Thursday, January 15, 2009

BUNKASA HARSHE DA AL’UMMAR HAUSAWA: DAGA ADABI ZUWA KIMIYYA DA FASAHAR SADARWA TA ZAMANI (1)

Gabatarwa

A tabbace yake cewa, duk al’ummar da ke son ci gaba, musamman a wannan zamani da muke ciki, dole ne tana bukatar ilimi daga kowane fannin rayuwa da ke ci a yanzu. Kuma kasancewar nau’ukan ilimin na samuwa ne cikin wasu harsuna dabam, hakan yasa dole kowace al’umma ta koyo wadannan ilimi ta hanyar koyon wadannan harsuna. Wannan ba karamin aiki bane sam, musamman a wannan lokaci ko zamani da fannonin rayuwa ke caccanzawa kamar kiftawar ido. Idan muka yi la’akari da tsarin yadda duniya ke bunkasa a yau, zamu ga cewa galibin kasashen da ake ganin sun ci gaba ta fannin kimiyyar kere-kere da na sadarwar zamani, daya cikin manyan dalilan da ya sawwake musu hakan shine samuwar ilimi cikin harshensu; ko wadanda suka koyo suka taskance a rubuce, ko kuma wadanda suka fassara daga wasu harsunan dabam. Wannan tasa koyon ilimin da kuma fahimtarsa a garesu ba wani abu bane mai wahala. To amma ga al’ummomin da ya zama dole su koyo wadannan harsuna don samun wannan ilimi, suna bukatar juya wannan ilimi su ma zuwa nasu harshen, don samun saukin fahimta da kuma dabbaka shi. Wannan shine halin da al’ummar Hausawa suka samu kansu a ciki, musamman a wannan zamani. A wannan zamani, idan mai karatu zai tambayi kanshi: shin wani ilimi ne cikin dukkan fannonin rayuwa da ake da su a duniyar yau, wanda Hausawa ke dashi a rubuce cikin harshensu? Amsar da zai samu ya danganci sanayyarsa ga rubuce-rubucen Hausa. Wannan ‘yar takaitacciyar kasida tsokaci ne kan bunkasar rubuce-rubuce a fannin adabin kirkirarrun labarai da sauran ilimi gaba daya cikin harshen Hausa, da kuma bayyana bukatuwar al’ummar Hausawa zuwa ga samuwar littafai cikin wasu fannonin ilimi tsantsa, musamman kan fannonin kimiyya da fasahar sadarwa ta zamani. Wannan ya zama dole musamman ta la’akari da cewa: dole ne kowace al’umma ta samu kwararru cikin dukkan fannonin ilimi, tare da samuwar ilimin wadannan fannoni cikin harshenta, don sawwake koyo da kuma dabbakawa.

Tsarin Rubuce-Rubucen Hausa

Tabbas akwai rubuce-rubuce da aka yi cikin harshen Hausa, wadanda suka shafi karantar da shi; irin su littafan koyon rubutu da karatu – daga firamare zuwa jami’a – da rubuce-rubucen binciken ilimi da Malaman Jami’a ke yi, da rubuce-rubucen tarihin kasar Hausa da makwabtanta, sai mujallu da jaridun Hausa, sai kuma rubuce-rubuce kan addinin musulunci da suka yadu kan nau’ukan ilimin addinin. Wannan a fili yake, kasancewar kaso mafi girma na Hausawan kasan nan musulmi ne. Amma idan mai karatu ya kara bincike, zai ga cewa fannin ilimin da yafi kowanne samun kaso mai girma wajen yawan littafai a harshen Hausa shine fannin rubutaccen adabin Hausa, bangaren kirkirarrun labarai, watau Hausa Fiction Literature kenan a Turance. Kirkirarrun labaran Hausa su suka fi yawa da kuma saurin yaduwa cikin dukkan fannin ilimin da aka yi rubutu kansu a harshen Hausa. Wannan bangare shi ya kwashi kashi hamsin cikin dari na rubuce-rubucen Hausa. Fannin ilimin addini kuma ya kwashi kashi talatin da biyar. Sauran fannoni kuma suka dauki ragowar kashi goma shabiyar da ya rage.

Wani bature mai suna Graham Furniss dan kasar Ingila da ke Cibiyar Bincike kan Kasaashen Gabas da na Afirka, watau School of Oriental and African Studies, mai kuma sha’awar bincike kan bunkasar rubuce-rubucen adabi cikin harshen Hausa, yana nan yana tattara sunaye tare da bayanan littafan da aka rubuta tun daga shekarar 1980 zuwa yau, ta hanyar daukan suna da kuma mawallafin littafi, da kamfanin dab’i, da kuma shekarar da aka buga littafin. Tun daga kan littafai irinsu Jamila da Jamilu na Ibrahim Mandawari, da In Da So Da Kauna na Ado Ahmad Gidan Dabibo, zuwa irinsu Shekara Ashirin na Rahma Amdulmajid da Sirrinsu na Maje El-Hajeej, duk ya taskance su a shafin gidan yanar sadarwarsa da ke http://hausa.soas.co.uk. A rahotonsa da na samu ranar 09/08/2006, ya tara littafai dubu daya da dari takwas da talatin da bakwai (1,837). Wannan, kamar yadda muka sani, kadan ne cikin abinda aka rubuta kuma ake kan rubutawa. Wannan aiki na bincike yana yinsa ne ta hadin-gwiwa da wasu kwararrun masana harshen Hausa da ke Jami’o’in Nijeriya, irinsu Farfesa Ibrahim Malumfashi da Farfesa Bello Bada da ke Jami’ar Danfodio a Sakkwato. Sai irinsu Farfesa Abdallah Uba Adamu da Farfesa Sa’idu Ahmad da ke Jami’ar Bayero a Kano da sauran masana.

Wadannan bayanai da Mr. Graham Furniss ke tattarawa na tattare da nakasa, don ba dukkan littafan da aka buga ya taskance ba; adadin wasu littafan basu cika ba - babu kashi na daya sai na biyu, wasu kuma babu kashi na biyu sai na daya. Kasancewar ba mazaunin Nijeriya bane shi, yana samun sunayen wadannan littafai ne daga wadannan masana da ke Jami’o’in Arewacin Nijeriya. Kamar yadda kowa ya sani ne, tun da bamu da wata cibiya ta musamman da ke nazari da lura da yawan littafan da ake dabba’awa a dukkan mako ko wata ko shekara, zai yi wahala a samu cikakken adadin wadannan littafai. Har wa yau, wannan kididdiga da Furniss ke yi, ya ta’allaka ne ga littafan adabi da ake wa lakabi da Adabin Kasuwar Kano (Kano Market Literature); wadannan kirkirarrun labarai ne na soyayya, kiyayya, mulki, zaman iyali, ci gaban al’umma, da almara (watau Science Fiction). A hakan ma, akwai wadanda aka rubuta cikin shekaru biyar da suka gabata, duk ba a kididdigesu ba cikin rahoton. Bai kuma damu da wadanda aka rubuta lokacin mulkin mallaka ba; wadanda hukumar mulkin mallaka ta dauki nauyin bugawa don ba ‘yan kasa samun “abin hira da koyon karatu”, wadanda su ma kashi saba’in cikin dari duk na kirkirarrun labarai ne da wasannin kwaikwayo – ko dai wadanda aka tarjama/fassara daga wani harshen zuwa harshen Hausa, ko kuma wadanda aka samu marubuta suka yi gasa wajen rubutawa (irinsu Ruwan Bagaja, Gamdoki, Magana Jari da sauransu). Har wa yau, bayan samun ‘yancin siyasa (daga 1960 zuwa 1979) akwai rubuce-rubuce da aka yi na kirkirarren labari, irinsu Kitsen Rogo na Abdulkadir Dangambo, da Matar Mutum Kabarinsa na Malam Bello Kagara, da sauransu. Duk wadannan rubuce-rubuce, basu cikin kididdigan Furniss. A takaice dai, duk da rashin cikan wannan rumbun bayanai na Furniss, wannan na iya zama sheda kan cewa fannin da yafi kowane fannin ilimi samun bunkasa da habbaka a kullum shine fannin rubutaccen adabin Hausa, musamman ma na kirkirarrun labarai.

Hakan ba abin zargi bane dari bisa dari, domin sanadiyyar hakan ma da dama cikin mutane sun koyi rubutu da karatun Hausa, wasu ma daga nan suka zarce suka koyi taurancin, wasu kuma, sanadiyyar hakan suka zama marubutan ire-iren wadannan littafai. Kuma ga dukkan wanda ya mallaki ilimin tarihin yaduwar ilimi, ya san ire-iren wadannan rubuce-rubuce su ne masu tabbatar da ilimin rubutu da karatu, tare da dasa shauki da son karatu a zukatan mutane. Abin sani ne kuwa cewa duk al’ummar da ke da sha’awar rubutu da karatu a dukkan lokuta, to ba ta tabewa. To amma idan muka yi la’akari da halin da duniya ke bunkasa wajen sauran fannonin ilimi da rayuwa, zai ga cewa ta’allakuwa ga bunkasa fannin kirkirarrun labarai kadai ba zai kai mu ga gaci ba, dole muna bukatar fadada bincike cikin sauran fannin ilimi don dabbaka su a aikace.

1 comment:

  1. ina bada shawara https://www.penpaland.com harshen musayar tushen website
    Android:http://app.appsgeyser.com/Penpaland

    ReplyDelete