Monday, September 7, 2009

Za a Fara Karban Sakon “Text” a Matsayin Sheda a Kotunan Nijeriya

Wani sabon kuduri da aka gabatar a majalisar Dattijai na neman da a yi wa dokar Kafa Sheda a Kotu ta shekarar 1945, watau 1945 Evidence Act, gyarar fuska wajen fadada hurumin nau’ukan bayanan da alkali zai iya karba a matsayin sheda daga wajen mai kara ko wanda ake kararsa, kafin ya yanke hukunci. Wannan kudiri da ya samu bitar farko a majalisar ranar Talatar makon da ya gabata, na neman Majalisar ne ta amince da gyarar fuskar da yake neman a yi wa dokar, wacce a cewarsa ta tsufa, musamman idan aka kwatanta hurumin da ta baiwa masu kawo kara ko gabatar da shedu na bayanai (documented evidence) ga alkali a kotu, da kuma irin ci gaban da ake kan samu musamman a fannin fasahar sadarwa.

Wannan doka mai suna 1945 Evidence Act dai ta kayyade cewa alkali bazai amince da kowane irin rubutatten bayani ba sai na asali, watau Original Document, mai dauke da tambarin yatsu (thump print) ko kuma sa hannu (signature), wanda hakan ke tabbatar da ingancinsu. Idan kuwa aka dauki wannan kaidi da dokar tayi, sai a ga cewa bayanan kafa hujja da suka samo asali daga Intanet ko kwamfuta ko wayar salula ko kuma wadanda ke taskance cikin ma’adanan kwamfuta irinsu Flash Drive, da Hard Disk Drive da sauransu, duk baza a karbe su a matsayin abin kafa hujja ba a kotu.

Wanda ya dauki nauyin wannan kudiri, watau Sanata Sola Akinyele, ya bayyana muhimmancin wannan gyarar fuska cikin wasikar neman magoya baya da ya raba wa abokanan aikinsa. A ciki yace yin hakan ya zama dole, ta la’akari da irin zamanin da muke ciki, mai dauke da hanyoyin taskancewa da samar da bayanai ta fuskoki daban-daban. Ya nuna cewa lallai akwai nakasu sosai wajen nau’ukan bayanan da alkali zai iya amincewa dasu a matsayin sheda. Yin amfani da wannan doka a halin da take ciki, a kuma cikin wannan zamani da muke ciki na iya haddasa salwantar hakkoki da dama. Domin, a cewarsa, akwai bayanai masu muhimmanci da inganci da ke taruwa sanadiyyar rayuwar yau da kullum da muke yi ta hanyar kasuwanci, musamman, wadanda kuma dokar Nijeriya ta amince a yi su. Idan har bayanan da suka shafi wadannan harkoki na kasuwanci basu da amfani a wajen alkali don kawai sun sha banban da nau’ukan bayanan da ake nema, to lallai hakkoki da dama zasu salwanta.

Don kara tabbatar da dalilansa, Sanata Sola ya kawo misali mai jawo hankalil ga duk wanda ya san tsarin sadarwa musamman na zamani a yau. Yace mu kaddara Malam “A” ya aika wa Malam “B” sakon Imel kan cewa ya bashi kwangilar kashe Malam “C” a kan kudi dala dubu dari biyu da hamsin ($250,000), ya kuma sanar dashi cewa ya aika masa da wadannan kudade ta hanyar aikawa da kudi na zamani da ya shafi kayan sadarwa, watau Electronic Money Transfer, don gabatar da wannan aiki ba matsala. Ana cikin haka, sai wani masanin harkar kwamfuta ya tsinci wannan sako na Imel da Malam “A” ya aika wa Malam “B”, kuma ganin an sanya rana da lokacin da za a zo a kashe Malam “C”, kuma ya san shi, sai kawai ya sanar dashi a boye. Nan da nan, sai Malam “C” ya sanar da ‘yan Sanda halin da yake ciki. Aka yi kwanton bauna, daidai lokacin da aka ajiye za a aiwatar da wannan kisa, sai ‘yan sanda suka cafke Malam “B” a gidan Malam “C”, da wuka da kuma igiya, watau kayayyakin aikinsa na kisa kenan. A wannan hali, ko an je kotu sai dai ran Malam “C” ya baci, domin dukkan hujjojin bayanai da zai gabatar basu cikin hurumin 1945 Evidence Act.

Da farko dai sakon Imel din da Malam “A” ya aika wa Malam “B” a cikin kwamfuta take, kuma ma ko da an buga sakon (printing) a jikin takarda, babu tambari ko sanya hannun wanda ya rubuta, balle ya zama hujja ga Malam “C”. Haka bayanan da ke nuna cewa Malam “A” ya aika wa Malam “B” kudi, wadanda banki zai gabatar ko wadanda Malam “C” zai kawo daga banki, duk tsarinsu daya ne da na Imel. Da wannan, Malam “A” zai tsira, don babu tabbatacce ko “karbabben” hujja da ke nuna cewa akwai hannunsa wajen wannan ta’asa. Idan ma ya ga dama, yana iya cewa sharri aka masa, ya kuma shigar da kara kan bata suna, in yayi nasara ya kwashi kudi. Shi kuma Malam “C” bai da hujja, in ma yayi sa’a Malam “A” bai shigar da karar bata suna a kansa ba kenan. Wanda zai kwana ciki kawai shine Malam “B”, wanda yaje aiwatar da aikin. Shi ma, idan yana da baki zai iya fitar da kansa, don bai fara komai ko ba. Don haka sai dai a bar Malam “C” da fargaba. Har wa yau, da ace Malam “B” ya yi gaugawa wajen aiwatar da wannan kisa, ko an kama shi sanadiyyar hujjojin da aka samo daga wadannan hanyoyi ko kayayyakin sadarwa, ba abinda za a yi wa Malam “A”. Haka zai tafi; salin-alin. Wannan ke nuna cewa wannan doka tamu ta tsufa, kuma dole a yi mata gyarar fuska. Domin a sauran kasashe ba haka lamarin yake ba.

Shahararrun sassan da ke neman gyarar fuska a wannan doka dai sun hada da sashi na biyu (Section 2), wanda ke bayanin nau’ukan bayanan da alkali zai iya karba a matsayin bayanan kafa hujja a kotu, inda kuma wannan kuduri ke neman a sanya cewa: “su kumshi bayanan da aka samo daga kwamfuta da sauran kayayyakin sadarwa”. Sai sashe na uku (Section 3), wanda shine ya killace ko kayyade ma’anar bayanai na hujja da alkali zai iya karba daga mai kara ko wanda ake tuhuma. Dangane da wannan sashe, wannan kuduri na neman da a fadada ma’anar “bayanai na hujja” daga “rubutattun bayanai kadai”, zuwa “rubutattun bayanai da ma wadanda ke makare a cikin kayayyaki ko hanyoyin sadarwa na zamani (irinsu kwamfuta, da Intanet, da wayar salula da ma’adanan bayanai)”. Wadannan, da ma wadansu daban, sune bangarorin da wannan kuduri ke son a musu gyaran fuska muddin ya samu karbuwa a majalisar. Har yanzu dai Majalisar Dattajai bata sanya ranar sauraron wannan kuduri a kashi na biyu ko ba. Idan har aka tattauna kuma a karshe aka samu amincewar kashi biyu cikin uku na mambobin majalisar, wannan kuduri na iya zama doka.

Duk da cewa yi wa wannan doka gyarar fuska na da muhimmanci, musamman idan muka yi la’akari da yadda galibin tsarin kasuwanci da sadarwa tsakanin jama’a ke bunkasa a yau, sai dai a daya bangaren kuma dole ne gwamnati ko kuma masu gabatar da wannan kuduri su yi hattara. Idan an yi wa masu gabatar da bayanan hujja da aka samo daga kwamfuta ko wadanda aka samo daga bankuna na hujjojin aikawa da karban kudade ta hanyar sadarwar zamani gata wajen wannan gyarar fuska, a daya bangaren kuma dole ne a kayyade irin nau’in sakon Imel din da za a iya kafa hujja dashi. Domin hanyoyin kirkirar Imel na bogi da aikawa da sakonnin bogi ta hanyar amfani da manhajojin Imel na kyauta (irinsu Yahoo!, da Gmail da Hotmail) suna nan da yawa. Wannan tasa ma da dama cikin ma’aikatu ke bude wa ma’aikatansu adireshin Imel na musamman, wanda ke dauke da manhajojin kamfanin ko ma’aikatar ke amfani dasu, don aikawa da sakonni kan abinda ya shafi aiki. Da wannan, duk abinda ya faru ana iya sanin mai adireshin Imel din cikin sauki. Kai ko da tare sakon da wani ma’aikaci ya aika aka yi a hanya, akwai manhajoji da ke iya nuna cewa an samu matsala nan take. Kuma ma’aikatar na iya daukan mataki nan take, ba tare da bata lokaci ba.

Amma ta amfani da adireshin Imel na kyauta wajen kafa hujja kan wani laifi ko ikirari da wani yayi na bukatar tsananin binciken kwararru kafin tantance gaskiya ko rashin gaskiyar wanda abin ya shafa. Haka abinda ya shafi sakonnin “text”, dole a samu cikakken bayanai kan irin nau’ukan sakonnin text din da suka dace a yarda dasu a matsayin bayanan hujja a kotu. Dole ne hukuma ta shigar da irin rawar da kamfanonin sadarwar wayar salula zasu taka wajen tabbatar da gaskiyar sakonnin da ake takaddama kansu ko son gabatar da su a matsayin hujja. Wannan shine abinda ake yi a wasu kasashe don tabbatar da hakkin jama’a. Amma idan aka bar abin galala, to za a samu rudani mai yawa, inda wasu zasu yi ta gabatar da sakonnin karya, don sun san ba tuntubar kamfanin waya za a yi ba. Wannan zai dada tsawaita lokacin yanke hukunci saboda daukaka kara da wasu zasu rika yi, ta inda a karshe ma mai hakki ya rasa hakkinsa.

A karshe dai, wannan gyarar fuska zai kawo dauki ga hakkokin jama’a, musamman kan abinda ya shafi tabbatar da hakkin wani ko korewa, kamar dai yadda Sanatan ya kawo misali don tabbatarwa. A daya bangaren kuma, muddin wannan kuduri ya samu wucewa zuwa matsayin doka, to dole ne hukuma ta tabbata an kayyade nau’ukan bayanai tare da fayyace rawar da kamfanonin sadarwa zasu taka wajen tabbatar da ingancin sakonni ko bayanan da ake tutiyar sun fito ne daga kamfanoninsu.

No comments:

Post a Comment