Zamunnan Baya
Dan Adam bai gushe ba a matsayinsa na halitta mai rai, mai kai-komo, mai irada da kuma kokarin ganin cinma manufofinsa a doron wannan kasa, wajen taskancewa ko kuma “adana” bayanan da ke kumshe da manufofinsa da ya cinma a baya, da wadanda yake kokarin ganin ya aiwatar da su, da kuma wadanda a nan gaba yake son aiwatarwa. A zamanin farko, dan Adam ya siffatu ne da dabi’ar taskance bayanai ta hanyar kwakwalwarsa kadai. Duk abinda zai iya tunawa, to shi ne bayanin da yake da iko a kansa. Wadanda ya mance su kuma, sun tafi kenan. Idan ba tuna su yayi ba sa’adda yake da bukatarsu, to sai dai wani lokaci.
Da tafiya tayi nisa, sai zamani ya sauya. Shagulgula suka dabaibaye dan Adam har ta kai ga ya fara gajiya wajen dogaro da kwakwalwarsa kadai don adanawa ko taskance bayanan da yake bukata wajen tafiyar da rayuwarsa ta yau da kullum. Wannan tasa, cikin hikimar da Allah ya bashi na tunani, ya kirkiri hanyar alamanta bayanansa kan abubuwan da ke muhallinsa. Misali, idan yana bukatar tunatar da kansa kan wani abu, sai yayi alama mai nasaba da wannan abin da yake son tunawa a jikin dutse ko tafin hannunsa ko jikinsa ko kuma fatan dabbobi da bawon itatuwan da ke gewaye dashi. Har wa yau, wadannan alamu da yake yi basu takaitu ga abubuwan da ke muhallinsa kadai ba, hatta ga jikinsa yana yi, don tunawa da dangi ko dan uwansa. Mun sha samun labarai kan abinda ya shafi asalin zane da mutane ke yi. Da dama aka ce ya samo asali ne daga alama da dangi ke yi wa ‘yan uwansu, don gane su, ko kuma wadanda fataken bayi ke yi bayin da suka saya, don hana su cakuduwa da na fatake ‘yan uwansu.
Wannan zamani shi ma bai gushe ba sai da dan Adam ya samu fikira wajen iya rubutu da kuma karanta abinda ya rubuta. Nan take sai ya sauya hanyar taskance bayanansa; daga zane ko alama da yake yi a saman karikitan da yaci karo dasu a muhallinsa ko kuma jikinsa, zuwa amfani da fasahar rubutu a kan duwatsu ko fatu ko makamantansu. Wannan tsari na rubutu da ya kirkira shi ma ya taimaka masa sosai wajen kawo masa ci gaba. Domin daga nan ne ya fara taskance fasahar yin abubuwa, da tarihi, da tsarin tafiyar da rayuwa a irin muhallin da yake, da dai sauran hanyoyin ci gaba.
Bai tabbata a kan haka ba, sai da Allah Ya sake hankaltar dashi wata hanyar daban. Hakan kuwa ya faru ne bayan wasu karnoni, sa’adda ya kirkiri fasahar rubutu da karatu a kan takarda tare da tara su waje daya a matsayin littafi, don ci gaba da tafiyar da rayuwa yadda ta kamata. Wannan tsari ya dada saukake hanyoyin da dan Adam yake bi wajen taskance ilimi da tafiyar da rayuwarsa, sama da hanyoyin baya. Domin yana cikin hanyar da tafi kowacce dadewa yana amfani da ita wajen taskance ilimi har zuwa wannan zamani da muke ciki. Domin ta hanyar littafai ne ya ci gaba da taskance ilimin kimiyya da fasaha da tarihi da hanyoyin mulki. Har wa yau bai tsaya a nan ba, a littafai ne yake taskance wakokinsa, da hotunansa, ta taswirorinsa, da duk wata alama da ke iya taimaka masa wajen tafiyar da rayuwarsa a ilmance.
Zamanin Yau
Tsakanin karni na shatakwas zuwa shatara, sai ya fara samo wasu hanyoyi da ya fara bi wajen taskance wasu nau’ukan bayanai na musamman, maimakon littafi da yake amfani da shi a baya. Misali, ya kirkiri wasu nau’ukan fasahar taskance wakoki ko sauti ko murya, ta yadda zai rika sauraronsu a duk lokacin da ya bukace su, ba sai ya rera su da kanshi ba, sabanin yadda abin yake in da a rubuce suke a littafi. Haka ya kirkiri fasahar da yake amfani da ita wajen samar da hotuna da taswira, sabanin lokutan baya da yake amfani da yatsun hannunsa wajen zana su ko yin tambarinsu a kan littafai ko shafin takarda. Sannan da tafiya tayi nisa, sai ya kirkiri fasahar taskance hotuna masu motsi, watau na bidiyo kenan, tare da hanyar yin hakan a aikace: watau fasahar aikin talabijin kenan. A yau kam, cikin taimakon Allah, dan Adam ya wayi gari da wasu fasahohi masu dimbin tasiri wajen taskance masa dukkan abinda ya kirkira na bayanai: daga rubutu, da hotuna masu motsi da daskararru, zuwa zane da taswira (maps), duk yana iya taskance su cikin ma’adana guda daya, mai daukan bayanai masu dimbin yawa, mai kuma amfani da wutar lantarki. Wannan ma’adana mai wannan tsari ita ake kira Digital Storage System.
Wadannan nau’ukan kayayyakin fasahar ma’adana da dan Adam ya kirkira dai sun hada da faya-fayan garmaho (Gramophone Records), da kaset na rediyo da bidiyo, da faya-fayan CD da na DVD, zuwa ma’adanar Floppy Disks, da Zip Disk, da Flash Drive, da Memory Card, da kuma uwa uba Hard Disk Drive, watau babbar ma’adanar kwamfuta kenan, wacce ke taskance dukkan manhajojin da ke dauke cikin kwamfuta, a kunne take ko a kashe. Wadannan hanyoyin taskance bayanai da a yau galibinsu ke kai-komo a hannayenmu, na da hannu wajen haddasa ci gaban da aka samu ta hanyar ilimi, da saukin samunsa, da haddasa kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da sauran nau’ukan ilimi. Kuma dukkan wannan kokari, kamar yadda zamu karanta nan gaba, dan Adam yayi su ne sanadiyyar wayewa da yake samu ta hanyar sauyin zamani, da kuma darasi da yake dauka wajen amfani da abubuwan da ya kirkira a baya: shin suna biyan bukata ko basu biya? Sannan ya sauya musu sifa ko yanayi, har aka kawo ga zamanin yau. A karshe, hakan ya dada haddasa masa ci gaba mai girma da tasiri a rayuwarsa, ta yadda ya wayi gari babu abinda ke masa hidima sai wadannan kayayyakin fasaha.
Idan mai karatu na biye damu a wannan shafi mai albarka, zai samu bayanai filla-filla kan kowanne daga cikin nau’ukan ma’adanan da sunayensu ya gabata a sama. Da wannan, zai ga irin ci gaban da aka samu, da irin yadda fasaha ke tasiri a rayuwar dan Adam wajen haddasa kikire-kirkire a fannoni da dama. Wannan har wa yau ke nuna cewa dan Adam halitta ne mai dauke da dimbin tunanin ci gaba da wayewa da kuma kirkire-kirkire. Amma kuma babu abinda ke jawo masa wadannan siffofi sai neman ilimi da kuma gwada abinda ya koya, watau aiki da ilimin kenan. Duk al’ummar da ta bi wannan hanya na daukan ilimi da kwatanta shi, za ta ci gaba. Wacce kuma ta karanta kadai bata kwatanta ba, ko kuma ta ma ki karatun gaba daya, sai dai kallo. Allah kiyashe mu! A ci gaba da kasancewa tare dace mu.
No comments:
Post a Comment