Ga kadan cikin wasikun masu karatu nan kamar yadda muka saba kawowa lokaci-lokaci. Wasu na riga na amsa su tun sadda aka aiko su, wasu kuma nayi alkawarin amsa su ne a wannan shafi; wasu sakonnin kuma ta hanyar wayar tarho aka yi su, na bayar da amsarsu nan take. Don haka wadanda aka bugo don yabo, sai dai muce Allah saka da alheri, don ba zan iya kawo dukkansu ba. Wadannan sakonni dai na text ne ko wadanda aka rubuto ta hanyar Imel, muna kuma kara nuna godiyarmu ga dukkan masu bugowa ko aiko da sako ta dukkan hanyoyin, Allah saka da alheri, ya kuma bar zumunci, amin summa amin. A halin yanzu ga sakonnin nan:
Malam Assalamu Alaikum, ina son cikakken bayani kan fai-fai guda biyu; na GARMAHO da na CD. A duniyar kimiyya da fasaha ya abin yake ne Malam? Na kasance ina da karancin shekaru. Allah ya taimaki Malam da almajiransa amin. – Aliyu Muktar Sa’idu, Kano: 08034332200, 07025815073
Hakika shafin Kimiyya da Fasaha na matukar godiya gareka saboda irin himmarka wajen bibiyar darussan da ake zubowa a wannan aji, ta hanyar bugo waya ko text da dai sauransu. Lallai fasahar faya-fayan Garmaho da na CD suna da alaka da juna, alaka ta asali kuwa, kuma na tabbata cikin masu karatu da karancin shekaru irinka basu san fai-fan garmaho ba, sai na CD. Na kuma tabbata akwai masu sha’awan son jin yadda wannan fasaha yake. In Allah Ya yarda muna nan tafe da jerin kasidu kan haka nan ba da dadewa ba. Mun gode. – Baban Sadiq
Assalamu Alaikum Baban Sadiq, godiya muke yi da binciken da kake yi. Kuma gudunmuwar ilimi da kake bayarwa sun amfanar. Da fatan za ka ci gaba da binciko mana abubuwan al’ajabi kana sanar da mu. Allah biya, ya jikan mahaifa, ya kara maka da mu ilimi mai amfani. Na gode. – Baban Auwal, Abdullahi A., Keffi, Nassarawa State: 08035974923
Baban Auwal, mu ke da godiya kwarai kan haka. Allah kara mana juriya da hakurin bin darussa. Allah taimake mu baki daya kan haka, amin. – Baban Sadiq
Assalamu Alaikum, don Allah ka daure ka buga mana littafi game da kwamfuta da Hausa. – Hon. Isa Tilde: 08023185801
Hon Isa mun gode da wannan shawara. Akwai littafin koyon kwamfuta da aka kaddamar a Kano makonni biyu da suka gabata. Na kuma tabbata zai fara yaduwa nan ba da dadewa ba. Sai a nema, kafin wanda na rubuta kan Fasahar Intanet ya bayyana in Allah Ya yarda. Mun gode. – Baban Sadiq
Assalamu Alaikum Baban Sadiq, fatan alheri. A bayaninka na Etisalat a cikin Jaridar AMINIYA ta ranar Jumu’a 28/11/2008, akwai abubuwan dubawa kamar biyu: na farko kyautar 300secs a wata ne ba a kullum ba. Na biyu, “Home Zone” yana nufin wuraren da za a yi ma saukin caji in ka kira kana wurin ne, ba wai in ka kira wuraren ba. Na gode. – Shehu Dahiru Fagge, Kano: 08060651115
Malam Shehu na gode da wannan fadakarwa da kayi min, kuma Allah saka da alherinsa, amin. Kamar yadda na sanar da kai ne a jawabin sakon Imel da na aika maka, cewa aiyuka sun ruda ni, sai na mance, shi yasa baka ga na fitar da gyarar a shafin AMINIYA ba. A yanzu ga shi nan, kuma Allah saka da alherinsa amin. – Baban Sadiq
Assalam na ga sakonka kuma na ji dadin kasancewar ka mai amsar gyara, da fatan Allah ya yi maka jagora ya kuma tallafawa wannan kamfani namu MEDIA TRUST. Ya kuma kara ma sa kwararrun ma'aikata irinka. Nagode. Naka a kodayaushe - Shehu Dahiru Fagge (Baba), shehudahir@yahoo.com.
Af, ashe ma ka samu sakon nawa kenan! To Allah sa mu dace baki daya, amin. – Baban Sadiq
Salaam, na rubuto ne domin in mika gaisuwa na, da fatan an yi sallah lafiya, allahumma amin. Abbas Amin: 07032997200
Lallai mun yi sallah lafiya Malam Abbas, mun kuma gode, Allah saka da allherinsa, amin summa amin. – Baban Sadiq
Baban Sadik, ka manta littafin “Mu Koyi gyaran Rediyo” na Musa Isa, da kuma “Ikon Allah (1-5).” Muna yaba kokarinka a wannan shafi. Allah Ya taimake mu. – Nasir G. Ahmad: 08065496902
Wannan haka yake Malam Nasiru, kuma na shigar da bayanin kamar yadda na tabbata ka karanta a kasidar karshe kan wannan maudu’i. Mun gode da tunantarwa, Allah bar zumunci. – Baban Sadiq
Baban Sadiq akwai wani bawan Allah ana kiransa Alhaji Isa Musa Gumel, ya rubuta littafi (mai suna) “Mu Koyi Gyaran Rediyo” (1-2), ma’aikacin NEPA ne, kuma mazaunin Kano. – Shazali Lawan Gumel, Gumel, Jigawa: 08060103506
Malam Shazali kai ma mun gode da wannan tunatarwa. Na kuma tabbata ka ga tunatarwarka mun shigar cikin kasida ta karshe kan wannan maudu’i. Mun gode. – Baban Sadiq
Assalamu Alaikum, Baban Sadiq shin zan iya samun littattafan Farfesa Muhammad Hambali Jinju a Kano? Kuma a wani waje? – Ahmad Muhammad Amoeva: 08066038946, 07028456188
Kamar yadda na sanar da kai, idan kaje “Bata” za ka samu in Allah ya yarda. Ko kuma kaje shagon sayar da littafai da ke Jami’ar Bayero, ko ka aika ABU Zaria. Allah sa a dace, amin. – Baban Sadiq
Baban Sadiq, kasancewar wannan shafi namu mai albarka na Kimiyya da Fasaha yana yin waiwaye, to ni ma ina son ai min fashin-baki a kan “Asusu” (Bank), da wasu nau’uka na cikinsa; kofar shiga, da kofar fita (bullet-proof security door), na’urar kirga kudi (counting machine),motar daukar kudi (bullion van). – Aliyu Mutkar Sa’id Kano: 08034332200
Malam Aliyu, idan na fahimci tambayarka, kana son bayanai ne kan nau’ukan fasahar da aka yi amfani dasu wajen kera wannan abubuwa da a yanzu ake amfani dasu wajen tafiyar da harkokin kudi. Insha’Allahu a hankali duk za a samu bayanai daya-bayan-daya. Komai a hankali ake binsa, saboda yanayin shafi da kuma lokaci. Allah sa mu dace, amin. – Baban Sadiq
Salamun Alaikum, Baban Sadiq, wutar lantarki (electricity); wasu kasashe na duniya suna hada wutar lantarkinsu ne ta karkashin kasa, mu kuma muna hada namu ne ta sama, gashi wasu wuraren ma har da mitar zamani (electricity meter). To Malam meye bambancinsu? Kuma ina yi wa Malam fatan alheri da murnar shiga sabuwar shekarar musulunci. – Aliyu Muktar Sa’id, Kano: 08034332200
Malam Aliyu ga dukkan alamu kana da sha’awa kan fannin fasahar kere-kere ne ko? Haka na hango. Dukkan tambayoyin ka can suke nufa. Na’am, bambanci tsakanin hada wutar lantarki ta kasa ko sama, ya danganta da yanayin wuri, da irin bigiren da kasar take, da kuma halin kudi ta bangaren gwamnati. A wasu kasashe sukan hada ta kasa ne saboda guje wa iska mai tsanani da suke fuskanta lokaci-lokaci, ko saboda guje wa barayi, da dai sauran hujjoji da su kadai suka sani. Masu yi ta kasa kuma a zahiri akwai lura da yanayin aljihunsu, ko kuma yanayin kasarsu. Don haka samun wani tsari ne ya fi inganci ya danganta da abinda kowace kasa ke da ikon yi, ko kuma irin yanayin da take rayuwa a ciki. – Baban Sadiq
Assalamu Alaikum, don Allah muna fatan za a yi mana bayani kan GPRS da kuma WAP. Mun gode. – Hashim Kafinta, Layin NYSC, Kongolam, Jihar Katsina: 08099659379
Malam Hashim mun gode da samun wannan sako naka. Sai dai kamar yadda na sha fada ne, bayanai kan tsarin GPRS da WAP sun yawaita a wannan shafi, don haka idan ba wata munasaba bace ta sake tasowa, sai dai a yi hakuri a je shafin MAKARANTAR KIMIYYA DA FASAHA da ke Intanet, a wannan adireshin: http://fasahar-intanet.blogspot.com. Wannan shine shafin da muke zuba dukkan kasidun da ake karanta su a wannan shafi. Za a samu bayanai gamsassu cikin kasida ta musamman da muka rubuta. Idan kaje kana iya buga kasidar ma kaje ka karanta a gida. A yi hakuri da wannan. Mun gode. – Baban Sadiq
Baban Sadiq, na karanta rubutunka na ranar 02/01/2009, kuma ina sanar da kai cewa akwai sabon littafi a kan kiwon lafiya na Hausa da Malam Abdulkarin Usamatu Katsina ya rubuta, kwanan nan. Yayi kokari sosai wajen bincike, kuma yayi Magana a kan abubuwa da dama. An kaddamar da littafin a Katsina da Kaduna. Ka neme shi. – Ahmad: 08028456627
Malam Ahmad mun gode da wannan sanarwa, Allah saka da alheri. Lallai wannan littafi abin nema ne, don ire-irensu basu yadu ba kamar yadda bayani ya gabata kwanakin baya. Mun gode. – Baban Sadiq
Na karanta shafin kimiya da fasaha da karubuta. don allah ina zan samu wannan littafi da da ambata a shafinka: Hacking for Dummies by Kevin Beaver? Don allah ka shigar dani cikin wadanda ake aikoma shafin kimiya da fasaha ta email (email mailing list). Na gode, sai naji daga gareka. Wassalam. Musa Ali: yaleintegrate@yahoo.com
Malam Musa na aiko maka sako cewa zan turo maka wannan littafi, amma daga baya nayi tunanin cewa littafin na da girma kuma hakan ke nuna cewa mizaninsa na bukatar lokaci kafin in dora shi a Intanet, daga nan in aiko maka. Idan na aiko maka, zai sake daukan lokaci kafin ka iya saukar da shi, musamman ma idan kwamfutar ba taka bace. Sai in kana bukata in sanya maka shi a cikin fai-fan CD, in aiko maka. Hakan ma sai in kana da kwamfuta za ka iya amfani dashi. Amsar bukatarka ta kuma ita ce: a yanzu bamu aikawa da kasidu ga masu karatu sai dai su je shafin da ake taskance kasidun a Intanet, wanda ke http://fasahar-intanet.blogspot.com. Da fatan ka gamsu. – Baban Sadiq
Assalamu Alaikum, da fatan kana lafiya, ya aiki? Dan Allah a fahimtar da ni ya ake yin (rajistar) Imel address a waya? Ina so nayi a waya ta, ya zan yi? - Hassan I. Adamu, Kurna, Kano: 08036268059
Malam Hassan na tabbata yanzu kam ka samu cikakken bayani kan yadda wannan tsari yake cikin makon da ya gabata a wannan shafi, da kuma sakonnin da na aiko maka ta wayarka. Idan baka gamsu ba, ko ka ci karo da wasu matsaloli, to ka bugo min waya sai in kara maka bayani. Mun gode. – Baban Sadiq
Salam, Baban Sadik ya aiki? Da fatan komai na tafiya daidai. Daga dalibarka, Fatima Bashir Ahmad, Jihar Kano.
Malam Fatima mun gode da gaisuwa, Allah saka da alheri ya kuma bar zumunci. A gaida Bashir karami, tare da Umman sa. Mun gode. – Baban Sadiq
Salamun Alaikum, Baban Sadiq tambaya ta itace, a duniya wace kasa ce ja gaba a harkar kimiyyar sadarwar bayanai (Information Technology - IT)? A bani tarihinta. Allah ya taimake ka da mu almajiran wannan shafi mai albarka na Kimiyya da Fasaha, amin. – Aliyu Muktar Sa’idu, Kano: 08034332200
Bayani kan kasar da ke ja gaba kan harkar “Information Technology” na bukatar sharhi kan gudunmuwar kowace kasa kan wannan harka. Duk da yake galibi na ganin kasar Amurka ce, amma bai kamata ta dauki wannan matsayi ita kadai ba; akwai kasashe irin su Jafan, da Koriya ta Kudu, da Singafo, inda a can ake kera dukkan masarrafan da ake lika wa kwamfuta, watau “micro-chips”, ko kuma “Processors”. Haka kuma, a kasar Sin ana kera da dama cikin kwarangwal din kwamfuta (Computer Hardware), da zuciyarta (motherboard) da sauran karikitai. Idan muka leka kasar Rasha, sai mu ga ita ce tafi kowace kasa yawan kwararru kan fasahar gina masarrafar kwamfuta, watau “Computer Programmers”. Haka kasar Indiya na samun kashi wajen goma zuwa ashirin na kudaden shigarta ne daga fannin gina manhajar kwamfuta da ‘yan kasar ke tallatawa a kasar da ma wasu kasashe. Don haka kasar Amurka dai suna ta tara, ko muce ita ce matattarar kamfanonin da ke yin harkar, amma galibin inda ake harkokin su ne wadannan kasashe. Allah sa mu dace, amin. – Baban Sadiq
Da fatan Baban Sadiq yana lafiya. Tambayata a nan ita ce, kamar ni da sana’ata ita ce aikin kafinta, wata manhaja zan shiga domin in duba abubuwan ci gaba a aiki na? Ko ba a samun irin namu? Da fatan Malam zai taimaka mini da amsa ta. Na gode, Allah Ya taimakemu baki daya, amin. – 08065432898
Malam na samu sakonka, kuma lallai akwai “irin naku” a Intanet. Za ka iya shiga, kayi bincike kan aikin kafinta da ire-iren kayayyakin aikin kafinta na zamani, da yadda za ka iya tsara shagonka tare da kyautata aikin, nesa ba kusa ba. Abinda kake bukata kawai shine ka san me kake son bincike a kanshi? Kayan aiki ne, ko tsarin aikin kafinta? Ko kuma ire-iren abubuwan da ake kerawa na zamani a sana’ar? Ya kuma zama ka san sunayensu da harshen Turanci, domin cikin wannan harshe ne bayanai suka fi yawaita. Sai ka je shafin “Google” da ke www.google.com, don binciko wadannan abubuwa. Don haka akwai irin naku! Allah sa mu dace baki daya, amin. – Baban Sadiq
Kammalawa
Wadannan su ne kadan cikin sakonnin da kuka aiko mana. Wanda bai ji an sanya nasa sakon ba yayi hakuri, sai wani lokaci. Bayan haka, muna kara godiya ga masu bugo waya. Saboda yawansu, da kuma ganin ba wani rajista na ajiye don taskance sunayensu ba, sai dai mu ce Allah saka musu da alheri musamman sanadiyyar kara karfafa min guiwa da suke yi a dukkan lokuta. Na gode, Allah saka da alheri har wa yau.
No comments:
Post a Comment