Tuesday, July 1, 2008

Labaran Mako

An Samu Alamar Dausayi a Duniyar Mirrik (http://www.bbc.co.uk/news): Binciken da kumbon Phoenix ya kai zuwa duniyar Mirrik (Mars) cikin makonnin da suka gabata na nuwa cewa akwai alamun dausayin kankara a wannan duniya, wanda hakan, a cewar kwararru, alama ce da ke nuna cewa dan Adam zai iya rayuwa a can. Wannan ziyara ta bincike da kumbon Phoenix ya kai zuwa Mirrik cikin watan Afrailu, ziyara ce ta musamman, wadda ta samu goyon bayan masu bincike kan sararin samaniya na kasar Jafan. Masu binciken da ke cikin wannan kumbo sun tafi ne da wani mutum-mutumi (robotic) mai kafafu da hannaye, wanda kuma shine ya kankaro nau’in kasar da ke can duniyar Mirrik, tare da daukan hoton muhalli da kuma ramukan da ya karto wannan kasa. Cikin burbushin nau’in kasar da ya debo ne masana suka samu alamar dausayi mai farin launi. Bayan wasu kwanaki, sai wannan dausayi ya bace daga nau’in kasar da aka debo. “Wannan”, a cewar Dakta Peter Smith, masani kan harkar falaki da sararin samaniya, “alama ce da ke nuna cewa kankara ce, ba wai gishiri, ba”, sabanin yadda wasu masana suke cewa da farkon gano wannan dausayi.

Duk da cewa binciken baya da aka yi a wannan duniya ya tabbatar da samuwar wannan dausayi mai dauke da kankara, babban manufar ziyarar Phoenix ita ce tabbatar da ko dan Adam na iya rayuwa a wannan nahiya ta duniya. Wannan mutum-mutumi dai ya dakatar da aikin tono kasar ne a yayin da daya daga cikin hannayensa ya ci karo da wani tsauri mai tsanani a yayin da yake aikin tonon. Tuni dai mazu wannan ziyara suka sauko wannan duniya tamu lafiya kalau, kuma ana can ana ci gaba da bincike kan nau’ukan kasa da kuma hotunan da kumbon Phoenix ya dauko, don samun tabbacin rayuwar dan Adam a wannan duniya ta Mirrik.

An Harba Kumbon Binciken Yanayi Zuwa Cikin Falaki (http://www.bbc.co.uk/news): Cikin makon da ya gabata ne Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta kasar Amurka, watau NASA, ta harba wani kumbo zuwa falakin wannan duniya don yin bincike na musamman kan yanayin da manyan tekunan duniya ke gudanuwa. Kumbon, mai suna Jason-2 Satellite, ya bar wannan duniya tamu ne safiyar Jumma’a, daidai karfe bakwai da minti arba’in da shida, ta hanyar roket mai suna Delta-2. Wannan bincike ne na hadin guiwa tsakanin kasar Amurka da kasar Faransa, inda ake son gano yanayin manyan tekunan duniya. Ana sa ran sakamakon wannan bincike zai taimaka wa hukumomin da ke lura da yanayi a duniya, ta hanyar samun bayanai masu gamsarwa kan hasashen yanayi a kullum. A lokacin ziyararsa, kumbon Jason-2 zai dauki hoton kusan kashi casa’in da biyar na dukkan manyan tekunan duniya, da karfin gudun ruwa da kuma jihar da galibin tekunan duniya ke bi. Don tantance yadda yanayi zai rika kasancewa a kullum. Jason-2 zai rika aiko da ire-iren wadannan hotuna da yake dauka ne a dukkan kwanaki goma, a yayin da yake yawo cikin falaki. A halin yanzu dai akwai kumbon Jason-1 da ke kai komo cikin falaki don irin wannan aiki. Da zarar ya isa cikin falaki, Jason-2 zai taya shi, inda zasu rika yawo tare, a tazarar da bata wuce na dakiku sittin ba.

Wasu Samari ‘Yan Dandatsa Sun Shiga Hannu (http://news.google.com): Wasu samari biyu a kwalejin Tesoro da ke Orange County a jihar Kalifoniya, sun shiga hannu. An gurfanar da Omar Khan dan shekara shatakwas, da Tanvir Singh shi ma dan shekara shatakwas ne a kotun koli da ke birnin Orange County na jihar Kalifoniya da ke Amurka. A cewar masu gabatar da kara, Omar Khan, wanda dalibi ne a wannan kwaleji, na fuskantar dauri ne sanadiyyar aikin dandatsanci da yayi wa kwamfutocin makarantar, a kokarinsa na canza darajar karatunsa. Khan, a cewar kuliya, ya aikata laifuka sittin da tara sanadiyyar wannan dandatsanci da yayi. Idan kuma ta sameshi da laifi karara, Omar Khan na fuskantar barazanar zaman gidan yari na tsawon shekaru talatin da takwas. A halin yanzu an bayar da belinsa kan dalar Amurka dubu hamsin ($50,000).

A nasa bangaren, Tanvir Singh na fuskantar tuhuma kan cin amanar kasa, da satan bayanai da canza su da kuma dukkan wani laifi da ya shafi yin amfani da kwamfuta wajen aikata ta’addanci. Wannan tuhuma ya biyo bayan kama shi da aka yi ne lokacin da ya samu shiga cikin kwamfutocin makarantar, ta hanyar satar kalmomin iznin shigar malaminsu, tare da kuma dasa manhajar leken asiri (spyware) a kwamfutar malamin (wacce ke jone kan gajeren zangon sadarwar makarantar), don samun damar ganin sakamakon karatunsa ta karshe, inda ya caccanza wasu daga darajojin “C” da “D” da “F”, zuwa darajar “A”, tare da na wasu abokanansa goma shabiyu. Bayan laifin shiga kwamfutar makarantar ba tare da izni ba da kotun ke tuhumarsa, har wa yau ta tuhumeshi da laifin satowa da kuma canza bayanan sirri, tare da bata kwamfutar ta hanyar dasa manhajar kwayar cutar kwamfuta da leken asiri. Sabanin abokinsa Khan, Singh na fuskantar barazanar dauri ne na tsawon shekaru uku.

Har way au, ana tuhumar dukkan samarin biyu da hada wajen tsara hanyar shiga gajeren zangon kwamfutar makarantar, wanda hakan zai basu damar yin yadda suke so da dukkan bayanan da ke cikin uwar garken makarantar gaba daya, musamman abinda ya shafi satar takardun jarrabawan da ba a riga aka rubuta sub a. Sheda a kan haka shine sakonnin wayar salula (text messages) da aka samu a wayoyin kowannensu, masu nuna alaka da abinda ke faruwa. A halin yanzu an daga wannan shari’a zuwa watan Yuli.

Kamfanin Yahoo! Ya Fadada Rumbun Imel Dinsa (http://news.zdnet.com): Kamfanin Yahoo! ya kara fadada rumbun Imel dinsa don baiwa masu bukatar rajistar akwatin Imel damar yi ba tare da matsala ba. Kafin wannan lokaci, manhajar Imel ta takaita ne da uwar garken “yahoo.com” kadai. Duk mai bude akwatin Imel da wannan uwar garke (mail server) yake mu’amala. Wannan tasa a karshe da wahala ka samu irin sunar da ke kake so, sai wanda uwar garken ta zaba maka. Idan ba wadanda suka bude adireshin Imel shekaru biyar da suka gabata ba, zaka samu sunayen adireshinsu na hadawa ne da lambobi (gamagari143@yahoo.com, a misali). Hakan bai rasa nasaba da yawan jama’a da suka yi rajista tsawon lokaci, kuma a ka’idar adireshin Imel, dole kowane adireshi ko suna ya zama shi kadai. Ba a samun sunaye biyu masu kama da juna. A halin yanzu akwai sunayen adireshin Imel sama da miliyan dari biyu da sittin da masu amfani da wannan uwar garke suka kirkira ko bude. Wannan ya tilasta wa hukumomin Yahoo! fadada wannan rumbu don baiwa masu rajista damar yin rajista da irin sunan da suke bukata ba wanda aka tilasta musu ba. Kamfanin ya kara wasu iyayen garke biyu; ymail.com, da kuma rocketmail.com. Rocketmail dai, idan ba a manta ba, tsohuwar manhajar Imel ce da kamfanin yahoo ya saya a shekarun baya, wacce a halin yanzu yake son yin amfani da ita don rajistar masu bude akwatin Imel.

Gidan yanar sadarwa na Yahoo! na cikin tsoffin gidajen yanar sadarwa masu dauke da manhajar Imel na kudi da na kyauta. Kamfanin ya shahara wajen harkar Imel, inda a halin yanzu ya bullo da tsarin shigar da manhajar Imel cikin wayoyin salula irin Blackberry da sauran makamantansu.

No comments:

Post a Comment