Friday, September 12, 2008

Wasu Cikin Sakonnin Masu Karatu

Ga kadan daga cikin sakonnin masu karatu. Galibi na bayar da amsarsu. Wadanda basu ga amsar su ba suyi hakuri, hakan ya ta’allaka ne da abubuwa da dama ; ko dai lokacin da ka aiko sakonka bani da halin aiko jawabi, ko kuma akwai bayanan da nake son tarawa. Bayan haka, zai dace masu karatu su rika la’akari da sakonnin da zasu aiko na neman karin bayani ta hanyar gajerun sakonnin wayar salula (SMS), da wadanda zasu aiko ta Imel. Sau tari wasu kan aiko sakon neman karin bayanin da bazai yiwu a bayar da amsa gamsasshiya ba ta hanyar text, amma mutum yace a rubuto masa jawabi ta nan. Idan mai karatu na son karin bayani cikakke, don Allah a rika aikowa ta hanyar Imel. Ina kara bayar da hakuri ga wadanda ban aiko musu da jawabin sakonninsu na neman karin bayani ba. Za a ji ni nan ba da dadewa ba in Allah Ya yarda. Wannan shafi na mika sakon gaisuwarsa ga dukkan masu karatu, musamman Malam Sani Na ‘Yan katsare da ke Jas tare da dukkan abokanansa, da Malam Hassan Al-Banna tare da abokinsa Malam Is’haaq, sai Malam Muntaka AbdulHadi, dukkansu a garin Zaria. Har wa yau, wannan shafi bazai mance da Malam Rabi’u Isa Ayagi ba da ke Kano, da Malam AbdusSalam da ke garin Jas. Sai Malam Abbas Amin da ke Zone 2 a nan Abuja, da kuma Malam Shazali Lawan da ke Zaburan Quarters a Gumel jihar Jigawa. Allah sa mu dace amin.

Salam Baban Sadik, ni dalibi ne a filinka na fasaha a Aminiya, ina da tambaya a kan kwamfuta don ina binciken maths, wato wacce ce mai kyau ?

- Rabi’u H. D/Ma, 08084888618

Assalamu Alaikum. Ina fatan kuna cikin koshin lafiya, Allah sa haka amin. Don Allah ina neman fassarar wadannan kalmomin a turancin kwamfuta ; NCI, SCSI, CMOS. In da hali a turo min amsar ta wannan lamba. Wassalam

- Uncle B. Bash, Jimeta, Yola – 07037133338

Assalamu Alaikum Malam ina fatan kana lafiya. Nine mai sauraronka a kowane mako. Don Allah malam wani abu nake tambaya ; ina son aikawa da sakon Imel ne ta Handset, to amma inda zan rubuta, ko na aika baya tafiya. Shine nake son bayani. Na gode.

- 08033598315

Na karanta tsokacinka a yau game da makamin kare-dangi wanda mujallar Aminiya ta yau ranar Jumu’a, 2 ga watan Rajad,1429 ta dauka, kuma na fahimci abubuwa da dama. Allah kara maka sani ya kuma yi maka jagora, amin.

- AbdurRahman Sa’ad, Kano - 08036918678

Salam, yaya aiki? Ina daya daga cikin mai karanta rubutunka na kimiyya da fasaha. Tambaya ta ita ce, idan na aika wa wani wasika ta Intanet shekara daya ko fiye, zan ya samun wasikan idan ina nema yanzu?

- Salihu Jibril, 08037882499

Salam, malami na barka da asuba. Mun ga ka rubuta bayani kan wayar salula, to kasancewar ni kurma ne, ina amfani da wayar salula kirar MYX-2 Sagem don tana da kara, amma ban sani ba ko ita ma tana haddasa cutar cancer. Don ban ga ka kawo sunanta ba. Idan amsar ita ce eh, to ina bukatar ka zayyana mani wadda ta dace da ni, kuma mai kara.

- Sulaiman Kr, 08084888618

Malam barka da yamma, ya aiki ya kokari? Allah Ya kara basira da fasaha, amin. Baban Sadiq, ni makarancin jaridar Aminiya ne musamman ma wannan shafi na Kimiyya da Fasaha. Da fatan ma wannan makon zamu sami laabrin da yafi na baya. Allah Ya taimake ka, amin.

- Aliyu Mukhtar Sa’idu (Baban Sadiq), 08034332200


No comments:

Post a Comment