, shine tasiri ko dangantakar da ke tsakanin Fasahar Intanet da kuma kwakwalwar dan Adam. Shin wace irin dangantaka ke tsakanin fasahar Intanet da kwakwalwan dan Adam? Me irin wannan danganta ke haifarwa, kuma me da me ke haddasa hakan? Ta yaya za a yi kuma a shawo kan hakan, idan da akwai matsala tattare da ita? Wannan zai taimaka ma dukkan mai mu’amala da fasahar Intanet samun saukin rayuwa.

Tsani

Hakika a tabbace yake cewa tasirin akwatin talabijin (TV) ya zarce wanda akwatin rediyo ke da shi, wajen tsumar da mai mu’amala da su a lokuta daban-daban. Domin a yayin da mai sauraron rediyo ke jin sakonnin da ke zuwa daga akwatin rediyon sa, mai kallon akwatin talabijin na sauraro ne tare da ganin hotuna masu motsi. Wannan, a cewar Malaman dabi’a (Psychologists), shi ya fi hanyar farko tasiri wajen da mai mu’amala da shi. Idan mu ka dauki wannan a matsayin mizani, sai mu ga cewa tasirin fasahar Intanet ga kwakwalwan mai mu’amala da ita, ya zarce na rediyo da talabijin. Don me? Saboda tasirin ji, da gani, da kuma mu’amala, duk a lokaci daya. Wannan ta sa duk wani mai mu’amala da fasahar Intanet ta hanyar kwamfuta, na shagala ne saboda wata dangantaka da ke tsakanin kwakwalwansa, da zuciya, masu sarrafa gabobin jikinsa (hannu, idanu da kunnuwa) don kulla alaka tsakaninsa da akwatin talabijin kwamfutar, wacce ke aikawa da sakonninsa zuwa wata tabbatacciyar duniya ta gaibu, mai kama da kawalwalniya. Dankari!

Watakil mai karatu yai tunanin mai ya kawo kalmar “kawalwalniya” cikin zancen, tun da an ce “tabbatacciyar duniya” ce? Domin kowa dai ya san cewa kawalwalniya wani irin yanayi ne a saman titin kwalta ko falallen dutse, wanda idan rana ta yi zafi ka na nesa, za ka rinka ganin alamar ruwa na walwala da malala a saman dutsen ko kwaltan. Idan ba zuwa in da abin yake ka yi ba, kai kace wata korama ce ko rafi na ruwa a saman kwaltan. Sai dai kuma da zaran ka nufi in da abin yake, sai ka iske sunan wani mawaki wai shi Wayam! Bahaushe kan yi amfani da wannan kalma wajen nuna rashin tabbacin abu, ko kuma wata siffa da abin ke da shi irin na rudi; babu tabbas! To mene ne alakar da ke tsakanin tabbaci da rashin tabbaci, a duniyar Intanet? Akwai alaka ko dangantaka. Idan kana mu’amala da fasahar Intanet da dukkan abinda ya shafe ta, kana sawwara wata irin duniya ce a kwakwalwarka, tsakaninka da abokin alakar ka ko manhajar da kake mu’amala da ita. Kuma karshen ta da za ka je in da yake, sai ka ga abin da ba shi bane kake sawwarawa. A wasu lokuta kuma, ga alakar kana yi, da abinda kake da tabbacin shi ne abin da kake alaka da shi, amma kuma idan aka nuna maka hakikaninsa, sai ka ga baya nan, kwata-kwata ma. To me yasa, bayan ga tabbaci ka samu da farko? Oho! Jama’a, ba almara muka zo yi ba wannan mako, ku fahimce ni sosai.

Musabbabai

Domin fahimtar wannan murdadden jawabi mai cike da rikitarwa, yana da kyau mu dubi musabbabai ko in ce ababen da ke haddasa samuwar irin wannan duniyar ko tabbaci mai kama da kawalwalniya, da kuma abin da hakan ke haifarwa ta fannin tunani sanadiyyar dadewar alaka da fasahar Intanet. Akwai dalilai da dama; za mu kawo shahararru ne kawai daga cikinsu, don samun mahanga kan wannan al’amari. Hanya ta farko ita ce ta hanyar Manhajar Hira ko Zauren Hira, wanda a turance muke kira Chatting ko kuma Chat Rooms. Ga mafi yawancin masu shiga Intanet don yin hira da abokanai ko kawayensu ko kuma wasu mutanen da a can za su hadu da su, Zauren Hira wani wuri ne mai wajen kebewa da mu’amala a wani siga da ya sha banban da duniyar zahiri da su ke ciki. Sanadiyyar haka sai ya zama sun samu wani wuri mai kima a zuciya da kwakwalwansu. Manhajojin da aka fi amfani da su wajen aiwatar da wannan hira su ne: Yahoo Messenger! (http://messenger.yahoo.com), ICQ Chat Messenger (http://www.icq.com), Windows Live Messenger (http://www.hotmail.com), da kuma American Online Chat Messenger (http://www.aol.com). Wannan hanya na da tasirin da haduwa fuska-da-fuska ba ta dashi ga masu saduwa. Misali, idan ka na hira da mutum ta hanyar Zauren Hira, akwai wasu maganganu da za ka iya gaya masa, wanda idan tare kuke a fili ba za ka iya ba. Har wa yau, dukkan manhajojin na da wasu alamu da za ka iya aika ma abokin hiranka, don sanar da shi halin da kake ciki na farin ciki (murmushi, dariya da kyacewa da bakin ciki) a lokacin da kuke tattaunawa. Wannan tasa zaurori irin wadannan suka zama wata matattara ta jama’a, wanda alakar da ke tsakaninsu a wannan wuri kan sha banban idan su ka hadu. Hanya ta biyu ita ce ta hanyar dandanli ko majalisun tattaunawa, watau Mailing Lists ko Bulletin Board; hanyoyin tattaunawa kan al’amuran rayuwa ta hanyar wasikar Imel, ko kuma ta hanyar gidan yanar sadarwa masu makalallun zaurorin hiran zo-ka-karanta-ka-tafi, watau Bulletin Board kenan. Yadda mutane ke taruwa su na hira da juna a zauren hira, haka suke tattaunawa a majalisun tattaunawa. Banbancin kawai hanyar farko ta fi tasiri wajen tabbatarwa da kuma dawwamar da alaka tsakanin masu mu’amala. Amma fa hanya ta biyun ita ma ba baya take ba wajen hada alaka mai karfi. Domin har aure a kan yi tsakanin masu mu’amala a majalisun tattaunawa. Kar ka kai abin da nisa; a nan Majalisar Tattaunawa ta Finafinan_Hausa (http://groups.yahoo.com/group/finafinan_hausa) ma an samu wadanda su ka kulla alakar aure a tsakaninsu sanadiyyar wannan hanya. Hakan ke nuna irin tasirin da wannan hanya ke da shi wajen shiryar da kwakwalwarsu da kautar da ita daga kebantuwa da duniyar zahiri kadai, wacce su ke cikinta a “jikince” (da gangar-jikinsu). Sai hanya ta gaba, wacce ke samuwa ta gidajen yanar sadarwa na wasannin kwamfuta, watau Computer Games ko Cartoon. A wadannan gidajen yanar sadarwa, in da mutum zai je ne ya kama mu’amala da wasu halittu ginannu a duniyar jiki ba rai ba, tasirin alaka dawwamammiya na dauke ma masu mu’amala hankali daga duniyar yau da gobe, zuwa wata duniya da mai hankalin ke surantawa a kwakwalwansa. A wadannan hanyoyin wasanni, za ka yi mu’amala ne da mahajojin wasannin kwamfuta (na lissafin wasa kwakwalwa, yake-yake, saye da sayarwa ta mutum-mutumi, dsr). Idan ka saba wasanni ta ire-iren wadannan manhajoji, tasirin hakan na iya sarrafa maka tunaninka zuwa wata duniya mai zaman kanta. Akwai kuma masu zuwa shiga Intanet don gudanar da binciken ilimi kan harkokin rayuwa daban-daban. Da dama cikinsu sun saba aiwatar da hakan, har suka wayi gari galibin bayanin da za su nema don gudanar da bincikensu dole ne ya zo daga Fasahar Intanet, idan ba haka ba, gani su ke bai cika ba wajen inganci. Ina da wani aboki yanzu haka, ko ma’anar kalma ce ta bace masa daga tunani, dole sai a Intanet zai nemo ta. Duk da cewa ga Kamus na turanci a aljihun teburinsa. Amma saboda fitinuwa da zazzabin alakar Intanet, ba ya iya hakurin dubawa. Sai kuma masu shiga Intanet don yin karatu; ya Allah makaranta suka shiga a ciki ko kuwa karanta labaru kawai su ke. Akwai jami’o’i da dama cikin Intanet; masu gudanar da karatu don samun shaidan ilimi kan fannoni daban-daban. Sau tari ko da dalibai ne, za ka samu tasirantuwansu da fasahar Intanet ya janye alakar da ke tsakaninsu da sauran dalibai a makaranta. Duk wani karatu da za su yi, idan ba ta wannan hanya bane, sai yai musu wani iri. Sai wadanda suka mayar da Intanet wata matattara ta karatun jaridu a kullum. Ba za ka ga sun taba sayan ko da shafi daya bane na jarida, amma duk labarin da za ka karanta a kowace jarida ce, za ka iske suna da bayani a kan shi. Masu wannan dabi’a basu sanin lokacin da hakan ke auran kwakwalwansu, har a wayi gari sun zama ‘yan makarantar Intanet. Na kusa da na karshe kuma su ne masu gudanar da saye da sayarwa ta hanyar Intanet, musamman a kasashen Turai da Amurka. Galibin su sai su yi kusan shekara (idan ba wata haja bace wacce ba a samunta a Intanet) ba ka gan su a kasuwa ba, sam sam! Hakan na da nashi tasiri wajen shirya musu wata tafkekiyar kasuwa a duniyar kwakwalwansu, wacce zai yi wahala su same ta a wani bigire na duniya, a zahirance. Sai hanya ta karshe, wacce ke rarake ma mai mu’amala sashen tunaninsa tabbatacce ya bar masa wata duniya kwakwalwantacciya a duniyar Intanet, shi ne ta hanyar abin da na kira Lilon Shirme! Lilon Shirme shi ne duk wani yawo da mutum zai yi a duniyar Intanet mara tabbatacciyar ma’ana da amfani da kuma manufa mai kyau a hankalce, ba ga al’umma kadai ba, a a, hatta ga mai yin ta. Wannan ya hada da yin lilo a gidajen yanar sadarwa na caca, da tambola da kuma shiga gidajen yanar sadarwan batsa da ashararanci. Sabawa da wannan irin lilo mara manufa da ma’ana na da nasa tasiri mai cike da munanan akidar barna da ke darsuwa a kwakwalwar mai yi. Dukkan wadannan hanyoyi na da tasiri daya ko biyu ko ma sama da haka, wajen samar da wata duniya tabbatacciya mai kama da kawalwalniya, a kwakwalwan mai yin lilo da tsallake-tsallake a duniyar Intanet. To a ina alakar ta ke, tsakanin tabbaci da rashinsa? Kuma me ye hakan ke haifarwa wajen sauya dabi’ar mai yi, bayan tsawon lokaci?

Alakar Tabbaci da Rashin sa

Kafin mu ci gaba, ina son mai karatu ya fahimci cewa, kasancewar dukkan hanyoyin da aka zayyana a sama na haddasa samuwar wata irin alaka mai wannan siffa, wacce ke darsuwa a kwakwalwan sa, ba shi ne abin zargi ba, dari bisa dari. A a, ishara ne kawai zuwa ga wani abin da zai iya kawo cutarwa ko jirkita dabi’a, ko kuma akasin sa, iya gwargwadon yadda mai yin hakan ya samu kansa a ciki. Dangane da abin da ya shafi alaka tsakanin tabbaci da rashin tabbaci kan abinda kwakwalwan mai mu’amala ke sawwarawa kuwa, abu ne mai saukin fahimta.

Ga wanda ya saba shiga zauren hira yana zance da budurwansa ko abokanansa (ya taba ganinsu ko bai taba ganinsu ba), dole ya rinka ganinsu, a cikin zuciyarsa ba ta gululun idonsa ba, a a, a kwakwalwance. Wannan kan sa ya rinka shaukinsu a ko da yaushe. Iya gwargwadon shakuwansa da su ko ita budurwan tasa ne zai iya nuna kadarin shagaltuwar tunaninsa da su ko ita. Kun ga a nan, yana sawwara abokansa ne a cikin zuciyarsa, tare da cikakken kalansu da nau’insu, kuma su na nan a tabbace. To amma abin ya zama kawalwalniya ne saboda a hakikanin asalinsu ba yadda su ke kwakwalwansa ke suranta masa su ba. Musamman ma idan bai taba ganinsu ba. Haka wanda ya saba shiga don wasan kwamfuta da Cartoons. A ko da yaushe hankalinsa na kan abinda ya saba wasa dasu ne, iya gwargwadon shakuwarsa da su, shi ma. Kuma ko da misali yake son bayarwa a wajen hira, zai samu kansa yana mai misali da su. Tabbas akwai manhajar da yake wasa da su a gidan yanar sadarwan. Wannan tabbaci kenan. Amma a hakikanin rayuwa ba su nan, ko kadan. Kuma ba zai gane hakan ba, sai lokacin da ya fita daga Intanet. Sai dai ya yi ta shaukin su, amma ba zai same su ba a zahirance. Haka wanda ya mayar da Intanet a matsayin makaranta, a kowane lokaci. Abinda zuciyar sa za ta rinka sawwara masa kenan: maranta cikakkiya. Kuma yana da tabbacin ta, a duk lokacin da ya shiga Intanet. Wannan tabbaci kenan. Amma da zaran ya fito hakikanin rayuwa fa? Sai dai shauki. Idan muka zo kan mai saye da sayarwa ma haka abin yake. Ya ki zuwa kasuwa ne watakil saboda ganin cewa abinda zai saya na samuwa ta hanyar Intanet. Da zaran ya saba da haka, sai ya ga ashe yana da kasuwa kebantacciya a kwakwalwansa, ba sai ya fita zuwa shagon da ke kofar gidansa ma ba, balle wata unguwa. A kullum ya tuna kasuwa, kwakwalwansa ba ta tuno masa da kasuwar unguwarsu, tabbacciya, a a, sai dai kasuwar Intanet, wacce zuciya ke sawwara masa ita. Tabbas akwai ta, tun da har gashi yana biya, ana kawo masa kayayyakin har gida. To amma a hakika ina kasuwar take? Ba ta, sam. Da zaran ya kashe kwamfutar ko ya rufe rariyar lilo da tsallake-tsallakensa shi kenan. Ko da kuwa gidan yanar sadarwan na da shago tabbatacce a zahira, idan ya je ba zai iya gudanar da komai ba, don ba don hakan aka yi shagon ba. An ajiye shagon ne don ajiyan hajojin. Idan ka saya ta hanyar Intanet, a dauka a kai maka gida ko ofis. Wannan shi ne hujjar alaka tsakanin tabbaci da rashin sa.

Kammalawa

Daga karshe, wadannan su ne hanyoyi da kuma tsarin alakar da ke tsakanin tunani ko kwakwalwan dan Adam mai sarrafa kwamfuta da Intanet, da kuma tabbacin abinda yake sawwara ma kansa ko rashinsa. A mako mai zuwa in Allah Ya yarda, za mu ji ko akwai wata illa da ke samuwa sanadiyyar hakan. Idan akwai, ina magani? Na san har zuwa yanzu mai karatu bai san in da wannan kasida ta sa gaba ba, saboda irin sarkakiyan da ke ciki. Kada ka damu, mako mai zuwa na ka ne. A biyo mu!

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)

Off Lagos Crescent, Unguwar Hausawa,

Garki II, Abuja. 080 34592444

Fasaha2007@yahoo.com

http://babansadiq.blogspot.com, http://fasahar-intanet.blogspot.com

Tuesday, July 17, 2007

Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake (Cyber Cafe)

Mabudin Kunnuwa

A makon da ya gabata, mun yi zama ne don nazari kan kasidun baya da tasirinsu wajen taimaka ma mai karatu kara saninsa da fahimtarsa kan wannan hanyar fasahar sadarwa da abinda ya shafe ta. A haka za mu ci gaba da kawo bayanai, muna zama lokaci-lokaci, don yin waiwaye, abinda wani bawan Allah mai suna Malam Bahaushe ya ce “adon tafiya” ne. A wannan mako, za mu yi bayani ne kan Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake, watau Cyber Café, a turance. A yanzu za mu dukufa!

Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake

Ma’anar Cyber Café shi ne Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake. Wuri ne da duk mai son shiga Intanet ke zuwa don ya sayi lokaci (sa’a daya ko mintuna talatin ko makamancin haka), don yin lilo da tsallake-tsallake a giza-gizan sadarwa ta duniya. Bayan Cyber Café, a kan yi amfani da kalmar Internet Café, duk da nufin abu daya. Wannan kalma ko kalmomi, kamar yadda muka sha sanarwa dangane da sauran kalmomin turancin da su ka danganci fasahar sadarwa, kalmomi ne baki, wadanda mai karatu zai sha wuya idan yace sai ya samu hakikanin ma’anarsu a cikin Kamus (Dictionary) na turanci. Tabbas akan samu wasu kalmomin, saboda yawan bita da ake ma kundayen kamus na turanci, amma sau tari sai ka nemi wata kalmar ka rasa, ba ma ta ma’anarta ake ba. Babban dalili kuwa shine, saurin yaduwan kalmomin ya zarce kusancin lokacin da ake daukawa wajen bitan kamus din, nesa ba kusa ba. A Hausance kuma, kalmar “Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake” kuma, Farfesa Abdallah Uba Adamu da ke Jami’ar Bayero ne (a iya sani na), ya kirkireta. Don haka mu ke biye da shi a kan wannan turba. Kuma duk da kiran da ya sha yi, cewa wadannan kalmomi (da wasu daban ba wadannan ba) ya kirkire su ne a bisa fahimtar da yayi na irin sakon da kalmar turancin ke son isarwa. Yana kuma kira ga masana harshen Hausa da ke Jami’o’in Arewacin Nijeriya, kai har ma waje, su yi bitan wadannan kalmomi don tabbatar da daidainsu ko rashin dacewarsu, har yanzu ban ji wani ya yi ko tari ba kan hakan. Don haka, idan ka ji an ce: “Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake”, to kada ka raba daya biyu: ana nufin Cyber Café ne, idan dan boko ne kai masanin turancin Ingilishi. Idan kuma dan uwa na ne kai, to ana nufin shago ko wata rumfa da ake zuwa don samun hanyoyin mu’amala da fasahar Intanet.

Tarihin Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake a kasashen duniya, musamman in da wannan fasaha yayi buruzi, tarihi ne dadadde. A kalla ma iya cewa dadewarsa daya ne, ko kasa da haka kadan, da dadewar fasahar Intanet din ita kanta. Idan ka je kasashen Turai da Amurka, da kasashen Gabas-ta-Tsakiya musamman, za ka samu shaguna kayatattu, masu cike da kayan alatu da kayan makulashe da kwamfutoci da sauran karikitai, don masu zuwa yin lilo da tsallake-tsallake a giza-gizan sadarwa ta duniya. Wannan Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake kenan, da tairhin kalma da lokacin bayyanar ta. To me da me ke cikin wannan mashakata, musamman a kasashenmu na Afirka?

Me Ke Ciki?

Ta la’akari da manufar kafa wannan shago ko mashakata, mai karatu zai iya hasashen me da me zai kasance a ciki. Galibin abin da ke cikin Mashakatar Tsallake-tsallake sun kasu kashi uku; kashi na farko su ne kwamfutoci, sai kayayyakin lantarki, masu taimakawa wajen sarrafa kwamfutar, irinsu UPS, Stabiliser, Wayoyi dsr.; sai kuma ma’aikata. A dukkan wani mashakata na lilo da tsallake-tsallake akwai kwamfutoci, wanda a kan su ne mai lilo zai yi duk abinda yake son yi. Wadannan kwamfutoci ba su da iyaka; ya danganta da girma da kuma karfin mai shago. A wasu wurare zaka iya samun kwamfutoci sama da ashirin. A wani wurin kuma ma basu wuce biyar; iya gwargwadon girman shago ne da karfin aljihu. A galibin biranen Nijeriya, yawan kwamfuta a cikin mashakatar tsallake-tsallake na danganta ne da yanayin wuri; akwai jama’ ko babu, masu sha’awan shiga. Duk wannan na daga cikin abinda ke tabbatar da yawan ko kiman girman shagon lilo da tsallake-tsallake. Wadannan kwamfutoci dai ana hada su ne da juna, a bisa tsarin gajeren zangon sadarwa, watau Local Area Network (LAN). Duk mashakatar da ka je ka samu kwamfutoci sama da daya, ana shiga Intanet ta cikinsu, to a hade suke da guda daya, wacce ake kira uwar garke, watau Server kenan a turance. Ita wannan Uwar Garke zaka samu tana gefe ne, an ajiye mata wanda ke kula da ita, ko kuma a wasu wurare ka same ta cikin wani daki daban. Ita ce kwamfutar da ke karban shafukan yanan gizo daga kamfanin da ke sadar da masu shagon (idan ta hanyar wasu suke samu), watau Internet Service Provider (ISP), ko kuma ta hanyar tauraron dan Adam mai suna Earthlink, idan kai tsaye su ke saduwa da giza-gizan sadarwa. Hakan kuwa na faruwa ne ta dalilin wani kafcecen dish na tauraron dan Adam (Satellite Dish) da ke taimaka masu. Idan wannan kwamfuta ta zuko, sai ta raba ma dukkan sauraron kwamfutocin da ke cikin mashakatar, kai tsaye, ba wai adana su take a tumbinta ba. Su kuma sauran kwamfutocin na samun wadannan shafuka ne ta hanyar wayoyin kebul, wanda ke hade da babban mahadar karban bayanai, watau Switch. Shi Switch wani dan karamin na’ura ne mai kafofin shigar da wayoyi, wanda ta wadannan kafofi yake raba duk abinda ya kwaso daga cikin Uwar Garken. Shi ya sa da zaran siginar Intanet ta dauke a kwamfutocin mutane, sai ka ji ana ta yi ma Operator (wanda ke lura da Uwar Garken kenan) ihu da surutu, musamman ganin cewa kudinsu na tafiya, kuma babu sigina. Dayan abubuwa uku ne ke haddasa daukewan sigina; ko dai ya zama hadari ya hadu ganga-ganga (ya Allah ruwa na sauka ne ko ba ya sauka), ko kuma masu lilo a saman Uwar Garken kwamfutar masu sadarwasu, sun yi yawa (ka kwatanta mana ka gani; ko da reshen itaciya ne aka samu masu lilo a hannayensa sun yi yawa, yaya? Dole yayi laushi ko ma ya karyo kasa da kowa da kowa); ko kuma ya zama ainihin wayar da ke sadar maka da sigina daga Uwar Garke ne ya cire. To bayan kwamfutoci, sai kuma sauran karikitan da ke taimaka musu aiwatar da ayyukansu. A sama mun ambaci Switch, idan babu shi, to babu Internet, gaba daya ma. Domin shi ne “dan aike”, mai sadar da kwamfuta da ‘yar uwanta. Sai kuma Uninterrupted Power Supply (UPS), wanda ke taimaka ma kwamfuta rike wuta na wani dan takadirin lokaci, idan an dauke wuta. Wasu su kan sanya ma kowace kwamfuta na ta, wasu kuma su sanya babba guda daya, wanda zai dauke dukkan kwamfutocin. Bayan nan kuma sai wayoyin kebul, amma ba kebul din da kowa ya sani ba ne. Shi wannan ana kiransa Data Cable. Waya ce wacce bayanai ko sauti ke iya wucewa ta cikinta, ba wutar lantarki ba kadai. Sai kuma Stabilizer, wanda duk na tabbata mun san shi, da irin aikin da yake yi. Banbancinsa da UPS shine; shi UPS kan yi sa’a guda ko minti talatin ko goma ko kuma mintuna biyar (ya danganta da girman mizaninsa), yana rike da wuta. Amma shi Stabilizer, aikinsa shi ne auna iya gwargwadon wutan da ake bukata, amma da zaran an dauke wuta, shi ma ya tafi kenan. Shi a kan yi amfani da shi ne don TV, ko Rediyo da wasu kayayyakin lantarki da ba kwamfuta ba. Bayan wadannan, sai kuma kujeru da tebura da ake zama a kai. Kashi na karshe cikin abin da ake samu cikin mashakatar lilo da tsallake-tsallake, shi ne ma’aikatan da ke tafiyar harkokin kasuwancin da ke ciki. Su ma kashi-kashi su ke; akwai injiniyoyi masu lura da kwamfuta idan an samu matsalar daukewar sigina ko lalacewar kwamfuta (ba dukkan mashakata ba ne ke da wanann). Sai kuma masu karban kudade da sayar maka da lokacin lilo. Su na yin hakan ne ta hanyar bayar da tiketi, wanda ke dauke da lambobi ko bakake. Idan ka zo kan kwamfuta sai ka shigar da su, don ka samu mashigi. Wannan tikiti ne zai rinka kididdige maka yawan lokacin da ya rage maka. Hakan na faruwa ne saboda su na amfani ne da wata masarrafa da ke fuskan kwamfuta; idan ba ka da wadannan lambobin da ke dauke a saman tikiti, babu shiga kenan. Wannan manhaja ana kiransa Cyber Lock. Kamar yadda bayani ya gabata ne, cewa wasu mashakatar ba su kai wasu ba. Don haka, a wasu wuraren ma za ka samu mutum daye ne ke komai (komai da ruwanka kenan). Wasu ma ba su da Cyber Lock; da agogo ake kididdigan lokacin da ka ci. Dankari!

Aikace-Aikace

Bayan sanin abubuwan da ke cikin mashakatar lilo da tsallake-tsallake, yana da kyau mai karatu ya san shin wani irin aiki su ke yi ne? Eh, na san na sanar da mu cewa waje ne na shiga Intanet, na kuma san da dama cikin masu karatu sun san yadda tsarinsa yake to amma ta yaya abin ke kasancewa? Shi Cyber Café waje ne mai tattare da aikace-aikace da dama. Duk da cewa shiga Intanet a ke, a wasu wuraren za ka samu abubuwa da dama. Wasu sun fadada mashakatar zuwa abinda a yanzu mu ke kira Business Center (ko Cibiyar Kasuwanci, a Hausance). Za a iya buga maka bayanai (Printing); za a iya layance maka ID Card ko wasu takardunka masu muhimmanci (Lamination), ko a daukan maka hoton hutunanka, don ka samu sanya su cikin kwamfuta (Scanning) da dai sauran aikace-aikace. Har wa yau, a mashakatar lilo da tsallake-tsallake ka na iya kwana ka na lilo a giza-gizan sadarwa (Overnight Browsing). Bayan nan, kana iya buga waya (Phone Calls), ko ka sayi katin wayar salula (Recharge Card), ko kuma a sawwara maka takardunka (Photocopy). A wasu manyan mashakatar lilo da tsallake-tsallake da su ka kasaita a manyan birane irin su Kano da Kaduna da Jas, da Uwa Uba Abuja, ana sayar da abin makulashe (cin-cin, lemon kwalba, alawa dsr). In ka na bukatar gidan yanan sadarwa na kashin kanka, suna iya gina ma ka, ka biya su. Kai idan ma so kake ka rinka shiga Intanet a kwamfutarka da ke gida, za su iya jona ka hanyarsu, kana biyansu duk wata. A takaice dai mashakatar lilo da tsallake-tsallake wuri ne mai tara jama’a (na gari da na banza), kuma yaduwarsa na rage yawan marasa aikin yi a gari (musamman birane), kuma ya na daga cikin manyan hanyoyin yaduwar arziki. A karshe kuma, makaranta ce babba, wacce sanadiyyarta da dama sun iya amfani da fasahar sadarwa irin tarho, kwamfuta da sauransu.

Shawarwari

Bayan duk mun ji wannan, zai dace har wa yau mu lura da wasu abubuwa, musamman ga masu taifyar da irin wadannan wurare, domin akwai bata-gari. Ba wasu ba ne kuwa illa masu zuwa suna aiwatar da harkokin harkalla na abinda ya shafi kasuwancin karya, da sunan wai su a kasashen waje su ke. Wadannan, idan mai karatu bai mance ba, su na daga cikin wadanda muka kawo bayanai a kansu cikin kasidarmu mai taken: “Spam”: Don Kawar Da Bakin Haure! Mayaudara ne da ke tafiyar da sana’ar sata da zamba cikin aminci ta hanyar fasahar Intanet. Kuma kashi casa’in da biyar cikinsu na amfani ne da mashakatar Lilo da tsallake-tsallake. Wannan ta sa hukumar Yaki da Zamba Cikin Aminci watau EFCC ta kulla da su. Ta bi kusan dukkan ire-iren wadannan mashakatar lilo da tsallake-tsallake tai musu rajista, don taimaka musu kame ire-iren masu wannan ta’ada, musamman a birane irinsu Legas da Abuja da Ibadan da Kaduna da Jas da sauran birane. Duk wanda aka san shi da wannan ta’ada, lallai dole ne a yi hankali da shi. Har wa yau akwai barayi masu shiga don ganin irin kalolin mutanen da ke shiga, idan ka fita a bi ka a kwace maka kudade. Su ma galibi a manyan birane ake samun su. Sai kuma kananan barayi (‘yan tsintau) masu sace ma jama’a wayoyin salularsu. Dole ne a rinka lura da masu shigowa suna yin lilo na Allah-da-Annabi, da masu shigowa don kailula da walagigi. Kai ma mai zuwa wajen, dole ka rinka lura da aljihun ka; duk abinda ka san ka je da shi wajen, ka lura da shi. Kuma mu daina zuwa don nuna takama da “son cinyewa”; shi ne, mutum yayi shiga irin ta takama da nuna cewa “ni mai kudi ne ko sukuni”. Galibin masu yin haka za ka samu samari ne irin mu (‘yan talatin da biyar zuwa kasa), kuma duk don ‘yan mata masu zuwa wajen ake yi. Wannan ke sa wa ka ga mashakatar tsallake-tsallake ta zama kamar wata daba ta samari da ‘yan mata. Duk sai a rinka lura da abinda zai kawo zaman lafiya da samun arikizi, ba abin da zai kawo tir ba.

Kammalawa

Daga karshe, za mu dakata a nan, sai wani mako. Duk abinda ba a fahimta ba a yi kokarin tambaya. In Allah Ya yarda za mu taimaka da bayanai iya gwargwadon fahimta. Kada a mance da Mudawannar Fasahar Intanet da ke: http://fasahar-intanet.blogpsot.com. Ina mika gaisuwa ta ga dukkan masu karatu. Sai wani mako.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)

Off Lagos Crescent, Anguwar Hausawa,

Garki II. 080 34592444 fasaha2007@yahoo.com

http://babansadiq.blogspot.com

Waiwaye Adon Tafiya (2)

Tuna Baya Shine Roko

Duk tafiyar da aka kawata ta da waiwaye, to akwai watakilancin samun nasara cikinta, in Allah Ya yarda. Da wannan muka ga dacewar ci gaba da wannan salo na “Waiwaye Adon Tafiya”, a wannan shafi mai albarka. Idan masu karatu basu mance ba, wannan shine karo na biyu da muka sake zama don yin nazari kan kasidun da suka gabata, kafin mu sake canza salon tafiya don ci gaba. A wancan karo mun yi waiwaye ne saboda ganin mun samu bayanai kan yadda ake sarrafa shafukan yanan gizo, da kuma tarihin da ke tattare da asalinsa. Wannan shine daman abinda ya kamata mai koyo ya sani. Hakan kuma ya faru ne a mako na bakwai da fara assasa wannan shafi. A yau sai ga mu a mako na ashirin da takwas! Tirkashi! Don haka naga dacewar mu sake zama don kallon baya; ina muka fito? A ina muke? Kuma ina muka dosa?

Kasidun Baya

Bayan gabatar da “Waiwaye Adon Tafiya” kashin farko, mun ci gaba ne da kasidar Matambayi Ba Ya Bata, ko Search Engine, a takaice. In da muka sanar da mai karatu hanyoyin da zasu taimaka masa nemo bayanai a giza-gizan sadarwa ta duniya. Daga nan sai muka sake sanar da masu karatu wasu daga cikin shugabannin da ke tafiyar da al’amura a duniyar Intanet. Wannan ya samu ne ta hanyar Shugabanni a Duniyar Intanet, wacce makalar Kwamfuta da Manhajojinta ta biyo baya. A makon da ya biyo wannan, sai muka kawo wasu tambayoyi guda biyu da masu karatu suka turo; daya kan Sakonnin Bogi ne, watau Spam Mails, sai kuma wanda ke neman bayani kan VoIP, ko kuma Voice Over Internet Protocol, a turance. Bayan dukkan wannan, sai muka jefo kasidu biyu - daya na bin daya – kan alakar Hausawa da Intanet, da kuma hanyoyin da Intanet zai iya shafan al’ummar Hausawa nan gaba. Daga nan kuma sai kasidar da tafi dukkan sauran shahara ta biyo baya, watau Fasahar Intanet a Wayar Salula. Akwai watakilancin ba za mu kawo kashi na biyunsa ba, sabanin yadda na fara tunani kafin wannan mako. Zan yi Karin bayani nan gaba. Ana cikin haka, sai muka ga dacewar fahimtar da mai karatu ire-iren hanyoyin da zai iya mu’amala da wasu kamfanoni ko hukumomin gwamnati ta hanyar Intanet, ba tare da yaje can inda ofishin hukumar yake ba. Wannan makala mun kacalcala ta ne zuwa kashi biyar, muka ba ta taken: Dangantakar Intanet Da Harkokin Rayuwa. Idan mai karatu bai mance ba, muna cikin barko wadannan bayanai ne muka dan yi ratsi, don jefo bayanai gamsassu kan yadda ake iya ragewa ko kuma rabuwa da sakinnin bogi. Taken wannan kasida kuwa itace: “Spam”: Don Kawar da Bakin Haure. Daga nan muka zarce taska don nemo ma mai karatu bayanai kan tarihi da habbaka da kuma yadda ake gina Mudawwanar taskance ra’ayoyi da tunani a giza-gizan sadarwa ta Intanet. Mudawwana (Weblog) #1, shine taken kasidar farko. Daga nan muka biyo kasidar makon da ke biye da wannan da kashi na biyu, watau Mudawwana (Weblog) #2. A bayyane yake cewa, bayan kasidar Fasahar Intanet a Wayar Salula, ba a samu kasidun da suka shahara, suka kuma yi tasiri a zukata da gabobin masu karatu ba irin wadannan. Abin da ya dada tabbatar mana da hakan kuwa shine, bayan sakonnin text da muka yi ta samu, da dama cikin masu karatu sun bude mudawwanai, wanda duk mun yi ta sanar da adireshin su a wannan shafi. Bayan haka, sai kuma muka fara zuwa ziyara takanas-ta-gizo, zuwa wasu daga cikin shahararrun gidajen yanar sadarwa masu muhimmanci ga al’umman Hausawa, a duniyar gizo. Mun fara ne da gidan yanan sadarwar Gamji.com. Daga nan muka biyo da na Kanoonline.com. A karshe muka yi zango a kasar Amurka, daidai gidan Malam Mohammad Hashim Gumel, mai gidan yanar sadarwan Gumel.com. Alal hakika mun karu sosai da wannan ziyara, domin a kalla mun san irin matsayin da wadannan gidajen yanar sadarwa suke dashi, da kuma irin bayanan da suke dauke dasu. Da kuma uwa-uba, irin tsarin da Uban Gidan Yanar yayi musu, don amfanar da masu ziyara. To, gama wannan ziyara ke da wuya, sai ga wani abu a kan matan Sarki, wanda saboda rashin kula, ba ido ba, ta kasa gani. Af, mun dade muna ta kwararo bayanai kan yadda ake shiga da kuma mu’amala da fasahar Intanet, amma bamu taba kawo bayani kan masarrafa ko manhajar da ke taimaka ma mai ziyara wannan aiki ba. Don haka sai muka jero kasidu biyu kan Rariyar Lilo da Tsallake-tsallake (Web Browser). A makalar farko muka kawo asali da kuma tarihin wannan manhaja mai muhimmanci a tarihin fasahar Intanet. A kasida ta biyu, wacce muka kawo cikin makon da ya gabata, sai muka kawo siffofin shahararriyar rariyar kamfanin Microsoft, watau Internet Explorer 6.0. Da wannan makala muka cike wannan zango na wannan lokaci. Idan mai karatu ya lura, zai ga cewa karantarwan wadannan kasidu da bayanansu suka gabata, sun sha banban nesa ba kusa ba, daga tsarin kasidun farko.

Sakonnin Masu Karatu

Duk da yake kusan dukkan mako mukan tabo daya ko biyu, a kalla, dangane da abinda ya shafi sakonnin masu karatu, a yau ya kamata mu yi kyakkyawan nazari kan irin abinda masu karatu ke rubutawa sakamakon kasidun da wannan shafi ke fitarwa, ta gwargwadon tunani da hangen nesan su. Ire-iren wadannan sakonni sun kasu kashi uku ne, dangane da nau’in bayanan da ke cikinsu. Kashi na farko sun kunshi sakonni ne na gaisuwa da yabo da kuma ban gajiya. Ina samun irin wadannan sakonni ta hanyar sakon text na wayar salula ko kuma ta Imel. Kashi na biyu kuma sun kunshi sakonnin neman Karin bayani kan abinda na rubuta a makon da ake ciki ko kuma wanda ya gabata. Sai kuma kashi na karshe, masu bayar da shawarwari kan abinda ya kamata a yi. Ga al’ada na kan mayar da jawabi ne kai tsaye, idan aiki bai rinjayeni ba. Wasu lokuta kuma ire-iren wadannan sakonni kan sameni ne (musamman ta hanyar text), a halin rashin kudi a cikin wayata. Idan na sanya wasu lokuta sai in kira, ko in mayar da jawabi, wasu lokuta kuma in shagala. Akwai wasu sakonni wadanda sun kunshi tambayoyi ne, ban kuma bayar da amsarsu ba don ganin cewa nan ba da dadewa ba zamu kawo bayanai kan haka. Don haka duk wanda ya rubuto don neman Karin bayani, amma bai samu amsa ba har yanzu, ya gafarceni. In Allah Ya yarda nan ba dadewa ba zai samu cikakken bayanai nan gaba. Muna bin abin ne daki-daki. Wanda kuma ya rubuto gaisuwa ko shawara shi ma bai ji wani bayani ba, don Allah yayi hakuri shi ma; komai da lokacinsa.

Maimaitattun Tambayoyi

Kafin mu karkare, zan so sanar da masu karatu cewa akwai wasu bangarori biyu da har yanzu da dama cikinmu bamu samu gamsuwa da su ba. ko dai saboda watakil bamu fara bin wannan shafi tun farko ba, ko kuma saboda irin takaitattun bayanan da ke cikinsa. Kada a mance, wannan shafi ne na jarida, wanda ba zamu iya kawo komai da komai a lokaci guda ta yadda kowa da kowa zai fahimta ko iya amfani da abinda ake karantarwa ba. Wannan ba abu bane mai yiwuwa a tsarin yau da kullum, da kuma tsarin tarbiyya irin ta karantarwa. Don haka maimaitattun tambayoyin neman Karin bayani ko shiryarwa da suka fi kowanne zuwa su ne kan Yadda ake shiga Intanet ta Wayar Salula, da kuma bayani kan yadda ake shiga shi kanshi Intanet din, a farkon al’amari. Kari a kan haka, wasu kan rubuto don neman Karin bayani kan wani littafi da zai taimaka musu wajen shiga Intanet. Wannan tasa na kebe wannan bangare don amsa wadannan tambayoyi, a karon karshe, in Allah Ya yarda. Ga bayanan nan kasa:

Intanet a Wayar Salula

Ga duk wanda ke biye da wannan shafi mako zuwa mako, ya san wannan na daga cikin kasidun da masu karatu suka fi damuwa dashi. Kuma a iya kokarin da nayi wajen bincike kan kasidan da na gabatar, nake ganin kamar idan muka kawo kashi na biyu, za a samu cakudewar fahimta, domin dukkan abinda ya kamata a ce na kawo dangane da shiga Intanet ta hanyar Wayar Salula, to na kawo shi. Abubuwan da suka rage kuma maimai ne kan na baya. Na kuma fahimci galibin masu neman bayani (ba Karin bayani ba) kan haka, da cewa basu samu karanta wannan makala bane. In kuma sun karanta, to dama basu fahimci matakan da aka kawo ba. Don haka nake baiwa ire-iren wadannan makaranta da su je Mudawwanar wannan shafi don samun kasidar kai tsaye a nan: http://fasahar-intanet.blogspot.com/2007/05/fasahar-intanet-wayar-saluala.html . A lura da adireshin, a kuma shigar dashi yadda yake a nan. Za a samu cikakken bayani in Allah Ya yarda.

Yadda ake Shiga Intanet

To, wannan kusan ita ce kasida ta biyu ko uku da muka gabatar a wannan shafi. Idan muka ce za mu sake koro bayani kan haka kuma, kamar mun koma baya ne. Don haka na ke son sanar da duk mai neman bayani kan haka da yaje Mashakatar Tsallake-tsallake (cyber café) da ke gari ko unguwar su, ya sanar da su cewa so yake ya bude Imel (kada y ace musu Intanet kawai zai shiga). Bayan haka, yana da kyau ya sanar dasu cewa bai taba shiga wannan muhalli ba, ko kuma a kalla bai saba mu’amala da kwamfuta ba. Su zasu koya masa yadda zai shiga, bayan sun bude masa akwatin Imel. Idan ma yai sa’a, to tare zasu bude; suna gaya masa yadda zai yi, shi kuma yana yi. . . har dai ya bude. Da zaran ya gama, nan zai fahimci cewa abin ba wani wahala bane dashi. Don haka sai ya lazimci zuwa a kullum. Ko kuma a kalla sau biyu a mako. Hakan ne zai sa ya samu kyakkyawar kwarewa kan wannan fasaha, in Allah Ya yarda.

Dangane da abinda ya shafi littafi kan Intanet kuma, mun sanar a wannan shafi cewa akwai littafi amma ana kan masa gyara ne tukunna, kafin fitowarsa. Kuma da zaran ya fito za a sanar a nan. Duk da cewa akwai littafai yan kanana da aka rubuta cikin harshen turanci, idan mai karatu yai sa’a ya same su, sai ya fara dasu. Don haka sai a ci gaba da hakuri; komai da lokacinsa.

Kammalawa

Daga karshe, a mako mai zuwa za mu juya akala zuwa wasu bangarori kuma, don fadada sanayyarmu ga wannan fasaha. Sai a biyo mu don samun cikakkun bayanai. A kuma rinka kwatanta abin da aka koya idan wanda ya shafi aikatawa ne a aikace. Domin wannan na daga cikin hanyoyi mafi muhimmanci wajen tabbatar da ilimi a kwakwalwar dan Adam. Ina mika godiya ta ga dukkan masu rubuto sakonni ta dukkan hanyoyi; da wanda na rubuto masa amsa ko na kira shi, da wanda ban kira ko bashi amsa ba, duk ina godiya. A rinka hakuri da ni, dan Adam nake; ba dukkan komai bane zan iya yi a lokaci guda. Kafin in karkare, ina mika godiya ta musamman ga Dakta Yusuf Adamu da ke Jami’ar Bayero da ke Kano. Mun gode da irin karfafa guiwa da yake ma wannan shafi a duk mako. Daga karshe ina mika godiyata ga kowa da kowa; ka rubuto ko ba ka rubuto ba! Allah hada fuskokinmu da alheri, amin.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)

Off Lagos Crescent, Anguwar Hausawa,

Gaki II – Abuja.

080 34592444 fasaha2007@yahoo.com

http://babansadiq.blogspot.com, http://fasahar-intanet.blogspot.com