Friday, January 25, 2008

Kwarewa a Fannin Fasahar Sadarwa (5)

Matashiya

Idan mai karatu na tare da mu cikin wannan silsila na Kwarewa a Fannin Fasahar Sadarwa, a yau zamu shiga mako na shida kenan cikin bayanin da muke yi na shahararrun fannonin da ke cikin ilimin fasahar sadarwa na zamani. A makon da ya gabata mun samu bayanai kan fannin dab’i da kuma zane-zane, watau Desktop Publishing. A yau kuma zamu ci gaba da bayani kan fannin adanawa da kuma taskance bayanai ta amfani da masarrafan rumbun bayanai ta kwamfuta, watau Database Administration kenan. Mai karatu zai ji abinda wannan fanni ya kumsa ; ta yaya zai iya kwarewa kan wannan fanni ; da kuma irin aikace-aikacen da ke jiran sa a matsayin sa na Kwararre kan Manhajan Rumbun Adana Bayanai na kwamfuta, ko kace Database Administrator kenan a Turance. Muje zuwa, wai Mahaukaci ya haye kan kwamfuta :

Fannin Database Administration (DBA)

Database Administration (DBA) shine ginawa da kuma tsara rumbun adana bayanai da taskance su a masarrafan da aka tanada don yin hakan, a cikin kwamfuta. Wannan fanni yana da matukar muhimmanci musamman cikin wannan zamani da muka samu kan mu. Yadda ka san mutane kan tanadi rumbu don zuba hatsin da suka girbe don sayarwa ko adanawa zuwa wani lokaci, to haka ake tara bayanai cikin rumbun kwamfuta tsibi-tsibi. Yadda ka san kowane rumbu na da kofar shiga, da hanyoyin tsaro don masu sata da kuma dabarun kariya saboda kwari masu bata shi da kuma hanyoyin fito da shi ba tare da wani tsaiko ba, to haka ake da manhaja ko masarrafa (Software) da ke taimakawa wajen shigar da bayanai, da tsara su a cikin rumbun, da tace su don samun wanda ake son dauka a lokacin da ake son hakan, da adana su zuwa tsawon lokaci, da gyatta su, da hanyoyin nemo su idan an tashi bukata, da kuma tanadin da ake musu don samun makwafin su saboda bacin rana. Idan mai karatu na lura da irin zamanin da ake ciki yanzu, ya san cewa “bayanai” ko ilimi rubutattu da duk wani bayani da zai iya zama sanadiyyar ci gaba a rayuwa, wani abu ne da ake bashi muhimmanci a yanzu. daga haruffa zuwa lambobi da taswirori da zane-zane da kuma hotuna masu motsi da ma marasa motsi, duk ana iya adana su cikin manhajan rumbun adana bayanai na kwamfuta, watau Database Management System (DBMS). Kwararrun da ke wannan aiki su ake kira Database Administrators, ko DBAs a turancin kwamfuta. Kuma su ne ke tsara manhajan da ke wannan aiki; su tsara hanyoyin shigar da bayanan ko lambobin ko hotunan; su tabbatar da ingancin sa ta hanyar tantance masu shigar da bayanan; su tabbatar da tsaro kan bayanan a yayin da aka shigar dasu, su kuma shirya ma ko-ta-kwana, watau duk wani abinda zai iya zama sanadi wajen salwantar bayanan, ta hanyar samun makwafin su a wata kwamfuta ko ma’adana daban. Bayan haka, su tabbatar cewa wannan makwafi da suka tanada zai wadatar, a yayin da wanda ake dasu cikin kwamfuta ko manhajan rumbun bayanan suka samu matsala. Ba sai an shiga rudu ba a zo a rasa wanda aka kwafa.

Idan mai karatu bai fahimci inda aka dosa ba har yanzu, watakila ya taba shiga banki don karban kudi; da zaran kashiya ya karbi cakinka (Cheque Slip) ko takardan umarnin karban kudin da ka cike (Withdrawal Slip), ka ga ya kama kallonka yana ta wasa da kwamfutarsa, bayanan da suka shafe yake zakulowa daga rumbun adana bayanan su, don ya tabbatar ko sheda ka, ta hanyar hotonka da ke cikin kwamfutarsa da kuma sanya hannunka (Signature). Watakila ka taba shiga gidan yanar sadarwan makarantar ku don cika fam da kuma biyan kudin makaranta; duk bayanan da ka shigar a shafin, rumbun adana bayanan makaratar suke wucewa, babu kakkautawa. Idan kana mu’amala da layin wayar salula na kamfanin MTN ko CELTEL ko MTEL ko GLOMOBILE, duk bayanan da kake bugawa da wadanda ake bugo maka kana amsawa, duk a cikin rumbun adana bayanan kamfanin suke makare. Haka ma galibin asibitoci musamman masu zaman kan su; sukan shigar da dukkan bayanan abokan huldansu ko marasa lafiyan da ake kawowa ne cikin rumbun adana bayanai. Ko da fam aka baka na takarda ka cike, to galibi akan shigar da bayanan da ka bayar ne cikin kwamfuta ta hanyar wannan manhaja na adana bayanai, watau Database. Kusan dukkan hukumomin gwamnatin tarayya da na jihohi suna amfani da wannan hanya wajen taskance bayanai don shugabanci. Daga jami’an tsaro irin su sojoji da sauran su, zuwa manyan kamfanoni, duk sun rungumi wannan tsari wajen adana bayanan su. A wasu kasashe, kusan dukkan jami’an tsaro irin ‘yan sanda da sojoji, duk suna da babban rumbun adana bayanan dukkan masu laifi da kuma ma’aikatan su. Wannan ke nuna muhimmancin da wannan fanni na Database Administration ke dashi. Shahararru cikin manhajojin da ke wannan aiki su ne: Microsoft Access (da ke cikin MS Office 2003 – 2007), Microsoft SQL Server 2000 da 2003, Oracle da dai sauransu.

Me Ake Bukata?

Don samun kwarewa a wannan fanni, mai karatu na bukatan shahara cikin daya daga cikin manhajojin da ke taimakawa wajen wannan tsari na adanawa da kuma taskance bayanai ta hanyar kwamfuta. Bayan iya rubutu da tsara shafuka, watau Computer Appreciation, dole ne ka kware kan daya daga cikin wadannan manhajoji da bayanin su ya gabata a sama. Ko dai ka zama Oracle Database Server Administrator (ODBSA), watau kwararre kan manhajan ginawa da kuma tsara rumbun adana bayanai na Oracle, ko ka shahara kan Micrisoft SQL Server 2000, ko 2003. Bayan wadannan, akwai wasu manhajojin da zaka iya kwarewa a kan su, amma a duniya wadannan ne suka fi shahara. Kuma zaka iya samun daman yin hakan ta hanyar manyan makarantun kwamfuta da ke manyan biranen kasan nan, irin su: NIIT, AFLON, MBM da APTECH, da ma wasu. A gaskiya wadannan kwasakwasai na da matukar tsada, musamman a matakin kwarewa. Duk da yake NIIT da ke da rassa a Abuja da Legas, da Kaduna da Kano da ma sauran jihohi kan shirya jarrabawa a duk shekara (cikin watan Yuli ko Agusta). Kowa na iya zama don rubutawa, kuma kyauta ake bayar da fam din. Idan ka samu iya makin da suke bukata, za a rage maka yawan kudin da zaka biya, iya gwargwadon kokarin ka. Idan ka samu shiga, za ka fara ne a matsayin dalibi da ke zuwa yana daukan karatu a wadannan makarantu. Idan ka gama wannan mataki, za a baka shedar gama karatu watau Certificate, kuma kana iya neman aiki da wannan takarda, ba matsala. Amma idan kana son karasawa matakin kwarewa, to dole ne ka sayi katin rubuta jarrabawan ta hanyar Intanet (Scratch Card), inda zaka shigar da bayanan da ke jikin katin, a baka daman zama don rubuta jarrabawar karshe don samun kwarewa a wannan fanni. Idan ka ci, za a aiko maka da sakamakon jarrabawan, tare da shahada ko shedar gamawa da kwarewa. Idan haka ta kasance, wannan shine abin farin ciki, domin duk ma’aikatar da kaje zaka samu aiki, muddin sun san kimar abinda kake rike dashi, da abinda zaka iya musu. Shiga wannan makaranta ko rubuta wannan jarrabawa basu bukatan wasu dogayen takardun shedan gama makaranta; da zaran ka mallaki shedar gama sakandare shikenan.

Abin Yi

Kana da abin yi sosai; kana da ayyuka masu tsoka da ke jiranka. Idan ma kayi sa’a kana da hazaka, tun daga makarantar zasu mallake ka, ka zama daya daga cikin masu karantar da sabbin dalibai, kamar dai yadda galibin jami’o’inmu ke yi a yanzu. Idan haka bai kasance ba, to duk ma’aikatar da ka sani tana mu’amala da kwamfuta tana iya daukan ka aiki; daga hukumomin gwamnati zuwa kamfanonin yan kasuwa da masu zaman kan su. Kai hatta manyan shaguna irinsu SAHAD Stores, UTC Development Stores, Leventis Stores, duk suna iya daukan ka aiki, musamman idan a wasu kasashe ne. Domin suna bukatar sanin nawa suka kashe kuma nawa suka shigo musu; suna son sanin yawan kwastomomin su, da irin kayayyakin da aka fi saya da kuma yawan cinikin da suke yi a kullum ko duk mako ko duk wata. Duk suna iya sanin wannan ta hanyar manhajan rumbun adanawa da kuma tsara bayanai. A turai, manyan shaguna irin su SAHAD Stores zaka samu suna da sashen kwamfuta, inda ake shigar da dukkan bayanan da suka danganci hajojin da suke sayarwa,da masu saye da kuma yawan cinikin da suke yi a kullum. A duk karshen shekara idan suna so, umarni kawai za a ba wannan manhaja ya taro dukkan bayanan da ake so na hajojin da aka sayar,da kwastomomin da suka saya da kuma yawan abinda aka sayar, da kuma cewa riba aka ci ko faduwa aka yi. Har wa yau, kana iya zama ka bude kamfanin ka, ka gina irin wannan manhaja, kana sayar ma kamfanoni suna biyanka kudin lasisi (Licence Fee) a duk shekara. Kai kuma kana taimaka musu wajen tsara musu manhajan, da karantar da ma’aikatansu da kuma basu shawarwari wajen kimtsa bayanan su. Kana iya aiki a banki da jami’o’i da asibitoci da duk wata hukuma ko ma’aikata ke mu’amala da al’umma a ko ina take. Wadannan kadan ne cikin ayyukan da zaka iya yi.

Kammalawa

A karshe, wannan fanni na Database Administration na cikin manyan fannoni masu muhimmanci, kuma wanda duk ya mallaki wannan ilimi zai samu shahara kebantacciya in Allah Ya yarda. Idan har wa yau mai karatu bai yanke shawara ba, kada ya damu. Mako mai zuwa muna nan tafe da wani fanni in Allah Ya yarda. A nan zan mika godiyata ga dukkan masu karatu, musamman Malam Hassan Abdullahi Kuyambana da abokin sa Malam Is’haq AbdulHadi da ke Zariya City. Ina musu godiya kwarai da irin tarban da suka mini a yayin da na ziyarci Zariya, a hanyata ta dawowa daga ziyarar aiki da na kai birnin Kano. Hakika naji dadin tattaunawar da mukai dasu, kuma duk da yake basu sani ba, na dauki wannan hiran kacokan dinta a wayar salula ta, kuma in Allah Ya yarda zan tsakuro mana muhimmai cikin abubuwan da muka zanta. Domin hira ce doguwa, wajen minti hamsin da dakiku arba’in, kuma daga farko har karshe a kan harkan fasahar sadarwa ne hiran ya dogara. Don haka nake kara godiya gare su, Allah Ya bar zumunci. Ina kuma neman uzuri wajen wasu daga cikin masu karatu da ke nan Zariya, wadanda ban sanar da su zuwa na ba, musamman Muntaka AbdulHadi dake Jami’ar Ahmadu Bello. A min afuwa, lokaci ne ya kure mani shi yasa. Allah sa mu dace gaba daya, amin.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)

Fasaha2007@yahoo.com 08034592444

No comments:

Post a Comment