Tuna Baya
Shekaru
25 da suka wuce bamu gushe ba wajen neman masarrafa ta musamman, mai ɗauke da
dukkan haruffan hausa masu lanƙwasa, a jere a kan allon rubutun kwamfuta, wato Keyboard, amma abin ya gagara har
yanzu. Akwai matakai da dama da ƙwararru
kan harshe da al’adun Hausawa suka yi a baya, wajen samar da makwafin abin da
ake buƙata, saboda gamsar da masu karatun harshen Hausa a littattafai ne ko a
kwamfuta. Galibin ƙoƙarin da aka yi a
baya sun ta’allaƙa ne da amfani da masarrafar tsarawa da gina haruffa mai suna Fontographer, don samar da haruffa masu
lanƙwasa, tare da kashe gurabun wasu haruffan turanci da ke jiki allon rubutu
(irin su: Q, da X, da alamu irinsu {, da }, da [, da kuma ]) don samar da su
cikin sauƙi. Wannan shi ne ƙoƙarin da Farfesa Abdallah Uba Adamu da ke
Tsangayar Malanta ta Jami’ar Bayero ya yi a baya.
Ya samar da rabiat true type font, da kuma abdalla
true type font, daga baya.
Ta
dukkan waɗannan hanyoyi guda biyu kana iya shigar da haruffa masu lanƙwasa a
cikin rubutunka, sannan kana iya amfani da su wajen bayyana dukkan haruffan
hausa masu lanƙwasa a littafinka. To
amma har yanzu da sauran rina a kaba.
Domin ba za ka iya amfani da su
wajen rubuta sakonnin Imel ba; kwamfutoci basu san da su ba. Idan ka tsara shafin
yanar gizo ta amfani da su, dole sai maginin yanar sadarwar yayi amfani da wata
ƙwarewa ta musamman wajen adana jakar haruffan (abdalla ko rabiat) kafin
haruffa masu lanƙwasa su bayyana a rubutun.
Wannan aiki ne ba ƙarami ba.
To
amma tunda a kullum ci gaba ake yi, a yanzu an gano cewa, cikin jerin
jakunkunan haruffan kwamfuta mai suna Arial
Unicode, akwai haruffan Hausa masu lanƙwasa, da dukkan wasu haruffa na
harsunan Afirka masu lanƙwasa. Ni kaina
sai cikin ‘yan makonnin da suka gabata na gano haka, sadda wani aiki ya haɗa da
Farfesa Abdallah Uba Adamu. Ya tuntuɓi
Dr. Sakkal, wanda shi ne maginin wannan tsarin haruffa na Arial Unicode, inda ya tabbatar masa cewa akwai waɗannan haruffa na
Hausa da ya gina a ciki. Sai dai matakan
samun wadannan haruffa da kuma hanyoyin shigar da su cikin rubutu a yayin da
kake rubutu, suna da ɗan tsawo. Shi yasa wataƙila ba ma kowa ya san da su ba,
wai kunu a makwabta. To amma dabara da
hikima sun gano su. Ga matakan samun waɗannan haruffa nan a fayyace:
Tsarin Shigar da Haruffa Masu Lanƙwasa
Ka
buɗo Microsoft Word, sai ka je
“Insert”, ka duba can ƙuryar dama daga sama, za ka “Symbol”, sai ka matsa alamar
da ke dama, hoton da ke ƙasa zai buɗo:
Sai
ka gangara kasa ka matsa “More Symbols”,
hoton da ke ƙasa zai buɗo:
Daga nan sai ka fara neman haruffa
masu lanƙwasa ɗaya bayan ɗaya. Kowanne
daga cikin haruffan nan shida yana da lambar da ake nemansa da shi. Idan kana neman D mai lanƙwasa, sai ka gangara ƙasa a shafin da ke sama,
inda aka rubuta “from”, ka zaɓi “Unicode (hex)”. Sai ka dawo baya wajen “Character Code”, ka
shigar da 018A, nan take za ka ga harafin, sai ka matsa “Insert”. Sai ka sake neman d mai lanƙwasa ta lambar: 0257, shi
ma zai bayyana, sai ka matsa “Insert”. Sai ka nemo harafin K mai lankwasa ta lambar:
0198. Ka nemo k mai lankwasa ta lambar: 0199. Ka nemo B mai lanƙwasa ta lambar: 0181. Ka
nemo b mai lanƙwasa ta lambar: 0253. Da zarar ka gama, sai ka rufe.
Idan ka koma “Insert”, ka sake budo
“Symbol” kamar yadda ya gabata, za ka ga dukkan haruffan da ka shigar dazu a
sama, kamar yadda yake a hoton farko da ke sama. Abin da ya rage yanzu shi ne yadda za ka riƙa samun waɗannan haruffa cikin sauƙi ba tare da sai ka sake
komawa wannan wuri ba. Idan kana amfani
da “Office 2007” ne, sai ka matsa alamar “Office Button” da ke ɓangaren hagu daga can sama, in kuma “Office 2010” ne,
ka matsa “File”, sai ka gangara “Word Options”. Idan ka matsa, shafi zai buɗo, sai ka duba bangaren hagu, ka matsa “Customize
Ribbon”. Da zarar ya buɗo, sai ka duba jadawalin farko daga hagu, inda aka
rubuta “Popular Commands”, sai ka matsa, ka zaɓi “All Commands”. Daga nan sai ka gangara, ka zaɓi “Symbol”, a ɓangaren dama kuma za ka ga “Add”, sai ka matsa. Za a shigar maka da tambarin samun haruffan
cikin sauƙi, a saman shafin da kake aiki, kamar yadda yake a hoton da
ke ƙasa:
Idan kana cikin rubutu, duk sadda ka
tashi buƙatar wani harafi mai lanƙwasa, ka matsa alamar
kawai, irin hoton farko dake sama zai bayyana, tare da dukkan harrufa masu lanƙwasa da ka shigar a karon
farko, sai ka zaɓi wanda kake so. Idan ka gama rubutu, sai ka matsa “ctrl + a”,
sai ka zaɓi nau’in haruffan (font
type) da kake son ƙasidar ta kasance. Ko “Calibri”,
ko “Times New Romans” ko duk wani nau’in
harafi da ke gungun haruffan “Arial
Unicode.”
Wani Abin
Lura
Wannan tsari yana da muhimmanci, kuma
da sauƙin sha’ani. Sannan
yana da gamewa. Domin zai yi wahala a yanzu a samu wata kwamfutar da ba ta ɗauke da wannan jerin haruffa na Arial Unicode. Sannan kuma
kana iya rubuta saƙon Imel mai ɗauke da haruffa masu lanƙwasa, kuma su bayyana a
kwamfutar wanda ka aika masa. Har wa
yau, kana iya amfani da kowane irin nau’in harafi, kamar su Calibri, ko Times New Roman, da dai sauransu, don ƙawata ƙasidarka.
Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba,
idan wanda ka aika masa Imel ya budo a wayar salularsa, muddin ƙaramar waya ce mai ɗauke da takaitattun jerin haruffa, ma’ana wacce ba ta ɗauke da Arial
Unicode, ba za ta nuna haruffan ba.
Sai dai wasu alamu marasa kan gado.
Haka idan shafin yanar gizo ne da aka rubuta ta amfani da wannan tsari,
duk wanda ya shiga ta wayar salularsa wacce ba ta da jerin haruffan Arial Unicode, ba zai iya ganin waɗannan haruffa masu lanƙwasa ba. To amma duk da haka, Hausawa sun ce, “Da babu
gwamma ba daɗi.”
Sai a gwada wannan tsari a gani, yana
da ƙayatarwa
natuka. Allah sa mu dace, amin.
I blog frequently and I truly thank you for your content.
ReplyDeleteThis article has really peaked my interest.
I will bookmark your blog and keep checking for new information about once a week.
I subscribed to your RSS feed as well.
Feel free to visit my web site tamil books
Assalamu alykum warahmatullah. Jazakallahu bi khairin ya Baban Sadik lallai waannan tsari ya yi. Da fatar Allah Ya kara maka ilimi mai albarka, Ya kuma shigar da kai al-Jannatul Firdaus tare da mu.
ReplyDelete