KWAMFUTOCIN TASHAR BINCIKEN SARARIN SAMANIYA SUN KAMU!
A hanyar komawa zuwa babbar tasahar sararin samaniya da ke dauke cikin kumbon binciken sararin samaniya da kasar Amurka ke dashi a can cikin falaki, injiniyoyin da aka kebe don wannan tafiya sun yi rashin sa’a, inda kwamfutocin tafi-da-gidanka da suka dauka don wannan ziyara ta aiki suka kamu da kwayoyin cutar kwamfuta, watau computer virus. Wani abin bakin ciki, inji Injiniya Greg Chamitoff, shugaban tawagar, shi ne wadannan kwayoyin cutar kwamfuta sun kama wadannan kwamfutoci ne jim kadan kafin su keta hazo, amma basu lura ba sai da suka isa masaukinsu a babbar tashar binciken sararin samaniya da ke can cikin falaki inda suke aiyukansu na bincike.
Duk da cewa wannan ba wani bakon abu bane a cewar Injiniya Greg, ba haka suka so ba, domin wannan zai yi tasiri wajen bata musu lokaci. A matsayinsa na wanda ke lura da kwamfutocin da ke wannan tasha, Greg yace zai yi iya kokarinsa wajen ganin ya share da kuma kona wadannan kwayoyin cutar kwamfuta, don kada su bata musu tsarin aiki. A halin yanzu dai akwai kwamfutocin tafi-da-gidanka (laptops) wajen guda uku da injiniyoyi ke amfani dasu a wannan tasha ta bincike cikin falaki, wadanda kuma da su ne ake taskancewa tare da aikawa da sakamakon binciken da ake yi zuwa cibiyar da ke lura da wannan tasha a wannan duniya tamu.
Bayanan baya dai sun nuna cewa galibin kwamfutocin da suke yawan kamuwa da kwayoyin cutar kwamfuta dai su ne wadanda Injiniyoyin kasar Rasha ke amfani da su a tashar, kuma sukan samu hanyoyin shiga ne gab da lokacin tashi daga wannan duniya tamu zuwa can sararin samaniya. Har zuwa yanzu dai ba a gano dalilin da ke haddasa wannan al’amari na kamuwa da kwayar cutar kwamfuta kafin tashi zuwa sararin samaniya ba, a cewar Injiniya Greg.
A wannan tasha ta binciken sararin samaniya dai akwai injiniyoyi guda uku wadanda suka hada da na kasar Amurka da Rasha, masu yin canjin aiki a tsakaninsu lokaci lokaci, don gudanar da aiyukan bincike da kuma lura da taurarin dan Adam da kasashen biyu suka harba don kasuwanci da sadarwa, ko don binciken ilimi da tsaron kasa.
AN GYARA FIKA-FIKAN KUMBON SARARIN SAMANIYA
Cikin ‘yan kwanakin da suka gabata ne injiniyoyi suka gano cewa kumbon tashar binciken sararin samaniyar kasar Amurka, watau US Space Shuttle, sun fara samun matsala wajen tafiyar da aikinsu. Wannan babbar barazana ce ga kumbon tashar gaba daya, domin wadannan fika-fikai su ne masu taskance masa makamashin hasken rana don tafiyar da aiyukansa, tare da cajin batirin da yake taimaka wa kumbon wajen wutar lantarki a yayin da inuwar wannan duniya tamu ta shamakance shi daga hasken rana. Ganin haka ya sa injiniyoyi suka bazama wajen neman hanyoyin gyara wadannan fika-fikai don kada su langwabe gaba daya.
Bayan sa’o’i bakwai da wadannan injiniyoyi suka kwahe suna ta hakilo, a karshe sun shawo kan wannan matsala, wacce ake kyautata zaton ta samo asali ne daga cikin injin da ke tafiyar da kumbon gaba daya. Gidan rediyon BBC sashen Turanci ya ruwaito cewa wadannan injiniyoyi sun gama wannan aiki ne ranar asabar din da ta gabata, bayan sa’o’i bakwai da suka shafe suna ta fama. A daya bangaren kuma, injiniyoyin da ke wannan tasha na kokarin nemo hanyoyin sarrafa ruwan sha, wanda ke daya daga cikin kalubalen da suke fama da shi a can inda suke. Ana dai sa ran su fara wannan bincike ne nan ba da dadewa ba, don kaucewa rashin ruwan sha a wannan muhalli mai matukar hadari a cikin sararin samaniya.
A KASAR ANDALUS, MAKABARTA TA ZAMA WAJEN TASKANCE MAKAMASHIN HASKEN RANA
Duniya mai yayi, in ji Hausawa. A daya daga cikin garuwan kasar Andalus (Spain) da ke tsakiyar nahiyar Turai mai suna Santa Coloma ne aka samu wani tsari da ya shafi girka sandunan faya-fayan taskance makamashin hasken rana, watau Solar Panels, don samun ingantacciyar wutar lantarki. Garin, dan karami ne mai dauke da mutane dubu dari da ashirin da hudu, matsattsen gari, mai fama da rashin yalwan filaye, bayan tsananin bukatar haske da makamashin wutar lantarki da yake fama dashi. Wannan ya tilasta wa mutanen garin neman hanya mafi sauki da za a iya bi don taskance musu makamashin hasken rana.
Da aka rasa wani fili isasshe, sai kamfanin da aka baiwa wannan aiki ya doshi makabartar garin, mai dauke da kabararruka sama da dubu hamsin, don gudanar da wannan aiki. Bayan nazari kan dacewar amfani da wannan makabarta, sai kamfanin ya sanar da gwamnatin karamar hukumar da za ta dauki nauyin aikin. Da wannan bayani ya shiga kunnen mutanen gari, sai suka kekasa kasa suka ce ba da yawunsu ba! Da kyar aka shawo kansu ta hanyar lalama da wayar da kai a kafafen yada labarai, tare da sanar dasu cewa za a kiyaye hurumin gawawwakin da ke wannan kushewa, inji Mr. Antoni Fogue, daya daga cikin jami’an gwamnati da aka damka wannan aiki a hannunsu.
A halin yanzu dai an fara shuka dirkokin da ke dauke da wadannan faya-fayan taskance hasken rana, inda kamfanin ya dasa guda dari hudu da sittin da biyu (462). Dirkokin karafan na dauke ne da farantan, masu fuskantar hasken rana, don taskance makamashin da ke kwaranyowa daga gareta a dukkan rana. Akwai tazara tsakaninsu da kabarurrukan, kusan fiye da tsawon mutumWadannan farantai sun fara aiki ne cikin makon da ya gabata, bayan shekaru uku da aka yi ana aikin, wanda ya cinye kasha biyar na fadin filin makabartar.
“A halin yanzu babu wata matsala daga wajen jama’a”, a cewar Mr. Antoni Fogue, “domin duk wanda yaje makabartar, sai ya ga cewa abin ya kayatar.” Mr. Fogue yaci gaba da cewa, “mun sha jin labarin garuruwa masu faya-fayan taskance hasken rana a sama kabarurruka a nan kasar, amma ba irin tsarinmu ba, wanda ya sanya farantan a can saman kabararurruka, dauke bisa dirkoki.” Wannan aiki dai yaci tsabar kudi dalar Amurka dubu dari tara ($900,000), wajen naira miliyan dari da bakwai da dubu dari kenan. Garin Santa Coloma dai na kasar Andalus ne, kuma gwamnati na kokarin samar da wannan sabuwar hanyar samun wutar lantarki ne don kauce wa dumamar yanayi.
No comments:
Post a Comment