Friday, September 12, 2008

Labaran Mako

Wasu ‘Yan Dandatsa Sun Shiga Hannu a Kasar Nedaland (http://news.yahoo.com): Wani dan Dandatsan kwamfuta (System Hacker) mai suna Leni de Abreu ya shiga hannu a kasar Nedalands, sanadiyyar tuhumarsa da laifin mallake wani gungun kwamfutoci da yake basu umarnin kai hari cikin kwamfutocin jama’a a duniya. Wannan saurayi dan shekara 35, wanda dan asalin kasar Brazil ne, an same shi da laifin wannan ta’asa ne tare da wani abokinsa dan kasar Nedalands mai suna Nordin Nasiri, ranar 29 ga watan Yuli na wannan shekara, kamar yadda Hukumar Shari’ar kasar Amurka ta sanar. Hukumar ta bayyana cewa muddin an samu wadannan samari biyu da hannu dumu-dumu cikin wannan ta’ada, suna iya fuskantar dauri na tsawon shekaru biyar, tare da tara na dalar Amurka dubu dari biyu da hamsin ($250,000), kwatankwacin kimar barnar da suka haddasa sanadiyyar wannan aiki nasu. An kama Leni ne da laifin mallakar gungun kwamfutoci sama da dubu dari da ke tarwatse a kasashe dabam-daban, kuma yake basu umarni wajen aikawa da sakonnin bogi (spam) ko kwayoyin cutar kwamfuta (computer virus) zuwa kwamfutocin kamfanoni da sauran jama’a a duniya. Wannan tsari na dandatsanci da a turancin kwamfuta ake kira Botnet (ko Robot Network a warware), shine hanya mafi sauki da galibin ‘yan dandatsa ke amfani dashi wajen cutar da kwamfutocin mutane a kasashen Turai da Amurka musamman. ‘Yan dandatsa kanyi amfani da wannan tsari ne wajen shigar da manhajojin kwamfuta masu yada wasikun Imel na bogi, da kuma kwayoyin cutar kwamfuta, cikin kwamfutocin jama’a ba tare da masu kwamfutar sun sani ba. Wasu kamfanoni kan dauke su haya, su biya su, don kawai su darkake kwamfutocin da ke dauke da gidajen yanar sadarwar abokan hamayyarsu a kasuwanci ko makamancin haka.

Leni, da abokinsa Nordin, sun mallaki wannan gungu na kwamfutoci ne da suke amfani dasu don samun kudade, inda suke bayar da haya don yin amfani dasu wajen kai hari ga kwamfutocin jama’a. A halin yanzu Leni na hannun hukumar kasar Nedalands, inda yake jiran a mika shi ga hukumomi a kasar Amurka don yanke masa hukunci. Shi kuma Nurdin na tsare a hannun hukumar kasar Nedalands din, inda shi ma yake jiran hukunci na karshe.

‘Yan Dandatsa Sun Barka Cikin Tangarahon Hukumar Tsaron Cikin Gidan Amurka (http://news.yahoo.com): Wasu ‘yan dandatsar wayar tarho (Phone Hackers) da ba a san ko su waye ba, sun barka cikin tsarin tarhon Hukumar Tsaron Cikin Gida na Amurka, watau Department of Homeland Security, suka buga wayar tarho zuwa wasu kasashe da ke Gabas-ta-Tsakiya da kuma Asiya. Wadannan ‘yan dandatsa sun samu wannan dama ne sanadiyyar waske na’urar wayar tangarahon hukumar, wacce ke amfani da tsarin sadarwa ta voicemail, don buga waya zuwa kasashen waje, musamman ma Gabas-ta-tsakiya. Mr.Tom Olshanski, mai Magana da yawun Hukumar Tsaron na Cikin Gida, yace wadannan ‘yan Dandatsa sun buga waya ne zuwa kasar Saudiyyah, da Afghanistan da Indiya da kuma kasar Yaman. Ya kara da cewa, mafi karancin lokacin da kowane kira ya dauke shine minti uku. Wasu kasashen kuwa an yi kira har na tsawon minti goma.

Shahararriyar kamfanin sadarwa ta wayar salula mai suna Sprint da ke nan Amurka ce dai ta gano wannan aikin dandatsa da aka yi tsawon kwanaki biyu ana yi, watau daga Asabar har zuwa Lahadin wannan mako da ya shige. Kuma adadin kudin da suka kashe wajen buga wannan waya ya kai dalar Amurka dubu goma shabiyu ($12,000), kwatankwacin naira miliyan daya da dubu dari biyar da sittin kenan.

A halin yanzu dai ana nan ana ta bincike don gano wadanda suka aikata wannan aiki, wanda ya tayar da hankalin hukumar fiye da yadda ake zato, musamman ta la’akari da kasashen da aka kira, da kuma tsawon lokacin da suka dauka suna kiran. An kuma gano wata kafa da suka bi ta ciki don shigewa cikin ginin, wacce a halin yanzu aka toshe ta nan take.

Hukumar Tsaron Cikin Gidan Amurka dai na amfani ne da tsarin wayar tangaraho na PBX, wanda tsohon yayi ne, kuma galibin masu dandatsan wayar tarho sun dade suna waske shi don yin waya a wasu wurare shekaru aru-aru. “Wannan tsari na sadarwa”, inji wani masanin fasahar sadarwa, “bai da wahalar waskewa, don haka masu wannan aiki basu bukatar wata kwarewa ta musamman wajen yin hakan.”

No comments:

Post a Comment