Assalaamu Alaikum Baban Sadik, ina fatan kana tare da iyalanka gaba
daya lafiya. Hakika ka yi tsokaci a kan
abu mai mahimmanci wanda ya dade yana damu na kuma yake halaka samarinmu, a
makalarka mai taken: "Rayuwar Matasanmu a Dandalin Facebook." Mun ji dadin wannan bayani naka, Allah ya
biya ka. Don bayan wannan bayani naka da
mako daya sai ga shi an samu mace da namiji matattu a mota a Kano, kuma duk ta
sanadiyyar soyayyar Facebook ne.
Sai dai ka yi bayanin cuta amma baka fadi magani ba. Don Allah kayi magana a kan abubuwan da suka
kamata matasa su mayar da hankalinsu a kai a Dandalin Facebook. Na gode.
Yusuf Mu'azu, ABU Zaria: 08031802438
Wa alaikumus salam, Malam Yusuf na gode da wannan tsokaci da ka yi
kan wancan makala, duk da cewa ban gama da wannan maudu'i ba. Kashin farko ne na fitar, kuma zan ci gaba in
Allah Ya yarda. Dangane da hanyoyin da
suka kamata a bi wajen magance ire-iren wadannan abubuwa, ai na fadi wasu daga
ciki a karshen makalar, watakila hankalinka bai kai kan bayanin bane shi
yasa. Zan ci gaba da wannan silsila har
sai illa ma sha'Allahu. Zan kuma gabatar
da wata silsilar kan hanyoyin da suka kamata mu rika shagaltar da kanmu don
samun ci gaba a Intanet ma gaba daya, ba wai Dandalin Facebook ba kadai. Sai dai dole ne ka san cewa shi gyara wani
abu ne da ke daukan lokacin kafin tasirinsa ya fara bayyana. Allah sa mu dace baki daya, amin.
Assalaamu Alaikum Baban Sadik, ina fatan kana lafiya. Na ji dadin rubutun da kayi na "Tsarin
Gadon Dabi'u da Siffofin Halitta."
Allah Ya kara maka basira, amin.
daga Alhaji Ibrahim: 08030840905
Wa alaikumus salam, Alhaji Ibrahim barka da warhaka. Na gode da wannan sako naka. Allah saka da
alheri amin. Kamar yadda ka karanta,
wannan kasida yanzu muka faro ta. Sai a ci gaba da kasancewa tare da mu.
GODIYA TA MUSAMMAN
Shafin Kimiyya da Kere-kere na mika godiyarsa ta musamman ga daya
daga cikin masu karatu da ta nemi iznin buga shahararriyar kasidar nan mai
taken: "Tsakanin Kwakwalwa da Zuciya: Wa Ke Samar da Tunani?" gaba
dayanta, zuwa dan karamin littafi, don raba wa jama'ar da suka halarci bikin
kannanta da aka yi a garin Birnin Gwari ranar Asabar, 09/06/2012. Kafin buga littafin, sai da ta nemi izni na
bata, sannan nayi bitar kasidar baki daya, kafin aka ba wanda zai dabba'a. Ta kuma aiko wa shafin Kimiyya da Kere-kere wani
adadi mai yawa na littafin da aka buga.
Allah saka mata da alheri, amin.
No comments:
Post a Comment