Tun bayyanar babban manhajar kwamfutar kamfanin Microsoft Corp mai suna Windows Vista watanni kusan goma sha daya da suka gabata, har yanzu haskenta sai kara dusashewa yake yi a fuskar masu amfani da kwamfuta; tsakanin kamfanoni da kuma daidaikun mutane. Idan ba a mance ba babban manhajar kwamfuta ta Windows dai ita ce mafi shahara a kasuwannin manhajar kwamfutoci a duniya, tun farkon bayyanar nau’in Windows 3.1 da kamfanin Microsoft Corp yayi shekaru goma sha bakwai da suka gabata. Hakan na damfare da tsarin sauki ne da kamfanin ke amfani da ita wajen gina wannan babbar manhaja, wanda sanadiyyar hakan miliyoyin mutane suka iya amfani da kwmfuta cikin sauki ta hanyar tsarin Graphical
User Interface, ko GUI a takaice. Shi kuma kamfanin yayi ta cika aljihunsa da biliyoyin daloli, inda a karshe ya zama kamfani mafi kasaita wajen shahara da ciniki a duniya. Shekara guda kafin fitowar nau’in Windows Vista, mutane sun yi ta Allah-Allah da fitowarta. A tunaninsu Vista
Babban abin da mutane suka fara ruduwa da shi a jikin Windows Vista shine tarin kyale-kyalen da ta zo dasu; daga hotuna zuwa shafukan manhajoji masu kayatarwa da shashantar da idon mai mu’amala da kwamfutar. To amma kamfanin Microsoft Corp ya mance cewa galibin masu mu’amala da kwamfuta yanzu musamman kamfanoni, ba damuwarsu bane kyale-kyale. Abin da aka fi damuwa da shi yanzu shine tagomashi, watau ingancin manhajar da ke sarrafa kwamfutar, da aminci da gaggawar aiwatar da aiyuka da dai sauransu. Dukkan wadannan, idan mai karatu ya dubi Vista, bata zo dasu ta dadi ba. Wannan yasa galibi suka juya wa wannan manhaja baya. Wasu manyan kamfanonin suka ce baza su juya zuwa Vista ba sai bayan ‘yan shekaru, lokacin da ake tunanin kamfanin Microsoft Corp ya kara wa manhajar inganci da tagomashi. Wasu kuma, suka ce atafaufau, ba su ba manhajar Windows Vista; sun tsaya kan nau’in Windows XP, idan an fito da wata manhajar bayan Vista, sa dubi dacewar yin hakan ko rashinsa. Wasu kuma, ‘yan zafi, suka daina amfani da manhajar Windows ma gaba daya, suka koma sauran nau’uka irin su Linux ko kuma Mac OX.
Matsalan farko da galibi ke ta kuka kansa shine yawan saibi. Idan ka baiwa manhajar Windows Vista umarnin budo maka wani shafi ko wata jakar adana bayananka da ke kwamfutar, sai ta gama yanga sannan ta biya maka bukata. Musamman idan kana yawo a shafukan yanar sadarwa ta duniya, watau Intanet. Sai ya zama ita ce ke baka umarni, wajen ganin damar bin umarninka, ba kai ba. Wannan tasa wasu ke mata kirari, cewa: “Windows Vista kyakkyawar budurwa ce mai yanga”. Wannan matasala na yawan saibi na cikin abinda ya sad a dama suka daina amfani da wannan manhaja ta Windows Vista gaba daya, duk da kyale-kyalen da take tare dasu. Wannan saibi har wa yau, shi ne ke haddasa mata yawan sumewa cikin kankanin lokaci, watau Hanging. Ko kuma yawan sandarar maka da masarrafan da kake amfani dasu ba tare da izininka ba. Haka kawai sai ka nemi ruhinsu ka rasa. Ka matsa, amma ba motsi. Wannan shi ake kira Crashing, kuma ba abinda yafi bata wa mai amfani da kwamuta rai irin wannan lamari; kana ji kana gani, ka kasa sarrafa abin da ke karkashin ikonka. Su kuma masu amfani da kwamfuta sun fi so su ji komai zam-zam, musamman dai kamfanoni da ke bukatar aiyukansu a lokacin da suke so.
Bayan wannan, daga cikin illolin Windows Vista akwai yawan cin makamashin kwamfutarka, watau System Resources. Kowace manhajar kwamfuta na amfani da karfin makamashin da ke tare da gangar-jikin kwamfutar ne, wanda shi ne misalin injin da ke baiwa mota karfin tunkudawa zuwa gaba ko baya. Da zarar ka kunna kwamfutarka, sai babbar manhajar ta rarraba wa dukkan karikitan da ke tafiyar da ruhin kwamfutar iya makamashin da suke bukata. Ragowar makamashin kuma sai ta adana maka su; da zarar ka bude wata masarrafa za ka yi amfani da ita, sai babbar manhajar ta yanko mata iya makamashin da take bukata don tafiyar da aikin da kake son yi da masarrafar. To amma saboda yanayi da kuma tsarin ginin manhajar Windows Vista, sai ya zama da zarar ka kunna, sai ta kwashe kusan dukkan makamashin kwamfutar, ta rarraba wa ‘yan kananan masarrafan da ke taimaka mata rayuwa (watau processes), kai kuma ka ji da kanka. Wannan tasa idan ka budo wata manhajar don yin wani aiki, sai kwamfutar ta fara saibi, domin karancin makamashi da take fama dashi. Daga nan sai ta sume a tsaye, ba tare da ka sani ba. In ta dama ne za ta aiko maka da sakon cewa: “This System is not responding”. Hatta kashewa ma baka iya yi, domin ba abinda ke jin umarninka balle ya karbi umarnin. Sai dai ka kashe ta karfi da yaji, sannan ka sake kunnawa.
Idan kuma ka tsira daga sharrin cinye makamashi mai haddasa mummunar saibi don kafcecen ma’adanar kwamfuta da kake da shi, to wata matsalar da baka tsira daga gare ta ba ita ce matsalar rashin kyakkyawar muhallin dasa wasu manhajoji. Abin so ne ga dukkan wanda ya mallaki kwamfuta ya ga ya samu damar dasa wasu manhajoji musamman irin su masarrafan sauraron karatun Kur’ani ko koyon karatu ko na rubutu da karatu da zane-zane. Babban matsalar Windows Vista shine rashin kyakkyawar muhalli da zai sawwake maka yin hakan, musamman a farkon fitowarta. Wannan shi ake kira “Software incompatibility” a turancin ilimin kwamfuta. Misali, ba dukkan mai amfani da Windows Vista ke iya sanya manhajar Alim a cikin kwamfutarsa ba, saboda wannan matsalar. Wannan matsala na faruwa ne saboda rashin manhajoji ko “jami’ai” masu sawwake yin hakan. Duk da cewa kamfanin Microsoft ya fitar da nau’in Vista na daya, watau Windows Vista Service Pack 1, wanda sanadiyyar hakan aka samu dan daidaito na a-zo-a-gani, har yanzu da sauran rina a kaba. Akwai sauran burbushin saibi tare da wannan manhaja. Wannan a tabbace yake kamar yadda wani kamfanin binciken ingancin kwamfuta yayi kwanakin baya Kamfanin ya nuna cewa har yanzu babbar manhajar Windows Vista na kasa da Windows XP wajen saibi da kashi arba’in. Wannan babban aibu ne ga kamfanin Microsoft Corp, domin hatta kamfanin Intel Corp, wanda abokin huldan Microsoft ne tun shekaru da dama, inda yake kera masarrafai masu tafiyar da ruhin kwamfuta, watau Micro-chip ko Processors, wadanda kuma galibi da su ake gwajin tasirin babbar manhajar a kwamfutoci, yaki ya juya kwamfutocinsa zuwa manhajar Windows Vista. An kididdige cewa wannan kamfani na Intel Corp ya mallaki kwamfutoci wajen dubu tamanin a kamfaninsa, amma duk da haka, tare da kusancinsa da kamfanin Microsoft Corp, yaki. Dalilinsa kuwa shine, har yanzu bai gamsu da ingancin wannan manhaja ko ba. Ba kamfanin Intel Corp kadai ba, akwai kamfanoni ko mutane da dama, kwararru kan harkar kwamfuta, sun ki komawa ko juyawa zuwa nahiyar Windows Vista, sun doge da tsohuwar Windows XP dinsu, asirinsu a rufe.
Ganin wannan bakin jini da babbar manhajar ke kara yi, duk kuwa da kokarin da kamfanin yake ta yi na tallace-tallace da kara wa manhajar kuzari, sai Microsoft Corp ya sanar da cewa zuwa karshen shekarar 2008 da farkon shekarar 2009, zai daina sayar da babbar manhajar Windows XP. Ga masu amfani da wannan manhaja kuma, za su ci gaba da samun tallafi ne zuwa shekarar 2010. Da zarar an wuce wannan shekara, to kai da Windows XP kuma sai dai ka yi ta bilinbituwa idan ka shiga matsala; domin kamfanin zai daina bayar da tallafi tare da daina sayar da manhajar ma gaba daya. Wannan barazana ce don yanke wa wasu kin juyawa zuwa Windows Vista hanzari idan suka ki amfani da manhajar. Su san cewa akwai iya lokacin da aka diba mata, don daina sayarwa ko bayar da tallafi. Kamfanin yayi wannan sanarwa ne cikin shekarar 2008 don cin ma manufar kado kan masu kyamar Vista. Amma wannan barazana bata biyan kudin sabulu ba.
Ranar 18 ga watan Agustan 2008, gidan yanar sanar sadarwa na Computer World ya hakaito binciken da wani kamfanin fasahar sadarwa yayi mai nuna cewa, duk da barazanar da kamfanin Microsoft Corp ke yi na daina sayarwa tare da bayar da tallafi ga manhajar Windows XP, kashi talatin da biyar cikin dari na kwamfutocin da aka saye su tsakanin watan Janairun 2008 zuwa watan Yuni, masu dauke da babbar manhajar Windows Vista, an canza musu manhaja zuwa Windows XP! Kamfanin yace ya gano hakan ne daga binciken da ya gudanar kan kwamfutocin tafi-da-gidanka da na kan tebur wajen guda dubu uku, inda kashi 35% suka tabbatar da cewa asalin manhajar da suka sayi kwamfutocinsu da ita Vista ce, amma daga suka kai wa kananan dilolin kwamfuta don a mayar musu zuwa manhajar Windows XP, ko kuma su da kansu suka goge manhajar Vista da ke dauke cikin kwamfutar, don sanya Windows XP. Wannan har wa yau ya tilasta wa manyan kamfanonin kwamfuta irin su Hewlett-Packard (HP), da Dell Incorp., bin wannan tafarki. A yanzu suna da tsarin da ke baiwa mai sayen sabuwar kwamfuta damar canza manhajar da ke ciki (wanda Windows Vista ce) zuwa Windows XP. Wannan sabon tsari, a cewar wadannan diloli, dama ce kamfanin Microsoft ya basu don ganin karkatan mutane zuwa manhajar Windows XP.
Ganin yawan karkatan mutane da dogewarsu kan Windows XP tasa kamfanin Microsoft Corp a ya sake daga lokacin da ya haddade a baya, don janye tsohuwar manhajar Windows XP, wacce har yanzu tauraronta ke haskakawa babu kakkautawa. Cikin sanarwar da ya fitar ranar 22 ga watan Disambar 2008, kamfanin Microsoft Corp yace ya janye sanarwarsa ta farko wacce a ciki yake bayyana cewa zai janye lasisin manhajar Windows XP daga kasuwa daga ranar 31 ga watan Janairun 2009. Kamfanin ya sanar da cewa saboda wasu dalilai, ya daga wannan lokaci zuwa karshen watan Mayu na shekarar da ake ciki, don baiwa kananan dilolin kwamfuta damar saya da kuma sayar da lasisin da suke ajiye dasu a shagunansu. Manyan diloli ko kamfanonin kwamfuta masu rakaba babbar manhajar kwamfuta tare da sabbin kwamfutocinsu irin su Hewlett-Packard (HP) da Dell, misali, su ma an basu damar ci gaba da sayar da tsohuwar manhajar Windows XP har zuwa karshen watan Yuli na wannan shekara. Duk wannan dai alamu ne da ke nuna cewa lallai kamfanin Microsoft Corp ya fahimci irin dogewar da jama’a suke yi wajen rashin amincewa da sabuwar manhajarsa uwar kyale-kyale da saibi. Kuma har yanzu jama’a basu daina warwason Windows XP ba a kasuwa; wadanda suka sayi Windows Vista kuma sai kwam-baya suke yi, don neman sauki da inganci. Kididdigan baya—bayan nan da aka yi cikin watan Nuwambar 2008 ya nuna cewa, a yayin da manhajar Windows Vista ke rike da kashi 20.5% na yawan masu saye, ita kuma manhajar Windows XP na rike ne da kashi 66.3% a kasuwar babbar manhajar kwamfuta a kasashen yamma. Babban abin da ya jawo wa Windows Vista wannan rashin farin jini kuwa shine yawan saibi mai haddasa wa kwamfutocin mutane sumewar da basu shirya ba. Kuma har wa yau, shi ne ke kara sanya haskenta dusashewa a sahun manyan manhajojin kwamfuta a duniya.
Vinveef-se_Manchester Melissa Hebert https://wakelet.com/wake/Y5aGWR_DSMcR-D4939gVy
ReplyDeletequicicourfa