A karon farko, kasar Iran ta harba tauraron dan Adam da ta kera a kasarta cikin falaki, a cewar shugaba Ahmadinajad, ranar Talata, 17 ga watan Fabairu, 2009. Hakan ya zo ne daidai lokacin da kasar ke bikin cika shekara 30 da kafa gwamnatin Islama, kuma ta fara hakan ne cikin kokarinta na ganin ta habaka bincike kan kimiyyar sararin samaniya don samar da ingantacciyar hanyar sadarwa da ilimi da kuma lura da lardunanta da ke fama da girgizar kasa lokaci-lokaci. Kamar yadda Shugaba Ahmadinajad ya sanar, gwamnatin kasar Iran ba don komai ta fara wadannan shirye-shirye ba kama hannun yaro ba sai don wadannan dalilai, da kuma ci gaba da kokarinta wajen samar da ingantacciyar zaman lafiya da lumana a duniya, sabanin yadda sauran kasashen Turai da Amurka ke tunani.
Jim kadan da harba wannan tauraron dan Adam da kasar ta sanya wa suna Omid, ma’ana “kyakkyawar fata” a harshen Farsi, jami’an gwamnati masu lura da shawagin taurarin dan Adam a sararin samaniya na kasar Amurka sun tabbatar da hakan, duk da yake sun ki yin wani karin bayani kan haka. A nasu bangaren su ma, hukumomin kasar Faransa sun sake tabbatar da haka, cewa lallai sun lura da wani sabon tauraron dan Adam da ya isa cikin falaki a wannan safiya. Sai dai kuma a nasu bangaren, sun nuna damuwarsu ga ire-iren “wadannan shirye-shiryen karkashin kasa kan harkar sararin samaniya da ana iya amfani da su wajen harba makamai masu guba”, a cewar Ministan Harkokin Waje na kasar, Mr. Eric Chevallier. Ire-iren wadannan ikirari da gurguwar fahimta dai sun dade suna kai-komo tsakanin kasashen Turai da Amurka tun sa’adda kasar ta fara shirinta na habaka makamashin Yuraniyon don samar da wutar lantarki ga mutanenta.
Shugaba Ahmadinajad dai yace wannan tauraron dan Adam da kasar ta harba ya isa muhallinsa cikin falaki, har ma ya fara shawagi, duk da cewa ba dukkan gabobinsa bane suka fara aiki kai tsaye. Sun kuma gane hakan ne ta hanyar sadarwa da tauraron ya samu yi da jami’an da ke lura da shawaginsa a kasar. Hakan ke nuna cewa lallai ya isa lafiya, tun da har ya fara shawagi. An kuma harba wannan tauraro na Omid cikin falaki ne ta hanyar mizail mai suna Safir-2, wanda yayi tafiyar kilomita kusan dari biyar daga sararin wannan samaniya tamu, kafin ya cilla tauraron don isa muhallinsa. Wannan mizail mai suna Safir-2 dai shine makamin da kasar Iran ta yi gwajinsa bayan an kera shi cikin watan Agustar shekarar da ta gabata, kuma makami ne mai matsakaicin zango wajen tafiya. Rahoton da gidajen rediyo a kasar suka bayar bayan harba wannan sabon tauraro zuwa falaki na nuwa cewa zai rika kewaya wannan duniya ne sau goma shabiyar a dukkan awanni ashirin da hudu na kowace rana. Kuma babban aikinsa shine taskancewa tare da aiko sakonni ko rahotanni zuwa cibiyar sararin samaniya da ke kasar. Yana da tafarkin sadarwa guda biyu, da kuma kunnuwar aika sakonni guda takwas, wadanda za su rika taimaka masa wajen aikawa da sakonnin da ya taskance zuwa wannan duniya tamu. Shugaban ya kara da cewa wannan wani hobbasa ne kasar ta yi wajen habaka harkar fasahar sadarwa a kasar. Bayan wannan yunkuri, in ji Ahmadinajad, abinda ya saura wa kasar Iran yanzu shine ta “ci gaba da ingantawa tare da habaka wadannan mizail da kuma karfinsu wajen daukan wasu taurarin dan Adam da suka fi wannan nauyi nan gaba”. Wannan ke nuna cewa nan gaba ma kasar za ta sake kerawa tare da harba wani tauraron dan Adam din cikin falaki. A karshe, shugaba Ahmadinajad ya ce “muna bukatar kimiyya ne don sadar da zumunci, da karfafa ‘yan uwantaka, tare da tabbatar da adalci.”
Wannan wata shagube ce ake ganin Shugaba Ahmadinajad ke wa sauran kasashen Turai da Amurka, wanda tuni ya sha zarginsu da nuna karfi wajen tirsasa wa sauran kasashen duniya don bin ra’ayinsu, duk da irin zaluncin da suka siffatu da shi, tare da azarbabi kan abinda ya shafi harkokin wasu kasashen dabam. Babbar damuwar wadannan kasashe dai kan wannan sabon shirin habaka fasahar sararin samaniya na kasar Iran shine, duk da cewa sun yarda sauran kasashe na yin haka ne wajen ciyar da kansu gaba wajen sadarwa, suna nuna damuwa ne da irin tsarin shugabancin da ke Iran, wacce a cewarsu, tana iya amfani da wadannan makaman mizail da take kerawa kuma ta ke cilla tauraron dan Adam da su, don kai hari ta sararin samaniya ga kasashen da bata ga-maciji da su. Amma kasar Iran ta karyata ire-iren wadannan jita-jita, inda take nuna cewa ba komai yasa ta fara wadannan shirye-shirye na sararin samaniya ba sai don lura da lardunanta da ke fama da girgizar kasa lokaci-lokaci, da kuma habaka harkar kimiyya da fasahar sadarwa don ci gaban al’ummarta. Tace a bayyane yake cewa kasar Amurka na amfani da ire-iren wadannan taurarin dan Adam da ta cilla cikin falaki ne don lura da kasashe irin su Afganistan da kasar Iraki, amma su a nasu bangaren, zasu yi hakan ne wajen kare kasarsu da mutuncinta a idon duniya.
Wannan dai shine tauraron dan Adam na farko da kasar ta cilla, wanda musamman ta kera shi da kudinta, da kuma kayan aikinta, a kuma kasarta. Sabanin wanda ta cilla cikin shekarar 2005 ta hadin gwiwa da kasar Rasha, wacce ake ganin ita ce ke da alhakin taimaka wa kasar Iran wajen habaka shirin ta na fasahar sararin samaniya da ma wanda take yi kan makamashin nukiliya a halin yanzu. A shekarar 2005 ne gwamnatin Iran ta ware kudi wuri na gugan wuri har dalar Amurka miliyan dari biyar don wannan shiri na habaka fasahar sararin samaniya, kuma a na sa ran kasar za ta sake cilla wasu taurarin guda uku, nan da shekarar 2010. Wannan ke nuna cewa har yanzu kasar Iran bata yi ko gizau ba daga ire-iren tuhume-tuhumen da kasashen Turai da Amurka ke mata a kullum, wanda hakan ke dada tayar musu da hankali. Basu gushe ba wajen shirya tarurruka tsakaninsu da jami’an gwamnatin Iran, wanda a cewar masu lura da siyasar duniya, suna hakan ne don tursasa wa kasar a siyasance, ta amince da tuhume-tuhumen da suke mata, don su tabbatar wa duniya gaskiyarsu. Sai dai ga dukkan alamu, hakan zai yi wahala, wai cire wando ta ka!
No comments:
Post a Comment