Makon Jiya:
Na tabbata mai karatu na tare da mu cikin makon da ya gabata, inda ya karanta bayanai kan fannin Web Design and Maintenance, watau ginawa da kuma tsara gidan yanar sadarwa ta Intanet. A cikin wancan kasidar ne muka yi bayani kan asalin wannan sana’a, da abinda sana’ar ta kumsa, da hanyoyin da mai karatu zai iya bi don samun kwarewa a cikin wannan fanni. A yau in Allah Ya yarda gashi mun sake dawowa da wani fannin kuma, watau Computer Repairs and Maintenance; fannin da ya shafi gyarawa da kuma lura da na’urar kwamfuta; me ke damunta, ta yaya ake gane zazzabin kwamfuta, wasu hanyoyi ake bi wajen magance mata wadannan matsaloli? Duk wannan fanni na gyarawa da kuma lura da wannan fasaha ya tattaro bayanai kan yadda al’amuran suke. A karshe mai karatu zai samu bayanai kan hanyoyin da zai bi wajen kwarewa a wannan fanni, kamar dai sauran fannonin da suka gabata. A biyo mu:
Fannin “Computer Repairs and Maintenance”
Wannan shine fannin da ke lura da abinda ya shafi gyarawa da kuma kanikancin kwamfuta; daga ruhin ta (watau Software) har zuwa gangar-jikin ta, ko kace Hardware a Turance. Wannan wani ilimi ne mai girman daraja, domin duk wani mai kwamfuta da masu wannan sana’a yake takama, musamman ma a kasashe masu tasowa irin su Nijeriya, inda masu gyarawa da lura da na’urar kwamfuta suke da matukar karanci, saboda karancin yaduwar wannan hanyar sadarwa. Masu gyaran kwamfuta sun kasu kashi biyu; masu gyara da kuma lura da matsalolin ruhin kwamfuta, watau Software. Sai kuma masu lura da kuma gyaran gangar-jikin kwamfutar gaba daya; daga talabijin kwamfutar zuwa asalin na’urar. Amma galibin lokuta zaka samu masu gyara sun kware ne a kan dukkan bangarorin biyu. Masu gyara da lura da kwamfuta su ne masu warware dukkan wata matsala da ke samun kwamfuta; su ne likitocin kwamfuta, kamar yadda ake da likitoci a asibitocin mu; su ne masu yi ma kwamfuta gata wajen gyatta mata ruhin ta, da kuma sake mata wani, idan wanda take dashi ya lalace ko tsufa; masu canza mata siffofinta gaba daya, idan ta fara gazawa; masu kara mata zaki da amo da kambama armashin ta gaba daya. Idan kwamfuta ta kasa tashi gaba daya, su za a kawo ma; idan ta kasa nemo ma’adanan ta, su za a kawo ma ; idan ta kasa budo ma’adanan ma gaba daya, su za a kawo ma ; idan ta kasa nuna hotunan bidiyo ko majigi, su za a kawo ma ; idan ta shiga zazzabi mai tsanani sanadiyyar kwayoyin cuta (Virus) da ta harbu dasu a Intanet ko ta hanyar wasu ma’adana bayanai da ake amfani dasu a kanta, duk dai su za a kawo ma. Kai, idan ma ka rasa me ke damunta, duk ka kawo musu, su zasu nemo maka matsalar da ke damun ta. Wannan sana’a ne mai muhimmanci a halin yanzu, saboda yaduwar kwamfutoci a jihohin duniya gaba daya. Iya yawan masu amfani da wannan fasaha, iya yawan matsalolin da za ta ci gaba da samu. Kamar dai mota ce ; idan kana amfani da ita, dole ne ka rinka lura da dabi’un ta. Idan sun fara canzawa, sai ka nemi dalili. In babu, sai ka nemi likita don ya nemo maka. To me ake bukata na ilimi da fasaha kafin mutum ya zama mai gyarawa da kuma lura da kwamfuta ?
Me Ake Bukata ?
Idan kana son zama mai gyarawa da kuma lura da rayuwar kwamfuta gaba daya, zaka iya. A kasashen Turai da America ko wasu kasashe da suka ci gaba, kana iya zuwa jami’a don ka koyi gyaran kwamfuta kadai. Idan ka gama za a baka shahada, kayi rajista da gwamnati don ka fara gyara wa jama’a kwamfutocin su. Domin a galibin jami’o’in su suna da fannin System Engineering, wanda shine ilimin da ake bukatan ka mallaka kafin ka fara wannan sana’a. Haka idan ka karanta Computer Science, akwai bangaren lura da kwamfuta gaba dayan ta, watau System Maintenance, kuma muddin ka mayar da hankali, kana iya zama mai gyarawa da kuma lura da kwamfuta. Dukkan wadannan suna bukatar shahadan karatu, kamar yadda bayani ya gabata a kasidar “Computer Science”. Kasancewan bamu da irin wadannan kwasakwasai na System Engineering kai tsaye a jami’o’inmu, akwai makarantu na koyon gyaran kwamfuta musamman, a kasashen mu. Galibin su makarantu ne masu rajista da gwamnati, kamar dai irin makarantun koyon sarrafa kwamfuta na kan titi. A irin wadannan makarantu, baka bukatar samun digiri ko difiloma. Idan kana da shahadar sakandare kadai ta isa. Idan ma akwai wanda ka san yana wannan aiki a shagon sa, kana iya samun sa, ku shirya ya rinka koya maka. Wannan ma zai fi taimaka maka, domin kana ganin tsarin gyaran ne a aikace. Wannan zai iya taimaka maka wajen yi masa tambayoyi masu muhimmanci kan gabar da ake gyara, ya kuma baka amsa mai gamsarwa. A irin wannan tsari kana iya koyon gyaran ba tare da kaidin wata takardan shahadar karatu ba. Sai dai wani abinda zai taimaka wa mai koyo shine ya tabbata yana iya rubutu da karatu cikin harshen turanci. Wannan na da muhimmanci, domin rashin hakan zai iya dakile kokarin sa. Domin dukkan bayanan da suka danganci wannan fasaha da turanci suke.
Idan kuma makarantar gyaran kaje, za a ba ka tarbiyya da horo na tsawon wasu watanni ko shekara, wanda zai ba ka daman sanin matsalolin kwamfuta da kuma yadda ake magance su. Za ka yi karatu cikin abinda ya shafi tarihin kwamfuta, da nau’ukan ta, da dabi’unta da kuma manhajojin ta. Har wa yau, zaka yi karatu kan abinda ya shafi gangar-jikin kwamfuta; da hanyoyin da wutar lantarki ke bi wajen isa gareta; da zuciyanta, wanda ke dauke da manya kuma muhimman bangarorin ta, watau motherboard. Sai kuma abinda ya shafi ma’adanan ta, watau storage system a Turance. Ma’adan ta kala-kala ne; akwai wanda ta ke dauke dashi, a can cikin na’uran ta, watau Hard Disk Drive (HDD). Sai kuma wadanda ake makala mata don debowa ko zuba mata bayanai iya gwargwado; zaka san alakar da ke tsakanin wadannan ma’adanai da kuma ruhinta ko sauran gangar-jikin ta gaba daya. Wannan zai baka daman lura da kuma gyara dukkan bangarorin da wannan fasaha ke dauke da su. Domin ana karatun ne tare da kwatanta aikin a aikace; za a kawo maka kwamfuta, a wargaje ta a gaban ka, a nemo abinda ke damun ta, a gyara. Sannan a mayar da shi inda aka ciro shi. Idan kuma lalacewa yayi, za a sanar da kai irin wanda ya kamata ka canza mata, ba kowanne ba. Daga nan za a fara baka kai ma ka wargaje ta, ka kuma mayar. Wani abin farin ciki dai shine, dukkan na’urorin kwamfuta da abinda ya shafi ruhin ta, babu wani bangare da ba za a iya canza shi ba; sai dai dole ne ka lura da irin wanda zai mata daidai, ba kowanne zaka samo ka kargafa mata ba. To da zaran ka gama karatu sai me?
Abin Yi
Ayyukan duk wani System Engineer bai wuce abinda muka fara zayyanawa a sama ba. Da farko dai idan ka kware, kana iya aiki a dukkan wata ma’aikata ko hukuma da ke da na’urorin kwamfuta kuma suke aiki da su. Har wa yau, ka ga dama ka bude shagon ka, kamar yadda mai gyaran rediyo ko talabijin keyi, mutane na kawo kwamfutocin su kana gyarawa. Ko kuma ka hada dukkan biyun don samun kudi da yawa. Kana iya bude makaranta, bayan shagon aiki, ka rinka koyar da wasu don a samu masu mayewa. Domin da babu makoya, da gwanaye sun kare tuni ai. A matsayin ka na System Engineer, aikin ka ne ka san abinda ke damun kwamfuta da zaran an kawo. Idan matsalar wutar lantarki ce, daga jona kwamfutar da wuta zaka gane. Idan kuma harbin ta aka yi da kwayoyin cutar kwamfuta (Computer Virus), kalubalen da ke gaban ka na farko shine ka san yadda zaka yi ka tsamo dukkan bayanan dake ciki don kada su salwanta, kafin ka goge ruhin gaba daya ka dora mata wani. Wannan shi ake kira Reformatting. Amma idan illar bai yi tsanani ba, kana iya nemo wadannan kwayoyin cuta, ka goge su daga ruhin kwamfutar, ta amfani da masarrafan Antivirus. Haka idan mizanin da take dashi ne yayi mata kadan, kana iya kara mata wani, watau Upgrading, sannan ka sanya mata wani ruhin sabo. Haka idan aka zo da kwamfuta, tana kawo wuta, amma kuma bata nuna komai a talabijin din ta, dole ne ka nemo dalili. Haka kwamfutar da aka zo da ita, bata iya mu’amala da wata kwamfutar ko da kuwa an jona mata abubuwan da ake bukata. Dole ne ka duba katin na’urar sadarwan ta da ke ciki, watau Network Card, ka ga halin da yake ciki. Haka ma idan bata nuna hotuna masu motsi ko babu sauti, dole ne ka duba Video Card ko kuma Sound Card, dangane da yadda matsalar take. Haka idan kwamfuta na kashe kan ta, ta kuma tashi kanta ba tare da wani ya taba ta ba (Restarting and Shutting Down). Harkan hauka ya shigo lamarin kenan. Dole ne ka gane me ke sa ta yin haka. Kana iya shiga Safe Mode, watau yanayin da zai baka daman ceto bayanan da ke cikin kwamfutar kafin ka fara likitancin ta. (Ana shiga Safe Mode ne ta hanyar matsa F8, da zaran ka kunna kwamfuta, kafin ta ce maka “Starting Up Windows”). Bayan dukkan wannan, aikin ka ne cirewa da kuma canza ma kwamfuta dukkan wani gaba da ke da matsala ko yake bukatar canji; kai ne likitanta, malamin ta, mai gyaranta, wanzamin ta, kuma uban gidan ta. Dankari!
Kammalawa
Wannan fanni na gyaran kwamfuta na da muhimmanci kamar sauran fannoni, kuma yana cikin fannonin da ke kara yaduwar fasahar amfani da kwamfuta a tsakanin jama’a. A mako mai zuwa zamu kawo fannin Network Administration, watau fannin da ke lura da kulla alaka tsakanin kwamfutoci a gida ko ofis ko ma’aikata. Idan mai karatu bai samu gamsuwa ba har yanzu, kada ya damu. Muna nan tafe in Allah Ya yarda. Ina mika sakon gaisuwata ga dukkan masu karatu; musamman ma masu aiko sakonnin text ko wasikun Imel ko bugo waya. A dakace mu!
Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)
Fasaha2007@yahoo.com 08034592444