Idan masu karatu basu mance ba, mun yi ta gabatar da bayanai da kasidu kan abin da ya shafi mu’amala da fasahar Intanet a wayar salula a lokuta dabam-daban. To amma har yanzu akwai sauran rina a kaba. Domin kusan a duk mako sai na samu sakon text ko wani ya bugo waya ta neman karin bayani kan yadda wannan tsari yake. Wannan yasa na sake neman lokaci don takaita bayanai masu gamsarwa a karo na karshe in Allah Ya yarda. Dangane da samun damar mu’amala da fasahar Intanet a wayar salula, akwai matakai ko ka’idoji kamar haka:
Abu na farko shine ka tabbata wayar salularka tana dauke da fasahar da ke sawwake samuwar Intanet a wayar, watau Wireless Application Protocol ko WAP a takaice. Wannan ita ce ginanniyar ka’idar da kowace waya mai iya wannan aiki ke dauke da ita. Za ka iya gane hakan ne kuwa ta hanyar kundin bayanan da wayar ta zo dashi, watau Phone Manual. Har wa yau, idan ka shiga cikin Menu, zaka iya gane hakan, ta hanyar samuwar mashigar “Web”, watau inda za ka shiga don samun damar mu’amala da shafukan Intanet. Idan ka tabbatar da hakan, wannan ke sanar da kai cewa wayar tana dauke da WAP, kuma za ta iya dauka tare da nuna shafuka masu dauke da bayanan da ke wasu kwamfutoci a ko ina suke a duniya. Har wa yau, akwai wasu wayoyin salula na musamman da ake sayar dasu a yanzu, wadanda ke zuwa da dukkan abinda kake bukata wajen mu’amala da fasahar Intanet da sakonnin Imel. Wadannan kuwa su ne wayoyin salula nau’ukan Black-berry, masu dauke da dukkan wata hanya ta sadarwa; daga masarrafan kwamfuta na rubutu da karatu da lissafi da adana bayanai, zuwa rariyar lilo da tsallake-tsallake (Web Browser), da manhajar Imel na musamman, da manhajar aikawa da gajeren sakonni ta hanyar Intanet, watau GPRS, sai kuma fasahar nuna jihohi da bigiren da mai mu’amala da ita yake, watau Global Positioning System (GPS). Ba a samun ire-iren wadannan nau’ukan wayoyin salula a kasuwa kamar sauran wayoyi, sai dai kaje wajen kamfanonin sadarwar wayar salula irin su MTN ko GLO ko kuma Etisalat, sannan za ka same su. Suna da tsada matuka. Bayan haka, sai abu na gaba.
Ya zama kamfananin da kake amfani da katinsu na sadarwa suna da tsarin sadarwa ta GPRS ko WAP. Abinda wannan ke nufi shine, ya zama suna da tsarin sadarwa ta Intanet a dukkan layukan da suke bai wa mutane. Wannan zai sa ka iya mu’amala da fasahar daga wayar salularka, domin ta can wayar za ta rika samun hanyar sadarwa da gidan yanar sadarwar da ka bukata. Misali, idan ka shigar da adireshin gidan yanar sadarwar Google cikin wayarka don binciken wasu kalmomi ko fannin ilimin, wayarka za ta mika wannan bukata taka ne zuwa uwar garken (Server) kamfanin wayar sadarwarka, ita kuma uwar garken ta jona alaka da kwamfutar da ke dauke da wannan shafi na Google da ke can Amurka, don dauko maka shafukan da kake bukata, kai tsaye. A nan Nijejriya, kamfanonin sadarwar wayar salula irin su MTN, GLO, Etisalat, Zain duk suna da wannan tsari. Don haka idan ka sayi katin, ko wayar da ke dauke da WAP kana bukatar kaje ofishinsu su saita maka wayar, don ka samu damar iya mu’amala da fasahar Intanet. Misali, na san kamfanin sadarwa ta GLO na yin haka ta hanyoyi biyu ne; ko dai ka kira cibiyarsu ta mu’amala da masu hulda dasu, watau Customer Center, ka gaya musu irin nau’in wayar da kake amfani da ita, da sunanka, da kuma inda kake da zama, sai su gaya maka cewa nan da awanni kaza, za a aiko maka da sakonnin text wadanda za ka taskance (ko adana) a cikin wayarka. Kasancewar wadannan sakonnin cikin wayarka ne zai sa ka samu damar sadarwa da na’urorin kamfanin don yin mu’amala da Intanet din. Duk sanda suka share ko ka mance ka share su, to nan take za ka rasa tsarin mu’amala da fasahar Intanet a wayarka. Ko kuma kawai kaje ofishinsu, don gabatar da dukkan abinda aka zayyana a sama. Sai kamfanin MTN, wadanda su ma zasu aiko maka da sakonnin text ne guda biyu, daya na bin daya, idan ka adana su cikin wayarka, nan take za ka fara shiga shafukan Intanet a wayarka. Sai abu na karshe.
Shine, mai karatu ya san cewa, ko da wayar salularsa na dauke da tsarin WAP, kuma kamfanin sadarwarsa ya hada shi da wannan tsari ta hanyar da bayanai suka gabata kansa, dole ne ya zama akwai tsarin sadarwar kamfanin a inda kake son yin mu’amala da wannan fasaha. Ma’ana, mu kaddara kamfanin MTN bai da tsarin sadarwa (watau Network Service) a birnin Katsina. Kai kuma ka saba da mu’amala da wannan fasaha ta hanyar wayar salularka a Kaduna, inda kake da cikakken tsarin sadarwar kamfanin MTN, idan kaje birnin Katsina, yadda ka rasa samun tsarin sadarwar buga waya da karba, haka za ka rasa tsarin mu’amala da fasahar Intanet a wannan bigire. Har wa yau, hatta a bigiren da ake da tsarin sadarwa, idan akwai matsalar sadarwa watau Network Fluctuation, baza ka iya samun sadarwa mai inganci ba. Sai a lura.
Sai wata tambaya kuma mai nasaba da wannan, watau yadda ake bude wasikar sadarwa ta Imel daga wayar salula. Da dama an yi ta rubutowa ko bugo waya don neman karin bayani. Don haka shi ma zan sanar da matakan da kuma hanyar da a tunani na tafi dacewa, don tsuke bakin aljihu. Don haka ga duk mai son ya bude akwatin wasikar hanyar sadarwa ta Intanet watau Imel (e-mail) ta hanyar wayar salularsa, bayan tabbatar da cewa wayar tana dauke da dukkan abinda zai sa a iya mu’amala da fasahar Intanet din, sai ya je inda ya saba shigar da adireshin gidan yanar sadarwar da yake son ziyarta (a wayar Nokia sai kaje sashen Go to Address, ka matsa, za ka ga inda aka rubuta “Enter Web Address”), ka shigar da adireshin gidan yanar da kake son bude Imel din da manhajarsu, misali: http://mail.yahoo.com (in na Yahoo! kake so), ko http://mail.google.com (idan na Google kake so), ko kuma http://www.hotmail.com (idan na Hotmail kake so) don samun shafin da ke dauke da fom din za ka cike. Wajen cike fom din ne zaka zabi suna (Username) da kuma kalmomin iznin shiga (Password) da sauran bayanan da ake bukata, don budewa. Da zarar ka aika da bayanan da ka cike, ka matsa alamar “send” da ke can karshen shafin fom din, za a zarce da kai ne zuwa akwatin wasikar hanyar sadarwar da ka bude, watau Inbox. Haka idan kana son aikawa da sakon Imel, sai ka nemi alamar “compose” ko “compose mail” don samun shafin da zaka rubuta sakonka.
Sai dai kuma, saboda tsawon lokacin da wadannan aiyuka zasu dauke ka a kan layi, kuma da ganin cewa duk mintuna ko awannin da ka kashe na damfare ne da kididdigar kudi da zaka biya, (kamar dai yadda kake biya idan ka buga waya) yasa bin wannan hanya wajen yin rajistar Imel ta wayar salula tsada matuka. Don haka shawarar da nake baiwa galibin masu rubutowa ko bugo waya kan wannan tsari ne, zuwa mashakatar lilo da tsallake-tsallake (watau Cyber Cafe) don yin rajista shi yafi sauki nesa ba kusa ba. Domin duk dadewarka baza ka yi awa guda kan aikin ba, kuma kana iya samun awa guda kan kudin da bai wuce naira dari da hamsin ba. Amma idan a wayar salula zaka yi, mu kaddara ka dauki tsawon mintuna goma sha biyar kafin ka gama, kafin ka farga an caje ka sama da naira dari hudu ko uku da hamsin, musamman idan kamfanin Glo ne ko na MTN. Don haka ni a shawarata zuwa Mashakatar lilo da tsallake-tsallake shi yafi sauki. Amma idan kuma babu wata mashaka mafi kusanci da inda kake, sai kayi lodi, sannan ka haye kan giza-gizan sadarwa don yin rajista.
No comments:
Post a Comment