Tuesday, July 1, 2008

Labaran Mako


Sagey Brian Zai Kai Ziyara Zuwa Sararin Samaniya (http://www.upi.com): Sagey Brian, daya cikin shugabannin kamfanin Google Inc. ya biya zunzurutun kudi dala miliyan biyar ($5m), wajen naira miliyan dari shida da hamsin kenan, don siyan tikitin kumbon kai ziyara a sararin samaniya don yawon shakatawa. Kamfanin Space Adventures da ke Virginia a kasar Amurka ya tabbatar da hakan cikin makon da ya gabata. Kamfanin yace duk da wannan kudi da ya biya, ba dole bane sai Brian yayi wannan tafiya, yana iya sayar da tikitin ga wani mai bukata kafin lokacin tafiyar. Har wa yau, yace wannan kashin farko kenan cikin kudaden da zai biya, ba wai duka ya biya ba. A nasa bangaren, Brian, wanda ya nuna farin cikinsa don samun wannan dama na kai ziyara zuwa sararin samaniya, ya sanar da cewa yana cikin masu sha’awan ganin wannan harka ta safarar mutane zuwa sararin samaniya ta habaka. Daga shekarar 2001 zuwa yanzu, kamfanin safarar masu kai ziyara sararin samaniya na kasar Rasha ta hanyar kumbo, ya kai mutane biyar don shawagi a sararin samaniya. Kuma a kalla kudin tikiti daya ya kai dalar Amurka miliyan ashirin, kwatankwacin naira biliyan biyu da miliyan dari shida da hamsin kenan.

Sagey Brian dai, tare da Andrew Page ne suka kafa kamfani da gidan yanar sadarwar manhajar matambayi-ba-ya-bata ta Google (www.google.com) cikin shekarar 1998. A halin yanzu kamfanin na gaba wajen samun kudaden shiga cikin jerin kamfanonin sadarwa, a duk shekara, inda aka kiyasta ya samu ribar dalar Amurka biliyan goma cikin shekarar 2006. Brian da Page dai na cikin matasan masu kudi a kasar Amurka.

Hukumar NASA ta Cilla Kumbon Bincike Cikin Falaki (http://www.nytimes.com): Hukumar habaka bincike cikin sararin samaniya da dukkan falakin wannan duniya, watau NASA, ta cilla wani kumbo zuwa falaki, don lura da kuma yin nazari kan wasu manyan buraguzan haske masu kai-komo cikin falaki ko hanyoyin taurarin da ke sararin wannan duniya tamu. Wannan kumbo, wanda hukumar ta aika ranar laraba, 12 ga watan Yuni, yana dauke ne da wani madubin hangen nesa na musamman watau telescope, wanda zai dauki hoton wadannan nau’ukan haske da ke haddasuwa kuma suna bacewa cikin kankanin lokaci. Bayan sa’a daya da rabi kumbon da ke dauke da wannan madubin hangen nesa ya isa muhallinsa a sararin samaniya, inda ya cilla madubin cikin falaki, bayan tafiyar mil 350 daga sararin wannan duniya tamu. Wannan shiri dai yaci a kalla dalar Amurka miliyan dari shida da casa’in ($690,000,000.00), kuma binciken hadin guiwa ne tsakanin hukumar NASA da kuma hukumar Makamashi ta Amurka, masu kokarin gano nau’in makamashin da ke cikin wannan haske.

Kafin wannan shekara, binciken baya da aka yi kan wadannan ire-iren hasken da ke darsuwa a cikin hanyoyin taurari ko falaki da a turance ake kira gamma-rays, ya nuna cewa wadannan nau’uka na haske na cillowa ne daga wasu ramuka ko koguna masu duhu, kuma ba su bayyana a sararin wannan samaniya tamu, balle a gansu. Wannan ya sa dole a je inda suke darsuwa, don yin nazari kansu. Nau’in hasken gamma-ray dai, shine matakin haske mafi kaifi da saurin maimaituwa wajen darkake abinda ya dosa a muhallinsa. Wasu daga cikin nau’ukan hasken dai sun hada da wankakken hasken rana da muke mu’amala dashi a wannan duniya tamu, da gundarin hasken rana wanda ke fitowa kai tsaye daga ranar, sai hasken da ke game duniya mara zafi. Daga cikin su har wa yau, akwai hasken da ke kasa da gani ko idon dan Adam, mai taimakawa wajen sadarwa ko dafa abinci, irin su hasken Microwave, da kuma makamashin Infra-red.

Sanarwa

Hukumar makarantar koyon ilimin kwamfuta da sassanta, watau NIIT, ta fara raba fom don yin jarabawar shiga da ake sa ran rubutawa cikin watan gobe, watau Yuli. Ga duk mai bukatar rubuta jarabawar, yana iya zuwa reshen Zenith International Bank da ke biranen kasar nan, don karban fom din. Kyauta ake bayarwa, ba ko sisin kwabo. Idan ka cike fom din ka mayar musu dashi, ko kuma ka kai reshen makarantar da ke Kaduna ko Kano ko Ibadan ko Legas ko kuma Abuja, idan a nan kake. idan lokacin rubuta jarabawar yayi, zasu aiko maka da adireshin inda zaka je don rubutawa. Ka’idar su ita ce, idan ka samu martaba ta karshe, watau “A++”, za a zaftare maka sama da dubu dari biyu cikin kudin da zaka biya. Idan ka samu “A” ko “B+”, za a rage maka kasa da haka, har dai iya kwazonka. Ga duk mai sha’awa, yaje reshen Zenith Bank ko kuma reshen makarantar, a daya daga cikin biranen da aka zayyana a sama.

Abdullahi Salihu Abubakar

08034592444; fasaha2007@yahoo.com

http://fasahar-intanet.blogspot.com

No comments:

Post a Comment