Gabatarwa
Kamar kowane irin halitta da Allah Madaukakin Sarki ya halitta, wannan tsari da yanayin da wannan duniya tamu ke gadanuwa na canzawa ne iya canjin zamanin da muke ciki; iya gwargwadon jujjuyawar dan Adam wajen nemo hanyar sarrafa wannan muhalli da Allah Ya zaunar dashi a ciki; iya gwargwadon ilimi da wayewarsa; iya girma ko fadin tasirin da zai yi wajen sarrafa wannan muhalli. Har wa yau, wannan tasiri na dan Adam na caccanzawa ne shi ma zamani-zamani. Don haka idan muka dubi bangaren lafiya, za mu ga cewa mutanen da suka yi rayuwa shekaru dari biyu ko sama da haka da suka gabata, basu san wata cuta mai suna kanjamau ba, ko ciwon siga, ko ciwon asma da dai sauransu. Haka kuma ire-iren cututtukar da aka yi fama da su cikin wadancan zamunna ko karnoni da suka gabata, a halin yanzu bamu dasu. Idan muka dubi bangaren sadarwa har wa yau, zamu sake ganin irin wannan bambanci; shekaru dari biyu da suka gabata babu wani fasaha da dan Adam ya kirkira a matsayin abin hawa daga gari zuwa gari, sai dai dabbobi irin dawaki da rakuma da jakuna da sauran makamantansu. Haka hanyoyin da yayi amfani dasu wajen sadar da sakonni a wancan lokaci, a yanzu duk ba a amfani dasu. Idan muka koma kan yanayin isar sakon kuma, shekaru dari ko tamanin da suka gabata, ba ma can nesa ba, ba kowa zai yarda ba idan aka ce masa nan gaba cikin ‘yan dakiku kana iya aika sako daga bangon duniya ta gabas zuwa bangonta da ke yamma, cikin kasa da minti daya! Amma yanzu ba yarda da yiwuwar hakan bane abin mamaki, a a, rashin yarda shine abin mamaki.
Duk dai wannan, a takaice, na nuna mana ne cewa iya nisan zamani, iya girma da nau’in tasirin da dan Adam ke yi a doron wannan kasa. In kuwa haka ne, to dole akwai amfani da yake samu, wanda a bayyane yake; ga motoci, ga jiragen sama, ga gidaje nau’uka dabam-daban, ga nau’ukan abinci nan kala-kala, ga kuma kayayyakin sadarwa da fasaha masu tasiri fiye da tunanin dan Adam wajen samar masa da amfani ta hanyar wayar da shi, da kara masa ilimi da hore masa hanyoyin sarrafa muhallinsa. Haka kuma a daya bangaren, akwai wasu illoli da suka haddasu sanadiyyar wannan juyin zamani da dan Adam ke samu a rayuwarsa. To wasu illoli ne? Akwai illoli da dama; ga karuwar cututtuka, ga matsalolin tattalin arzikin kasa – irin su yawaitan marasa aikin yi, talauci da ire-irensu - ga rashin zaman lafiya ga al’umma, ga rashin sukuni ga daidaikun mutane, ga kuma uwa uba, dumamar yanayi da muhallin da ake rayuwa ciki. Wannan matsala ta dumamar yanayi da a harshen Turanci ake kira Global Warming, na cikin manyan matsalolin da duniyar yau ke fama da su, musamman a kasashen da suke ikirarin ci gaba a fannonin tafiyar da rayuwa. Shin, me ake nufi da “dumamar yanayi”? Yaushe duniya ta fara samun irin wannan matsala da har Turawa ke ganin babu matsala irin ta a yanzu? Me ke haddasa haka? Wasu illoli wannan matsala ta dumamar yanayi ke haddasawa? A karshe, me duniya (ina nufin kasashen Turai da Amerika) ke yi wajen ragewa ko takaita shi? Cikin wannan silsila da muka faro yau, zamu gabatar da amsoshin wadannan tambayoyi iya gwargwadon hali da sani. Hakan na da muhimmanci don samun karuwar ilimi, musamman ganin cewa wannan kalma ta “Dumamar Yanayi” ko Global Warming a harshen Turanci, na cikin kalmomin da kusan a kullum sai an ambace su a kafafen watsa labaru, har kafafen watsa labaru cikin harshen Hausa da ke sauran kasashen duniya. Na kuma tabbata da dama cikinmu bamu taba damuwa da neman bayani kan ma’ana ko abinda wannan kalma ta kunsa ba. To ga budi Allah Ya kawo cikin sauki. Sai a gyara zama don bibiyar wannan shafi sau da kafa. Sai dai kafin mu shiga fagen bayani kan dumamar yanayi, ga wata ‘yar tunatarwa nan.
Tsarin Turawa Wajen Binciken Kimiyya
Yana da kyau a kullum mai karatu ya fahimci tsarin da turawa ke amfani da shi wajen binciken da suke yi musamman na ilimi kan abinda ya shafi kimiyya da fasaha. Wannan zai sa ka fahimci abubuwa da dama; mai yasa suke danganta kaza ga kaza? Me ya sa suke ganin kaza ne ya haddasa kaza ba Allah ba a misali? A takaice, shin duk abinda suka binciko ne daidai ko kuwa? In haka ne, mai yasa wasu lokuta suke fadan wasu abubuwa sabanin yadda Allah Ya fade su ko yadda yake a zahiri ko a Kur’ani? To ga amsa. A karo na farko dai, ‘yan Adam ne irinmu; suna da tawaya da nakasa irin wacce muke da ita, iya gwrgwadon sani ko jahiltar abinda suke tutiyar saninsa. Sannan, kashi casa’in da takwas cikin dari (98%) na masu binciken kimiyya ba musulmi bane. A wasu lokuta ma ba Kiristoci bane su. Galibinsu basu da addini. A inda aka samu Kiristoci ko Musulmi a wasu fannonin, zaka samu addini baya tasiri a rayuwarsu. To me yasa?
An samu wani zamani a kasashen Turai, daidai lokacin da suke kokarin fitowa daga kaidin jahilci a dukkan bangaren rayuwa (watau Dark Ages), inda aka yi ta samun masana a fannonin rayuwa musamman na kimiyya suna ta kirkirar abubuwan mamaki da dama, irin su Galileo, wanda ya kirkiro na’urar hangen nesa da a Turance ake kira Telescope. Ba shi kadai ba, akwai da dama da suka yi zamani daya. Daidai wannan lokaci kuma shugabannin majami’a ne ke da karfi, watau addinin Kirista kenan. Sai aka shiga kama su, ana karkashe su; don me zasu rika binciko abubuwa irin haka? Wannan, a cewar wadannan shugabanni, ya saba wa karantarwar addininsu, kuma fito-na-fito ne da Ubangiji, inji su. Don haka duk wanda aka samu ya kirkiro wani abu mai ban mamaki, sai kawai a kashe shi. Haka dai abubuwa suka ci gaba da faruwa har zuwa lokacin da ruwa ya kare wa kada, lokacin da mulki ya koma hannun ‘yan boko, wanda kuma sun san abubuwan da suka faru a baya. Suna samun shugabanci, sai suka yi juyin juya hali, inda aka tumbuke shugabannin addini daga mulki zuwa majami’ansu. Kuma sakamakon wannan ta’addanci da Malaman majami’a suka yi a baya, wadannan sabbin shugabanni suka sanya dokar raba shugabanci da addini, ko kuma dukkan wata ka’ida ta rayuwa aka raba ta da addini; in za ka yi addininka, a cewar wannan ka’ida, ka yi a gidanka, ko a wajen ibadanka, amma ba a bainar jama’a ko hukumomin gwamnati ba. Wannan tsari, kamar yadda na tabbata duk mun santa, ita ake kira Secularism, kuma daga cikinta ne aka fitar da wata ka’ida da galibin malamai masu binciken kimiyya a Turai suke amfani da ita.
Wannan ka’ida dai ‘yar zahiriyya ce. Kuma ka’ida ce da a Turance ake kira The Cause and Effects Theory. Wannan ka’ida abinda ta kumsa shine, “duk abinda ka ga ya faru ko yake faruwa, to dole wani abu ne yayi sanadiyyarsa, kuma wannan abin da yayi sanadi, dole ne ya zama ana ganin shi ko jin shi ko iya taba shi”. In kuwa babu daya cikin wannan, to, zamani ko tsawon lokaci ne ke tafiyar da shi, amma ba wai wani Allah ba. Basu yarda akwai wani mai tafiyar da duniya, mai haddasa faruwar abubuwan da ke faruwa a zahiri ba, in dai ba ganin shi ake yi, ko jin shi ko kuma hankaltarsa ba. Ma’ana, su basu yarda wani abu na iya faruwa ba tare da samun wata alama bayyananniya da ke sanadin faruwarsa ba. Inda suka kasa gane dalili kuwa, sai su yi kirdadon wani dalili na wucin-gadi, sannan su ci gaba da bincike. Abinda ya sha karfinsu kuma tun fil azal, sai su jingina shi ga dabi’a kawai, watau Nature, kamar yadda suke fada. Kai kuma Musulmi ka saba da yin imani da abinda baka gani ba, watau gaibu, don shine asalin addini da imani. Dole kaji abin yai maka bambarakwai, wai namiji da sunan Rakiya!
Bayan wannan tunani ko ka’ida da suka kudurce, Allah Ya hore musu kayan bincike. Don haka duk abinda hankalinsu bai kwanta da shi ba, sai su bincika. Wasu lokuta sakamakon bincikensu ya zama daidai da abinda Allah ya fada ko tsara. Wasu lokuta kuma sakamakon ya karyata abinda Allah Ya fada, ko kuma rabi ya dace, rabi ya kauce. Wasu lokuta abinda suka tabbatar a matsayin sakamakon wani bincike, ya canza sanadiyyar tsawon zamani da yawaitan ilimi da canjin tsarin bincike. Wannan ke sa ka samu ka’idojin fahimtar wani nau’in ilimi sama da guda biyar. Hakan na faruwa ne saboda karancin kayan aikin mai bincike, da karancin fahimtar mai bincike, da kuma kasawarsa wajen sanin komai da komai game da abinda yake bincike. Dole kuwa haka ta kasance, domin shi mai bincike ba Allah bane, halittarsa aka yi. To amma tunda su ba damuwa suka yi da hakkin Allah ba, idan ma suna da addinin kenan, sai kawai su toge a kan sakamakon bincikensu. Kuma tunda su ne da kafafen watsa labarai, su ne ke tsara wa duniya tsarin karantar ilimi da bincike, su ne ke tsara ka’idojin bincike da karatu da karantarwa, sai su rubuta abinda yayi musu daidai, su watso wa duniya don kowa ya ci gaba da tafiya a kan turbarsu. Hakan shine daidai a garesu, domin duniya ce manufarsu, kuma ita suka sa a gaba. Duk abinda ya wuce wannan duniyar, to sai dai ka basu labari, amma ba su baka ba.
A musulunci ba yin amfani da wannan ka’ida bane kuskure, a a, illa dai dole ne ka hada da cewa Allah ya kaddara wa kowane abu lokaci da yanayi da kimtsi da kuma tsarin da yake gudanuwa. Ko ka yarda ko kada ka yarda, wannan abin a haka zai ci gaba da kasancewa zuwa lokacin da Allah Ya haddade masa. Wasu kan ce tunda wannan ita ce dabi’a da tsarin turawa wajen bincike, to kenan galibin abinda suke fada a matsayin sakamako duk karya ne, kuma baza mu yi amfani da shi ba. Wannan kuskure ne babba. Abinda ya kamata shine a yi amfani da abinda suka fada wanda zai kaimu ga samun rayuwa mai sauki da warware dukkan matsalolinmu a matsayinmu na al’umma, wanda ya saba masa kuma, ko zai kai mu ga halaka, dole ne a guje masa. Hanya mafi sauki a karshe dai ita ce samun ‘yancin kai a ilimance; mu yi karatun, mu yi binciken da kanmu, a nan kadai zamu iya gane zurfin karyarsu ko rashinsa. Don haka, a cikin wannan dan karamin bincike da zamu gabatar kan dumamar yanayi zamu rika cakuda dalilai ne tsakanin wadanda bincike ya tabbatar dasu a wannan zamani, da kuma wadanda daman can akwai su a zamunnan baya. Abubuwa ne da suke tabbatattu kana iya jinsu, wasu kuma kana iya fahimtarsu idan ka kwatanta lokacin da kake rayuwa ciki yanzu da lokutan baya. Don haka duk abinda ba a fahimta ba a yi tambaya. Allah sa mu dace, amin. (Zamu ci gaba)
No comments:
Post a Comment