Monday, November 16, 2009

Asali da Samuwar Wayar Salula

Gabatarwa

Saboda samclip_image002uwa da kuma yaduwar fasahar sadarwa ta wayar salula a yau, an wayi gari, kamar yadda nake sanar da Malam Abubakar AbdurRahman (Dodo), wanda ke lura da wannan shafi na Kimiyya da Fasaha, cewa cikin kashi dari na sakonnin tes da na Imel da nake samu a lokuta dabam-daban daga wajen masu karanta wannan shafi, kashi sittin duk tambayoyi ne a kan ka’ida da kuma yadda ake mu’amala da wayar salula ko kuma hanyoyin sadarwa na zamani da ke jikin wayar; irinsu fasahar Bluetooth da Infra-red da kuma hanyar sadarwa ta Intanet. Wannan ke nuna cewa galibin masu karatu na da kishirwan bayanai kan wannan fasaha har yanzu. Wannan kuwa dole ya faru, domin fasaha ce wacce a kullum ake amfani da ita. Kuma duk da cewa na sanya ka’ida da dokar cewa na rufe karba da kuma buga sakonnin tes da suka shafi wannan fasaha a wannan shafi, har yanzu ba a daina aiko sakonnin tambayoyi da neman Karin bayani a kan wayar salula ba. Duk da barazanar da na yi ta yi kuwa. A karshe dai nayi tunanin cewa, “tunda daman shafin don masu karatu ake gabatar dashi, don kayatar dasu, da ilmantar dasu, da kuma fadakar dasu kan sabbin abubuwa, me zai hana a dauke dokar, a nemo hanyar gamsarwa?” Da wannan dai na yanke shawarar gabatar da doguwar kasida mai dauke da dukkan wani abinda ya shafi wannan fasahar sadarwa ta zamani da ake kira wayar salula ko kuma Mobile Phone ko Cell phone, a turance.

Daga wannan mako in Allah Ya yarda, shafin Kimiyya da Fasaha zai ware wani yanki don kwararo bayanai kan yadda tsari da kimtsin wayar salula yake. Daga ma’ana zuwa asali da samuwar wayar salula, zuwa bayani kan zamunnan wayar salula, da nau’ukan wayar salula; da yanayin sadarwar wayar iska (Wireless Communication), da bangarorin wayar salula, da alakar wayar salula da kwamfuta, da masarrafan da wayar salula ke dauke dasu, da cututtukan wayar salula, da nau’ukan manhajojin wayar salula, da amfanin wayar salula, da cutarwar wayar salula, da tsarin mu’amala ko amfani da wayar salula, da tasirin wayar salula kan rayuwar mai amfani da ita, da aljihunsa, da muhallinsa, da iyalinsa, da kuma al’ummarsa…kai, da duk wani abinda zamu iya tunowa kan abinda ya shafi wannan fasaha a yau. Don haka sai a bi shafin a hankali. Hausawa suka ce “hanyar lafiya, a bi ta da shekara.” Don haka, wadannan kasidu da zasu zo, sakamakon bincike ne mai zurfi, iya gwargwadon hali. Da fatan masu karatu baza su kosa da tsawonsu ba. Zan yi hakan ne don neman kosar da ku, iya gwargwado. Ban ce komai da komai zai samu ba, amma zan zurfafa, zan fadada, zan kuma tsawaita. A babin fadakarwa, kowane kasida zai zo ne da takensa. A yau zamu yi tsokaci ne kan “Ma’ana da Asalin Samuwar Wayar Salula” a duniya. Mu je zuwa, wai mahaukaci ya hau kura.

Ma’anar “Wayar Salula”

Da dama cikinmu idan an tambaye mu ma’anar wayar salula, ba abinda zamu ce illa “wayar da ke hannunmu, wacce muke yin kira ko amsa kira da ita.” Wannan ma’ana ce mai kyau, sai dai kuma a ilmin fasahar sadarwa ta zamani, tana bukatar fadadawa da Karin bayani. A takaice dai me ake nufi da wayar salula, a ilmance? Idan aka ce Wayar Salula, ko Mobile Phone ko Cell Phone a turance, ana nufin “Wayar tafi-da-gidanka ko wayar hannu, mai amfani da siginar rediyo (Radio Signal) don karbar kira ko amsa kira tsakaninta da waya ‘yar uwarta, a iya kadadar tashar sadarwa (Base Station).”

Galibin wayoyin salula na dauke ne da Katin SIM (Subscriber Identification Module), mai kumshe da lambar wayar mai ita, da kuma ma’adanar lambobin mutane (Contacts Memory). Wannan ke nuna mana cewa kafin a kira wayar salula da wannan suna har ta amsa, dole ne a samu abubuwa guda hudu tare da ita. Abu na farko shine ita kanta wayar, watau wayar hannu. Abu na biyu kuma shine Katin SIM, wanda ke dauke da lambar mai wayar. Abu na uku kuma shine samuwar tsarin sadarwa ta wayar iska mai dauke da siginar rediyo a tsakanin wayar salula da wata wayar. Sai abu na hudu, watau tashar sadarwa, ko Base Station kamar yadda bayani ya gabata a sama. Ita kuma tana samuwa ne daga kamfanin sadarwar da ya bayar da Katin SIM din da ke cikin wayar. Sai da wadannan abubuwa guda hudu za a iya amfani da wayar salula don kiran wani ko amsa kiransa.

Da wayar salula mai dauke da wadancan sifofi guda hudu, kana iya kiran wani da ita, ko ya kira ka, ko kayi amfani da fasahar Intanet in har kamfanin na da wannan tsari, ka iya aika sako ta amfani da fasahar Bluetooth ko Infra-red, ko ka iya amfani da wayar a matsayin makalutun sadarwa ta Intanet, watau Modem, don shiga Yanar Sadarwa ta Duniya. Da irin wannan waya har wa yau, kana iya aiwatar da harkokin kasuwanci, ka aika da sakonnin tes, ka yi mu’amala da bankinka, ko likitanka, ko malaminka, ko matarka, ko ‘yar uwarka ko kanenka da dai sauran abubuwan da mai amfani da waya ta hanyar kamfani ke iya yi. Da irin wannan tsari na sadarwa ne aka wayi gari duniya ta rikide da zumunci a tsakanin kayayyaki da hanyoyin sadarwa. Misali, akwai alaka mai karfi na sadarwa a tsakanin wayar salula da kwamfuta – da Intanet ko babu. Akwai alaka mai kwari tsakanin kwamfuta da gidajen talabijin, da gidajen rediyo. Akwai alaka har wa yau a tsakanin gidajen jaridu da fasahar Intanet, da wayar salula, da kuma dukkan sauran kafafen watsa labarai. Sanadiyyar wannan gamayya an samu canjin tsarin kere-keren kayayyakin amfani a gida, inda aka wayi gari ana kera su tare da sinadaran sadarwa mai kulla alaka tsakaninsu da sauran ababen sadarwa da ake amfani da su a gida ko ofis. Sanadiyyar haka kana iya samun na’urar dumama abinci mai amfani da fasahar Bluetooth, ko na’urar buga bayanai (Printer) mai amfani da fasahar Bluetooth ita ma, kuma da haka kana iya basu umarni su karba ta hanyar wayar salula ko kwamfutarka ko na’urar talabijin dinka. Wannan gamayya na zumunci a tsakanin kayayyakin sadarwar zamani shi ake kira Network Convergence a fannin fasahar sadarwa ta zamani. Kuma kashi sittin cikin dari na sanadinsa daga wayar salula ne. In kuwa haka ne, ta yaya aka samo wannan fasaha mai matukar tasiri a duniya?

Asali da Samuwar Wayar Salula

Wayar salula ta samo asali ne shekaru kusan dari da suka gabata, daga kasashe guda shida, musamman. Wadannan kasashe dai su ne: Kasar Amurka, da Ingila (ko kace Burtaniya), da Jamus, da Rasha (ko Rusasshiyar Daular Sobiet), da Suwidin, da kuma kasar Finland. Idan ka cire kasar Amurka, duk sauran kasashen na nahiyar Turai ne. Kuma sabanin yadda muke ganin wayar salula irin ta yau, wannan fasaha ta samo asali ne daga kananan rediyon sadarwa masu amfani da tsarin hanyar sadarwa biyu (Two-way Radio), wadanda ake sanyawa a cikin motocin haya, ko motocin daukan marasa lafiya, ko motocin ‘yan sanda. A wancan lokaci ana kiransu Radio Rigs, kuma basu amfani da babbar tashar sadarwa na tarho ta kasa, saboda rashin lambar waya da suke fama da shi. Ire-iren wadannan wayoyi ko rediyon sadarwa suna amfani ne da hanyoyi biyu kadai, don sadarwa, kuma dole ne ya zama wanda zai kira ka yana da irinta; daga kai sai shi kadai. Kamar yadda bayani ya gabata, suna makale ne a cikin mota. Sai a mota ake iya amfani dasu. Daga baya aka kera wadanda ake iya rikewa a hannu, amma kuma baka iya amfani dasu sai ka jona su da wutar mota, ta hanyar makalutun kunna sigari da ke cikin mota, watau Cigarette Lighter Plug. Dole sai ta haka, domin basu da batir, kuma basu da siginar rediyo da ke jone da tashar sadarwa. Wadannan nau’ukan kuma su aka kira Bag Phones a wancan lokaci. Domin kana iya sanya su a cikin jaka kayi yawo dasu, sai dai kuma basu da bambanci da wadanda ke cikin mota. Wannan fasaha a kasar Amurka aka kirkireta, kuma hakan ya faro ne tun shekarar 1911.

Cikin shekarar 1926 sai wannan fasaha ta yadu zuwa kasar Jamus, inda aka kayatar da ita, aka sanya mata suna Radio Telephony. Tsarinsu duk iri daya ne; ana amfani da su ne a manyan jiragen kasa da ke daukan mutane daga birnin Berlin zuwa birnin Hamburg, duk a kasar Jamus. Har wa yau an yi amfani dasu a jiragen sama, inda matuka jirgi ke amfani dasu don sadarwa tsakaninsu da ma’aikatan tashar jirgi. Sannan a karshe kasar Jamus ta sanya su a cikin manyan tankunan yakinta da tayi amfani da su a lokacin yakin duniya na biyu. Ana shiga shekarar 1940 sai kamfanin Motorola da ke kasar Amurka ya canza wa wannan fasaha tsari, inda ya bullo da wayoyin hannu masu matukar girma da nauyi. Domin kowane daya zai kai kaurin damtsen hannun matashi a yau, kuma suna dauke ne da batir. Wadannan su ne wayoyin da ya sanya musu suna Walkie Talkie, kuma ya kera wa Hukumar Sojin Amurka ne. Da aka haura zuwa 1946 sai aka samu wasu injiniyoyi ‘yan kasar Rasha guda biyu; da D.G. Shapiro da kuma Zaharchenko, wadanda suka yi wani bincike kan tsarin sadarwa, har suka yi gwaji a mota. Wannan tsari ya kumshi tsarin sadarwa ta wayar salula mai cin kilomita 20, kuma sabanin binciken da wasu suka yi a baya, wannan tsari na su Zaharchenko na iya hada alaka tsakanin wadannan wayoyin salula na wancan lokaci da kuma tashar sadarwa da ke kasar. Wannan, a iya bincike na, shine yunkurin da aka fara yi don hada alaka tsakanin wayoyi da kuma tashar sadarwa a tsarin amfani da wayar salula irin ta zamani. Shapiro da Zaharchenko sun yi kokari ta wannan bangare.

Da aka shiga shekarar 1947 sai aka samu wasu injiniyoyi daga kamfanin binciken kimiyya na Bell Labs da ke kasar Amurka, masu suna Douglas H. Ring, da kuma Rae Young, suka gudanar da wani bincike na musamman su ma kan sadarwa a tsarin sadarwar rediyo tsibi-tsibi. Sun gabatar da wannan bincike ne don amfanin wayar salula da ke makale cikin motoci. To amma saboda rashin samuwar fasahar wayar salular da za ta dace da wannan tsari da suka bullo dashi, sai ba a dabbaka ba. Haka wannan bincike mai maiko ya shiga kundin tarihi, ya kama bacci.

Ana cikin haka, sai ga kamfanin Ericsson (ko Sony Ericsson) a shekarar 1956 da wata sabuwar fasaha mai suna Mobile Telephone system A, ko MTA a gajarce. Ta bullo da wannan sabuwar waya ce a kasar Suwidin. Sai dai, kamar nau’in Walkie Talkie, su ma suna da dan karen nauyi. Kowanne daga cikinsu ya kai nauyin kilogram arba’in (40kg). Amma daga baya sai kamfanin ya dada kayatar dashi, inda ya mayar dashi mai nauyin kilogiram tara (9kg). Hakan ya faru ne a shekarar 1965. Ya zuwa shekarar 1983, kamfanin ya samu kwastomomi har dari shida, wadanda suka saya, kuma suke amfani da wannan nau’in waya. Abin dai bai dore ba, domin cikin shekarar aka dakatar da sayar da wannan waya nau’in MTA.

Daga nan kuma sai guguwar bincike ta sake komawa kasar Rasha, cikin shekarar 1957, lokacin da wani matashi injiniya mai suna Injiniya Leonid Kupriyonovich ya kirkiri wata sabuwar wayar salula da ya sa mata suna ta amfani da haruffan sunayensa, watau LK-1. Daga baya aka sake wa wayar suna zuwa “Radiophone”. Wannan nau’in waya dai waya ce ta salula, mai dauke da kunnuwan sadarwa (Antenna), kuma kai tsaye take amfani da tashar sadarwar kasar Rasha. Nauyinta duk bai shige Kilogiram uku ba (3kg), tana kama tashar sadarwa a tazarar kilomita ashirin zuwa talatin (20 – 30km), kuma kasancewarta mai amfani da batir, kana iya yin kira har na tsawon sa’o’i ashirin zuwa talatin shi ma, batirin bai dauke ba. Wannan ci gaba ne sosai, idan muka yi la’akari da yanayin binciken da aka yi a baya. A shekarar 1958 sai wannan matashi ya kara kayatar da wannan waya tasa, inda nauyinta ya gangaro zuwa giram dari biyar kacal (500gm).

Har zuwa zamanin da injiniya Leonid ya gudanar da bincike ya kuma samar da wayarsa ta LK-1, ana amfani wayoyin salula ne a wuri guda. Inda kake, nan kadai zaka iya kira. Duk kuwa da cewa wayoyin na yin hakan ne ta hanyar jonuwa da tashar sadarwa ta kasashen da suke ciki. Amma tsarin sadarwar a waje daya kawai take. Da zarar ka fice daga unguwa ko garinku, to shikenan. Baka iya buga waya ko amsa kira. Sai cikin shekarar 1970, lokacin da wani kwararren injiniya mai suna Amos Joel Jnr da ke aiki a Cibiyar Bincike ta Bell Labs a kasar Amurka ya bullo da wani “tsarin sadar da yanayin sadarwa daga zango zuwa zango” da ya sanya wa suna “Call Handoff”. Wannan tsari ne ke bayar da damar yin kira ko amsa kira ta amfani da gamammiyar tsarin sadarwa tsakanin zangunan sadarwa. Misali, kana iya kiran wani alhalin kana tuki ko tafiya a kasa, daga unguwa ko garinku inda tashar sadarwarku take, har ka fice zuwa wata tashar ba tare da sadarwar ta yanke ba. Wannan sabon tsari ya taimaka gaya, inda a karshe aka samu kamfanin sadarwar tarho mai suna AT&T da ke kasar Amurka ta ci gaba da amfani dashi, har ta samar da tsarin sadarwa mai suna Advance Mobile Phone Service (AMPS) a tsarin sadarwa nau’in Analog. Hakan ya faru ne a shekarar 1971. Daga nan kuma Hukumar Kasar Finland ita ma ta samar da nata tsarin mai suna ART, duk a shekarar. Wannan dai a karshe, shi ya ci gaba da haifar da samuwar kamfanonin sadarwar wayar salula a duniya, tare da kayatar da tsarin sadarwa mai inganci, daga wani zamani zuwa wani, har zuwa wannan zamani da muke ciki.

No comments:

Post a Comment