Monday, February 25, 2013

Amsoshin Wasikun Masu Karatu (2)

Wannan shi ne kashi na biyu na "Amsoshin Wasikun Masu Karatu."  Kamar sauran lokutan baya, ban hada da wadanda na amsa su ba. Akwai wadanda aka aiko ta Imel, su ma na amsa su, don haka ban sako su cikin wadanda na amsa a wannan mako ba. Kamar yadda sanarwa ta gabata a makon jiya, a halin yanzu na loda dukkan kasidun da suka gabata a shekarar 2012, duk mai so sai ya shiga Mudawwanan da ke shafukanmu, kamar yadda aka saba. Na gode.

…………………………………………………………..

Baban Sadik, Allah ya saka maka da alheri da fadakarwar da kake yi wa al'umma.   Da fatar Allah ya barmu tare, amin.  Daga Nasiru Sani Gusau, Jihar Zamfara.

Ina godiya matuka Malam Nasiru, Allah saka maka kaima da alheri, ya kuma ji kan mahaifa. Na gode da addu'ar da ka min, Allah bar zumunci, amin.

Fatan alhairi a gare mu, kuma da fatan kana lafiya kamar yadda nake lafiya.  Baban Sadiq, shin, zan iya tura sakon Imel ta hanyar tsarin 'MMS' ga wanda nake son tura wa, alhali ban bude Imel ba? Na gode. Prince Babani Yola

Da farko dai tukun, duk wayar da ke da tsarin aika sako ta hanyar MMS, to, lallai kana iya aikawa da sakon Imel ta hanyar da ta ake yin hakan, ba sai ta hanyar MMS ba.  Bayan haka, ana iya aikawa da sakonnin hotuna ne ko bayanan tes ta hanyar MMS, amma ba sakon Imel ba.  Ma'ana, tsarin aika sako ta Imel wani tsari ne mai dauke da nasa ka'idojin aika sako na musamman.  Shi yasa idan ka bukaci aika sakon Imel ta wayarka, muddin tana dauke da wadannan ka'idoji, nan take za ta kaika inda masarrafar Imel take in akwai.  Don haka, ba a aika sakon Imel ta hanyar MMS, sai ta tsarin Imel, domin dukkansu (da Imel da MMS) suna amfani ne da Intanet wajen daukan sako daga wayar da aka aika su zuwa wata waya ko kwamfutar da ke dauke da adireshin da aka aika.  Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum, da fatan Baban Sadik bai manta da roko na ba na tura min laccar da ka gabatar a katsina. Na gode!

Wa alaikumus salaam, lallai kam na tura maka. Ina kyautata zaton ka samu sakon tuni.  Allah sa mu dace, amin.

Assalaamu alaikum Baban Sadik. Don Allah, tsakanin uwa da uba wa yaro yafi gado wajen siffa.  Saboda mafi yawan mutune sun fi debo kamannin iyayensu mata da dabiunsu.  Za ka ga uba fari tas amma in matarsa baka ce sai aga mafi yawan yayansa bakake.  Haka nan za a ga mutum baki kirin amma in matarsa fara ce sai aga mafi yawan 'ya'yansa farare.  Daga Mahfuz Tasiu Kano

A gaida Mahfooz, sannu da kokari.  Wannan tsokaci ne kan abin da ka lura dashi.  Amma na yi bayani iya gwargwado a kasidun da suka gabata kan wannan al'mari, da hujjoji na hadisai da kuma bayanan masana kimiyyar halitta na zamani cewa, tsakanin Uba da Uwa akwai nau'ukan dabi'un halitta da suke raba wa 'ya'yansu.  Domin 'ya'ya sukan yi kamaiceceniya da dayan iyayensu ne sanadiyyar rinjiyar dabi'a da siffar halitta da kowanne cikin iyayensu nasu keyi.  Misali, idan dabi'ar halittar Uba (Paternal Genes) a bangaren launin jiki sun fi na Uwa karfi (wato yana da "Dominant Trait"), 'ya'yansa za su yi kama da shi a wannan bangaren.  Sannan idan uwar tana da rinjayen dabi'ar halitta a bangaren saurin fushi, to, ana iya samun wasu 'ya'yan su zama masu masu saurin fushi, ko da kuwa sunyi kama da mahaifinsu wajen launin jiki. Sannan  Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya nuna cewa lallai idan maniyyin namiji ya zama a saman na macen (ko ya rigayi nata, ya zama a sama), to dan da za a samu ta sanadiyyar wannan haduwa zai yi kama da mahaifinsa ne. A takaice dai kamaiceceniya ta fuska ko launin fatar jiki, ba ita ce kadai kamaiceceniya ba, akwai dabi'un zuci, da tsawon jiki, da girma ko sirantakar gabobin jiki, da launin gashin kai, da tsarin hakora, da tsarin fadi ko sirantakar yatsu da dai sauransu, wanda idan aka yi la'akari dasu, za a ga ko da 'ya'ya sun biyo Uwarsu a launi, ta wani bangaren bai hana suyi kama da mahaifinsu, idan aka yi la'akari da wadancan dalilai.  Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum Baban Sadiq ya aiki?  Don Allah ka kara taimaka mini da wani adireshin gidan yanar sadarwa na Muslunci, wanda zan rika aika tambaya ana bani amsa da hausa.  Kwanaki ka bani na www.islama-qa.com to, sai dai ina son na harshen Hausa ne.  Da fatan babu matsala nagode.  Usman Muazu Funtua, Katsina State

Wa alaikumus salam, Malam Usman bark aka dai.  Kamar yadda kace, wanda na baka kwanakin bayan na harshen Turanci ne, ma'ana da harshen Turanci ake aika tambaya, haka ma cikin harshen Turanci ake amsawa. Wannan shafi da na baka dai shi ne shafi mafi shahara a Intanet kan abin da ya shafi aikawa da karbar amsar fatawowi kan al'amuran Musulunci.  A gaskiya a halin yanzu dai ban san wani shafi karbabbe, cikin harshen Hausa, wanda ke karba da kuma amsa tambayoyi kan sha'anin Musulunci ba.  Wannan ne ma yasa na baka wannan din.  Tabbas  akwai wasu shafukan yanar sadarwa na wasu kungiyoyi inda malamansu ke amsa tambayoyi, amma ba wai musamman aka gina shafukan don amsa tambayoyi ba.  Amma idan kana da shafi a Dandalin Facebook, kana iya neman duk malamin da hankalinka ya kwanta dashi, ka shiga shafinsa don aika tambayarka, za a baka amsa.  Akwai malamai da dama 'yan Najeriya, shahararru, kuma Hausawa, masu shafuka a Dandalin Facebook.  Kuma muddin ka aika tambaya za su amsa maka in Allah yaso.  Allah sa a dace, amin.

Salamun alaikum Baban Sadik, don Allah yaya zan mayar da shafin Facebook di na ya zama dandali? Kuma wane ne Harun Yahya, da gudunmawarsa a kimiyance? Abul-waraqat Ayagi.

Dubun gaisuwa ga Abul Waraqaat. Dangane da abin da ya shafi canza shafin Facebook ya koma Dandali, sai dai ka bude Dandali na musamman, wanda shafin ke bayar da damar budewa, wato "Group" ko "Page."  Galibin shahararrun malamai da shugabanninmu na siyasa suna da shafuka ko Dandali na musamman a shafin Facebook.  Idan kana bukata ba sai ka canza shafinka ba, wanda zai zama mai wahala a gareka, kana iya bude Dandali na Musamman. Idan ka shiga shafinka, ka gangara kasa daga bangaren hagu, za ka ga inda aka rubuta "Create a Group,"  kana shiga za ka ga yadda ake budewa, babu wahala.

Dangane da Harun Yahya kuma, wani shahararren mai bincike ne kan fannin halitta a musulunce, da bambance-bambancen da ke tsakanin mahangar Kur'ani da mahangar Malaman kimiyyar karnoni biyar zuwa yau.  Asalin sunansa shi ne Adnan Oktar, kuma an haife shi ne a birnin Ankara na kasar Turkiyya cikin shekarar 1956, yana da shekaru 57 kenan a duniya yanzu. Ya yi karatunsa gaba daya a birnin Istanbul na kasar Turkiyya, inda ya karanta fannin Falsafa. Adnan Oktar mutum ne mai sha'awa kan binciken malaman kimiyya musamman na wannan zamani, tare da gwama fahimtarsu da wanda ke cikin Kur'ani ko Hadisai ingantattu.  Littafin farko da ya fara fitarwa shi ne "The Atlas of Creation," wanda babban kundi ne kan bayanan da suka shafi halittu, da tsarin halittarsu, da hotunansu, da kuma mu'jizar Allah da ke cikin halittatarsu.  Bayan  wannan akwai rubuce-rubuce da yawa da ya yi daga baya, duk a kan fannin kimiyyar halittu ne da sama da kasa da duwatsu da kuma sararin samaniya.  A halin yanzu yana da gidan rediyo na musamman inda yake tattaunawa kan asalin halitta, da kuma shafukan yanar gizo masu dauke da dukkan rubuce-rubucensa.

Ya yi suna a kasashen Yamma, saboda yada rubuce-rubucensa da yake yi a duk sadda aka buga. Yakan aika su kyauta ga shahararrun masana kimiyya, da jami'o'n kasasashen turai da Amurka baki daya.  Duk da cewa galibinsu ba su yaba abin da yake yi ko yake rubutawa, amma hakan dai ya yi tasiri wajen jawo hankalin turawa da dama kan ayoyin Kur'ani da ke bayani kan halitta baki daya.  Ga duk mai son karin bayani kan rayuwarsa da rubuce-rubucensa, ana iya samu a shafinsa na yanar gizo da ke: www.harunyahya.com. Da fatan an gamsu.


13 comments:

  1. Hi there, I log оn to your blogs on a гegular baѕіѕ.
    Your humoristic stylе is witty, keep doing whаt
    уou're doing!

    My blog post :: Seo company dallas

    ReplyDelete
  2. The two namеs aге enough to tell thе real
    stоry behinԁ the selection of this hаiгcut.

    Nicоle Polizzi, also callеԁ Ѕnooki, has her own faѕhіon
    stylе whеn she ωeaгѕ a puff sleeve
    short metallіc grey dress. Сaitlin shows her tenderness and could ԁгаw comρariѕons to the way Nоrah Jones approacheѕ a tune.


    Мy blog post :: red shoes

    ReplyDelete
  3. Hi! This is my 1st comment here so I just wanted to give a quick shout out
    and tell you I truly enjoy reading through your posts.

    Can you suggest any other blogs/websites/forums that cover the same subjects?
    Many thanks!

    my site - (0) (0 Votes)

    ReplyDelete
  4. Finallу we reаlized that іt just neеdеԁ mοre tіme to breаthe (I wοuld have preferгеԁ it dеcаntеd) befοге the cοmplex rich taste, soft
    and vеlνety wіth рlenty of goοd fruit came through with its satіsfyingly long smooth
    finish. It can be the Microsοft сeгtifісatiοn eхamіnatіon code for - Forefгont
    Protectіon fοr Еndpоintѕ аnd Applіcatiοns,
    Confіguring. Perѕevеranсe liteгally means: tο
    perѕist in spitе of difficulties.

    my web blog - spring shoes

    ReplyDelete
  5. None оf thesе words mean anything ωіthout actual follow-through on the ρart οf thе manager rеsponsible for heг department.

    The cost of comрeting in the smartphonе spacе іs growing higher and the patent cοld war looks set to eхplode
    into violencе. Next, revisіt your reference list and start picking uр the phonе.


    My webpage bizspeaking

    ReplyDelete
  6. Hmm it seems like your site ate my first comment (it was super long) so I guess I'll just sum it up what I submitted and say, I'm thoroughly
    enjoying your blog. I too am an aspiring blog writer but I'm still new to the whole thing. Do you have any suggestions for newbie blog writers? I'd
    really appreciate it.

    Feel free to visit my web site ... advice

    ReplyDelete
  7. Allah Ya saka da alheri, Barka da sallah, Allah ya maimaita mana

    ReplyDelete
  8. slm, malam abdullahi nayi emailed naka amma ba reply (nurawisdominfo@gmail.com). kayi zabi me kyau ina nufin your blogging platform domin WordPress nada rauni sosai musamman idan attacker yana amfani da acunetix, amma yanzu ddos ne kawai hadarin, sai na jika.

    ReplyDelete
  9. Hmm yana kama da shafin da ka samu na farko (yana da lokaci mai tsawo) don haka ina tsammanin zan ninka abin da na gabatar kuma in ce ina lafiya

    ji dadin blog ɗinku. Har ila yau, ina son rubutun ra'ayin kanka a yanar gizo amma ina har yanzu ba daidai ba. Kuna da wasu shawarwari don sabon blog blog? Zan so
    gaske yaba da shi.

    read more hausa news like this here

    ReplyDelete
  10. A cikin harshen Hausa, wanda ke karba da kuma amsa tambayoyi kan sha'anin Musulunci ba. Wannan ne ma yasa na baka wannan din. Tabbas akwai wasu shafukan yanar sadarwa na wasu kungiyoyi inda malamansu ke amsa tambayoyi, amma ba wai musamman aka gina shafukan don amsa tambayoyi ba. Amma idan kana da shafi a Dandalin Facebook, kana iya neman duk malamin da hankalinka

    Richard juwah
    Hausa NG Hausa NG

    ReplyDelete
  11. Hmm yana kama da shafin da ka samu na farko (yana da lokaci mai tsawo) don haka ina tsammanin zan ninka abin da na gabatar kuma in ce ina lafiya

    nsu ke amsa tambayoyi , amma ba wai musamman aka gina shafukan don amsa tambayoyi ba. Amma idan kana da shafi a Dandalin Facebook.


    Hausa news website

    ReplyDelete