Bayan makonni da muka shafe muna tattaunawa kan kwamfuta da fasahar Intanet, daga wannan mako zamu juya akalarmu zuwa wasu fannoni na kimiyya da fasaha, musamman kan yadda samuwar hakan ke tasiri wajen rayuwarmu a ilimance da sauran hanyoyi. Don haka a wannan mako mun kawo wasu daga cikin muhimman labarai ne kan fannin kimiyya da fasaha. A makonni masu zuwa in Allah Ya yarda, za mu ci gaba da kwararo bayanai kan wasu fannonin kuma. Kuma kamar yadda aka saba, idan akwai tambayoyi ko bayanan neman Karin bayani, sai a rubuto ko bugo waya. A ci gaba da kasancewa tare da mu.
Steve Ballmer Zai yi Ritaya nan da Shekaru Goma (http://www.pcmag.com): Shugaban kamfanin Microsoft mai ci yanzu, watau Steve Ballmer, ya bayyana cewa da zarar dansa na karshe ya samu shiga jami’a, nan da shekaru tara ko goma masu zuwa, zai yi ritaya daga shugabancin wannan kamfani. Ballmer, wanda ya gaji shugabancin kamfanin daga tsohon shugaba Bill Gates, ya bayyana hakan ne a lokacin wata dina da kungiyar kamfanonin lantarki ta Amurka (American Electronics Association) ta shirya. Steve yace “nayi shekaru ashirin da takwas a kamfanin Microsoft…don haka nake gaya wa mutane cewa zan ci gaba da zama a wannan kamfani har lokacin da da na na karshe zai shiga jami’a; nan da shekaru tara ko goma kenan masu zuwa.” Ya ci gaba da cewa “nan da shekaru goma masu zuwa muna sa ran ci gaba da kirkiro sabbin hanyoyin ci gaba na sadarwa, masu inganci.”
Steve Ballmer dai na cikin wadanda suka taimaka wajen bunkasa wannan kamfani na Microsoft tun bayan kafa kamfanin a shekarar 1975, lokacin da Bill Gates da abokinsa Paul Allen suke ta kai-komo tsakanin Amurka da kasar Jafan. A halin yanzu shine shugaba mai ci, kuma yana da kebantacciyar baiwa wajen ilimin lissafi da fasahar sadarwa.
Za a Kirkiri Sabon Kumbon Binciken Sararin Samaniya Mai Zaman Kansa (http://www.astronomytoday.com): Hukumar Binciken Kimiyyar Tsaron kasar Amurka watau Defense Advanced Research Project Agency – DARPA) ta bayar da kwamgilar kera wani sabon kumbon binciken sararin samaniya mai zaman kansa. Wannan sabon kumbo, wanda zai sha bamban da sauran kumbon binciken Amurka na yanzu, za a kera shi ne don aiwatar da wani bincike na musamman a sararin samaniya. Kumbon, a cewar kamfanin binciken sararin samaniya mai zaman kanta ta Aurora, wacce kuma aka baiwa kwangilar kerawa, zai zama mai zaman kansa ne a sararin samaniya, bai da direba balle masu lura da kai-komonsa a ciki. A cewar wannan kamfani, wannan kumbu na iya rayuwa tsawon shekaru biyar a sararin samaniya yana aiwatar da bincike ta hanyar kai-komonsa ba tare da wata matsala ba. Wannan ya sha bamban da nau’ukan kumbon da ake amfani dasu a yanzu, wadanda ke bukatar direba da mai lura da shawaginsu a duk inda suka je. Galibinsu kan yi shawagi ne na tsawon awanni ko kwanaki, daga baya su sauko, bayan sun gama binciken da suka je yi, wanda galibi ya kunshi daukan hotunan wasu wurare ne da kuma taskance bayanai kan yanayin wasu duniyoyin.
An Kera Kwamfuta Mafi Sauri a Duniya (http://ap.google.com): An kera kwamfuta mafi sauri wajen sarrafa bayanai da daukan umarnin mai mu’amala da ita a duniya. Irin wannan kwamfuta a halin yanzu ita ce mafi sauri da inganci a duniya a yanzu, domin tana iya sarrafa bayanai sama da tiriliyon dubu a cikin dakika (second) daya. Sashen bincike da makamashi na kamfanin kwamfuta ta IBM Corp. ya bayyana hakan a ranar litinin da ta gabata. Kamfanin yace za a yi amfani da wannan kwamfuta ne aikin binkasa makamashin nokiliyi na kasar. Wannan kwamfuta, wacce aka sanya wa suna Roadrunner, na iya sarrafa bayanai sama da tiriliyon dubu daya cikin kasa da dakika guda. Samuel Bodman, shugaban sashen makamashi na kamfanin IBM Corp. yace bayan amfani wajen bunkasa harkar nukiliya da wannan kwamfuta za ta yi, ana sa ran amfani da ita wajen bunkasa harkar makamashi a duniya, da kuma wasu hanyoyin bunkasa ilimi da binciken.
Kumbon Binciken Sararin Samaniya ya Kammala Aikinsa (http://news.google.com): Masu ziyarar bincike a cibiyar binciken sararin samaniya sun kammala aikinsu ranar litinin na wannan mako, kuma ana sa ran dawowansu ranar laraba. Masu ziyarar binciken sun kai ziyara ne zuwa duniyar Mirrik, watau Mars, don yin bincike kan samuwar ruwa da yanayin kasar da ke wannan duniya, ko dan Adam na iya yin aiyukan da yake yi a wannan duniya ta mu da muke rayuwa ciki. Wannan bincike ne na hadin-guiwa tsakanin kwararru kan ilimin sararin samaniya na kasar Amurka na da kasar Jafan. Kumbon na dauke ne da manyan direbobi biyu da kuma sauran mutane takwas masu rakiya. Sun yi wannan tafiya ne da wani mutum-mutumi (Robotic) wanda aka kashe wajen dalar Amurka biliyan daya ($1billion) wajen kera shi. Shine ya taimaka musu wajen karto yanayin kasan da ke wannan duniya ta Mirrik, da irin nau’in yanayin da ke wannan bigire. Yana kuma dauke ne da hannaye shida, wadanda direbobin suka yi amfani dasu wajen wannan aiki. A safiyar litinin na wannan mako aka kalmashe dukkan hannayen wannan mutum-mutumi gaba daya, kuma zuwa ranar laraba wadannan kwararru zasu taso zuwa wannan duniya tamu. Amma kafin nan, direbobin sun yi wa juna bankwana, don da zarar an wayi garin laraba, kowa zai kama hanyarsa.
Hukumar PEF ta Baiwa Makarantu Tallafin Kwamfutoci (http://www.dailytrust.com): Hukumar Petroleum Equalization Fund, watau PEF, ta baiwa makarantar sakandare ta Tudun Wada, da ke Zone 4, a Abuja tallafin kwamfutoci guda goma don bunkasa harkar karantarwa da inganta ilimi a babban birnin tarayyar Abuja. Tallafin, wanda ya hada da na’urar dab’i, watau printer, guda goma, da kuma na’urar taskance wutar lantarki ta wucin-gadi, watau UPS, su ma guda goma, na cikin yunkurin da wannan hukuma ke yi wajen taimaka wa al’umma ta hanyar inganta ilimi, a cewar babban sakataren hukumar, watau Mrs Adefunke Kasali. Ta kuma bukaci daliban makarantar da su ma su taimaka wa wasu yayin da suka gama makaranta suka samu kansu a halin taimakawa. Sannan, “ku matsa wa malamanku don su koya muku amfani da wadannan kwamfutoci’, inji babban sakataren, a yayin da take jawabi wajen mika wadannan kyaututtuka ga hukumar makarantar.
No comments:
Post a Comment