Monday, March 16, 2009

Rage Dumamar Yanayi ta Hanyar Attakar Rana

Kwanakin baya muna tattaunawa tare da wani aboki na a ofis, yana ta fama da wayar salulaclip_image002rsa, wacce babu caji ko na aranyo, ya kuma nemi na’urar caji (watau Charger) wacce ta dace da wayar salularsa (‘Yar Kasar Sin ce), amma ya rasa. Sai kawai yayi tsuki, yace: “wai don Allah me zai hana a fara kera wayoyin salula masu amfani da makamashin hasken rana ne?” Sai kawai na fashe da dariya, nace masa: “me kake ci na baka na zuba? Ka tuna fa, rashin samuwan hakan a yanzu ba kasawa bane, lokaci ne kawai bai yi ba.” Na kara jawo hankalinsa da cewa, shekaru ashirin da suka gabata zai yi wahala ka samu agogon hannu mai amfani da hasken rana (Solar Clock), ko kuma na’urar lissafi (Solar Calculator). Amma yanzu fa? Ga su nan birjik, sai ka zabi wanda kake so. Don haka ba abin mamaki bane idan nace a halin yanzu ma akwai kokari makamancin hakan, kan abinda ya shafi wayar salula. Komai a hankali a ke yin sa. Bayan haka kuma, idan aka kera ba nan take za a fara sayarwa ba, sai an dauki shekara ko wasu shekaru ana gwaji, kafin masu saye da sayarwa su samu a kasuwa.

Kasa da mako guda da yin wannan hira tamu, sai ga rahonni da ke nuna samuwar kwamfuta da kuma mota masu aiki da attaka ko makamashin hasken rana. Wadanan su ne ci gaba da ake ci gaba da samu a kokarin da ake yi na ganin an rage dumamar yanayi a duniya, ta hanyar sauya hanyoyin amfani da makamashi. Kamfanin LG da ke kasar Koriya ta Kudu ne ya kirkiri wannan kwamfuta mai amfani da hasken rana a yayin da kake amfani da kwamfutar a waje. Kamfanin yace yayi wannan hobbasa ne saboda yawan korafi da yake samu daga kwastomominsa, kan cewa kwamfutocin da yake kerawa na cinye musu makamashin batirinsu, nesa ba kusa ba. Kai ba kwamfutoci kadai ba, hatta na’urar sanyaya ruwa (watau firji) da talabijin da kamfanin ke kerawa, duk da ingancinsu, basu wasa wajen aiki da makamashi fiye da kima. Wannan tasa kamfanin ya sake lale, wajen bullo da kwamfutar hannu da ta kan tebur mai amfani da hasken rana idan kana waje. A yayin da kake gida kuma sai ka sauya tsari wajen amfani da wutar lantarki. Kamfanin ya kuma tabbatar da cewa zai fitar da wannan kwamfuta ne cikin wannan sabuwar shekara da muka shiga, don fara sayarwa. A yayin da ka fito cikin haske ka kunna wannan kwamfuta na kamfanin LG, zai rika taskance kashi saba’in da biyar na makamashin da yake tafiyar da kansa ne daga hasken da ke muhallin da kake. Kashi ashirin da biyar kuma daga batir. Don haka masu amfani da shi sun samu saukin matsalar makamashi.

A daya bangaren kuma, cikin watan Disambar shekarar da ta gabata ne wani bawan Allah dan kasar Suwizalandclip_image004 ya tike tafiyarsa da ya faro watanni shida da suka wuce a kan motar da aka kera mai amfani da makamashin hasken rana zalla. Cikin watan Yunin 2008 ne Injiniya Louis Palmer, dan shekara 36, ya fara shawagi a wannan mota daga kasarsa, zuwa kasashen Turai da Gabas ta Tsakiya, da Asiya da Austiraliya da New Ziland, da America, inda a karshe, ranar 17 ga watan Disamba ya tike wannan shawagi a kasar Poland, daidai lokacin da ake fara taron yunkurin da kasashen duniya ke yi na ganin an rage dumamar yanayi a duniya. Wannan mota, wacce ‘yar karama ce mai wurin zaman mutum biyu kadai, na dauke ne da wani tafkeken farantin taskance hasken rana, don kara wa motar kuzari. Injiniya Palmer dai yace tun da ya faro wannan shawagi tasa ta kewaya duniya a wannan mota, bai yi mu’amala da man fetur ba.

Injiniya Palmer dai ya kewaya kasashe arba’in ne, wadanda suka tattaro dukkan nahiyoyin duniya gaba daya. Manufar kera wannan mota kuma shine yin gwaji don ganin yiwuwar rage dumamar yanayin duniya da ake ta samu sanadiyyar amfani da makamashin man fetur ko gaz ko dizil masu haddasa hayaki. A cewar kwararru, wannan ke nuna cewa nan da wasu shekaru masu zuwa jama’a za su fara hawa mota ko Babura masu amfani da hasken rana zalla, wadanda basu bukatar man fetur ko wani nau’in makamashi mai haddasa hayaki. Wadannan abubuwa guda biyu kuwa, a cewar masu lura da ci gaban duniya, na cikin sabbin sauyin da duniya zai samu a shekarar 2009.

No comments:

Post a Comment