Gabatarwa
Duk wanda ya karanta tarihi da kuma asalin fasahar Intanet, zai ga cewa asalin manufar da ta haddasa bunkasa da kwarjinin wannan fasaha ita ce manufar yada ilimi da samunsa cikin sauki. Wannan manufa kuwa ita ce kan gaba har a yanzu. Domin haka ne galibin masu bincike suke karade duniyar Intanet don samun abin dogaro wajen bincikensu - daga dalibai zuwa malamai; daga masu bincike zuwa masu neman karin ilimi; daga ‘yan kasuwa zuwa masu binciken sanin ingancin hajojin da suke bukatar saye. Har wa yau, idan kana neman babban dalilin da yake haddasa karancin masu bincike a dakunan karatu, musamman a kasashe masu tasowa, za ka ga cewa fasahar Intanet ce. Domin muddin bayanai kake nema masu nasaba da kuma alaka da abin da kake bincike, cikin lokaci da kuma yanayi mai sauki, to ka je farfajiyar Intanet. Wannan ba ya nufin cewa fasahar Intanet kadai mai bincike zai dogara da ita wajen bincikensa. Domin akwai abubuwa da dama da ba lallai bane ya same su. Sai dai kuma, kamar yadda duk wani mai bincike ya sani ne, duk bayanan da za su zama madogara a gareshi wajen bincikensa suna dauke ne da wasu siffofi masu muhimmanci; kamar nasaba, da saukin samu, da alaka da kuma tsari. A bayyane yake cewa fasahar Intanet a yau duk ta kumshi bayanai masu wadannan siffofi, komai kankantar bayanan kuwa. In kuwa haka ne, kenan mai karatu ko binciken ilimi bai da wadatuwa da fasahar Intanet a yayin da yake bincikensa. Ga duk wani mai binciken ilimi ta hanyar fasahar Intanet, dole ne ya kiyaye wasu ka’idoji ko matakai da za su taimaka masa kai wa ga nasara. Domin kuwa wani muhalli ne mai dauke da nau’ukan bayanai fiye da tunanin mai bincike. Wannan shi ke nufin cewa dole ne duk wani mai binciken ilimi a wannan muhalli ya samu wasu ka’idoji da za su taimaka masa samun abinda yake nema. In kuwa ba haka ba, to sai ya bace. Ire-iren wadannan matakai ko ka’idoji sun hada da:
Ingancin Bayanai
Abin da duk wani mai bincike ke so a farkon lamari shine ya samu bayanai ingantattu da za su taimaka masa samun kyakkyawan natija a bincikensa. Domin a Intanet akwai bayanai nau’uka dabam-dadan, wadanda wasu suka rubuta su da manufofo dabam-daban, har wa yau. Idan kana bincike ne a kan amfanin wani abu ko muhimmancin wani abu, za ka samu bayanai kan haka, sannan da bayanai masu akasin hakan. Akwai hanyoyi guda biyu da duk mai bincike zai bi don tabbatar da ingancin bayanan da yake son dauka a yayin da yake aikin bincikensa. Hanyar farko ita ce: ka tabbatar da marubucin kasidar ko makalar da ka samu. Wa ya rubuta? Dole ne ka tabbatar da wanda ya rubuta kasidar ko makalar. Domin wannan zai ba ka damar ambaton madogaranka a karashen binciken da kayi. Bayan nan, ka tabbata ka san wani kan fannin da kake son gabatar da bincike a kai. Hakan zai dada taimaka maka wajen fahimtar manufar marubucin. Hanya ta biyu ita ce: ka tabbata cewa marubucin ya ambaci madogaransa a ciki ko karshen kasidar. Wannan ma zai taimaka sosai wajen fadada bincike. Idan cikin wasu littafai ne ya tsamo bayanan, hakan zai sa ka neme su misali, don fadadawa.
Abu na karshe kan abin da ya shafi ingancin bayanai, shine muhallin da ka samu bayanai ko kasidar. Ba kowane gidan yanar sadarwa zaka je don neman bayanai ba. Ba kuma kowanne cikin sakamakon binciken da aka turo maka ke dauke da ingantaccen bayanin da kake nema ba. Dole ne ka nemi muhallin da ke da alaka da fannin bincikenka, don samun natija mai kyau. Misali, kana neman bayanai ne ko kasidu akan hanyoyin da ke haddasa hauhawan farashin kayayyakin masarufi a cikin al’umma (Causes of Inflation in an economy). Dole ne ka doshi gidajen yanar sadarwar da ke da alaka da fannin tattalin arzikin kasa ko hada-hadar kasuwanci. Bayan nan, wasu cikin gidajen yanar sadarwar da ake samun bayanai ingantattu sun hada da: rubutattun kasidun da ake samu daga gidajen yanar sadarwar jaridu da mujallu, da makarantu ko jami’o’i da kuma hukumomin da fannin ya shafe su. Haka kuma, ana samun kasidu masu inganci a gidajen yanar sadarwar malaman jami’a ko kwararru kan fannonin da me bincike ke neman bayanai kan su. In da hali, mai karatu ya kiyaye kansa daga tsamo bayanai daga mudawwanai zalla, watau Blogs. Domin galibin bayanan da ke ire-iren wadannan mudawwanai, ko dai na tallace-tallace ne, ko kuma suna dauke ne da tsantsar son zuciya; ma’ana, zallar ra’ayin marubucinsu, wanda ba lallai bane ya fadi hujjojinsa ba a ciki. Tabbas a kan samu bayanai ingantattu a wasu mudawwanan, amma da dama duk hauragiya ne a cikinsu. A takaice dai, kada ka takaita kanka da su; duk da cewa hakan ya danganci irin bayanan da kake nema ne a bincikenka.
Nasabar Bayanai
Abu na biyu da duk mai bincike ya kamata ya kiyaye shine, alakar da ke tsakanin bayanan da ya samu, da kuma binciken da yake yi. Kada ka rudu da taken kasida ko makala kadai. Ka karanta sadararorin da ke ciki, don tantance alakar da ke akwai da maudu’in da kake bincike a kai. Idan kuwa ba haka ba, sai ka tara bayanai marasa amfani, wadanda kuma ba za su baka natijar bincike mai kyau ba. Bayan nan, cikin abin da zai taimaka maka sanin alakar da ke tsakanin kasidar da ka samu da kuma bangaren da kake bincike akwai sanin yaushe aka rubuta kasidar? Ta yiwu kana neman bayanai ne kan dalilan da suka haddasa rushewar tattalin arzikin kasa a duniya cikin shekarar 2008. Da ka yi tambaya sai aka turo maka kasidu masu taken: “dalilan rushewar tattalin arzikin kasa a duniya” kadai, babu shekara a cikin taken shekarar. Kana ganin haka kai kuma, sai ka budo kasidar, ba tare da karanta kadan cikin mukaddimar ba, ka dinga loda wa kwamfutarka don taskancewa. Sai kaje gida sai kawai ka ga ashe kasidar na Magana ne kan dalilan rushewar tattalin azikin kasa a duniya cikin shekarar 1930, watau gamammiyar matsalar farko da tattalin arzikin kasashen duniya ya fara samu. Ka ga dai ga shi taken kasidar daya ne, kuma kan matsala daya, amma alakar shekara ko lokacin faruwa ta raba su. Wanann kuma ke nuna cewa wannan kasidar ba za ta maka cikakkiyar amfani ba cikin binciken da kake yi. Abu na karshe da ya kamata mai binciken ilimi ta hanyar Fasahar Intanet ya kiyaye shi ne yin amfani da kalmomi masu siffatawa ko kwatanta abin da yake so. Bayan haka, dole ne mai bincike ya san cewa da wahala ya samu wata kasida rubutacciya mai take da tsari da kuma zubin rubutu irin wanda yake bincike a kai. Domin galibin abin da kowa ya sani ne cewa amfanin bincike shine zuwa ko samar da wani abu sabo, wanda wani bai irinsa ko makamancinsa ba. Don haka dole ne ka yi amfani da Kalmar da za ta siffata wa manhajar neman bayanai irin nau’in bayanan da kake so. Sannan kuma ka sani, ba wai taken kasidar da kake rubutawa kadai zaka rubuta wajen neman bayanai ba, a a. Dole ne ka kacalcala kasidar da kake bincike a kai zuwa mataki-mataki ko sashe-sashe. Ka kuma ayyana irin nau’in bayanan da kake so a kowane mataki, watau Outlines kenan. Wannan zai sawwake maka samun bayanai masu nasaba da kasidar, ya kuma sawwake maka tsarin rubutun a yayin da ka tashi rubutawa. Misali, sai malaminka a makaranta ya baka aikin gida da ka rubuta kasida mai shafi goma, kan dalilan da ke haddasa yawan hadarurruka a kan titunan Nijeriya (Causes of Road Accidents in Nigeria). Idan ka tashi bincike, za ka nemo bayanai ne kan tsarin kare hadarruka a Nijeria, da kuma hukumomin da ke lura da hakan a Nijeriya, sannan, a karshe, ka kawo bayanai kan dalilan da ke haddasa wadannan hadarurruka a kan titunan kasar. Wannan ke nuna cewa ba kalma daya kawai za ka yi amfani da ita ba wajen binciken bayanan da kake nema. Kana bukatar kalmomi a kalla uku zuwa hudu, kamar haka: (1) System of road safety in Nigeria, (2) Road safety regulators in Nigeria, (3) Causes of Road Accidents in Nigeria. Idan ka bi wannan tsari kai kanka za ka san cewa ka samu sauki, kuma rubutun ba zai maka wahala ba. A karshe kuma, duk wanda ya karanta ya san cewa lallai ka fahimci abinda ake son ka da rubutawa. Bayan haka, sai abu na karshe:
Ina Zan Je?
Kammalawa
Fasahar Intanet duniya ce makamanciyar wacce muke rayuwa ciki, amma a wani irin tsari da kimtsi da ya sha bamban da wannan duniyar tamu da zahiri. Duk abin da kake bukata na bayanai kan wani nau’in ilimi a duniya, in Allah Ya yarda kuwa za ka same shi. A wani lokacin kyauta, a wani lokacin kuma sai ka biya taro da kwabonka. Duk da haka, samuwar fasahar Intanet a wannan zamani da muke ciki ya samar da dama ga dalibai zuwa har malamansu, wajen fadada binciken ilimi da kuma sanayya kan wannan duniya ta mu da irin al’ummar da ke makare cikinta. Duk da yake yin hakan ba ya samuwa ta dadi ba tare da mai bincike ya san wasu ka’idoji ko matakan da zasu sawwake masa binciken ba. Dole ya kiyaye ingancin bayanan da zai ci karo dasu yayin da yake nema; ya kuma fahimci alakar da ke tsakanin bayanan da kuma fannin bincikensa. Idan ya san wannan, abu na karshe da ya rage masa shine yin amfani da kalmomin da zasu nemo masa abin da yake so, a muhallin da ya dace da wannan fannin da yake bincike a ciki. Da wannan, sai mai bincike ya tsinci dame a kala.
Salam, barka da war haka Baban Sadiq, sannu da kokari. Allah taimaka, amin.
ReplyDeleteIsa Adam