Thursday, January 15, 2009

Labaran Mako

NIGCOMSAT-1 Ya Samu Matsala Cikin Falaki

Tauraron dan Adam da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta harba cikin falaki shekara da wasu watanni da suka gabata mai suna NIGCOMSAT-1, ya samu matsala a halin shawaginsa cikin falaki. Hukumar da ke lura da tauraron, watau Nigerian Communication Satellite, ta bayyana haka cikin makon da ya gabata. Hukumar tace ta gane hakan ne sanadiyyar yakewar sadarwa tsakanin tauraron na NIGCOMSAT-1, da kuma cibiyar da ke lura da shawaginsa a falaki, wanda hakan ke nuna cewa ya daina aiki sanadiyyar wasu matsaloli da ya ci karo dasu a cikin falakin da yake sulmiya. Wannan, a cewar Hukumar, “shi yasa aka dakatar dashi.”

A farkon al’amari dai akwai jita-jita da ake ta yadawa cewa tauraron ya bace ne, ba a ma san inda yake ba cikin falaki. Wannan tasa jama’a suka yi ta mamakin wannan zance mara kan-gado: “ta yaya za a ce ya bace, bayan harba shi aka yi, kuma ana lura dashi?”, a cewar wani bawan Allah mai suna Malam Murtala Baba Aminu Kalgo. Amma daga baya sai Hukumar ta tabbatar da cewa ba bacewa yayi ba, ya samu matsala ne da fika-fikansa masu taskance masa makamashin hasken rana, watau solar panels, wanda hakan ke taimaka masa wajen cajin batirin da yake dauke da shi. Wannan tasa injinsa ya tsaya, don batirin yayi rauni, baya iya juya injin da ke gudanar da tauraron gaba daya. Ga al’ada kowane tauraron dan Adam na da hanyoyin samun wutar lantarki ne kashi biyu; akwai batir mai taimaka masa yin rayuwa cikin dare ko duk lokacin da wannan duniya tamu tayi masa shamaki daga hasken rana, da kuma fika-fikai biyu masu kallon rana. Aikinsu shine taskance makamashin hasken rana, wanda tauraron ke amfani dashi kai tsaye, tare da taimaka wa batirin yin caji lokacin yini.

A karshe dai Hukumar ta baiwa kamfanonin da wannan matsala ta shafa hakuri, da kuma cewa kada su damu, za a sada su da wani kamfanin da zai ci gaba da basu bayanan da suke bukata, kafin gwamnatin Nijeriya ta samu wani tauraron daga kamfanin da ya kera NIGCOMSAT-1. Wannan ke nuna cewa NIGCOMSAT-1 ya kwanta dama kenan. Hakan ya haddasa kace-nace a tsakanin ‘yan Nijeriya masu lura da abinda ke kai ya kawo. Shin wannan na nufin cibiyar da ke lura da wannan tauraro ba ta ganin shawagin da yake yi kenan a aikace cikin falaki, sai dai kawai ta samu sakonni daga gareshi? Kenan ba don sun kasa samun sakonni daga tauraron ba, da shikenan, sai ya zama sharar cikin falaki (space junk), ba wanda ya damu. Amma sai dai kuma sabanin yadda mutane ke zato, bah aka lamarin yake ba. Kamfanin da ke lura da wannan tauraro dai ta dakatar dashi cikin falaki, cikin wani irin yanayin da kanikawansa zasu iya duba shi don gano cikakken dalilin da ya haddasa masa wannan tsayawa cikin kankanin lokacin.

Gwamnatin Nijeriya dai ta mallaki tauraron NIGCOMSAT-1 ne cikin shekarar 2007 ta hannun wani kamfanin sadarwa na kasar SIN (China), a kan kudin da kimarsa ta kai Naira Biliyon Arba’in (N40B). Manufar mallakar wannan tauraro shine don taskance bayanan da suka shafi yanayi (Weather Forecast), da kuma taimaka wa kamfanonin sadarwa wajen yada bayanai. Har wa yau, akwai gidajen rediyo na FM da ke amfani da wannann tauraro wajen yada shirye-shiryensu. Wadannan kamfanonin sadarwa na biyan gwamnatin tarayya kudaden wannan aiki ne a duk farkon watanni hudu. Yanzu haka akwai kamfanonin da suka biya kudi ba tare da sun amfana da ko harafi guda ba, sai tauraron ya kwanta dama. Wannan tasa dole a hada su da kamfanin da zai basu bayanan da suke bukata, kafin a samu wani tauraron dabam.

Tasirin Fasahar Intanet Kan Nasarar Barack Obama

Gagarumar nasarar da Mr. Barack Obamaclip_image002 ya samu a zaben shugaban kasa da aka gabatar a Amurka makonni biyu da suka gabata ya samu tagomashi ne daga tasirin hanyar sadarwa ta Intanet da yayi amfani da ita wajen kamfen da kuma neman agaji daga ‘yan kasa da ke ciki har wajen kasar Amurka. Wani kididdiga da wani gidan yanar sadarwa ya fitar kwanaki biyu bayan zaben, ya nuna cewa kashi sittin cikin dari na tallafin kudi (donations) da Mr. Barack Obama ya samu duk ta hanyar Intanet ne. Kuma duk da cewa Mr. John McCain, abokin hamayyarsa ne ya fara amfani da wannan hanya ta Intanet wajen yin kamfen, amma Mr. Barack Obama ya shallake shi nesa ba kusa ba, inda bayan yayi tasiri a zukatan masu shawagi a Intanet ‘yan kasar Amurka (da ma wasu kasashe), ya kuma ci gaba, inda ya samu karbuwa har gidan yanar sadarwarsa ya zama wani dandalin bayar da tallafi da gudummuwar kudi.

Bayan gidan yanar sadarwar da ya gina don gabatar da kamfen, wanda ke http://www.barackobama.com, wadanda suka dada taimakawa su ne gidajen yanar sadarwar magoya bayansa, wadanda tasirinsu ya fi na gidan yanar sadarwarsa. “Shine ya fara amfani da sabbin hanyoyin yada manufofi wajen neman magoya baya, ya kuma nemi goyon bayan wasu sabbin kungiyoyi, sannan ya sauya tsarin yadda ake yakin neman zabe a Amurka”, inji Mr. Simon Rosenberg, tsohon shugaban kungiyar yakin neman zaben Mr. Bill Clinton a shekarar 1992. A yayin da wasu ke kokarin sanin manufofi da kuma tsare-tsaren Mr. Barack Obama ta hanyar gidan yanar da ya tanada a Intanet, dubunnan magoya bayansa, ‘yan a-mutun-Obama, suna can sun kirkiri gidajen yanar sadarwa don taimaka masa yin hakan, tare da shirya tarurrukan neman agaji da tallafin kudi ta hanyar wadannan gidajen yanar sadarwa. An kirkiri a kalla kungiyoyi sama da dubu talatin da uku ta wadannan gidajen yanar sadarwa. Kuma an kiyasta cewa Mr. Barack Obama ya samu tallafin kudi daga magoya bayansa, wadanda suka bayar da tallafinsu ta hanyar katin adashin bankinsu (watau Credit card) a gidan yanar, sama da dalar Amurka miliyan dari shida ($600M) – wajen naira biliyan saba’in da daya da miliyan dari hudu kenan (=N=71.4B)! Wannan zunzurutun kudade an same su ne daga mutane miliyan uku – tsakanin kwabo da taro da sisi da sule. A tarihin siyasar Amurka, babu wanda ya taba kashe kudi wajen yakin neman zabe irin Mr. Barack Obama. Domin a yayin da abokin hamayyarsa Mr. John McCain ya kashe dalar Amurka miliyan dari tara da ‘yan kai, Mr. Barack Obama ya kashe dalar Amurka biliyan daya da miliyan dari shida da arba’in ($1,640M) - . Kusan dukkan wadannan kudade tallafi ne daga magoya baya.

Bayan hanyar sadarwa ta Intanet da Obama yayi amfani da ita, miliyoyin magoya bayansa da aka ribato ta wannan hanya sun yi amfani da hanyar tarho, musamman wayar salula, wajen nemo masa magoya baya a sauran jihohi; daga ‘yan uwa zuwa abokan arziki. Har wa yau, shi kansa Mr. Obama yayi amfani da tsarin gajeren sakon wayar salula, watau SMS, wajen aikawa da sakonni ga magoya bayansa. Duk wanda ke son a rika aiko masa da sako, sai ya aika da kalmar “hope” zuwa wasu lambobi da aka bayar, don a taskance lambar wayarsa. Wannan ya sa Mr. Barack ya samu karbuwar da ba a samu wanda ya samu irin sa ba a siyar Amurka. Ya samu gagarumar nasarar da ba a samu wanda ya samu irinsa ba, sannan sanadiyyarsa, an samu fitowar masu jefa kuri’a, inda kashi tamanin cikin dari suka fito don jefa kuri’arsu, wanda ba a taba samun irin sa ba tun shekaru dari da suka gabata. Don haka kwana daya da samun nasarar Mr. Obama, jaridu sun yi karanci a birnin Washington, inda aka yi ta warwasonsu kamar kosai. Wasu su kwashi biyar, wasu shida, wasu goma. Kai wasu ma dauri guda suke son a sayar musu. Wannan tasa sai da kamfanonin sayar da jaridu suka kafa doka, cewa duk wanda ya zo saya, kwara daya za a sayar masa, don wasu ma su samu. Wasu kamfanonin sai da suka kara buga wasu kwafe. Misali, jaridar The Washington Times ta kara buga kwafe dubu sittin, don wadanda ta buga sun yi karanci. Duk dai wannan, kamar yadda mai karatu ya sani, saboda shaharar Mr. Obama ne; kowa na son ya samu tarihi a gidansa; wasu ma su ce don jikokin su su taso ne su gani.

Kamfanin Sadarwa na Etisalat Ya Iso Birnin Abuja

Idan ba a mance ba, cikin shekarar 2006 ne gwamnatin tarayya karkashin shugabancin tsohon shugaban kasa Obasanjo, ta baiwa kamfanin Etisalat lasisin fara hada-hadar sadarwar wayar salula nau’in GSM a Nijeriya gaba daya. Wannan lasisi ya fito ne daga Hukumar Bunkasa Harkar Sadarwa ta kasa, watau National Communications Commission (NCC), wacce ke da alhakin sanya farashi da kuma ka’idojin da duk wani kamfanin sadarwa zai biya ko bi, don samun gabatar da harkar sadarwa a Nijeriya.

Bayan lasisin da aka baiwa kamfanin a shekarar 2006, ya dau tsawon shekara daya da rabi yana ta tsare-tsaren kafuwa don fara tafiyar da harkokinsa a kasar; ta hanyar kafa cibiyoyin sadarwa masu dauke da na’urorin sadarwarsa, da mallakar ofishi a wurare irin su Legas da ma wasu manyan biranen kasan. Bayan haka, kamfanin yayi ta maza wajen biyan kafafen yada labarai don tallata hajojinsa kafin wannan lokaci. Har wa yau, kamfanin bai tsaya a nan ba, yayi amfani da kafar hanyar sadarwa ta Intanet, watau ta hanyar gidan yanar sadarwarsa da ke http://www.etisalat.com.ng, don soyar da hajojinsa ga masu sha’awar hulda dashi, ta hanyar yin tayin kyautar lamba ta musamman (special number) ga duk wanda ke so.

Yadda abin yake shine, za ka shiga gidan yanar sadarwar ne a adireshin da ke http://www.etisalat.com.ng, sai kaje kai tsaye zuwa shafin da ke maka wannan tayi, wanda ke zauren gidan yanar (Homepage), ka shigar da lambar da kake amfani da ita a yanzu a wayar salularka. Sai ka matsa alamar “send”, wacce za ta cillo maka wasu lambobi guda biyar nan take, da ake son ka shigar cikin shafin da ka aika da lambarka. Kana gama shigarwa, sai ka matsa alamar “confirm”, wacce a karon karshe za ta aiko maka da lambar da kamfanin ya tanada maka ta musamman. Za a zaftare lambobi ukun farko ne na lambarka, sai a bar maka sauran. Misali, idan kana da lamba kamar haka 080-247-88040, sai su baka lamba makamanciyarta, kamar haka 080-987-88040. A cikin sakon, akwai wasu lambobi guda bakwai, watau pass cord, wadanda ake son ka taskance a cikin wayarka. Da zarar kamfanin ya fara aiki (kamar yadda ya fara yanzu), sai kaje ofishinsu ka nuna musu lambar da aka tanada maka, tare da wadannan lambobi na pass cord. Da zarar ka je, zasu karbi lambobin, su shigar cikin kwamfutarsu, don tabbatar da cewa lallai haka ne. Sai su baka katin SIM din kamfanin. Idan ka samu lamba ta wannan hanya, kamfanin zai rika baka kyautar dakiku dari uku (30 seconds), ko mintuna biyar a kowace rana, kyauta; ka buga zuwa duk jihar da kake so a Nijeriya. Sannan kana da damar zaban garuruwa goma da kake son a rika maka sauki yayin da ka buga waya zuwa wadannan wurare. Wannan tsari na zaban garin da kake son a maka saukin caji, shi suke kira Home Zone.

Wannan kamfani na Etisalat dai babban kamfanin sadarwa ne na wayar salula da ke da rassa a kasashe sama da goma sha-hudu a Gabas-ta-Tsakiya. Daga cikinsu akwai irinsu Saudiyya da Kuwait da Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa, watau United Arab Emirates. Kamfanin ya fara aiki ne a birnin tarayyar Abuja cikin makonni uku da suka gabata, kuma katin SIM dinsa naira dari biyu ne. Da zarar ka saya ka sanya, kana iya amfani dashi a dukkan kasar da kamfanin ke aiki. Kana iya mu’amala da fasahar Intanet muddin wayar salularka ta mallaki fasahar yin hakan, ka aika ko karbi sakonnin text. Haka idan ka kashe wayarka, duk wanda ya bugo alhalin wayar na kashe, za a sanar dashi halin da wayar ke ciki, sannan da zarar ka kunna, za a aiko maka da sakon text cewa “wane . . .ko kuma lamba kaza da kaza sun bugo lokacin da wayarka ke kashe”. Idan kana son ganin lambarka kai tsaye daga wayar salularka, akwai lambobin da za ka matsa, sai lambar ta bayyana nan take. Wannan duk kyauta ne! Bayan wannan, kamfanin na da wasu hajojin sadarwa masu kayatarwa da babu wani kamfanin sadarwa mai irinsa a nan Nijeriya. Kuma farashin cajinsa kusan daya ne da na kamfanin MTN, amma ya sha bamban da kamfanin MTN wajen yawaitan hajoji masu sawwake farashi ko kuma masu kayatarwa, wadanda kyauta zaka same su ba tare da ka kashe kwabonka ba.

Ko shakka babu, bayyanar kamfanin Etisalat a sahun kamfanoni masu hada-hadar harkar sadarwa a Nijeriya zai kara haddasa saukin farashin caji da wasu kamfanonin ke yi mara misali, ya kuma sa wasu hajojin su samu inganci. Misali, sanin kowa ne cewa daya daga cikin babbar matsalar da kamfanonin sadarwar wayar salula ke addabar masu mu’amala dasu itace rashin ingancin yanayin sadarwa, watau Network Service. Duk wanda yayi amfani da tsarin sadarwa ta Etisalat, zai samu bambanci nesa ba kusa ba. Duk da yake ta haka kowane kamfani ya faro, amma daga baya idan rumbun bayanansa suka cika da lambobi, sai a fara samun matsala. Sai dai, galibin masu amfani da layin Etisalat a kasashe irin su Hadaddiyar Daular Larabawa, musamman birnin Dubai, sun shaida cewa lallai yanayin sadarwar kamfanin na da inganci da aminci. Amma, kamar yadda muka sani ne, komai na Nijeriya ya sha bamban da sauran kasashe.

Fatanmu dai shine jama’a su samu ingantacciyar yanayin sadarwa, da farashi mai sauki da kuma mu’amala mai kyau daga wajen ma’aikatan kamfanin Etisalat; ba ayi ta cika maka kunne da kade-kade ba duk sadda ka bukaci a warware maka wata matsala. Barka da zuwa Nijeriya, ITTISAALAAT!

No comments:

Post a Comment