Babban Baƙo
A
yau makonni hudu kenan cif-cif da shigan wannan wata na Ramalana mai alfarma,
kuma mai tarin albarka. Babu wanda ke da
shakku kan muhimmancin wannan wata a duniyar Musulunci baki ɗaya.
Daga cikin masu nuna farin cikinsu, da sauya rayuwarsu don dacewa da
yanayin watan, tare da neman ɗimbin
tabarrakin da ke cikinsa, har da matasanmu, waɗanda
ke kaikomo da'iman a duniyar kayayyakin fasahar sadarwar zamani; daga fasahar
Intanet zuwa wayoyin salula; daga manhajar sadarwar Imel, da na Dandalin yin
abota da sadar da zumunci, zuwa manhajar saƙonnin
tes na wayar salula, da shahararriyar manhajar hirar ga-ni-ga-ka ta wayar
BlackBerry, wato BB Chat.
A
yau za mu dubi irin rayuwar da matasanmu suka yi ne daga kamawar wannan wata
zuwa yau da ake sa ran ƙarewarsa
ko gobe, in Allah ya yarda. Don daɗa fahimtar yadda waɗannan kayayyakin sadarwar zamani ke tasiri a
rayuwarmu baki ɗaya;
shin, mu ne ke tasiri wajen sauya ma'amalarmu a cikinsu ko kuwa su ne ke yin
tasiri wajen yin hakan? Idan su ne,
shin, mummunar tasiri ce ko kyakkyawa?
Sai a biyo mu kamar yadda aka saba.
Fasahar
Intanet
Wajen
ma'amala da fasahar Intanet a matsayin fasaha mai tasiri cikin hanyoyin
sadarwar da ake tinƙaho
da su a wannan zamani, matasanmu sun tsunduma tsundum wajen faɗakar da juna ne. Idan muka koma kan tattaunawar da matasa ke
yi a Majalisun Tattaunawa (Internet Groups) na ƙauyukan
Intanet (Cyber Communities), za mu fahimci haka ƙarara. Wasu kan aiko da saƙonnin faɗakarwa
kan shigan wata, wasu kan falalar watan, wasu kan nau'ukan ibadar da ake yi ne
a watan, wasu kuma kan ɗimbin
ladan da aka tanada wa masu aikata alheri ne a watan. Ana yin hakan ne ta hanyar kawo hujjoji daga
ayoyin Ƙur'ani mai girma ko Hadisan Manzon Allah
(tsira da amincin Allah su ƙara
tabbata a gare shi) ingantattu. A wasu
lokuta wasu hadisan da ake kafa hujja da su ba ingantattu bane. To amma dai, duk ana yin hakan ne don faɗakar da juna, da neman tsira wajen Allah. Kowa "Malam" ne a wannan wata, kowa
"Mai wa'azi" a wannan wata, kowa ya zama mutumin kirki.
A
majalisun tattaunawa na musamman irin su Majalisar Marubuta, da Majalisar
Fina-finan Hausa, da Majalisar Hausa da Hausawa, da sauran makamantansu, duk
jama'a kan ajiye wasu daga cikin maudu'in da aka kafa majalisar dominsa, su ɓuge da faɗakarwa
na musamman kan wannan wata. Masu lura
da waɗannan majalisu basu cika tsaurara doka ba kan
kauce wa maudu'i, duk saboda wannan wata mai alfarma.
Dandalin
Abota da Zumunci
Haka
lamarin yake a dandalin abota da zumunci na Intanet, musamman a Dandalin
Facebook. Kowa ya zama mai wa'azi. Akwai masu farkar da jama'a a duk talatainin
dare, don su sahuru, kada su makara.
Akwai masu tashi "ƙiyamullaili"
(sallar dare), ta hanyar Facebook. Kana
iya gane hakan ne daga saƙonnin
da suke aikawa a shafinsu, cewa: "Anybody awake?" Ma'ana, "Akwai wanda ke farke
yanzu?" Akwai masu sanar da faɗuwar rana, don a yi buɗe baki, ko shan ruwa, kamar yadda muka saba faɗa.
Bayan haka, akwai masu taimaka wa masu azumi da hadisi ɗaya a dukkan rana. Sukan aiko da hadisi kan wani aiki na ibada
mahimmi da aka shar'anta a cikin wannan wata mai ƙarewa
a yau ko gobe. Bayan su, akwai majalisun
tattaunawa da koyar da tarbiyyar rayuwar musulunci da kyawawan al'adun
Bahaushe, inda ake gabatar da tafsirin watan Ramalana, duk a Dandalin Facebook. A ire-iren waɗannan majalisu akwai malamai masu karantar da
mambobin majalisar. A duk wayewar gari
sukan aiko ayoyin Ƙur'ani
gundarinsu, sannan su yi sharhi kansu, don faɗakar
da jama'a. Duk mai neman ƙarin bayani kan yi tambaya kan abin da bai
fahimta ba, don a masa bayani sosai ya gane.
A
wasu majalisun kuma ana faɗakarwa
ne ta hanyar gasar kacici-kacici, amma a fannin shara'ar musulunci, don
fahimtar da jama'a dunƙulallun
nau'ukan ilimin da suka faku gare su.
Wasu lokuta kuma a kawo wasu labarai na abubuwan da suka faru haƙiƙatan,
ko dai a Najeriya ko a wasu ƙasashe,
don ƙarin faɗakarwa
ga mambobin majalisar.
A
yayin da wasu ke ƙoƙarin faɗakarwa,
wasu kuma suna can suna ta raha. Sukan
gayyaci abokanansu zuwa shan ruwa amma ta shafin Dandalin Facebook. Wasu kan aiko da hotunan nau'ukan abincin da
za su ci ko suke ci, wasu kuma su aiko da hotunan wasu nau'ukan abinci mai daɗi daga wasu ƙasashe. Wasu kan aiko da hotunan kayayyakin marmari
don zolayar abokanansu. Wata ne mai
alfarma da galibi ake cikin raha hatta a Dandalin abota da zumunci, musamman
Dandalin Facebook.
Akwai
kuma waɗanda a kullum ba su da wani aiki, ba su da
wani zance, illa cillo ayoyin Ƙur'ani
zuwa shafukansu don amfanin kansu da na abokanansu. waɗannan
ayoyin Ƙur'ani dai daga wasu gidajen yanar sadarwar
Intanet ne suke karɓo
su, sanadiyyar rajista da suka yi a can.
Duk wayewar gari ko duk sadda suka ga dama, za su shiga shafin gidan
yanar, su cillo ayar da suke buƙata
zuwa shafinsu ba tare da wata matsala ba.
Yin hakan ya ƙaru
matuƙa da shigan watan Ramalana.
A
ɗaya ɓangaren
kuma an samu raguwar yawaitan hotunar batsa da ashararanci, da zantuka marasa
amfani, da kalmomi na rashin ladabi da a baya suka zama ruwan dare a tsakanin
matasanmu da ke shawagi a shafin Dandalin Facebook. Duk sadda wani ya ɗan yi fushi kan abin da aka masa, nan take sai
a bashi haƙuri, idan ya ƙi
amincewa, sai a tuna masa cewa a "Watan Rahama" fa ake, sai ya saduda
nan take. Hotunan 'yan mata sun ragu,
haka ma waɗanda samari ke aikowa. Hotunan da suka fi shahara a tsakanin matasa
su ne masu ɗauke da sunan watan Ramalana, ko dai cikin
harshen Larabci ko cikin harshen Turanci, da hotuna masu nasaba da watan, da
kuma wasu guraren ibada, kamar masallacin harami da ke Makka, da masallacin
Madina, da dai sauransu alamu masu dangantaka da Musulunci. A taƙaice
dai, tsarin 'yan uwantaka ya daɗa
ƙulluwa a tsakanin matasa. Kowa na ƙoƙarin kamewa wajen aikata wani abin assha a
fili, saboda alfarmar wannan wata na Ramalana.
Da haka rayuwa za ta ci gaba da kasancewa da'iman, musamman a ɓangaren matasanmu, da al'amura sun gyaru matuƙa. Amma
ko a yanzu ma dai tubarkalla.
Wayoyin
Salula
A
ɓangaren sadarwar wayar salula ma an samu ci
gaba sosai. Matasa sun shagaltu da
nau'ukan ayyukan ibada wajen yaɗa
sanayya kan hukunce-hukuncen da suka shafi wannan wata na Ramalana. Ana sanar da shigan watan nan take saƙonnin tes suka fara shawagi a tsakanin matasa. Bayan yinin farko yayi wafati, sai saƙonnin hadisai masu alaƙa da watan, don faɗakarwa.
Sai dai saboda bambancin tsari da yanayi da kuma mahalli, saƙonnin Dandalin zumunci da abota sun fi yawan
maimaituwa, da yawa, da kuma gamewa. Su
kuma saƙonnin tes sun fi sauƙin ma'amala, da sauƙin samu, da sauƙin
aikawa, ba tare da matsala ba.
Masarrafar
BB Chat
Bayan
masarrafar saƙonnin tes da ke wayar salula, akwai
shahararriyar manhajar hirar ga-ni-ga-ka da ke nau'in wayar BlackBerry, wato
BB Chat. Wannan masarrafa ce ta
musamman wacce ke taimakawa wajen aiwatar da hirar yanzu-yanzu, amma ta hanyar
wayar BlackBerry. Galibin samari kan kusan kwana suna zance da 'yan
matansu ta hanyar wannan manhaja, idan su ma suna da wayar BlackBerry. Ba komai ya sa haka ba sai don sauƙin ma'amalarsa, da cewa ko ba ka da ko sisi a
wayarka, kana iya hira da duk wanda kake son hira da shi babu matsala. A cikin wannan wata an samu ƙaruwar faɗakarwa
ta wannan hanya sosai. Kowa ya zama mai wa'azi, mai faɗakarwa na musamman. Kuma tasirin hakan ya zama
mai gamewa, saboda a kowane hali kake kana iya aiwatar da sadarwa, tunda ta
wayar salula ne, kuma ba ka buƙatar
sai da kuɗi a wayarka; a kwance kake a ɗaki, ko a tsaye kake a tashar mota, ko a zaune
kake a falo, duk kana iya aiwatar da sadarwa cikin sauƙi.
Kammalawa
Daga
bayanan da suka gabata, a tabbace yake cewa wannan wata mai alfarma da ke mana
bankwana yayi tasiri matuka wajen sauya wa matasanmu rayuwarsu, kuma hakan ya
fito fili cikin ayyukansu na bayyane (Allah kaɗai
ya keɓanta da sanin abin da ke ɓoye).
Wannan abin sha'awa ne, kuma da samari za su ci gaba da kasancewa haka,
ko kwatanta rabin wannan sauyi da ya bayyana daga rayuwarsu cikin wannan wata,
da rayuwa ta ƙara inganci, nesa ba kusa ba. Muna roƙon
Allah ya bamu dacewa cikin al'amuranmu baki ɗaya,
ya karɓi dukkan ayyukan da muka gabatar cikin wannan
wata da sauran watannin da suka gabata, da waɗanda
ke tafe, ya kuma sa su zama tafarkin tsari a gare mu ranar Ƙiyama, amin.
No comments:
Post a Comment