Monday, October 13, 2008

Tarihi da Nau'ukan Tauraron Dan Adam (1)

Gabatarwa

Watakil mai karatu bai taba damuwa da sanin abinda ke dauko masa hotunan da ke bayyana a fuskar talabijin din giclip_image002dansa ba, har yake gani, musamman ma shirye-shiryen da ake nuna masa a halin da ake gudanar dasu, watau live programs. Na kuma tabbata, galibi bamu damu da sanin ta ina gidajen talabijin din gida da na kasashen waje ke samun bayanai kan yanayin wannan duniya tamu ba, dangane da zafi ko dumi ko sanyi; a wasu lokuta mukan yi tsammanin zuwan ruwan sama, a wasu lokuta na yini ko dare. Daga ina hukumomin tsaron kasashen duniya (musamman soji) ke samun bayanai kan bigiren da wasu abokan gaba suke, ko irin shirin da suke yi na kawo hari ko makamancin haka? Tsarin sadarwa ta wayar-iska (wireless communication) na tarho da kuma wanda ke hada alaka tsakanin kwamfuta da wata kwamfutar ‘yar uwanta a tsarin Intanet, abubuwa ne masu ban mamaki idan akai wa mai karatu bayani irin wacce kwakwalwarsa za ta iya dauka, kan yadda abin yake. To amma a hakikanin gaskiya, idan aka fito fili don bayyana masa tsarin, yana iya jayayya da labarin, don irin abin ta’ajjabin da ke dauke cikin tsarin. Daga ina na’urorin ke samun abinda ke hada alaka a tsakaninsu, har ma da na’urar wayar salula da mai amfani da ita ke rike da ita. Daga ina muke samun abinda ke sadar da akwatin rediyo ko talabijin din mu da sinadaran sadarwar da muke ji ko gani? Daga ina kwamfutarmu ke janyo sindaran bayanan da muke ta’ammali dasu a gidajen yanar sadarwar da ke dauke cikin wasu kwamfutocin da ke wata duniyar dabam? Duk wannan, idan mai karatu bai sani ba, bai kuma damu da ya tambaya ba, suna samuwa ne ta wasu taurarin wucin-gadi da dan Adam ya cilla ko harba su zuwa sararin samaniyar wannan duniya tamu, masu shawagi na wasu takaitattun lokuta ko zamunna, don haskowa, ko dauko hotuna ko janyo sinadaran sadarwa da cillo su wannan duniya tamu, don amfaninmu. Allah Buwayi gagara-misali!

A takaice, wannan duniya tamu na rayuwa ne ta yin makwabtaka da wasu duniyoyin, na taurari ne rana ko wata ko kuma wasu duniyoyi ne irin wacce muke ciki. Kowanne daga cikin wadannan duniyoyi na gudanuwa ne a wani falaki nasa da ya takaitu dashi. Abinda ake ce wa falaki shine wata hanya abin bi, wacce halittun da ke gudanuwa a sararin samaniya ke bi a halin rayuwarsu. Allah Ya bamu labarin a cikin Kur’ani, cikin Suratu Yasin, cewa: “kuma rana tana tafiya ne zuwa ga wata matabbata nata. Wannan kaddarawar Mabuwayi ne, Masani (watau Allah). Kuma da wata, mun kaddara masa manziloli (masaukai da yake rayuwa cikinsu), har ya koma kamar tsumagiyar murlin dabino. Rana ba ya kamata a gareta ta riski wata. Haka kuma dare ba ya kamata a gareshi ya tsere wa yini; kuma dukkansu cikin wani falaki suke sulmuya.” Kowane daga cikinsu, kamar yadda ayar karshe ta nuna, yana sulmuya (watau iwo ko gudana) ne a cikin wata hanya ko tafarki da ke sama. Wannan tafarki ko hanya ita ce ake kira “falaki” a Hausar kimiyyar sararin samaniya, ko kuma Orbit, a Turance. Yadda gidajenmu ke makwabtaka da juna a wannan duniya tamu, haka su ma wadannan halittu ke makwabtaka da juna. Sai dai su a can, duk da makwabtakan da ke tsakaninsu, kowa da hanyarsa. A wannan duniya da wadannan halittu manya ke rayuwa, akwai iska nau’i iri-iri, akwai sanyi da zafin rana, akwai haske da duhu, sannan akwai nau’ukan sidanarai irin na haske (radiation), da sinadaran maganadisu (magnetic waves), da sinadaran iska (waves) masu kadawa suna janyowa ko aikawa da sakonni daga bigire zuwa bigire, akwai kuma sinadaran maganadisun lantarki (electromagnetic waves), masu barbaran juna don samar da hasken lantarki da muke amfani dashi a wannan duniya tamu.

Sannan a cikin wannan duniya na manyan halittu da bayaninsu ya gabata, akan samu wasu buraguzai na sassan jikin taurarin da muddar rayuwarsu tazo karshe, masu yankewa suna fadowa zuwa wannan duniya da muke ciki, lokaci-lokaci. Wadannan abubuwa masu fadowa wadanda a turance ake kiransu meteorite, asalinsu jiki ne na wasu taurari. Kamar kowace halitta ta Ubangiji, taurari da wata da rana da wannan duniya tamu da ma sauran duniyoyin da ke rayuwa a gurabunsu, na da iya shekaru ko zamanin da Allah Ya ajiye ko yanke musu. Su taurari da zarar sun kare zamaninsu, sai haskensu ya bice, su tsattsage, sai buraguzansu su tarwatse su keto cikin wannan duniya tamu ko wasu wurare dabam, a yanayi irin na duwatsu. Wadannan su ake kira meteoroid, idan sun fado duniyarmu. Amma asalin sunansu kafin fadowarsu wannan duniya tamu shine meteorite, watau buraguzan taurari masu haske. Amma da zarar sun balgace sun keto cikin wannan duniya tamu, sai su sauya launi da yanayi, su zama balgacen dutse mai karfi. A wannan yanayi sunansu meteoroid. Irin wadannan buraguzai ne suka fado cikin jihar Sakkwato a nan Nijeriya shekarun baya. Duk tauraron da kwanakinsa suka kare a muhallinsa, haka yake zama. Daga nan Allah Ya kara hallitan wasu taurarin, su ci gaba da rayuwa, kamar dai yadda muke. Wannan tasa har yanzu malaman kimiyyar sararin samaniya suka kasa gano adadin taurarin da ke sama. Domin a kullum Allah kan halicci wasu ne, bayan wasu sun kwanta dama.

Wadannan, a takaice, su ne abubuwan da ke makare a sararin samaniya, da zarar ka bar wannan duniya tamu. Kuma kamar yadda bayanai suka gabata, kowannensu na makwabtaka ne dan uwansa, amma duk da haka, kowa da tafarkin da yake bi, wanda yake a siffar da’ira ko kuri; ma’ana kewayawa suke a cikin hanyoyinsu. Wadannan hanyoyi kuma su ne falaki. Rana na da nata falakin. Wata na da nasa falakin. Taurari na da nasu falakin. Sauran duniyoyi irin wanda muke ciki suna da nasu falakin. Akwai kuma yanayi na tsananin haske da tsananin duhu, da tsananin sanyi da tsananin zafi, da tsananin iska mai kadawa wacce dan Adam ba ya iya jure wa bugawanta ko kadan; sannan akwai wadannan buraguzai da ke kai-komo a yanayin da ya dace da tarwatsewarsu. Wannan, shine irin yanayin da ke can sararin samaniya. Allah na iya sarrafa wadannan halittu kuma iya sonsa, a lokacin da ya so, a kuma irin yanayin da ya so. A kuma cikin wannan duniya ne dukkan abubuwan da dan Adam ke kerawa ya cilla su don samo masa bayanai, suke kewaya don gudanar da rayuwarsu a yayin da suke shawagi a cikin falakin duniya ko halittar da aka harba su zuwa gareta. Zamu karanta bayanai kan wadannan taurari na wucin-gadi da muke kira Tauraron Dan Adam ko Artificial Satellite, a turance. Me ye su? Nau’i nawa ake dasu? Ta yaya ake harba su zuwa wancan duniya da muka yi bayaninsa a sama? Wani irin rayuwa suke yi a can? A ina suke shawagi idan sun isa can inda aka harba su? Ta yaya suke aiko sakonnin da suka taskance a halin shawaginsu? Ta yaya ake iya sarrafa su daga wannan duniya tamu a halin shawaginsu a can? Wasu irin matsaloli suke fuskanta a wannan duniya da suke rayuwa ciki? A karshe, idan rayuwarsu ta kare, ta yaya suke shigowa wannan duniya tamu; a raye ko a mace? Sai dai fa kada mai karatu ya rudu; duk bayanan da suka gabata da wadanda ke zuwa nan gaba kan wadannan halittu, ba ya nuna cewa wadannan halittu sun kai sama na daya ne, a a, a saman duniya suke, kamar yadda Allah Ya fada a cikin Kur’ani. Basu ma kai sama ta daya ba. A dakace mu!

No comments:

Post a Comment