Yaduwar hanyar sadarwa ta wayar salula a duniya ta haddasa jita-jita a tsakanin masu mu’amala da wannan sassaukar hanyar sadarwa. Wannan jita-jita wacce ta shafi irin illolin da ke dauke da wayar salula ko rashinsu, bata tsaya ko takaitu da kasashe masu tasowa ba kadai, hatta a kasashen da suka ci gaba, inda aka kirkiri wannan fasaha, ana samun wannan jita-jita. Kai kusan ma dai ta fi yaduwa ma a can wajensu. Wannan tasa wasu cibiyoyin bincike na asibitoci da wasu jami’o’in da ke wadannan kasashe suka shiga dakunan bincike don gano ko akwai alaka tabbatacciya tsakanin yawaita amfani da wayar salula da kuma lafiyar dan Adam, musamman samuwar cutar sankara, ko cancer a turance. Kafin mu yi nisa, yana da kyau mu san cewa ba wai cutar sankara kadai ba, akwai jita-jita da dama da ke yawo cewa mutumin da ke yawaita amfani da wayar salula na tsawon lokaci, yana iya zama bakarare, watau ya kasa haihuwa, saboda rashin tagomashin da maniyyinsa zai samu sanadiyyar hakan. To meye hakikanin gaskiyar wadannan jita-jita da ke yawo?

Dangane da abinda ya shafi rashin haihuwa sanadiyyar amfani da wayar salula na tsawon shekaru ko lokaci, wani gidan yanar sadarwa na kwararru kan harkar haihuwa da abinda ke haddasa ko rage samuwarsa, mai suna Reproductive Biomedicine Online, ya tabbatar da cewa babu wata alaka ko hujja tabbatacciya da ke nuna hakan, ko kadan. Wannan tabbaci ya biyo bayan wani bincike ne da wani asibitin haihuwa dake kasar Amurka yayi cikin watan Janairun da ya gabata, cewa ana iya samun raunin kwayar halitta dake cikin maniyyin namiji da ka iya rage masa karfin haihuwa, idan ya dauki tsawon shekaru yana amfani da wayar salula. Sakamakon wannan bincike ya ta’allake ne da nazarin da asibitin yayi
A daya bangaren kuma, kwararru
Amma a nata bangaren, Hukumar Abinci da Magunguna ta kasar bata yarda da galibin sakamakon wadannan bincike ba. Domin, ta la’akari da bincike nau’i uku da aka gabatar
Wannan takaddama da ake ta tafkawa dai ta samu ne sanadiyyar rashin wata tabbatacciyar ka’ida ko mataki da masu binciken ke amfani da su don gane alaka a tsakanin yawan amfani da wayar salula da kuma cutar sankara, a misali. A yayin da wasu ke amfani da shekaru uku wajen gane tasiri, wasu sun ce za a iya samun alaka ne idan yawan amfani da wayar salula ya kai tsawon shekaru goma. Wasu binciken da aka gabatar a kasashe irin su Isra’ila da Siwidin na nuna cewa akwai alaka. Wadanda aka gabatar a wasu kasashe kuma na nuna babu alaka. Wannan tasa da dama cikin masana ke ganin hanya mafi sauki ita ce mutum ya kiyaye ka’idojin amfani da wayar salula. Hakan na cikin abinda wasu masana cutukan kwakwalwa da Larry King yayi hira dasu cikin watan Mayu a shirinsa mai suna Larry King Live, suke ganin dacewarsa; suka ce in ma akwai, a kalla mutum ya samu kariya. Idan kuma babu alaka, to daman abinda ake so kenan. Daga cikin hanyoyin akwai yin amfani da na’urar jin Magana ta kunne, watau Ear Piece, ko kuma sanya wayar a tsarin Speaker Phone, lokacin da kake amsa waya ko kiran wani. Wannan zai sa ka tsira daga tururin hasken da ke fitowa daga jikin wayar; maimakon ya zarce zuwa kwakwalwarka, sai ya bi iska. Domin rigakafi, inji Hausawa, ya fi magani.
No comments:
Post a Comment