Monday, March 30, 2009

Wasu Cikin Labarai

“Sinadaran Batir Za Su Dada Samun Tagomashi” – A Cewar Sakamakon Wani Bincike

clip_image002Ga dukkan alamu, nan da shekaru uku masu zuwa duk wani mai amfani da batir nau’in Lithium-ion Phospate, watau nau’in batiran da muke amfani dasu a wayoyin salularmu da kwamfutocin tafi-da-gidanka (Laptop), da na’urar taskance wutar lantarki (UPS) da sauran makamantansu, zai samu sauki wajen takaitan lokacin caji da kuma karkon rayuwa wajen amfani da shi. Abinda wannan ke nufi shine, nan gaba kana iya caja batirin wayar salularka cikin kasa da minti daya! Ba ma nan aka tsaya ba, batirinka na iya shekaru uku ko sama da haka ba tare da karkonsa ya ragu ba. Wannan shine abinda sakamakon wani bincike da wasu masana kimiyyar lantarki suka gudanar a Cibiyar Fasaha da ke Massachusettes, watau Massachusettes Institute of Technology (MIT) ya tabbatar. Sakamakon binciken, wanda mujallar Nature ta hakaito ranar 12 ga Maris yace masu wannan bincike sun yi tsawon shekaru biyar suna fafatawa kafin gano manyan dalilan da ke jawo saibi wajen cajin batir yayin da aka jona shi da wutar lantarki, duk kuwa da cewa sinadaran lantarkin nau’in Neutrons da ke ciki suna aikinsu yadda ya kamata. Wanda kafin wannan lokaci galibin masanan lantarki na alakanta rashin cajin ire-iren wadannan batira cikin sauri ne da cewa sinadaran da ke ciki ne basu kai-komo cikin gaugawa don tara makamashin lantarkin da batirin ke bukata. Amma a cewar Injiniya Gerbrad Ceder da Byoungwoo Kan, shugabannin tawagar injiniyoyin da suka kaddamar da wannan bincike, wannan ba shine dalilin da ke sa wayar salula ta dauki kusan sa’a guda tana caji ba kafin batirin ya cika, a misali.

Batir nau’in Lithium-ion Phospate dai shine nau’in batiran da wayoyin salula da sauran kayayyakin fasahar zamani masu amfani da batir ke amfani dashi. Har wa yau akwai motocin zamani masu amfani da wannan batiri su ma. Wannan nau’in batir dai ya samu wannan shahara ne sanadiyyar iya taskance makamashin lantarki da yake yi idan an hada shi da wutar lantarki, ya kuma ci gaba da amfani da wanda ya taskance, har sai yayi kasa, sannan a sake caja shi. Wannan ya saba wa batira irin na agogon bango ko na tocila, wadanda da zarar sun yi rauni shikenan, sai dai ka zubar dasu ka sayo wasu. Amma nau’in Lithium-ion Phospate, kana iya shekaru dasu; sai dai kawai ka rika caji idan sun yi kasa, don kara musu kuzari. Matsalar da ke tattare da ire-iren wadannan batira dai a cewan masana fasahar lantarki, shine idan ka jona su da wuta sai sun yi kusan awa guda ko sama da haka, kafin su yi cajin da zai dauke ka kwanaki biyu ko uku kana amfani dasu. Kafin wannan rahoto da aka fitar, galibin masana harkar lantarki na danganta matsalar ne ga yanayin tafiyar sindaran Neutron da ke cikin batirin, wadanda aikinsu ne su rika caja batirin ta hanyar yin tsere a tsakaninsu daga hagu zuwa dama, duk sa’adda ka jona wayar ko batirin kana caji, suna shiga wasu yan ramuka (watau Tunnels) da aka tanada musu. Wannan kai-komo da suke yi shi ke tara makamashin lantarkin da wannan batir ke bukata. Da zarar ya cika, ka jona wa wayar salularka a misali, sai su fara kai-komo daga dama zuwa hagu, duk lokacin da ka kunna wayar. Wannan safa-da-marwa da suke yi, shi zai rika rage yawan makamashin lantarkin da ya taru yayin da suke caja wayar, har sai ya kare. Sannan su canja yanayin tafiya idan ka jona wayar da wutar lantarki don yin caji a karo na gaba. Tsohuwar sakamakon da masana suka fitar a baya ita ce: wadannan sinadarai na Neutron basu tafiya cikin gaugawa don tara makamashin lantarkin da wayar ke bukata ne, shi yasa wayar ke daukar kusan awa guda ko sama da haka kafin cajin ya cika. To amma sakamakon da Injiniya Ceder da abokan bincikensa suka fitar makon jiya ya karyata wannan tsohuwar zato da masana harkar lantarki ke da ita shekaru aru-aru.

Injiniya Ceder yace sun yi nazarin wannan safa-da-marwa da sinadaran Neutron ke yi yayin caji basu samu wata matsala da abinda ya shafi yanayin tafiyarsu ba, sam ko kadan. Suka ce sun lura da wannan tafiya ta hanyar na’urar kwamfuta, inda suka jona batir nau’in Lithium-ion Phospate, suna kallon yadda wadannan sinadaran na Neutron ke tafiya a guje, suna gudanar da aikinsu yadda ya kamata. Wannan, a cewarsu, ba shine matsalar da ke haddasa rashin cajin batir din da wuri ba. Suka ce matsalar da ke haddasa wannan saibi wajen caji ita ce: ba dukkan wadannan sinadaran na Neutron ne ke shigewa cikin wadannan ramuka da aka tanada musu ba a lokaci guda. Galibinsu, musamman wadanda ke sama-sama, suna sulmuya ne a wofi, basu samun damar shiga ramin balle caji yayi sama cikin lokaci. Abinda zai warware wannan matsala kuwa, a cewar wadannan injiniyoyi, shine a sake tsara wasu ramukan (Tunnels) daga sama (watau cikin kogin sinadaran da ke cikin batirin kenan), don baiwa wadannan sinadaran da ke sulmuya a sama damar samun shiga su ma, don kauce wa sulmuyar wofi da suka yi ta fama da shi a baya. Wannan shine kadai abinda zai sa batir ya dauki karancin lokaci wajen caji, kuma bayan haka ma, zai samo rayuwa mai karko da inganci.

Wannan ikirari ba da ka suka yi shi ba. Rahoton da Injiniya Kan da tawagarsu ya fitar a mujallar Nature, yace sun aiwatar da bincike kan batira guda biyu; batir na farko sabo ne, wanda suka kera ta hanyar amfani da sabon tsarin da suka tabbatar a bincikensu, dayan kuma irin wanda kowa ke amfani ne dashi, ma’ana mai dauke da tsohuwar fasaha kenan. Dukkan batiran mizaninsu daya ne, sinadaran da ke cikinsu iri daya ne, kuma dukkansu nau’in Lithium-ion Phospate ne. Da suka jona su da caji, batirin farko mai dauke da sabuwar fasaha ya samu cikakkiyar caji tsakanin dakiku goma zuwa ashirin (10 – 20 Seconds), yayin da dayan batirin mai dauke da tsohuwar fasaha ya dauki tsawon mintuna shida (6 minutes) kafin ya cika. Sun kuma sake tabbatar da cewa lallai wannan batir mai dauke da sabuwar fasaha zai yi karko fiye da wanda ake amfani da shi a yanzu. A karshe suka tabbatar da cewa: “samun damar caji da kuma amfani da batira cikin sauki da gaugawa zai dada samar da damar kera wasu sabbin kayayyakin fasaha ne, wanda hakan ke iya zama sanadiyyar tafiyar da rayuwa cikin sauki da inganci”. Tuni dai hukumar NASA da kuma Hukumar Makamashi na kasar Amurka suka karbi sakamakon wannan bincike da hannu bibbiyu. Kuma har an samu wasu kamfanonin fasaha guda biyu ma da suka karbi lasisin amfani da wannan sabuwar fasaha ta inganta batir nau’in Lithium-ion. Nan da shekaru uku masu zuwa ake sa ran fitar wadannan batira masu dauke da wannan sabuwar fasaha.

“Duniya Na Dada Dusashewa Sanadiyyar Gurbatar Yanayi” – Bincike

Tun wajajen shekclip_image004arun 1970s zuwa yau, yanayin da duniya ke gudanuwa a ciki sai dada tabarbarewa yake sanadiyyar gurbatar yanayi da ke samun karfin gwiwa daga gurbatattun abubuwa a yanayin iskar da ake shaka ko ake fitarwa, ko hayaki ko kuma kura da ke tudadowa sanadiyyar juye-juyen dan Adam wajen neman abin tasarrufi. Wannan tabbaci ya fito ne daga sakamakon wani bincike da wasu kwararru kan hanyar yanayi da muhalli da ke Jami’ar Tekzas (University of Texas) da Jami’ar Mariland (Maryland University) da ke kasar Amurka. Rahoton, wanda Farfesa Robert Dickinson da ke Jami’ar Texas da wasu kwararru biyu daga Jami’ar Meriland suka fitar a makon da ya gabata, ya tabbatar da cewa an samu raguwar kaifin gani tsakanin mutum biyu da ke hangar juna daga ‘yar madaidaiciyar tazara, sanadiyyar karuwar kura da hayaki mai haddasa dusashewar ido. An kuma gano cewa an samu wannan raguwar kaifin gani ne daga alkaluman bayanai da aka samo daga shekarar 1973 zuwa shekarar 2007 daga cibiyoyin tantance yanayi (watau Metreological Center) guda dubu uku da dari biyu da hamsin da ke warwatse a kasashen duniya.

Masu wannan bincike suka ce manya cikin dalilan da ke haddasa hakan kuwa su ne hayakin da ke fitowa daga motoci masu amfani da man fetur da gas, da kuma hayakin kone-kone na daji da kurmi, da kuma gagarumar gobara ko wutar daji ke yawan tashi a dazukan Amurka da Ostiraliya ko wasu wurare. Bayan haka, daga cikin abubuwan da ke dada sanyan yanayin duniya ke dada dusashewa akwai kurar da ke fita daga hayakin wuta da ke ci a yayin dukkan wata kone-kone. Masu wannan bincike suka taruwar wadannan na gurbata yanayin haske ko annurin da duniya ke dauke dashi, ta yadda hakan ke iya shafar lafiyar ganin dan Adam da rage masa kaifi, tare da haddasa masa cututtuka masu alaka da huhu da dai sauransu. Kwararrun suka wannan yanayi ya fi muni a kasashen da ke gabashi da kudancin Asiya, da nahiyar Amurka da Ostiraliya da kuma nahiyar Amurka. Amma nahiyar Turai da Arewacin Amurka basu samu karuwar wannan yanayi mai muni ba, saboda dokokin hana kone-kone da rage dumamar yanayi da suka assasa kuma suke lura da su.

Wannan rahoto har wa yau ya kara tabbatar da cewa kasashe irinsu Sin da Indiya su suka fi kowa dalilan da ke fitar da wannan mummunar yanayi na kura da hayaki da sinadarai masu kashe kaifin ganin dan Adam, bayan gurbata yanayi da suke yi. Manyan cikin wadannan dalilai su ne yawaitan manyan masana’antun sarrafa kayayyakin abinci da abin hawa da sauran abubuwan more rayuwa, wadanda ke fitar hayaki da kura sanadiyyar kone-konen makamashin da suke amfani dashi a kullum. Bayan nan, su suka fi sauran kasashe yawan ababen hawa masu fitar da hayaki mai gurbata yanayi. Illar hakan, muddin ba duniya bata hada kai wajen rage dalilan da ke janyo dumama da gurbatar yanayi ba, to za a ci gaba da kasancewa cikin hadari mai girma, a cewar wadannan kwararru. Domin yawaitan kan haddasa matsananciyar sanyi mai daskararwa, ko tsananin zafi mai cutarwa ga sararin samaniyan wannan duniya. Sannan, yawan bazuwar wannan hayaki na aikawa wani haske mai kaifi zuwa sararin samaniya wanda ke rage yawan makamashin da ke dauke cikin hasken rana da ke shigowa wannan duniya tamu don amfanar da mu, ko kuma ya hadiye makamashin, ta hanyar hana shi tasiri.

No comments:

Post a Comment