Kowace Sauki da Matsalarta
Idan ba sauki bace mai damfare da asalin shari’ar musulunci, kowace sauki na tafe ne da irin nau’in matsalarta. Wannan ka’ida ce ta rayuwa sananniya, musamman idan mai karatu yayi la’akari da sabuwar tsarin cirewa ko karbar kudi da bankunan Nijeriya suka bullo da ita mai suna Automatic Teller Machine, ko kuma ATM a takaice. Wannan na’ura ta ATM tana dirke ne a bakin kofar kusan dukkan bankunan Nijeriya da ke manyan biranen kasar nan, wacce kwastomomin bankunan ke amfani da katin da bankinsu ya basu, don cire kudadensu ba tare da sun shiga cikin bankin sunyi layi don karba daga wajen ma’aikatan bankin ba. Wannan kati shi ake kira ATM Card, a turance. Katin na kumshe ne da bayanai kan taskar ajiyarka; da lambar taskar ajiyarka, da wasu lambobi na musamman, da kalmomin iznin shirgarka (PIN Cord), sa kuma sinadaran Chip, masu hada alaka tsakanin katinka da injin ATM, da kuma kwamfutocin bankin da kake ajiya, don sheda ka ta wadannan lambobi. Ta hanyar wannan kati kana iya cire kudi daga taskarka, ko ka duba yawan abinda kake dashi a ciki, ko aiwatar da wasu aiyuka irin su sayen katin wayar salula na kamfanin MTN da dai sauran aiyuka masu nasaba da hakan. Sannan, sai wanda ke bukata ake bashi; idan ba ka bukata, ba dole bane sai ka karba, duk dadewar da kayi kana mu’amala da bankin. Amma duk da haka, yana da kyau ka san cewa muddin bankinka ya sanar da kai cewa akwai katin ATM ya tanada maka, ba tare da cewa kai ne ka rubuta kana so ba, to yana da kyau kayi dayan abu biyu; ko dai kaje ka karba ne tun wuri, ka soma amfani dashi, muddin kana bukata kenan. Ko kuma kaje kace musu baka bukata, sai a san cewa baka karba ba. Yin hakan na da muhimmanci kamar yadda mai karatu zai san dalili nan gaba.
Lokacin da wannan kati ya fara fitowa da dama cikin mutane sunyi farin ciki da zuwansa, musamman wadanda ke ajiya da tsoffin bankuna irin su First Bank da Union Bank da Afribank da dai sauran bankuna masu dogon layi wajen karba ko zuba kudi a kullum. Hakan ya basu damar cire kudadensu duk lokacin da suke so; daga fitowar alfijir zuwa ketowar wani alfijir din – awanni ashirin da hudu kana iya cire kudinka daga banki ba tare da shiga ka bi layi ba, ko kuma jira lokacin bude bankin ba, wanda daga karfe takwas din safiyar kowane rana ne zuwa karfe hudu ko biyar na yamma. Wannan ba karamar sauki bace, a cewar da dama cikin masu ajiya da bankuna a Nijeriya, musamman ma manyan birane irin su Kano da Kaduda da Abuja da Legas da Fatakwal da sauran birane. Kamfanin da ke dillancin wadannan mashuna na ATM dai shine kamfanin INTERSWITCH. Shi ke da na’urorin da ke hada alaka tsakaninsu da mashin din ATM da ke girke a kofofin wadannan bankuna, da kuma kwamfutocinsu masu dauke da bayanan taskar ajiyar mutane. Wannan kamfani na INTERSWITCH yayi fice kan wannan sana’a, kuma ba shi da abokin hamayya a harkar. Duk bankunan Nijeriya da katinansa suke amfani wajen baiwa kwastomominsu damar cire kudi ta hanyar na’urar ATM. Duk da yake nau’ukan mashin ya sha bamban tsakanin bankuna, amma dai kamfani daya ne ke tafiyar da al’amuran.
Matsalolin “ATM” A Nijeriya
Bayan kusan shekaru uku da fara amfani da wannan sabuwar hanya ta mu’amala tsakanin mutane da bankunansu, a yanzu matsaloli sun fara kunno kai babu kakkautawa. Wannan ka’ida ce ta rayuwa, kuma babu makawa dole sai an samu hakan, musamman ta la’akari da inda wannan tsari ya samo asali, watau kasashen Turai. A wadannan kasashe, wadanda tun sama da shekaru ashirin suke amfani da wannan tsari na ATM da ma wadansu tsare-tsare makamantansa, sun dade da samun ire-iren matsaloli makamantan wadanda suka fara kunno kai a Nijeriya. Kamar dai ire-iren matsalolin da suka shafi wayar salula ce da kuma tsarin sadarwa ta wayar tarho da muke ta fama dasu a yanzu.
Matsalolin ATM a Nijeriya suna da yawa. Kuma ga dukkan alamu ba iyakacinsu ba kenan, akwai saura (duk da yake ba fatan karuwarsu muke yi ba). Mafi muni daga cikin su shine kana zaune kawai sai kaji sakon text ya shigo cikin wayar salularka, cewa: “ka cire naira dubu kaza daga taskar ajiyarka ta hanyar ATM, a rana kaza, da karfe kaza, a kuma gari kaza”. Ta yiwu a lokacin da ka samu wannan sako ma baka taba amfani da katin ba, bayan ka karba. Ko kuma kana amfani da katin, amma ba kai bane ka cire kudin; hasali ma dai watakil baka taba zuwa garin da aka ce ka cire kudinka ta ATM din da ke can ba. Tirkashi! Haka ya taba faruwa da wani bawan Allah dan Gombe. Babban yayansa da muke aiki wuri guda yake sanar dani cikin shekarar da ta gabata, cewa an aiko masa sakon text cewa ya cire naira dubu dari biyu cikin taskarsa ta hanyar ATM, a Legas. A cikin sakon aka sanar dashi rana da kuma lokacin da aka ce ya cire kudaden. Ai nan take hankalinsa ya tashi. Domin bai taba zuwa birnin Ikko ba. Na biyu kuma, tunda aka bashi katin, bai taba amfani dashi ba balle ace ko sacewa aka yi. A karshe ya duba katin da aka bashi, ga katin nan tare dashi. Amma yanzu banki na sanar dashi cewa an cire zunzurutun kudi har naira dubu dari biyu daga taskarsa. Daidai lokacin da abin ke faruwa yake sanar dani, ya kuma ce zai je bankin don su daddale. Ban san yaya suka kare ba. Amma ban da tabbacin ya samu biyan bukata, kamar yadda zamu ji wani labarin makamancinsa nan gaba. Shin wannan maita ne ko kuwa mene ne? Ga kati na tare dashi, bai taba zuwa birnin Legas ba a rayuwarsa gaba daya, amma an ce ya cire kudade daga taskarsa. Wannan lamari ya tayar masa da hankali sosai.
Labari na biyu makamancin wannan shi ma wani ma’aikacinmu ya sanar dani, don abin ya faru ga wani dan uwansa ne na jini, kamar dai labarin baya, kuma daidai lokacin da bankin ya yanke hukuncinsa mara dadin ji yake gaya mini. Wannan dan uwan nasa ya saba amfani da katin, amma kuma badakalar da aka yi masa a Legas ne, bayan shi yana zaune ne a nan Abuja, ga katinsa na tare dashi. Sakon farko da ya samu ana sanar dashi ne cewa ya cire naira dubu dari daga taskarsa, a safiyar da text din ta shigo. Wannan abu ya faru ne da sassafe, tun bai fita aiki ba. Aka ce a Legas ya cire kudaden, a ranar, da karfe kaza. Yana cikin shan mamaki irin na bakin ciki, sai ga wani sakon ya sake shigowa, mai sanar dashi cewa ya kara cire naira dubu dari daga taskarsa! Babban Magana, wai Dansanda ya ga gawar soja. Wannan abu ya tayar masa da hankali inda nan take ya garzaya bankin don sanar da su. Bayan sanar dasu, sai suka ce masa ya rubuta takardar korafi kan abinda ya faru, don hakan zai taimaka musu wajen warware matsalar. Ya rubuta nan take ya basu. Bayan wasu ‘yan kwanaki, sai suka aiko masa da wasika cewa sai dai ya dau na Annabawa, domin sun duba basu ga inda suke da laifi ko zama sanadi wajen faruwar wannan lamari ba. Don haka sai dai kawai yayi hakuri. Ire-iren wadannan sun faru ga mutane da dama musamman masu ajiya a birane irin Abuja da Kano da Legas.
Bayan wadannan manyan matsaloli da makamantansu, akwai kuma ‘yan kananan matsaloli masu cin rai da wannan mashin na ATM ke dauke dasu. Da farko dai, ba wani abin mamaki bane ka kwaso sauri a gaggauce don cire kudi, sai kawai a ce maka babu kudi a cikin mashin din. A wasu lokuta kuma, sai ka sanya katin ka cire kudin, sai ya makale a cikin mashin din yaki fitowa. Idan ma baka yi sa’a ba, sai ka bukaci kudin, a ce babu, kuma katin ya makale. Wannan abu da cin rai yake, musamman idan hakan ya faru da kai ne cikin dare, kuma ranar asabar ko lahadi. Sai dai kayi hakuri, don mai gadi bazai iya ciro maka katinka daga cikin wannan na’ura ba. Wasu bankuna kuma ko da katin su kayi amfani sai sun cire maka naira dari biyu. Idan ka je mashin din wani bankin kuma, da wannan katin, bankin zai cire naira dari, kamar yadda aka saba, bankinka kuma ya sake cire maka naira dari biyu. Har wa yau, wata matsala da ba kowa ke son ta ba ita ce matsalar rashin kimar kudin da kake bukata. Misali, idan kaje cire kudi, kana iya sanya yawan kudin da kake so (dubu daya, ko dubu biyu, ko dubu biyu da dari biyar ko makamantan hakan). Kowane banki ka’idarsa dabam ne wajen baka damar cire kudi. Wasu bankunan sai dai ka cire dubu daya ko biyu ko uku; ma’ana ba su da tsarin ‘yan dari biyar-biyar. Ba za ka iya cire naira dubu biyu da dari biyar ba; ko dai ka cire dubu uku ne, ko kuma ka hakura da dubu biyu. Matsaloli ire-iren wadannan mai ajiya na iya hakuri dasu, amma irin wadanda bayani ya gabata kansu a sama ba kowa zai iya lamunce musu ba. To meye dalilin da ke haddasa faruwar ire-iren wadancan matsaloli?
Musabbabai
Dole akwai matsala, to amma me ke haddasa matsalar? Wannan shine abin da galibin masu ajiya a bankuna ke damuwa a kai. Wannan tasa da yawa suka daina amfani da katin; wasu kuma suka ki karba ma gaba daya. Domin a cewarsu, kada su buda wa wani dan iska kafa; suna aiki shi kuma yana kwashe musu kudade a wofi! Akwai dalilai da dama da ke haddasa wannan mummunan ta’ada ta sace wa mutane kudade ta irin wannan hanya mai ban mamaki. Da farko dai, masu yin wannan aiki ‘yan dandatsa ne, watau ATM Hackers. Sunan wannan mummunar sana’a tasu kuma shine ATM Skimming, a Turance. Kamar yadda ake da ‘yan dandatsa a harkar kwamfuta, to haka ake da su a bangaren tsarin ATM. Masu wannan aiki kuma sun samo fasahar yin hakan ne ta hanyoyi biyu; ko dai ta amfani da kwarewa irin ta kwakwalwarsu kan harkar sata, ko kuma ta hanyar koyon ilimin yin hakan daga kasashen Turai inda wannan aiki yayi kaurin suna, ta hanyar Intanet. Hanyar farko da suke bi ita ce ta hanyar kera katinan ATM makamantan wadanda bankuna ke bayarwa, amma na bogi. Sai dai kuma duk dabararka ba za ka iya gane bambanckin da ke tsakaninsu ba. Daman katin holoko ne. Idan kamfanin INTERSWITCH ya aika wa bankuna, sai su kuma su kirkiri lambobi da kuma kalomomin iznin shiga (PIN Cord) na wuin gadi da suke baiwa kwastomominsu. Shi yasa idan kaje karbar katin, sai a ce ka jira (a wasu bankunan kenan). Za a je ne a darsana wa katin wasu sinadarai masu dauke da wadannan lambobi da bankin ke bayarwa, ta hanyar wata na’ura da suke amfani da ita, kamar dai yadda kamfanonin wayar salula ke darsana wa katin SIM lambobin wayar da suke sayarwa. Asalin katin ai holoko ne. Sai an darsana masa wadannan sinadarai sannan za ka iya amfani da shi.
Don haka idan suka kera wadannan katuna, abu daya kawai ya rage musu. Wannan abu kuwa shine na’urar da ake amfani da ita wajen darsana wadannan bayanai masu dauke da lambobin taskar masu ajiya. A nan ne fa gizo ke sakar. Su kadai suka san hanyoyin da suke bi wajen satar bayanan taskokin ajiyar mutane. Suna iya samun haka ta hanyar satar katin wasu, su tace bayanan da ke ciki ta hanyar kwamfuta, sannan su ci gaba da tatsar mai taskar, ko da kuwa an bashi wani katin. A wasu lokuta kuma suna amfani ne da dabarun satar bayanan sirrin mutane, ta hanyar lekenka a yayin da kake kokarin cire kudi. Suna iya tsayawa a bayanka, gab da kai, ta yadda suna iya ganin wasu kalmomi ko haruffa ka danna don cire kudinka. Idan suka san wadannan, sun gama komai. Ba sai sun saci katinka ba, a a. Suna iya amfani da wani katin holoko, don aiwatar da wannan aiki cikin sauki. A wasu lokuta kuma, suna iya samun bayanai daga jikin ‘yan rasitin da ake watsarwa a farfajiyar bankin. Da dama cikin mutane basu san tasirin barin rasitin taskarsu ba a yayin da suka cire kudi, duk da cewa sun baiwa mashin din umarni da ya ciro musu bayanai kan abinda ya rage a cikin taskarsu bayan kudin da suka cire. Har wa yau, a wasu lokuta masu wannan ta’ada na iya dasa wata ‘yar karamar na’ura mai satar bayanan sirri a daidai wurin da ake shigar da katin. Da zarar ka gama cire kudadenka, wannan na’ura za ta taskance bayanan da kayi amfani dasu. Su kuma sai su zagayo daga baya su cire, don tace bayanan da ke ciki. Sun fi yin wannan a wuraren da babu cikakkiyar tsaro.
Sabuwar hanyar da suka sake bullowa da ita kwanan nan kuma ita ce rudar mutane (musamman ‘yan Nijeriya masu akwatin wasikar sadarwa ta Imel) ta hanyar Intanet. Suna yin hakan ne ta hanyar sakonnin bogi, watau Spam Mails. Sakonnin sata da zamba cikin aminci, wadanda ake aiko wa mutane ba tare da su suka bukace su ba. Kwanakin baya akwai labarai da suke ta kai komo cikin biranen Abuja da Legas cewa wasu ‘yan Dandatsa sun afka wa kwamfutoci da kuma na’urorin kamfanin INTERSWITCH, inda suka saci bayanan sirrin mutane, suka yi ta ta’addanci wajen wawashe musu kudade. Wannan ya tilasta wa da yawa cikin bankunan da ke wadannan birane biyu sauya tsarinsu na ATM, inda suka caccanza wa dukkan masu rike da katinan ATM dinsu kalmomin iznin shigarsu (PIN Cord). Daidai lokacin da wannan abu ke faruwa naje don cire kudi na ta amfani da katin da daya cikin bankunan da nake mu’amala dasu ya bani. Nan take na kasa shiga. Aka ce mini wai kalmomin da na shigar ba daidai suke ba. Don haka sai na shiga ciki, inda na samu jami’in da ke lura da wannan fanni, shine yake min bayani makamantan rade-radin da nai ta ji a baya. To sai masu wannan ta’ada ta Intanet suka dauki wannan dalili don rudar mutane ta hanyar sace musu kalmomin iznin shiga da kuma bayanan taskarsu, cikin sauki. Yadda abin ya faru kuwa shine, na shiga akwatin wasikar hanyar sadarwata ta Imel ranar litinin, 15 ga watan Janairun 2009, sai na ga sakon Imel wai daga kamfanin INTERSWITCH zuwa gare ni. Abin ya bani mamaki. Yaushe na fara alaka da kamfanin kai tsaye, balle har ya san adireshin Imel di na? Sai dai na bude. Nan take na samu sanarwa cewa wai kamfanin na kara inganta hanyoyin mu’amalarsa da kwastomominsa ne, don haka ake sanar dani don amfanin kai na, da in yi maza-maza wajen bayar da wasu bayanai da suka shafi katin ATM dina don tsira daga ‘yan Dandatsa. A kasan bayanan naci karo da rariyar likau, wacce aka ce in bi don ta kai ni shafin da zan bayar da bayanan da ake bukatar in bayar. Ina ganin haka sai mamaki ya kama ni. Da na duba kirjin sakon (watau Header), sai na gane sakon bogi ne. Wasu ne kawai ke son satan bayanan sirri na cikin sauki, don su rika yashe min taska ta ba tare da wani gumi ba. A saman sakon babu adireshin Imel dina a matsayi na na wanda aka aiko wa sako, sannan babu adireshin kamfanin INTERSWITCH, a matsayinsu na masu aikowa. Sai dai na bi rariyar, inda ta kai ni shafi mai dauke da wuraren shigar da bayanai: suna na, da lambobin iznin shiga na, da adireshin Imel dina, da lambar tarho dina, da kuma lambar da ke dauke a jikin kati na. Ina shiga wannan shafi, sai manhajar da ke lura da kwayoyin cutar kwamfuta da ke kwamfutata ta sanar dani nan take, cewa ta cafke wani kwayan cutar kwamfuta (watau Computer Virus) guda daya, ta kone shi har lahira. Nan dai na tabbatar da cewa sakon bogi ne, kuma barayin Intanet ne ‘yan Nijeriya ke amfani dashi wajen yaudarar mutane don sace musu kudade cikin sauki. Sai na zarce zuwa gidan yanar sadarwar kamfanin INTERSWITCH don tabbatar da gaskiyar wannan sako ko rashinsa. Ina zuwa zauren gidan, sai aka min barka da shigowa da wata sanarwa ta gargadi kan barayin Intanet masu yaudarar mutane, da kuma cewa idan na sake na basu bayanan kati na, to ni na sano. Daga nan na ci gaba da samun ire-iren wadannan sakonni a sigogi dabam-daban. Sai na samu natsuwa kan hukuncin da na yanke.
Me Ya Kamata Mu Yi?
To me ya kamata mai ajiya a banki, mai kuma amfani da katin ATM ya kamata yayi a irin wannan yanayi da lokaci mai cike da rudani makamancin wanda muka karanta a baya? Akwai abin yi da dama; daga wanda zaka iya yi a matsayinka na mai amfani da katin, zuwa matsayin da bankuna zasu dauka, tare da na Hukumomin Gwamnatin Tarayya masu lura da wadannan bankuna. Da farko dai idan kana rike da wannan kati kuma kana son ci gaba da amfani dashi, to dole ne ka rika adana shi sosai. Kada ka bari wani ya san kalmomin iznin shiganka sai wanda ka amince masa. Sannan idan kazo zaban kalmomin iznin shiga da zaka rika amfani dasu wajen aiwatar da cire kudade ko wani abu dabam, to ka guji yin amfani da lambobin ranar haihuwarka. Da dama cikin mutane kan yi amfani ne da kwanar watan ranar haihuwarsu (date of birth), wanda kuma hakan shi yafi saukin ganewa wajen wadannan ‘yan ta’adda. Bayan haka, idan kana da katin sai ya bace, to maza ka garzaya zuwa ofishin ‘yan sanda ka sanar, don a baka takardar sheda kan haka, sannan kaje kotu da kuma bankin da kake ajiya dasu, don sanar dasu halin da katin ya shiga. Idan ka bata lokaci, duk wanda ya sace katin ko ya tsinta, akwai yiwuwan iya amfani dashi dari-bisa-dari. Amma idan ka kai kara nan take, za a canza maka wani, a kuma bata dukkan bayanan da ke wancan dayan don ya zama kai kadai kawai ke da damar shiga taskar. Idan ka zo cire kudi, ka rika lura da yanayin mutane. Idan ka ga mutum ya like maka a layi wajen cire kudi, to dole ne ka canza wuri, ko kuma a kalla ka bashi damar ya yi abinda ya zo yi, in ya gama, sai ka cire kudinka. A kul ka amince wani na like da kai a kafadarka, lokacin da kake danne-dannen cire kudi. Sai ya sha ka musilla baka sani ba. Haka kuma, ka lakanci siffar mashin din da kake cire kudi daga gareta, idan wuri daya kake zuwa a kullum. Duk ranar da ka ga yanayin ta ya canza musamman wajen sanya katin nan, to kayi hattara. Bayan haka, idan ka san baka bukatar rasiti, to kada ka umarci mashin din da ya fitar maka. A karshe idan ka daina amfani da katin, to ko dai ba mayar da shi ne zuwa ga bankin da ya baka, ko kuma ka kona ko binne shi gaba daya. A daya bangaren kuma, idan hankalinka bai kwanta ba, to kada ka karbi katin. Ka hakura da zuwa bankin don cire kudinka kawai. Idan kuma kana da taskokin ajiya guda biyu a banki daya, to a kul ka kuskura ka hada su cikin kati guda. Ka bar daya mai kati, dayan kuma haka kawai. Wannan zai sa duk lokacin da kaji al’amura sun rikice na sace-sace, sai kawai ka kwashe kudadenka daga taskar da ke da kati zuwa wacce bata da shi. Ka kuma tsare katinka sosai, idan kana da yawan mantuwa ka samu wani wuri na musamman don boye shi, kada ka yar dashi a halin kai-komonka. Idan kana mu’amala da fasahar Intanet, duk wanda ya aiko maka da sakon Imel cewa ana son ka bayar da bayanai kan katinka, to dole ka yi hattara da ire-iren wadannan sakonni. Idan a kwamfutarka kake karanta sakon, kada ma ka bude. In kuwa ba haka ba, to akwai yiwuwar kwamfutar za ta kamu da kwayoyin cutar kwamfuta masu hallaka ruhin ko haukatar da ita. Don haka a yi hattara ta kowane fanni.
A bangaren bankuna kuma, tabbas an san ba lallai bane su dauki dawainiyar hasarar da mutane suka yi musamman wanda ya shafi sakaci wajen adana kati da bayanan da suka shafi hakan, wanda kuma hakan ke haddasa irin wannan ta’ada mummuna, amma kuma dole ne su dauki dawainiyar ilimantar da kwastomominsu kan muhimmancin tsaro. Duk sanda suka samu labara kan wata badakala da wasu ke yi wajen sace-sace a wannan tsari, dole su sanar dasu. Domin a yanzu dai kam babu wannan hanya ta ilmantarwa ko kadan. Wannan bai kamata ba. Sannan dole ne su sanya tsaro sosai wajen wadannan mashina na ATM, su rika lura da wadanda ke lazimtar wajen a kullum ba don zuwa cire kudi ba, sai dai kawai su zauna a gefe suna lura da jujjuyawar mutane. Wannan bai kamata ba ko kadan. Hukumar babban bankin Nijeriya ma tana da nata hakkin da ya kamata ta rika lura dashi. Shine ta tilasta wa wadannan bankuna, tare da kamfanin INTERSWITCH ganin suna amfani da hanya mafi inganci wajen tsare dukiya da bayanan mutane a dukkan na’urorinsu. Hukumar EFCC ma tana da nata hakkin, wajen ganin ta samo hanyar cafke masu rudar mutane ta hanyar Intanet. Da wannan, sai kayi amfani da katin ATM dinka lafiya. Amma idan ba haka ba, to da sauran rina a kaba! Allah Ya tsare mu, amin.
No comments:
Post a Comment