Tuna Baya….
Wadanda suka saba
karanta wannan shafi tun farkon farawa sun san cewa a duk karshen zango, mukan
zauna don tattaunawa da juna, da kuma yin waiwaye, abin da Malam Bahaushe ke
kira "Adon tafiya." A yanzu
shekarun wannan shafi namu biyar kenan da watanni shida cif-cif. Kuma wannan shi ne zama na biyar da za mu yi,
don yin bitar darussan da muka yi ta kwasa a baya. Ga wadanda basu san wannan tsari da shafin ke
gudanuwa a kai ba, shafin Kimiyya da Kere-kere ya samo asali ne cikin
watan Oktoba na shekarar 2006; farkon taken shafin shi ne: Kimiyya da
Fasaha. Mun kuma yi waiwaye karo na
daya, da na biyu, da na uku ne a tsakanin shekarar 2006 zuwa 2008. Zama na karshe da muka yi, wanda shi ne
waiwaye na hudu, ya zo ne cikin watan Satumba na shekarar 2008, daidai lokacin
da shafin ya cika shekaru biyu kenan. Ga
shi mun sake dawowa a yau don yin nazari kan kasidun baya, a karo na biyar,
kamar yadda masu karatu za su gani daga taken kasidar. A yau ma za mu yi nazari ne kan darussan da
muka koya a wannan zango, wanda shi ne mafi tsawo tun da shafin ya faro. Domin rabon da muyi zama irin wannan, shekaru
uku da rabi kenan. Bayan haka, za mu ga
yawan kasidun da muka kawo a zangon, da abin da suke karantarwa, da irin
usulubin da muke bi wajen tafiyar da shafin, da tsarin mu'amala da masu karatu,
da kasidun da ba a gama su ba, sannan mu ji inda za mu dosa a zangon da ke
tafe?
Me Muka Koya Daga
Darussan Baya?
Da farko dai,
wannan shafi ya faro ne da kasidu kan fasahar Intanet da sadarwa zalla. Daga baya ne muka sauya wa shafin take daga: Kimiyya
da Fasaha zuwa Kimiyya da Kere-kere.
Wannan sauyin take ya samo asali ne sanadiyyar sauyin nau'ukan
fannonin da shafin ke magana a kai. Daga
fasahar Intanet da wayar salula zuwa sauran fannonin kimiyya da kere-kere, da
sararin samaniya, da sinadarai, da halittar jikin dan adam, da kuma fannonin
dabi'u da zamantakewa. Ya zuwa makon da
ya gabata, mun gabatar da kasidu guda 210 kan dukkan wadancan fannoni. Idan muka hada da kasidar wannan mako, sun zama
211 kenan. A waiwaye adon tafiya na
farko muna da kasidu 7. A zango na biyu
muna da kasidu 22. A zango na uku muna
da kasidu 17. A zango na hudu muna da
kasidu 33. A zango na karshe, wanda shi
ne muke bitarsa a yau, muna da kasidu guda 132. Dukkan wadannan kasidu suna nan
daram!
A wannan zango,
kamar yadda mai karatu ya gani, muna da kasidu 132 ne. Saboda yawansu ba zan iya kawo su daya bayan
daya ba. Sai dai shahararru daga cikinsu
wadanda suka hada da: "Dumamar Yanayi" (Global Warming), inda
muka ji bayanai kan dalilan da ke haddasa dumamar yanayi da illolinsu. Sai kasidar "Na'urar ATM", da
kasidar "Bunkasa Harshe da Al'ummar Hausawa" ta hanyar kimiyya da
fasahar sadarwa. Sai kasidar
"Binciken Malaman Kimiyya kan Tsibirin Bamuda" (Bermuda Triangle),
tsibirin da turawa ke hasashen cewa akwai kwankwamai a cikinsa. Mun kuma kawo kasida kan "Fasahar
Ma'adanar Bayanai", inda muka yi bayani kan tarihi da asalin faya-fayan
garmaho, da CD da kuma DVD. Sai
shahararriyar kasida mai take: "Kimiyyar Kur'ani da ta Zamani: A Ina Aka
Hadu?", wanda shafi wajen 18 ne.
Sai kasidar da tayi mana bayani mai tsawo kan dalilan da ke sa kasashen
duniya ke sanya wa fasahar Intanet takunkumi, mai take: "Yadda Kasashe Ke
Sanya wa Fasahar Intanet Takunkumi."
Sai kuma kasida ta musamman, wacce tafi kowanne tsawo kuma har yanzu ba
mu gama ta ba, mai take: "Bayani Kan Wayar Salula." Zuwa yanzu ta kai
shafuka 58! Idan mai karatu bai mance
ba, mun yi azama ne don gabatar da bayani kan dukkan abin da ya shafi tsarin
mu'amala da wayar salula.
Sai kuma kasidar da
ta yi mana bayani na wucin gadi kan Dandalin Facebook, mai take:
"Dandalin Facebook a Mahangar Binciken Ilmi." Ta shahara ita ma. Sai kasida mai take: "Yadda Ake Tono
Danyen Mai da Tace Shi," da kasida ta musamman kan Ruwa, mai take:
"Yadda Ruwa ke Samuwa, da Sinadaran da ke Cikinsa." Gama wannan kasida ke da wuya sai muka
kwararo bayanai kan fasahar amfani da haske wajen taskance bayanai, cikin
kasida mai take: "Fasahar Optical Fiber", wanda tsari ne da ke
lura da yadda ake sarrafa bayanai ta hanyar kunun gilasai, da haske. Wani lamarin sai ilmi, Jama'a. A gaba sai ga kasidar "Ciyar da Najeriya
Gaba ta Hanyar Kimiyya da Fasahar Sadarwa." Sai bayani mai taken:
"Tallafin Hasken Laser ga Fannin Likitanci." Bayan wannan kuma
sai kasida kan badakalar da shafin Wikileaks ke hankadowa, mai take:
"Yadda Shafin Wikileaks ke Sauya Tsarin Samar da Bayanai a
Intanet." Sai kuma littafin Dakta
Adnan Abdulhamid da muke fassarawa mai take: "Fahimta ta Kan Fannin Ilmin
Sararin Samaniya." Wannan littafin
ma ko rabinsa bamu yi ba. Daga nan sai kasidar: "Tsarin Gudanarwar
Kwakwalwar Dan Adam," wadda a cikinta
mai karatu ya samu bayanai kan yadda kwakwalwa ke sarrafa bayanai. Sai kuma kasida guda wadda ke dauke da jerin
bayanai kan gwarzon kokarin da Gwaraza suka yi a karnonin baya, mai take:
"Mazan Jiya da Yau a Fannin Kimiyya da Fasahar Kere-kere." Ana cikin
haka ne sai tsohon Shugaban kamfanin Apple mai suna Steve Jobs ya ce ga
garinku. Wannan yasa muka fassara
shahararriyar jawabin da yayi wa daliban Jami'ar Stanford a shekarar 1995. Mun kuma ba kasidar taken: "Steve Jobs:
Gwarzo a Fannin Kimiyyar Sadarwa ya Kwanta Dama."
Bayan wannan jawabi kuma sai kasidar da muka
kawo mai bayani kan yadda haske ke samuwa, ciki har da bakan gizo, mai take:
"Samuwar Haske da Yanayinsa."
Sai ga kasidar: "Tsaunuka Masu Aman Wuta" ta biyo baya. Wannan kasida ita ma ta shahara, domin mun
kawo ta ne daidai lokacin da wani tokar kunun dutse ya toshe sararin samaniyar
kasashen turai sanadiyyar ambaliyar wuta da duwatsun kasar Iceland suka
yi. Sai kuma kasida mai taken:
"Jirage Masu Sarrafa Kansu" (Drone Airplanes). Daga nan sai kasidar karshe wadda tazo kan
tsarin tunani tsakanin kwakwalwa da zuciya, mai take: "Tsakanin Kwakwalwa
da Zuciya, Wa Ke Samar da Tunani?"
Wannan ita ce kasidar da tafi kowacce shahara, da kuma kima wajen zurfin
bincike, da kashe lokaci, da kuma shauki wajen masu karatu. Shafuka 29 ne gaba dayanta. Wadannan su ne shahararru daga cikinsu. Akwai labaru da muka kawo, da amsoshin
wasikun masu karatu, da dai sauransu. Na
kuma tabbata masu karatu sun amfana matuka da wadannan kasidu da suka zo a
wannan zango.
Ina Muka Dosa
Daga Nan?
Akwai wadanda za
mu ci gaba da su a zangon da ke tafe, irin su "Bayani Kan Wayar
Salula," da fassarar littafin Dakta Adnan mai taken: "Fahimta ta Kan
Fannin Ilmin Sararin Samaniya," da kuma jerin kasidu kan "Mazan Jiya
da Yau a Fannin Kimiyya da Kere-kere."
Wadannan za mu ci gaba da kawo su.
Sai kuma kasidu kan fasahar Intanet, wanda idan masu karatu suka lura,
za su ga a zangon da ya gabata mun rage kawo bayanai kan wannan fanni
matuka. A zangon gaba za mu fadada in
Allah yaso. Sannan za mu ci gaba da kawo
bayanai kan fannin dabi'ar dan adam, musamman wajen tunani, da fahimta, da kuma
hankalta. Za mu ci gaba da bibiyar sakamakon binciken malaman kimiyyar
kwakwalwa da zuciya har wa yau, don jin kwakwaf kan sabon nau'in binciken da
ake yi dangane da asalin tunani, tsakanin zuciya da kwakwalwa. A daya bangaren kuma za mu yi bincike na
musamman cikin yardar Allah, dangane da yanayin rai, da samuwarsa; musamman
bangaren da ya shafi rayuwa da mutuwa, da yanayin rai a halin barci da farke,
da dai sauran bayanai masu alaka da hakan. Sai a kasance tare da mu.
Mu'amala da Masu
Karatu
Kamar yadda muka
faro a baya, mun ci gaba da mu'amala da masu karatun wannan shafi ta hanyoyi
uku; hanyar farko ita ce ta kira ta hanyar wayar tarho/salula. Hanya ta biyu
kuma ta hanyar sakonnin tes, wato gajerun sakonnin wayar salula kenan. Hanya ta uku kuma ita ce hanyar sakonnin
Imel. Ta wadannan hanyoyi ne nake samun
sakonnin masu karatu, kuma nakan amsa musu tambayoyinsu ta wadannan hanyoyi ko
ta hanyar bugawa a shafin jarida. Wasu
kan ce kada in buga sakonsu, nakan kame ba na bugawa. Saboda mu'amala da masu karatu na daga cikin abubuwan da nake
basu muhimmanci sosai a wannan shafi.
Wannan ta sa ko tuki nake yi wani ya kira ni nakan bashi amsa in har zan
iya. Nakan amsa wa masu aiko tes nan
take idan abin da suke bukata ba ya bukatar dogon bincike. Haka duk sadda Allah ya kaddare ni da shiga
jakar wasikar Imel, nakan duba kuma in amsa wa masu neman karin bayani ko neman
a aiko musu da kasidu. A takaice dai
nakan yi iya kokari na wajen ganin na gamsar da masu karatu. To amma duk da haka, dan adam ne ni; tara
nake ban cika goma ba.
Daga cikin rauni
na akwai gazawa ta wajen bin tsarin da nace zan rika bi wajen tafiyar da wannan
shafi. A baya nace zan rika buga sakonnin
masu karatu a duk mako idan na samu, amma ban yi ba. Sannan nace zan rika cakuda fannonin ilmin da
kasidun ke zuwa kansu a duk mako (misali in cakuda kasidar fasahar Intanet da
na kimiyyar sinadarai), wannan ma ban yi ba.
Sannan akwai wadanda suka aiko tambayoyi ta tes, masu saukin amsa, amma
har yanzu da nake wannan rubutu ban basu amsa ba. wadannan su ne manya daga cikin laifuka na. Ga jawabi kan wadannan. Da farko dai, babban abin da yasa na saba
wadannan alkawurra shi ne, akwai shagulgula na aiki da karatu da suka
dabaibayeni, wadanda kuma ban hararo su ba sadda nake kafa wa kaina wadancan
ka'idoji. Ku yi hakuri, ba ku bi na
bashin bayani. A duk mako nakan kashe a
kalla sa'o'i hamsin ne a ofis. Bayan
aikin ofis, akwai lacca da nake gabatarwa a duk ranar jumu'a sau biyu; daya da
rana, daya tsakanin magriba da isha'i.
Ranar asabar ma nakan gabatar da lacca tsakanin magariba da isha'i. Ranar lahadi ma haka. Haka ranar laraba, duk ina gabatar da laccoci
cikin wadannan lokuta. Sannan dole ne in
tanadi lokutan da zan yi karatu kafin kowace lacca. Sannan akwai lacca guda,
wadda dole ne in zauna in rubuta ta, kafin gabatar da ita. Sannan ga lokacin zama don gudanar da bincike
kan kasidar da ake bugawa a wannan shafi.
Idan tambayoyi ne masu tsauri su ma suna bukatar bincike. Sannan ga iyali, ga 'yan uwa, ga dawainiya da
hakkokin zamantakewa da ke kaina. Ku yi
hakuri, dole ce tasa na fada. Domin
akwai wadanda ke jin haushi na kan wasu bukatu da ban biya musu ba. A yi hakuri, dan adam ne ni.
Daga cikin
wadanda na saba musu akwai shahararrun daliban wannan shafi. Akwai Aliyu Sa'idu IT, da Abul Waraqaat, watau
Rabi'u Ayagi, da Yusuf Muhammad Gagarawa, da kuma Ibrahim Muhammad da ke Toro a
Bauchi. Duk ku gafarce ni. Ni ma wasu
daga cikin masu karatu sun min laifi sosai, amma na yafe. Sau tari ana mini filashin, har yanzu ba a
daina ba. Amma na daina fushi. Duk sadda
aka yi filashin sai in kira, da zarar an dauka ba na bari a dora mini nauyi,
sai ince a daina min filashin, in da bukata a kira. Sai a bani hakuri. Sannan na fahimci wasu lokuta kuskure ne ke
haddasawa. Na sha ganin filashin, idan
na kira, sai a bani hakuri a ce: "Yara ne suka matsa wayar ban sani
ba." To, ina kira ga jama'a, don
Allah in ba tsananin bukata ba, a daina taskance lambar wayata a waya, musamman
dai matan aure. Don Allah. Tunda akwai jaridar tana nan, idan an tashi
bukata a rika dubawa. Ba sai an taskance
lambar a waya ba. Na san gamsuwa da ake
yi ne ta jawo haka, amma a rika lura da wasu al'amuran kuma. Zuciya ba ta da kashi.
Kammalawa
A karshe, ina
kyautata zaton masu karatu za su ci gaba da hakuri da ni. Ni ma zan rika daurewa kan wasu
abubuwan. Haka rayuwa take daman. Daga cikin kasidun da na zayyana ko wadanda
suka gabata a zangon baya, duk wanda ke da bukata, sai ya rubuto, ya kuma gaya
min wacce yake so, sai in tura masa. A
halin yanzu na fara raba kasidar Tunani tsakanin Kwakwalwa da Zuciya a Dandalin
Facebook. Mutane sama da 15 sun
bukata kuma na tura musu. Duk mai
bukatar kasidar sai ya turo mini adireshin Imel dinsa, in tura masa. Shafuka 31 ne, har da shafin bangon farko da
shafin bayanan da kasidar ke dauke da su. Idan Allah ya kai mu mako mai zuwa za
mu kawo kasida mai taken: "Rayuwar Matasanmu a Dandalin Facebook."
Na gode matuka kan addu'o'inku, da nasihohinku, da kulawarku, da kuma
kasancewarku a tare da ni a wannan shafi a duk mako.
No comments:
Post a Comment