Friday, March 2, 2007

Dangantakar Intanet da Harkokin Rayuwa (3)

Makonni biyu da suka gabata mun kawo bayanai kan alakar da ke tsakanin Intanet da harkokin yau da kullum. Inda muka sanar da mai karatu abubuwa da dama na abinda ya shafi harkokin rayuwa da yadda ake gabatar dasu a duniyar Intanet. Duk da yake mun yi alkawarin kawo samfurin yadda ake hakan a aikace daga wasu daga cikin gidajen yanan sadarwan wasu hukumomi ko kamfanoni ko bankuna, a wannan mako, zan so su mu yi tsokaci ne kan fa’i’dojin da ke tattare da yin hakan a yau. In ya so sai mu kawo misalai a aikace a mako mai zuwa. Wannan zai taimaka ma mai karatu sanin dalilan da suka sa galibin kamfanoni da hukumomin gwamnati ke ta kai gwauro suna kai mari wajen gina gidajen yanan sadarwa da kuma shigar da harkokin da ke tsakaninsu da abokan huldansu zuwa can, duk da dan Karen tsadan da yin hakan ke tattare dashi.

Manufofi:

A bayyane yake cewa dangantakar da ke tsakanin Intanet da harkokin rayuwa tafi karfi a kasashen da suka ci gaba ta fannin tattalin arziki. Amma a kasashe masu tasowa, hakan bai da wani karfin tasiri a kan tattalin arzikinsu. A yanzu ne kusan dukkan kasashen ke ta kokarin ganin cewa sun cin ma wannan matsayi na kulla alaka tsakanin harkokin rayuwa da kuma Intanet. Hakan na da matukar muhimmanci musamman ta bangaren ci gaban al’umma da kuma tattalin arzikin kasa. Dalilan da suka sa hakan kuwa sun sha banban, dangane da yanayin kasa da kuma dabakan masu hulda ko abokan hulda. Ga dai dunkulallun manufofin yin hakan nan, a fayyace:

Saukin Mu’amala/Rayuwa:

Tabbas, daga cikin fa’idojin da fasahar Intanet ke dauke da su, akwai sawwake hanyoyin gudanar da rayuwa. Wannan kuwa ya shafi masu kamfaononin ne da abokan huldansu da kuma kasa baki daya. Gudanar da wasu daga cikin harkokin rayuwa a Intanet na rage wahalhalun da masu gudanar da hulda ke fuskanta a rayuwarsu ta yau da kullum. Galibin al’amuran da zaka dauki tsawon lokaci kana gudanar dasu, a yanzu sai ka yi su cikin kankanin lokaci, ba tare da ka kashe kudin mota ko ka kona mai zuwa inda zaka gudanar da harkan ba. Misali, wanda ke son yin rajista don rubuta jarrabawar JAMB, ba sai yayi sawu hudu ko biyar ba kafin ya gama gudanar da hakan. Da zaran ya sayo fam din ko katin biya (scratch card), shikenan, alakar saduwa ta kare tsakaninsa da jami’an JAMB. Domin zai iya yin rajista a gidan yanan sadarwansu, ya aika da bayanan da suke bukata daga gareshi, ya kuma jira don sanin inda zai je ya rubuta jarrabawansa. Haka idan sakamakon jarabawa ya fito, ba sai ya je inda suke ba. Sai kawai ya shiga gidan yanan sadarwansu, don duba sakamakon jarrabawansa. Ka ga hakan ya sawwake masa kashe kudin mota da kai-komo da zai yi ta yi. Da naira dari kadai, sai ya gudanar da komai a mashakatar tsallake-tsallake (cyber cafĂ©).

Cikakken Tsari:

Daga cikin fa’idojin da ke tattare da aiwatar da harkokin rayuwa ta yanan gizo shine don samun cikakken tsari, musamman a kasa irin Nijeriya inda ake yawan samun cinkoso da tsaiko sanadiyyar rashin cikakken tsari a hukumomin gwamnati ko makarantu. Na kan tuna wahalan da dalibai ke sha a Jami’o’in kasan nan, da zaran an fara biyan kudin makaranta ko rajista. Sai a kusan wata daya ba a gama rajista ba, saboda layi da ake bi wajen karban rasiti da sauran takardu. Amma a yanzu, cikin mako daya ko biyu an gama. Domin kati kawai zaka saya, kaje ka shigar da kwasa-kwasan da zaka yi a wannan zango, sannan ka jira makaranta ta tabbatar maka da su. Wannan ya rage yawan cinkoso, ya kuma haddasa tsari da lumana cikin harkokin hukumomin gwamnati musamman. Haka a bankuna, wannan ya rage dogayen layukan da ake samu a wasu bankuna, musamman a manyan biranen Nijeriya.

Ilimi da Kwarewa:

Galibin dalibai a manyan makarantun kasan nan sun iya sarrafa kwamfuta ne sanadiyyar wannan alaka da ke tsakanin Intanet da harkokin rayuwa. Wasu ma basu taba hada kai da guiwa da Intanet ba sai sanadiyyar cike fam na jarrabawa ko kuma wajen yin rajista a zangunan karatu. Wanda watakil ba don haka ba, babu abinda zai hada su da wannan fasaha. Wannan ke nuna mana cewa, nan da wasu ‘yan shekaru masu zuwa, yawan masu amfani da fasahar Intanet zai karu ninki-ba-ninki, saboda wannan alaka. Wannan a fili yake, domin kusan dukkan makarantu sun mallaka ko kuma suna kan hanyan mallakan gidan yanan sadarwa, a sabon tsarin E-Government da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa yanzu. Yin hakan zai kara ma mutane sha’awan wannan fasaha na sadarwa, da kuma kwarewa wajen amfani da shi. Haka ma ga wadanda ke da saibi wajen karban sauyi da canjin zaman duniya, tilasta musu alaka da Intanet zai zama sanadiyyar samun canji a rayuwarsu.

Zabi:

Galibin harkokin da ake gudanar dasu ta fuska daya, zasu sawwaka yanzu. Maimakon a ce dole sai ta kafa daya kadai zaka iya gudanar dasu, a yanzu al’umma za ta samu zabi ta hanyar Intanet. Duk da yake wannan ya danganta ne da irin yanayin harkan. Harkokin banki a misali, zasu samu kafa biyu. Ga wanda ke son sanin abinda ke cikin taskansa, ba lalai bane ya je har bankin, a a, sai kawai ya shiga gidan yanan sadarwansu, don sanin nawa ya rage masa. Nan gaba ma akwai alaman samun wani tsari na gudanar da harkokin kudi, wanda ba ka bukatar zuwa banki, a Intanet kawai zaka iya gudanar dasu. Duk wannan zai samu ne sanadiyyar karfafa alakar da ke tsakanin Intanet da harkokin rayuwa.

Kudaden Shiga:

Ga kamfanoni ko hukumomin gwamnati, karfafa alakar da ke tsakanin Intanet da harkokin da suke gudanarwa ba karamin alheri zai jawo musu ba, ciki har da yawaitan kudaden shiga (Income). Mu dauki hukumar JAMB a misali. A farkon al’amari, babban hanyar samun kudin shigansu shine ta hanyar sayar da fam, wanda dalibi zai cika, ya kuma dawo musu da shi. Amma a yanzu saboda zabi da suke dashi, fam din sun mayar dashi cikin faya-fayan CD, tare da katin biya (scratch card). Sannan idan sakamakon jarrabawan ya fito, dalibai na da zabin sayan wani katin biyan (scratch card) don duba me suka samu, ko kuma su jira har sai an fitar da sakamakon, wanda ke daukan tsawon lokaci Haka hukumar WAEC ita ma, duk ta haka suke samun kare-karen kudaden shiga. Idan muka koma bangaren bankuna sai mu ga su ma haka abin yake a wajen su.

Ci Gaban Tattalin Arziki:

Duk da yake mafi yawancin mutane na ganin cewa zuwan sabbin hanyoyin sadarwa na zamani ba alheri bane, musamman ga ma’aikata, a gaskiya in muka duba zamu ga cewa hakan na tattare da wani kashi mafi girma na alheri, ga kowa da kowa. Abinda kawai ma’aiakaci zai yi shine ya yi kokarin koyon wannan sabon ilimi ba tare da bata lokaci ba. Ba lallai bane sai kayi aikin gwamnati. Akwai hanyoyin samun arziki da dama a cikin Intanet da harkan kwamfuta, birjik. Don haka akwai hanyoyin samun arziki da dama idan alaka ta kullu sosai tsakanin Intanet da Harkokin rayuwa. Kamfanoni zasu habbaka, ayyukan yi zasu yawaita sannan za a samu cikakkiyar tsari wajen gudanar da ayyuka a hukumomin gwamnati.

Cikawa:

A mako mai zuwa zamu ci gaba da wannan tattaunawa, inda zamu kawo misalai in Allah Ya yarda. Kada a mance da kundin sirrin Makarantar Fasahar Sadarwa, inda za a samu kasidun da suka gabata a wannan shafi. Adireshin dai shine: http://fasahar-intanet.blogspot.com. Duk wanda ke da wata tambaya na iya rubuto mani a adireshin Imel da ke kasa, kamar yadda aka saba.

No comments:

Post a Comment