Tuna Baya Shine Roko
A yayin da kamfanin Media Trust, mai buga jaridar AMINIYA ke bukin cika shekaru biyu da fara wannan jarida mai matukar farin jini, mu ma a wannan shafi na Kimiyya da Fasaha, bayan taya AMINIYA murnar kaiwa wannan lokaci, na farin cikin sheda wa masu karatu cewa a cikin mako mai zuwa, shafin Kimiyya da Fasaha zai cika shakaru biyu cur! Ga wadanda suka fara bibiyan wannan shafi daga lokacin da ya fara bayyana zuwa yanzu, watakil suna iya tuna kasidar farko da ta fara bayyana a wannan shafi, mai taken Fasahar Intanet a Saukake (1). Hakan ya faro ne cikin watan Okotobar shekarar 2006. A yau, cikin yardan Allah, sai ga mu gab da Oktoba ta shekarar 2008. Shekara kwana, in ji Bahaushe! Wannan tasa muka ga dacewar zama na musamman, kamar yadda muka yi a lokutan baya, don yin waiwaye; abinda Malam Bahaushe ke kira adon tafiya.
Darussan Baya
Wannan shafi na Kimiyya da Fasaha ya faro ne da kasidu kan Fasahar Intanet da yadda ake mu’amala da ita. Mun kuma kasa kasidun da ke bayyana a wannan shafi ne zuwa marhala-marhala, don saita masu karatu a kan hanya; su fahimci tsarin da hanyoyi da kimiyyar sadarwa da ta maddar rayuwa da muhalli ke gudanuwa da samuwa. A yanzu mun zo karshen marhala ta biyar kenan. A marhalar farko, mun gabatar da kasidu ne kan hanyoyin mu’amala da fasahar Intanet zalla. Kasidun sun gudanu ne a tsarin karantarwa da ke kumshe da kwatance da misalai. Daga abinda ya shafi tarihi da bunkasar Intanet, zuwa yadda ake shiga shafukan yanar sadarwa, da yadda ake gina gidan yanar sadarwa da kuma amfanin da ke tattare da fasahar Intanet din gaba daya. A marhala ta biyu, sai tsarin kasidun ya canza, zuwa sanayya kan masu hakkin lura da kuma gyarta fasahar Intanet, da alakar Intanet da harkokin rayuwa, da zuwan Intanet kasar Hausa, da masarrafar lilo da tsallake-tsallake, da manhajar Imel da kuma yadda ake ginawa da lura da Mudawwanar Intanet, watau Weblog ko Blog. Kasidar da tafi kowacce shahara a wannan marhala, ita ce wacce na rubuta kan Fasahar Intanet a Wayar Salula. A wannan marhala ne masu karatu suka fara rubuto sakonnin text da bugo waya, saboda tasirin abinda suke karantawa da karuwa dashi. Mun gama wannan marhala ne, kamar wanda ya gabace shi, da yin zama don waiwaye. A marhala na uku, sai muka tunkudo kasidu kan Dunkulallun Ka’idojin Mu’amala da Fasahar Intanet, da kuma Tasirin Fasahar Intanet ga Kwakwalwar dan Adam. Sai kuma kasidu kan Nau’ukan Fasahar Sadarwa a Intanet. Muka kuma kawo kasidu kan tsarin sadarwa a tsakanin kwamfutoci, da nau’in sadarwa a tsakanin wayar salula da kwamfuta. Wadannan kasidu ne masu tsawo da muka guggutsira su zuwa makonni. Kafin mu karkare wannan marhala da waiwaye adon tafiya, idan masu karatu basu mance ba, mun gabatar da kasidu da suka yi tasiri sosai kan Tsarin Sadarwa na Wayar Salula, watau Wireless Communication. Daga nan muka tsallaka zuwa marhala ta hudu, wacce ke dauke da kasidu masu kayatarwa su ma, kan Tsarin Sadarwa ta Bluetooth, da Tsarin Sadarwa ta Infrared, da kuma kasidu guda goma, kan yadda mai karatu zai iya kwarewa a fannin fasahar sadarwa ta zamani. Wadannan kasidu na kwarewa a fannin fasahar sadarwa, su ma sunyi tasiri sosai, inda masu karatu suka ta bugo waya ko aiko sakonnin neman karin bayani kan wadannan fannoni. Kafin mu karkare wannan marhala, mun tunkudo kasidu wajen bakwai, kan Kwayar Cutar Kwamfuta (Computer Virus), da kuma ‘Yan Dandatsa, watau Hackers, masu fasowa cikin kwamfutocin mutane a ko ina take a duniya, don aiwatar da ta’addanci na sata ko zalunci ko makamantansu. Wannan ita ce marhala mafi tsawo kuma wacce tafi yawan kasidu, cikin dukkan marhalolin da suka gabata. A karshe sai muka shiga marhala ta biyar, wacce tsarin darussan shafin ya sauya daga wadanda suka bayyana lokutan baya. A wannan marhala ne muka shiga bayanai kan sauran fannonin kimiyya sosai ; daga kimiyyar sararin samaniya zuwa kimiyyar maddar sinadarai da kuma muhalli. Saboda halin zaman dar-dar da duniya ke ciki da farfaganda da ake ta yadawa kan kasashe irinsu Iran da Koriya ta Arewa musamman, na ga dacewar gabatar da kasidu kan Asali da Tarihi da kuma Bunkasar Makamin Nukiliya a Duniya. Mun samu bayanai kan asali da tarihi, da kuma nau’ukan makamin, da mummunan tasirinsa da kuma kasashen da suka mallaki wannan makami. A karshe muka kawo bayanai kan dokar hana yaduwar makamin, da kuma hukumar da ke lura da wannan hani. A cikin marhalar dai har wa yau, mun kawo kasidu kan makamashin hasken rana, wanda bamu gama ba. Da kuma bayanai kan Fasahar Sadarwa ta GPRS, da Tsarin Sadarwa ta Rediyo a Intanet, sai kuma tsokaci da muka yi kan bambancin da ke tsakanin manhajar Windows XP da Windows Vista. Mun kawo labarai kan kimiyyar sararin samaniya da kuma alakar Wayar Salula da cutar sankara (Cancer). A karshe muka jefo kasida ta karshe kan na’urar Beran Kwamfuta da kuma yadda ake mu’amala da ita. Dukkan wadannan kasidu, suna nan a taskance cikin Mudawwanar wannan shafi da ke: http://fasahar-intanet.blogspot.com.
Me Muka Koya?
A dukkan marhalolin da suka gabata muna samun sakonnin masu karatu, na neman karin bayani ko na sambarka. Ta haka na fahimci himma da kuma tsananin sha’awar da galibin masu karatu ke da ita kan harkar kimiyya da fasahar sadarwa. Wanda har wa yau ke nuna cewa, galibin masu karatu na da sha’awar ci gaba da karatu ko kwatanta abinda suka karanta ko koya, amma babban matsalar wasu daga cikin su ita ce harshen Turanci. Sau tari na kan sanar da su cewa ko basu ji ko iya turanci ba, zasu iya koyan wannan ilimi, har su kware a kai. Har wa yau, galibin masu karatu hankalinsu yafi komawa kan koyan ilimin kwamfuta da Intanet, ko gina gidan yanar sadarwa, ko koyon gyarar kwamfuta da wayar salula, ko kuma karantar da ilimin don dacewa da zamani. Na fahimci hakan ne ta hanyar sakonnin text da nake samu ko masu bugo waya suna sanar dani ko neman karin bayani kan abinda suke son yi. Da dama sun shiga makaranta don koyon sabon ilimin kimiyyar sadarwa sanadiyyar kasidun da suke karantawa a wannan shafi. A halin yanzu akwai kungiyoyin makaranta jaridar AMINIYA (‘yan makarantar shafin Kimiyya da Fasaha) a jihohi dabam-daban a Arewacin Nijeriya. Akwai makarantar Malam Sani Na ‘Yan katsare da ke Jas, tare da abokansa. Akwai makarantar su Malam Hasan Al-Banna da ke garin Zariya, tare da abokansa irin su Malam Ishak AbdulHadi, tare da Muntaka Abdul-Hadi da ke Jami’ar ABU. Kwanakin baya da na je ziyarar aiki a Kano ina dawowa na sauka a Zariya, mun zanta da su Malam Hassan har na tsawon awa guda kan harkar kimiyyar sadarwa ta zamani. Haka akwai makarantar Malam Shazali Lawal da ke Zaburan Quarters a Gumel. Akwai kuma masu karatu na hakika a Kano da dama; daya daga cikinsu shine Malam Rabi’u Isa Ayagi. Akwai irinsu Malam Abdulsalam da ke Jas. Haka a nan Abuja akwai masu karatu da dama ke Wuse Zone 2, da Hukumar Kudi ta Tarayya (Ministry of Finance) irinsu Malam Mahmoud Muhammad, da kuma Makarantar Horar da Malamai da ke Zuba. Akwai wasu a Maiduguri, da Legas, da Katsina da Malumfashi da Gombe da Zamfara da Birnin Kebbi da Nassarawa, da Bauchi da Kaduna garin Gwamna, da Sokoto, da Yola da Jimeta da sauran wurare.
Kasidun da suka fi tasiri wajen masu karatu su ne wadanda suka shafi fasahar Intanet, musamman kan Mudawwana (Blog); da dama cikin masu karatu sun bude nasu, inda suke zuba bayanai da yada ra’ayoyinsu. Sai kuma kasida kan Fasahar Intanet a Wayar Salula, da kuma tsarin sadarwa ta wayar-iska. Hakika masu karatu sun tasirantu da wadannan kasidu. Don har yanzu akwai masu bugowa suna neman karin bayani kan haka. Ni kaina na san kasidun sun rubutu sosai, saboda kwakkwafi da na bi wajen rubuta su. Sai kuma kasida kan Fasahar Bluetooth da Infrared da kuma GPRS. Na sha tambaya kansu kam. Cikin kasidun baya-bayan nan, akwai kasidu kan Makamin Nukiliya, su ma sunyi tasiri sosai wajen masu karatu. Ni kaina na jigatu wajen rubuta su; don lokaci da aka kashe wajen bincike da kuma juya kalmomin zuwa harshen Hausa. Muna mika godiya zuwa ga Allah kan haka.
Daga Nan Sai Ina?
Hakika dukkan tafiyar da ke neman samun nasara, dole ta kasance da mahanga. Da zarar mun gama bikin cika shekara biyu da kafuwa, zamu ci gaba da koro kasidu da labarai kan kimiyya da fasahar sadarwa, da kuma kimiyyar sararin samaniya, da kimiyyar madda da kuma sinadaran da ke muhallin da muke rayuwa a ciki. Wannan zai shafi ilimi kan kwamfuta da Intanet, da kumbon sararin samaniya, da kimiyyar lissafi da kimiyyar madda, da kuma bincike ko ci gaba da ake samu a wadannan fannoni na rayuwa da ilimi. Hakika, idan akwai wani nau’in ilimi da galibin mutanenmu suka rasa, shine samuwar ire-iren wadannan fannoni a rubuce cikin harshen Hausa. A bayyane yake cewa kashi saba’in ko tamanin na littafan da ke kai-komo a tsakanin al’ummar Hausawa kan fannin kirkirarrun labarai ne, watau Fiction. Littafai ko bayanai kan fannonin ilimi tabbatattu basu yadu ba, sam ko kadan. Wanda kuma duk al’ummar da ke bukatar ci gaba, dole ne ya zama ilimin kimiyya da fasahar kere-kere ya zauna da kafafunsa; za a neme shi, a kuma same shi cikin sauki. Wanda hakan baya yiyuwa a yanzu, in ba ta hanyoyi irin wadannan ba. Don haka a ci gaba da kasancewa tare damu a wannan shafi. Akwai mudawwana ta musamman da muka tanada don taskance dukkan wadannan kasidu, wacce za a iya samun ta a wannan adireshin da ke sama. A iya rubuto sakonnin text (08034592444), da na Imel (fasaha2007@yahoo.com) don neman karin bayani. Kuma kamar yadda na sanar kwanakin baya, akwai littafai na nan tafe kan fannoni da dama cikin ilimin fasahar sadarwa cikin harshen Hausa.
Kammalawa
A karshe, muna mika dimbin gaisuwarmu ga dukkan masu karatu a ko ina suke. Ba za mu iya ambaton sunan kowa da kowa ba. Sai dai, kamar yadda muka saba, zamu ci gaba da sanya sakonnin da kuke aiko mana lokaci-lokaci. Kamar kullum, duk wanda ya rubuto don neman karin bayani amma bai samu jawabi ba, yayi hakuri. Ina nan tafe in Allah Ya so. Ina kuma mika godiyata ga sauran ma’aikatan AMINIYA da Media Trust gaba dayansu, musamman Malam Balarabe, da Malama Lubabatu I. Garba (Gwaggo Lubabatu), da Malam “Liman”, da Malam Abubakar AbdurRahman (Dodorido), mai kula da wannan shafi a kullum, da Malam Bashir Yahuza Malumfashi (Gizago). A karshe, godiya ta musamman zuwa ga Editar AMINIYA, watau Malam Bello Muhammad Zaki. Allah saka da alheri da irin gudummuwar da ake bani a kullum. A ci gaba da kasancewa tare da mu.
Assalamu alyakum brother you want blogger any paid template for free
ReplyDelete