Friday, September 12, 2008

Wasu Cikin Labaran Mako

Hukumar NASA Za ta Sayi Wani Kumbon Sararin Samaniyar Kasar Jafan (http://www.reuters.com): Hukumar lura da zirga-zirgan masu bincike a sararin samaniya ta kasar Amurka, watau NASA, ta fara cinikin wani tafkeken kumbun binciken sararin samaniya na kasar Jafan. Hukumar Sararin Samaniya ta kasar Jafan ta tabbatar da hakan cikin mako. Wannan tafkeken kumbo, wanda Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Jafar tare da hadin guiwar kamfanin Mitsubishi Heavy Industries, an kiyasta farashin kowani daya a kimanin Yen Biliyan goma sha hudu, wajen dalar Amurka miliyan dari da talatin da daya kenan.

Hukumar NASA ta fara wannan ciniki ne don cike gurbin manyan kumbon kai kaya da abinci zuwa tashar binciken sararin samaniyarta ne da take shirin jinginar da su zuwa shekarar 2010, saboda tsufa da suka yi. Wannan tasa ya zama dole ta tanadi wadanda zasu maye gurbin su, don tabbatar da cewa binciken sararin samaniyar da hukumar ke gabatarwa bai samu tsaiko ba. Duk da cewa hukumar ta fara wani shiri na taimaka wa wasu manyan kamfanonin Amurka wajen kera irin wannan kumbo cikin watan Afrailun day a gabata, da alamar wadannan kamfanoni ba za su iya cin ma wannan lokaci da hukumar ta kayyade ba. Wannan, a cewar jaridar Yomiuri da ke kasar Jafan, na iya zama dalili mai karfi da ya karkato Hukumar NASA zuwa kasar Jafan don cinikin wannan tafkeken kumbon daukan kaya mai suna H-2 Transfer Vehicle, ko kuma HTV a gajarce.

Wannan kumbon daukan kaya zuwa sararin samaniya na HTV da kasar Jafan ke kerawa yana da karfin daukan tan shida zuwa tashar bincike ta sararin samaniya, kuma ana sa ran za a kaddamar dashi ne nan bad a dadewa ba.

Kamfanin Symbian ya Koma Hannun NOKIA

Shahararren kamfanin nan mai tsarawa da kuma kera babban manhajar wayar salula da ke landan, watau Symbian zai koma hannun kamfanin NOKIA nan bad a dadewa ba. Kamfanin NOKIA ya mallaki wannan kamfani ne sanadiyyar sayan ragowar kashi sittin da biyar na hannun jarin kamfanin, kuma masu lura da harkokin wayar salula da manhajarta na ganin wannan ba karamin yunkuri kamfanin NOKIA yayi ba, wajen mallake kasuwar wayoyin salula a duniya.

Wannan kamfani na Symbian dai aikinsa shine gina manhajojin wayoyin salula masu inganci, kuma kafin wannan mamaya da kamfanin NOKIA ya kai masa, shine kamfanin da yayi fice wajen samar da kayatattun babban manhajar wayar salula, watau Mobile Phone Operating System a duniya. Domin manyan kamfanonin kera wayar salula irinsu SonyErricsson da Motorola da kamfanin Nokia, duk suna sanya babban manhajarsa cikin wasu daga cikin wayoyin salularsu. Wani abinda wannan kamfani na Symbian ya shahara dashi har way au shine, kusan dukkan manyan wayoyin salula na musamman nau’in Black-berry da ire-irensa, duk suna amfani ne da babban manhajarsa.

Wasu daga cikin kayatattun siffofin wannan manhaja ta kamfanin Symbian sun e: samuwar hanyoyin mu’amala da fasahar Intanet, da wasikun Imel da hanyar sadarwa ta Rediyo da Talabijin da hanyoyin taskance hotuna da wakoki da kuma murya, sai tsarin aikawa da kuma karbar sakonni na text, da fasahar sadarwa ta GPRS. Wasu kebantattun hanyoyin mu’amala da wayar salula da wannan manhaja take takama dasu basu faduwa sai mai karatu ya gansu a aikace.

Wannan tasa da dama cikin masu lura da bunkasar wayar salula a duniya ke ganin cewa kamfanin NOKIA na dosar mamaye kasuwar ce gaba daya. Don a yanzu ma dai shine a gaba wajen kera ingantattun wayoyin salula a duniya, kuma gashi ya saye kamfani mafi girma, mai gina babban manhajar wayar salular ma gaba daya.

No comments:

Post a Comment