Yaduwar hanyar sadarwa ta wayar salula a duniya ta haddasa jita-jita a tsakanin masu mu’amala da wannan sassaukar hanyar sadarwa. Wannan jita-jita wacce ta shafi irin illolin da ke dauke da wayar salula ko rashinsu, bata tsaya ko takaitu da kasashe masu tasowa ba kadai, hatta a kasashen da suka ci gaba, inda aka kirkiri wannan fasaha, ana samun wannan jita-jita. Kai kusan ma dai ta fi yaduwa ma a can wajensu. Wannan tasa wasu cibiyoyin bincike na asibitoci da wasu jami’o’in da ke wadannan kasashe suka shiga dakunan bincike don gano ko akwai alaka tabbatacciya tsakanin yawaita amfani da wayar salula da kuma lafiyar dan Adam, musamman samuwar cutar sankara, ko cancer a turance. Kafin mu yi nisa, yana da kyau mu san cewa ba wai cutar sankara kadai ba, akwai jita-jita da dama da ke yawo cewa mutumin da ke yawaita amfani da wayar salula na tsawon lokaci, yana iya zama bakarare, watau ya kasa haihuwa, saboda rashin tagomashin da maniyyinsa zai samu sanadiyyar hakan. To meye hakikanin gaskiyar wadannan jita-jita da ke yawo?
Yaduwar hanyar sadarwa ta wayar salula a duniya ta haddasa jita-jita a tsakanin masu mu’amala da wannan sassaukar hanyar sadarwa. Wannan jita-jita wacce ta shafi irin illolin da ke dauke da wayar salula ko rashinsu, bata tsaya ko takaitu da kasashe masu tasowa ba kadai, hatta a kasashen da suka ci gaba, inda aka kirkiri wannan fasaha, ana samun wannan jita-jita. Kai kusan ma dai ta fi yaduwa ma a can wajensu. Wannan tasa wasu cibiyoyin bincike na asibitoci da wasu jami’o’in da ke wadannan kasashe suka shiga dakunan bincike don gano ko akwai alaka tabbatacciya tsakanin yawaita amfani da wayar salula da kuma lafiyar dan Adam, musamman samuwar cutar sankara, ko cancer a turance. Kafin mu yi nisa, yana da kyau mu san cewa ba wai cutar sankara kadai ba, akwai jita-jita da dama da ke yawo cewa mutumin da ke yawaita amfani da wayar salula na tsawon lokaci, yana iya zama bakarare, watau ya kasa haihuwa, saboda rashin tagomashin da maniyyinsa zai samu sanadiyyar hakan. To meye hakikanin gaskiyar wadannan jita-jita da ke yawo?
Dangane da abinda ya shafi rashin haihuwa sanadiyyar amfani da wayar salula na tsawon shekaru ko lokaci, wani gidan yanar sadarwa na kwararru kan harkar haihuwa da abinda ke haddasa ko rage samuwarsa, mai suna Reproductive Biomedicine Online, ya tabbatar da cewa babu wata alaka ko hujja tabbatacciya da ke nuna hakan, ko kadan. Wannan tabbaci ya biyo bayan wani bincike ne da wani asibitin haihuwa dake kasar Amurka yayi cikin watan Janairun da ya gabata, cewa ana iya samun raunin kwayar halitta dake cikin maniyyin namiji da ka iya rage masa karfin haihuwa, idan ya dauki tsawon shekaru yana amfani da wayar salula. Sakamakon wannan bincike ya ta’allake ne da nazarin da asibitin yayi kan wasu mazaje dari uku da sittin da daya, wanda ke nuna raguwar karfin maniyyin wadannan mazaje, sanadiyyar tsawon lokacin da suka dauka suna mu’amala da wayar salula a rayuwarsu. Har wa yau, akwai bincike da wata cibiya ta yi kan wasu beraye na tsawon makonni goma shatakwas, inda a kullum ake dumama su cikin tururin walkiyar dake fitowa daga cikin wayar salula a yayin da ake amsawa ko yin Magana da wanda aka kira, na tsawon sa’o’i shida. Sakamakon wannan bincike, Kaman wanda ya gabace shi, shi ma ya nuna samuwar raguwar inganci ko tagomashin maniyyin wadannan beraye daidai wannan lokaci. Wannan tasa masu binciken suka kulla alaka a tsakanin yawaita amfani da wayar salula da kuma raguwar tagomashin kwayoyin haihuwan da ke cikin maniyyin namiji. Sai dai, a nata bangaren, cibiyar magungunan haihuwa mai suna Reproductive Biomedicine Online tace ba lalai bane wannan alaka ta zama tabbatacciya. Idan ma akwai alakar, to bata kai wani matsayin da za ta zama abin damuwa ba. Maimakon haka ma, tsananin gurbatar yanayi (pollution) da yawan shan taba sigari sun fi hadari wajen haddasa rashin haihuwa fiye da hadarin lazimtar amfani da wayar salula.
A daya bangaren kuma, kwararru kan cutar sankara, musamman wacce ta shafi kwakwalwa, ra’ayoyin su sun sha bamban kan samuwar alaka tsakanin amfani da wayar salula da kuma samuwar cutar a kwakwalwar mai yi. Akwai nau’ukan cutar sankara guda biyu da ake danganta samuwarsu ga yawan amfani da wayar salula. Wannan jita-jita, a cewar kwararru, ya samo asali ne sanadiyyar tururin hasken da ke fitowa a yayin da mai amfani da wayar salula ke yi, wanda kuma ke shigewa kai tsaya zuwa kwakwalwarsa. Hakan, a cewar wasu masu binciken alaka, kan haddasa samuwar wani curin tsokar nama a kwakwalwar mutum. Wannan curin tsoka kuma da zarar ta bunkasa, sai ta haddasa samuwar nau’ukan ciwon sankara, watau cancer, iri biyu. Nau’i na farko ita wacce ke samuwa ta dalilin curin tsoka da ke tsirowa a kwakwalwa, wacce idan ta bunkasa, tana iya takura wa muhallin da jijiyoyin kwakwalwa suke, har ta toshe su, ta hana su sakewa. Wannan, inji masanan, a karshe, yana haifar da toshewar hanyoyin numfashi da dan Adam ke amfani dasu wajen tafiyar da rayuwarsa. Wannan nau’in sankara ita ake kira Glioma tumor. Sai nau’i na biyu, wacce ke samuwa a mahadar da ke tsakanin kunne da kwakwalwa, wacce ake wa lakabi da Acoustic neuroma tumor. Duk da cewa wannan nau’in bata da hadari sosai, amma tana iya haddasa rashin sukuni idan ta bunkasa ita ma. Wannan tasa Hukumar Cutar Sankara ta kasar Amurka, watau American Cancer Society ta bayar da sanarwar cewa, akwai tabbacin alaka tsakanin wannan cuta ta sankara da yawan amfani da wayar salula.
Amma a nata bangaren, Hukumar Abinci da Magunguna ta kasar bata yarda da galibin sakamakon wadannan bincike ba. Domin, ta la’akari da bincike nau’i uku da aka gabatar kan haka tun shekarar 2000, babu wani abin damuwa kan kamuwa da cutar sankara don an dauki tsawon lokaci ana amfani da wayar salula. Wannan shine ra’ayin Kungiyar Kamfanonin Sadarwa ta Wayar Iska, watau CTIA-Wireless Association. Wannan kungiya tace “dangane da binciken da aka gabatar a baya, akwai tabbacin babu wata hadari da wayar salula ka iya haifarwa ga lafiyar masu amfani da ita.”
Wannan takaddama da ake ta tafkawa dai ta samu ne sanadiyyar rashin wata tabbatacciyar ka’ida ko mataki da masu binciken ke amfani da su don gane alaka a tsakanin yawan amfani da wayar salula da kuma cutar sankara, a misali. A yayin da wasu ke amfani da shekaru uku wajen gane tasiri, wasu sun ce za a iya samun alaka ne idan yawan amfani da wayar salula ya kai tsawon shekaru goma. Wasu binciken da aka gabatar a kasashe irin su Isra’ila da Siwidin na nuna cewa akwai alaka. Wadanda aka gabatar a wasu kasashe kuma na nuna babu alaka. Wannan tasa da dama cikin masana ke ganin hanya mafi sauki ita ce mutum ya kiyaye ka’idojin amfani da wayar salula. Hakan na cikin abinda wasu masana cutukan kwakwalwa da Larry King yayi hira dasu cikin watan Mayu a shirinsa mai suna Larry King Live, suke ganin dacewarsa; suka ce in ma akwai, a kalla mutum ya samu kariya. Idan kuma babu alaka, to daman abinda ake so kenan. Daga cikin hanyoyin akwai yin amfani da na’urar jin Magana ta kunne, watau Ear Piece, ko kuma sanya wayar a tsarin Speaker Phone, lokacin da kake amsa waya ko kiran wani. Wannan zai sa ka tsira daga tururin hasken da ke fitowa daga jikin wayar; maimakon ya zarce zuwa kwakwalwarka, sai ya bi iska. Domin rigakafi, inji Hausawa, ya fi magani.