Bangaren Ilimi:
Kamar yadda muka yi alkawari a makon da ya gabata, a yau zamu fara jero samfurin alakar da ke tsakanin Intanet da harkokin rayuwa, kamar yadda ake gudanar da su a harkokin yau da kullum. Zamu dauki bangaren harkan ilimi, inda za mu kawo tsarin yin rajista ga mai son rubuta jarrabawan shiga babban makaranta (watau makarantun gaba da sakandare kenan). Zamu shiga gidan yanan sadarwan Hukumar Shirya Jarrabawan Shiga Manyan Makarantu, watau Joint Admissions and Matriculation Board, ko JAMB, a takaice. Tsarin babu wani wahala, amma alfanun da ke tattare da hakan baya lissafuwa, kamar yadda muka zayyana wasu muhimmai daga cikinsu a makon da ya gabata.
JAMB:
JAMB ita ce hukumar gwamnati, mai lura da kuma shirya jarrabawan shiga manyan makarantun gaba da sakandare. Wadannan makarantu sun hada da kwalejin horas da malamai (Colleges of Educatioon), Kwalejin fasaha (Polytechnics) da kuma Jami’o’I (Universities). Ta
A halin yanzu wannan hukuma ta canza tsarin sayar da wannan fam da take sayar ma masu son rubuta wannan jarrabawa. A yanzu duk mai son rubuta wannan jarrabawa, zai sayi katin biya ne (scratch card), wanda zaka bambare, ka shigar da bayanan da ke kumshe cikinsa, a gidan yanan sadarwansu da ke Intanet. Wannan hanya da suka bullo da ita, ta rage yawan wahalhalun da dalibai ke shiga daga lokacin rajista zuwa lokacin rubuta jarrabawa. Da zaran dalibi ya sayo wannan kati wanda ke tare da littafin da zai yi masa jagora wajen zaben kwasakwasan da yake son karanta a makarantar gaba da sakandare, sai ya nufi mashakatar tsallake-tsallake (cyber café), don yin rajista.
Da zaran ka gama shigar da dukkan bayanan da ake bukata, da hotonka da komai da komai. Daga nan sai ka mika musu bayanai, ka saurari sako
Idan sakamakon jarrabawa ya fito kuma, sai ka sake sayan kati don dubawa ko ka yi nasara. A jikin katin da ka sayo, zaka ga adireshin gidan yanan sadarwan da zaka shiga. Ba wacce ka shiga bane da farko. Adireshin kuwa shine: http://www.jambonline.org. Da zaran ka shigo shafin, sai kawai ka kankare katin, zaka ci karo ka nambobi kashi biyu; kashin farko shine “Serial Number” da kuma “Pin Number”.
Idan ka shigo shafin farko, zaka ga tambarin irin katin da ka sayo daga hannun hagu. A dama kuma zaka ga inda aka rubuta “Login Here”, ma’ana, “shiga ta nan”. Akwai wuraren shigar da bayanai guda uku, kamar yadda mai karatu zai gani a shafin da ke gefe. A filin farko, wanda ke sama, zaka shigar da namban rasitin da aka baka a wajen sayo katin, na farko kenan. A filin da ke biye dashi, sai ka shigar da “Serial Number”, wanda zaka
A mako mai zuwa, zamu dan ratse don kawo cikakkun bayanai kan sakonnin “Spam”, watau sakonnin da mai karatu zai yi ta cin karo dasu a jakar wasikar sadarwansa, ba tare da sanin wanda ya aiko masa su ba. Hakan ya faru ne saboda sakonnin tambayoyi da nake ta samu daga masu karatu. Sai mun sadu.
LABARU DAGA INTANET
Google na Shirin Kera Wayar Salula (http://www.abcnews.go.com): A yayin da kowa ke shaukin fitowar wayar tafi-da-gidanka na kamfanin Apple (iPhone), babban kamfanin Matambayi Ba Ya Bata ta duniya, watau Google Inc., na shirin shigowa kasuwar wayar salula (na tafi-da-gidanka). Bayanai sun tabbatar da haka daga jami’an kamfanin, wanda a halin yanzu tayi hayan kwararru dari don tsara yadda wannan waya ta salula zata kasance. Kamfanin Google Inc. dai ta dade da nuna sha’awarta wajen shigowa wannan bangare na kasuwanci, ta hanyar bullo da manhajoji da masarrafan kwamfuta da dama masu amfani cikin wayar salula. Daga cikin ire-iren wadannan manhajoji akwai taswiran Google, watau Google Map, da masarrafan Matambayi Ba Ya Bata na wayoyin tafi-da-gidanka, watau Mobile Search da dai sauransu. A yanzu kamfanin Google Inc. na shirin shiga wata yarjejeniya ne da kamfanin kera wayoyin tafi-da-gidanka na kasar Jafan, watau Samsung, wajen kera wannan waya da ta fara bincike a kansa.
Google ta Kulla Yarjejeniya da Gwamnatocin
No comments:
Post a Comment