Thursday, March 1, 2007

Dangantakar Intanet da Harkokin Rayuwa (2)

Matashiya:

Idan masu karatu basu mance ba, a makon da ya gabata mun yi mukaddima kan dangantakar da ke tsakanin Intanet da harkokin rayuwa, da kuma matakan da masu kamfanoni ko hukumomin gwamnati zasu bi wajen hulda da abokan harkansu. A yau zamu ci gaba da wannan tattaunawa, inda zamu dubi wasu fannoni na rayuwa ta bangaren kasuwanci da kuma alakokin da zasu iya shiga tsakanin mai karatu da wasu ma’aikatu, masu tilasta masa mu’amala dasu ta hanyar Intanet. Wannan zai dada wayar mana da kai, musamman kan abinda muke nufi idan muka ce “Intanet ya shafi rayuwar Hausawa”. Domin wadannan dunkulallun kalmomi ne da muka yi ta ambatonsu da jimawa. A yanzu ne zamu fara ganin aikatacciyar ma’anarsu a fadade, kafin zuwan kebantaccen alakar da zai kullu tsakanin Hausawa da Intanet. A yau zamu dauki bangaren harkan banki, fansho, makarantu, neman aiki, da kuma alaka da hukumomin gwamnati.

Bankuna:

A halin yanzu muna da bankuna guda ashirin da biyar a kasan nan, kuma kowanne daga cikinsu na da gidan yanan sadarwa. Bayan kusan dukkan harkokin kudi da kasuwanci da bayar da bashi da suke yi, wanda ke tattare cikin tsarin da a turance ake kira Universal Banking, wadannan bankuna sun kama sabuwar hanyar tafiyar da hada-hadan kudi na zamani da ake yayi a yanzu, watau Electronic Banking, ko E-Banking, a takaice. Electronic Banking shine gabatar da harkoki da hada-hadan kudi ta dukkan wata hanyar sadarwa ta zamani da ake amfani da ita yanzu; daga wayar tarho, kwamfuta, intanet, radiyo da dai sauransu. Daya daga cikin manyan dirkokin da ake ji dasu a wannan sabuwar tsari ita ce fasahar Intanet. Wannan tasa dukkan bankunan suke da gidajen yanan sadarwa don aiwatar da wannan sabon tsari. Kuma duk da yake kashi casa’in cikin dari na harkokinsu suna gudanar dasu ne ta hanyar mu’amala da abokan huldansu, nan gaba galibin wadannan huldodi duk zasu koma kan Fasahar Sadarwa ta Intanet. Don a halin yanzu akwai bankuna da dama da ke gudanar da mu’amala tsakaninsu da kwastomominsu ta hanyar Intanet. Duk lokacin da suke bukatan sanin nawa ke cikin taskansu (account), ba sai sun je bankin ba, sai dai kawai su ziayarci gidan yanan sadarwan, don ganin abinda suke dashi. Idan idan wasu huldodin suke son gudanarwa, Kaman sayan kudaden wasu kasashe ko canja su, (foreign exchange), akwai fam a cikin gidajen yanan sadarwan bankin, inda zasu cika, sannan su kira ma’aikatan bankin, don karasa wannan harka ta kasuwanci. Haka idan sabon taska (account) kake son budewa da wani banki, duk ba sai kaje bankin ba. Kana iya samun fam a gidan yanan sadarwansu, ka cika, in yaso sai dai kawai su ganka da hoto da sauran bayanai. Nan gaba akwai tabbacin cewa dukkan wadannan mu’amuloli zasu dada saukaka, kuma ya zama kusan komai zaka iya yinsa ta Intanet, ko da ba tilas bane, wannan zai taimaka matuka wajen rage cunkoso a bankin da dai sauran alfanun da sai an kai wannan mataki zasu bayana.

Makarantu:

A bangaren ilimi ma an ci gaba, don kusan dukkan manyan makarantu da ke Nijeriya (musamman na Arewa), suna da gidajen yanan sadarwa. A jami’o’I kuwa, daga abinda ya shafi sanin makarantar, da ka’I’dojin neman shiga da cika fam, da samun shi kanshi fam din da kuma uwa uba yin rajista idan an samu shiga, duk ta Intanet ake gabatar dasu yanzu. Misali, a jami’ar Abuja (Abuja University), idan kana son fam na neman shiga (admission form), katin biya (scratch card) zaka saya, kaje gidan yanan sadarwansu, ka cika fam, ka dauki namban fam din da ka cika, sannan ka aika musu, kai tsaye a gidan yanan sadarwan. Idan sunayen wadanda suka yi nasaran samun shiga ya fito, nan ma wani katin zaka sake saya, ka shiga gidan yanan sadarwansu, don dubawa ko ka dace. Idan ka dace, a nan zaka gani. Sai ka buga (print) shaidar samunka (admission slip), ka kai makarantar don a baka ta asali. Dukkan wadannan, a da, kai tsaye ake gudanar dasu a makarantar, wanda hakan ke haddasa samun cunkoso da rashin tsari, musamman idan daliban da aka dauka suna da yawa. Wannan shine tsarin da yanzu ake bi wajen rubuta jarabawan JAMB, da WAEC/GCE/NECO. Wannan ke nuna mana kuma cewa mu’amala da fasahar Intanet ya zama dole, muddin muna son tafiya da zamani da tsarin da ta dace.

Mu’amala da Hukumomin Gwamnati:

A wani tsari da take kan bullo dashi wanda zai sawwake hanyoyin mu’amala da hukumominta don samun sauki da ingantacciyar dangantaka, gwamnatin tarayya ta kirkiro tsarin E-Government, shekaru kusan uku da suka gabata. Wannan tsari mataki-mataki ne, kuma yana farawa ne da gina ma dukkan hukumomon gwamnati gidajen yanan sadarwa, wanda zai zama hanyar farko wajen kulla mu’amala da wadannan hukumomi, ba sai kaje inda suke ba. A kasa irin Singafo (Singapore), wacce ita ce kasa ta farko da ta fara aiki da wannan tsari cikin shekarar 2000, (daga gareta kasashen Ingila da Amurka suka koyo), komai zaka yi, muddin ya shafi alaka ne tsakaninka da hukumomin gwamnati, ba ka bukatar zuwa inda wadannan hukumomi suke, sam sam. Intanet kawai zaka je, ka nemi banganren da kake son mu’amala dashi, ka yi abinda kake so. Idan bako ne kai, kuma kana son gida ko hotal wurin kwana, ko makarantar da zaka yi karatu, duk ta Intanet zaka iya komai. Sai bayan an gama ne zaka je a nuna maka gidan da ka saya ko kama haya, babu bata lokaci ko kadan. Don haka Nijeriya ta bullo da wannan tsari, wanda a halin yanzu yake cikin jariranta. Amma duk da haka, akwai hukumomin gwamnati wadanda kusan rabin abinda kake so a can idan kaje, duk zaka same su a gidan yanan sadarwansu. Misali, hukumar shigi-da-fici ta kasa (Nigerian Immigration Service), na da fam da zaka iya cikewa na neman fasgon kasar waje (International Passport), a gidan yanan sadarwansu. A nan Abuja, idan fuloti kake so, akwai fam a gidan yanan sadarwan hukumar bunkasa birnin tarayya (FCDA), wacce ta tanada don haka. Za kuma ka samu fam din neman takardan dindindin na gidanka, watau Certificate of Occupancy (C of O), sai ka cika ka aika musu. Bayan haka, hatta gwamnatocin jihohi su ma suna cikin wannan tsari. Sai dai kamar yadda na fada ne da farko, wannan tsari na matakin farko ne, nan gaba akwai tabbacin yaduwarsa, kuma yana da kyau mu mallaki makami kafin zuwan yaki.

Neman Aiki:

Kamar yadda muka sani ne, a yanzu duniya na kan gamewa ne ta sanadiyyar sabbin hanyoyin sadarwa da suke ta bullowa a kullum. Wannan tasa akidu da al’adu suke cudanya da juna, a daya bangaren kuma tsare-tsaren aiwatar da harkokin rayuwa ma kusan suna son su zama iri daya. A yanzu zaka iya samun bayanai kan gurabun aiki da ake neman masu cike su, a wata kasar daban, ba ma kasarku ba. Za kuma ka iya aika musu da bayanai kan dukkan abinda ya shafeka; karatun da ka yi da irin matsayin da ka rike, idan yayi daidai da abinda suke bukata, su aiko maka. Bayan haka, galibin masu neman ma’aikata a Nijeriya suna amfani ne da gidan yanan sadarwa, inda zaka samu fam ka cika, ba sai ma ka turo musu takardunka ba, bayanan da ke cikin fam din ma kadai ya ishesu. Wannan zai tabbatar musu da gamsuwarsu da kai ko rashinsa. Neman aiki yanzu ya kusan komawa kan fasahar Intanet. Kusan dukkan hukumomin gwamnati da kamfanoni, suna amfani ne da gidajen yanan sadarwansu don sanarwa da kuma karban takardun neman aiki ko bayanan da suke bukata. Ta akwatin wasikar sadarwanka na Imel zasu aiko maka da jawabi. Idan kayi nasara, a nan zaka gani. Idan kuma baka yi nasara ba, to baka ganin komai. Wannan ke nuna mana cewa a kalla mutum na bukatar bude akwatin wasikar sadarwa ta Imel, a kalla. Domin dukkan wadannan huldodi hanyoyi biyu suke dasu, idan ka aika, dole a aiko maka. Kai a wasu wuraren ma, babu yadda za a yi ka shiga wajen mika wasu bayanan sai kana da adireshin Imel. Don haka sai mu dage.

Tsarin Fansho Na Kasa:

A sabon tsarin fansho na kasa wanda gwamnati ta bullo dashi cikin shekarar 2003, dukkan ma’aikacin da ke Nijeriya zai samu kamfanin da zata rinka ajiye masa fanshonsa ne a duk wata. Babu ruwan hukumomin gwamnati da ajiye hakkin ma’aikata. Idan ya bar aiki, sai kawai ya zarce wajensu don karban abinda ya tara. Wadannan kamfanoni ana kiransu Pension Fund Administrators (PFA), kuma tsarinsu daya ne da na bankuna. Zasu bude maka taskar ajiya (account), wanda a duk wata ma’aikatar da kake aiki zata rinka aiko da kason fanshonka, wanda ake cirewa daga albashinka, da kuma wanda gwamnati ke agaza maka dashi. Dalilin kawo wannan bangare shine, don su ma galibin aikace-aikacensu ta Intanet suke gabatarwa. Tabbas kamar a jihohi, zai iya yiwuwa kai tsaye suke mu’amala da mutane, amma a nan birnin tarayya, ko da ka cike fam kai tsaye, zasu baka kalmomin iznin shiga ne da suna (username and password), wanda da su zasu rinka shaida ka a gidan yanan sadarwansu idan ka je duba balas din ka. Wanda wannan shima sai kana mu’amala da fasahar intanet. Idan kuwa ba haka ba, to karshenta ka samu kanka kana mai safa da marwa a duk wata don duba balas dinka, ko a duk lokacin da ka bukata.

Daga karshe, wadannan su ne wasu daga cikin fannonin da a halin yanzu ake gudanar da harkokin rayuwa na yau da kullum ta hanyar fasahar sadarwa a cikinsu. Akwai tabbacin nan gaba tsarin da suke kai a yanzu na yin mu’amala tsakaninsu da kwastomomi ko abokan hulda kai tsaye, zai canza sosai. Idan mun samu dama, a mako mai zuwa zamu fara kawo misalai daga bankuna ko wasu hukumomi, na yadda ake gudanar da harkokin da suka shafe su ta hanyar gidan yanan sadarwansu. Ina kuma kara tunatar damu kundin sirrin da aka bude don amfanin masu karatu, inda nake zuba kasidun da aka buga a wannan shafi. Za a samu wannan kundi a http://fasahar-intanet.blogspot.com. A lura, babu “www”. Yadda aka aka gansu a rubuce a sama, haka za a shigar cikin “address bar”. Sai wani makon.

No comments:

Post a Comment