Wednesday, February 13, 2013

Amsoshin Wasikun Masu Karatu (2)



Matashiya

Wannan shi ne kashi na biyu na sakonnin masu karatu, kamar yadda muka yi alkawari a makon da ya gabata. Da fatan za a ci gaba da rubuto mana kamar yadda aka saba.  Kada a manta a rika rubuta suna, da adireshi a karshen kowace tambaya ko sakon tes/Imel.  Duk sakon da babu suna da adireshi ba za a buga ta ba.  Da fatan za a kiyaye. 

………………………………………………………………….

Assalamu alaikum Baban Sadiq, ina da waya nau'in Samsung D780. Jiya na yi rajistar shafin Facebook ta hanyar Opera, amma sun ki yi. Daga Maikudi

Wa alaikumus salaam, Malam Maikudi, ta yiwu kana so ne kace kayi kokarin yin rajistar amma abin ya gagara.  Sai dai baka yi bayanin irin matsalar da ka ci karo da ita ba.  Shin, babu tsarin Intanet ne da zai sadar da kai da shafin Dandalin Facebook, ko dai ka shiga shafin, amma abin ne ya gagara? Sai na fahimci hakikanin matsalar da ka fuskanta kafin in iya baka jawabi mai gamsarwa.

Assalamu alaikum Malam, Allah ya taimake ka. Bayan haka, ina so ka taimakeni da sanin yawan kalmomin da zan yi amfani da su. Domin ina son yin rajistar akwatin Imail ne a shafin Facebook, amma na kasa.  Dalibinka Musa Adam, Mile 12, lagos.

Wa alaikumus salam, Malam Musa Adam barka ka dai.  Babu wani haddi kan yawan kalmomin da za a yi amfani da su wajen bude adireshin Imel, sai dai kalmomin iznin shiga, wato Password. Sai dai kuma, ya danganci a kan wace irin na'ura kake son yin rajista; shin, a kwamfuta ne ko ta wayar salula?  In dai ta kwamfuta ne, to dole ne sai da adireshin Imel.  Amma idan ta wayar salula ne kana iya amfani da lambobin wayar salularka.  Adireshin Imel na samuwa ne ta hanyar yin rajista a daya daga gidajen yanar sadarwar manhajar Imel, irin su: Yahoo! (www.yahoo.com), ko Google Mail (http://mail.google.com).  Idan ka shiga shafin sai ka matsa inda aka rubuta "Sign Up."  Amma idan ta wayar salula ne ba ya yiwuwa, dole sai kayi amfani da kwamfuta wajen rajista.  Da fatan ka gamsu.

Baban Sadik don Allah yaya zan yi rajistar shafin Facebook a kan wayata? Daga Umar Minister; 08185110085

Malam Umar, idan kana bukatar yin rajistar shafin Facebook, ka je: http://www.facebook.com/mobile, za ka ga inda aka rubuta "Install Facebook on Your Phone," a can kasa kuma an rubuta "Install."  Ka matsa alamar kasa, za a saukar maka da manhajar Facebook a kan wayarka.  Daga nan sai ka yi rajista cikin sauki.  Wannan ita ce hanya mafi sauki.  Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum, Malam mun gode da kasidar da ka fara gabatar mana mai taken 'tsarin amfani da wayar salula'. Allah ya saka da alhairi.  Daga: Muhammad Sani Idris.

Wa alaikumus salam, Malam Muhammad ina godiya matuka ni ma. Allah saka da alheri, amin summa amin.

Assalamu alaikum, Baban Sadik na karanta bayaninka a kan sakonnin tes, musamman musu turo tes na adu'o'i su ce ka tura wa mutane kaza. Kamar a baya ne kafin samuwar wayar salula, sai ayi ta yada wani labari cewa (wai) limamin madina ne yayi mafarki. Sai ace kayi photocopy ka tura wa mutane 11 kada ya wuce lokaci kaza ba ka ba kowa ba.  To, Allah ya saka maka da alhairinsa a bisa wannan fadakarwa da kayi.  Na gode. Daga Baban Zara (Iman).

Wa alaikumus salam, ina matukar godiya da wannan tsokaci da kayi mana baki daya, Baban Zara.  Allah saka da alheri. Wajibi ne a kanmu duk inda muka ga wani abu makamancin haka mu yi tambaya, ba wai da zarar an turo mana sai kawai mu kama bugawa muna raba wa jama'a ba.  Idan wani ya tambaye mu sai ranmu ya baci.  Allah ya dada shiryar damu tafarki madaidaici, amin.  Na gode!

Baban Sadik da Fatan kana lafiya, amin.  Ka sosa mini inda yake min kaikayi game da tarihin Neil Aldrin Amstrong da yadda yayi tafiyarsa da nasarorinsa.  Zan so inji na Yuri Gagarin; shin, ba tafiyar hadin guiwa suka yi da Neil bane? Wa ya riga wani?  Me ya bambanta su?  Sannan kawo yanzu mutane nawa ne suka yi irin wannan tafiya?  Ina godiya Allah ya kara basira.  Daga Sharif Awwal Falala, Fct-Abuja

Malam Bashir Falala, ina godiya da wannan tsokaci naka kan tafiye-tafiyen Neil Armstrong.  Dangane da tambayoyinka, da farko dai, Yuri Gagarin ya riga Neil Asmtrong zuwa sararin samaniya, da kusan shekaru goma.    Don haka ba tare suka yi tafiyar ba.  A takaice ma dai, said a Yuri Gagarin ya rasa rayuwarsa a shawagin da yaje da wani jirgi da dadewa kafin Neil yayi nasa tafiyar.  Babban abin da ya bambanta tafiye-tafiyen nasu kuwa shi ne, Yuri Gagarin yayi tafiya ne a lokacin da kasar Rasha ke gwajin yiwuwar daidaituwar Kumbo da mahayansa a sararin samaniya.  Sun kuma cinma wannan buri, wajen rigan kasar Amurka yin wannan aiki, tare da zama na farko wajen aiwatar da wannan gagarumin aiki.  Amma tafiyar Neil da abokan aikinsa kuwa ta zo ne bayan zuwa sararin samaniya ya fara zama ruwan dare.  Duk da cewa su ne na farko wajen sauka a kan duniyar wata, kamar yadda bayanai suka gabata.  A halin yanzu ba ni da kididdiga kan yawan mutane ko mahayar da suka yi safara zuwa sararin samaniya a tarihin duniya, domin ba abu ne da ya faru a kasa daya ba kadai.  Da fatan ka gamsu.

Salamun alaikum Baban Sadik, wai da gaske ne idan hadari ya hadu a sararin samaniya, a kan iya amfani da kayan kimiyya wajen kawar da yiwuwar samun ruwan sama?  Daga Sulaiman Kurma, Dutsin-ma.

Wa alaikumus salam, Malam Sulaiman barka ka dai. Lallai ban taba samun bayanai masu nuna yiwuwar hakan ba a halin yanzu.  Na dai san akwai wadanda ake kira a kauyuka suna aiwatar da surkulle na sihiri don ganin sun "daure hadari" kamar yadda suke cewa, idan an tashi biki kuma ga hadari ya hadu.  Idan kuma suka gama sai ka ga ba a yi ruwan ba.  Wannan, a iya tabbaci na, ba kokarinsu bane.  Dayan biyu; ko dai daman Allah bai kaddara samuwar ruwan a wannan bigire bane, ko kuma Allah na haddasa hakan ne don su kara dulmiya cikin duhun kafircinsu.  Amma duk mai hankali ya san cewa idan Allah yayi niyyar aiwatar da wani abu, babu mai iya hana shi yiwuwa ko faruwa, a lokacin da yake so, da yanayin da yake so, da kuma muhallin da yake so.  Amma a bangaren fannin kimiyya kam ban da masaniya.  Akwai tsarin haddasa ruwan sama na wucin gadi da kamfanonin hada fina-finan kasar Amurka ke yi, mai suna "Artificial Rainfall," wanda hakan bai wuce iya bigiren da suke son yinsa.  Wannan ba wani abin birgewa bane.  Amma hana ruwan sama zuba bayan Allah ya aiko shi, ban da masaniya.  Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum, Baban Sadik a halin yanzu akwai mai irin wanan aiki na Neil Aldrin Armstrong a duniya kuwa? Daga Salisu Nagaidan, Jama'are Jihar Bauchi; 08063461480

Wa alaikumus salam, Malam Salisu barka dai.  Amsar tambayarka ita ce: Eh!  Ai tsarin safara zuwa sararin samaniya a wannan zamani ma ya fi sauki fiye da baya, saboda ci gaban fannin kimiyya da kere-kere da duniya ke tinkaho da shi.  An yi tafiye-tafiye da dama bayan tafiyar su Neil Armstrong, musamman zuwa wasu duniyoyin ma, ba duniyar wata kadai ba.  Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum Baban Sadiq, yaya kake? Da fatan kana lafiya. Ina sonsanin shin, da wani irin sinadari ne kumbon Apollo yake amfani domin tafiya?  Daga Nura Bappayo soja

Wa alaikumus salam, Malam Nura barka ka dai.  Idan na fahimci tambayarka, kana nufin 
sinadaran makamashin lantarki ne.  In eh, na yi bayanin cewa kowane Kumbo da ake amfani da shi zuwa sararin samaniya, yana amfai ne da makamashin hasken rana, wato "Solar Energy."  Domin shi ne abin da yafi saukin samuwa a halin bulaguro, domin akwai hasken rana a duk inda zai kutsa a halin tafiyarsa. Har zuwa wannan lokaci da duniya ke tinkahon ci gaba a fannin kimiyya, da makamashin hasken rana kumbon zuwa sararin samaniya ke amfani. Sai dai yanayin girman farantin da ke taskance wannan makamashi ya sha bamban da wanda aka 
kera a baya.  Da fatan ka gamsu.

Salamun alaikum, barka da war haka. Don Allah ina so kayi mini bayani a kan bambancin hankali da tunani. Kuma tunda dabbobi jinsin halittu ne masu zuciya da kwakwalwa, shin su ma suna tunani ne kamar mutum? Ali Niggiez

Wa alaikumus salam, Malam Aliyu barka da warhaka.  Lallai dabbobi masu zuciya da kwakwalwa su ma suna tunani, sosai ma.  Sai dai tunaninmu ya sha bamban da nasu.  Suna da hankali, amma irin hankalin da yayi daidai da tsarin rayuwarsu. Suna yin tunani, amma irin tunanin da yayi daidai da tsarin halittarsu.  Sabanin dan adam, tunani da hankalin wadannan dabbobi bai wuce kan yadda za su nemi abinci, da abin sha, da guje wa abokin gaba, da neman tsari daga abin da zai cutar dasu, da kuma lura da 'ya'yansu, da hanyar saduwa don samun yaduwa.  Wadannan su ne iya kaidin tunani da hankaltar dabbobi irin wadannan.  Amma kan abin da ya shafi kirkire-kirkire a duniyar dan adam, wannan kam ba su da shi.  Bambancin da ke tsakanin tunani da hankali kuwa shi ne, tunani yana samun asali ne tsakanin zuciya da kwakwalwa.  Shi kuma hankali daya ne daga cikin kayayyakin aikin kwakwalwa, wadanda kwakwalwar ke amani da su wajen daidaitawa ko saita tsarin tunani.  Shi yasa, mahaukaci kan yi tunani, kamar yadda mai lafiya ma kanyi.  Amma bambancinsu shi ne, tunanin mahaukaci bai da tsari da saiti na musamman, don ba shi da hankali.  A yayin da tunanin mai hankali ke samun tsari da matakai, saboda akwai hankali a tare da shi. Da fatan ka gamsu.

No comments:

Post a Comment