A baya bayanai sun gabata kan tasirin mu'amala da wayar salula, ga
al'umma baki daya, da kuma tasirin hakan ga kebantattun mutane. Wannan na da muhimmanci wajen taimawa wa mai
amfani da wayar salula ya san yadda zai yi, don kada ya afka cikin wadannan munanan
tasiri su shafe shi. Duk wani abu na mu'amala
yana da bangare biyu ne; da bangaren amfani, da kuma bangaren cutarwa. Ya
danganci yadda mai amfani da abin yayi.
A yau kuma ga bayanai kan tsarin amfani da wayar salula a warware. Domin sanin tsarin amfani da wayar salula ne
zai taimaka wa mai mu'amala fahimtar hanyoyin da zai bi wajen magance dukkan
matsalolin da ke jawo munanan tasiri wajen mu'amala da wayar salula. Ga bayanan
nan tafe:
Sayan Wayar Salula
A al'adance, kafin aiwatar da duk wani abu da wayar salula, mai
mu'amala yana da bukatar mallakar wayar salular tukun. Duk da cewa ba duk mai amfani da wayar salula
bane yake mallakarta. Akwai wadanda suke kira da karbar kira daga 'yan uwansu
ba tare da sun mallaki waya ba. Sai dai ba su da yawa, musamman ma da ya zama
wayoyin salula sun kara araha yanzu, sanadiyyar yawaitarsu a kasuwa, da samun
nau'uka daban-daban, daga kamfanonin kera waya musamman na kasar Sin (China).
Mallakar wayar salula shi ne abu na farko, ga duk mai son sanin tsarin amfani
da wayar. Kowace wayar salula kan zo ne
da kundin sarrafa ta, wato "Manual" kenan a harshen Turanci. Sai dai kuma a galibin lokuta, irin yadda muke
amfani da waya ta kowane yanayi kan sa idan ta samu matsala mu kasa samun
bayanai kan yadda za mu gyara. A wasu lokuta ma bamu cika damuwa da wannan
kundi da waya kan zo da shi ba, duk da muhimmancinsa.
Akwai wayoyin salula nau'uka daban-daban. Sau tari jama'a kan aiko
sakon tes ko su kira suna neman bayani kan wace irin waya ya kamata su saya?
Sai in rasa amsar da zan basu. Wasu
lokuta sai na musu tambaya: "wace irin bukata kake da ita a waya?"
Irin amsar da na samu, shi ke bani hasken basu shawarar da ta danganci
bukatunsu. Babu wata wayar salula daya
tinkwal da za ace ta fi kowacce. Illa dai kowacce da yanayinta, da irin
tsarinta, da kuma wasu siffofi da ta kebanta dasu. Haka kamfanonin waya ke kera su. Akwai wacce
musamman don sawwake mu'amala da Intanet aka kera ta. Akwai wacce don iya aika
sakon tes aka kera ta. Akwai wacce musamman don sauraron sauti aka kera
ta. Ga su nan dai. Wannan ke nuna mana
cewa lallai babu wata wayar salula wacce za a ce ta fi kowanne.
Idan muka fahimci haka, sai mu san cewa abin da muke bukata kadai
ya kamata mu rika la'akari da shi a jikin waya.
Kada ka ga jama'a na ta yayin waya, kawai kaima ka je ka saya, don kana
da kudi. In har kana da manufar da ta sa kake son waya, a karshe za ka ga cewa
wannan wayar da ake yayi bata dace da kai ba. Na sha samun mutane da yawa da ke
cewa, sun sayi waya sabuwa don sun ji ana ta kuranta ta, amma daga baya sai
suka ga ashe wacce suke amfani da ita a baya ma ta fi ta. Me yasa? Saboda abubuwan da suke bukata babu
su a cikin sabuwar wayar. Don haka mu
kiyaye; abin da muke bukata a waya kadai ya kamata mu yi la'akari da shi idan
muka tashi sayan waya. Ba wayar salula kadai ba, hatta mota, ko mashin/babur,
ko talabijin, ko kwamfuta, duk wannan ka'ida ta kamata mu rika amfani da ita
wajen sayansu. Idan bukatarka yawaita rubutun tes ne, wato SMS, ka bincika,
akwai wayoyin da ke da wannan dama mai kayatarwa, daga allon shigar da
bayanansu (Keypad), zuwa masarrafar rubuta sakon (SMS Application), duk za su
kayatar da kai. Idan kuma kana son waya
ce mai bayyana sauti sosai kamar zai fasa dodon kunne, duk akwai. Idan kana son mai sawwake mu'amala ne da
fasahar Intanet, duk akwai. Sai ka duba
bukatarka, sannan ka dubi yanayin waya kafin ka saya. Dole ne ka san cewa, biyan bukata ya fi dogon
buri.
Idan ka zo sayan wayar salula har wa yau, ka lura da abubuwa guda
biyu. Abu na farko shi ne
aljihunka. Zai iya yiwuwa akwai wayar da
kake so, amma kuma karfinka bai kai ba. Ka hakura da wacce karfinka zai iya
mallaka. Kada wata sabuwar waya ta burge ka.
Idan za ka iya sayar da wacce kake amfani da ita ka cika kudi ka sayi
wata, ka yi. Idan ka san ba za ka iya
ba, ka nisanci cin bashi don sayan wayar salula idan ba tsananin lalura bane ya
haddasa haka. Idan kuwa ba haka ba sai
ka mutu da bashi. Domin sababbin wayoyi
sun dinga bayyana kenan, ba za su kare ba.
Dole ne mutum ya zama mai tattali.
Duk abin da ka san ya fi karfin aljihunka, kuma ba za ka iya mallakarsa
ta dadi da kwanciyar hankali ba, to, ka hakura da shi. Allah bai yi yatsun hannayenmu daidai ba
wajen tsawo, balle samunmu. Abu na biyu
da ya kamata kayi la'akari da shi kuma shi ne mahallin da kake. Idan kana rayuwa ne a inda barayin waya sun
yawaita, ko inda sa-ido ya zama ruwan dare, to, ka zama mai kaffa-kaffa wajen
sayan waya mai tsada. Idan kuma har ka
saya, to ka zama mai alkinta ta. Idan
kuwa ba haka ba, to sai a sha ka musilla, in ji wani mawaki dan kasar Jega.
Yin Kira da Amsa Kira
Wannan shi ne babban wazifar wayar salula na farko, tun fil
azal. Kafin duk wasu kyale-kyale su samu
a jikin wayar salula, abu na farko da aka fara samarwa a waya shi ne tsarin amsawa
da karbar kira na sauti. Tsarin aiwatar
da kira shi ne abu na farko kuma wanda ya fi maimaituwa wajen mu'amala da
kowace wayar salula. Akwai maballai da
aka tanada don amsa kira idan aka kira ka. Haka akwai inda za ka matsa, ka
shigar da lambar wanda kake son kira. Da
zarar ka matsa, aiki ya kare maka, sai dai sauraro. Idan ya daga kirar za ka
gane, domin za ka ji wayar ta daina ruri (Ringing). Daga nan sai ka yi masa sallama idan musulmi
ne. Idan kuma da ya daga kirar ya maka sallama, saboda ya san layin, sai ka
amsa. Amma dai mu sani, kalmar
"Hello" ko halo da muke cewa a yayin yin kira, bata dace ba. Ko a turai, wanda ya daga waya shi yake cewa
"Hello". Domin kalmar
"Hello" harshen Faransanci ce, wacce aka yi amfani da ita a karni na
sha tara (19TH Century), kuma Turawa na amfani da ita ne don jawo
hankalin abokin magana. Don haka, wanda
ya daga waya shi ke cewa halo, shi kuma mai kira ya gabatar da kansa. To amma duk musulmi ya kamata ya lazimci
kalmar sallama, wato "Assalaamu Alaikum" a kowane lokaci, ba sai an
zo shiga gida kadai ba. Domin tsarin
aiwatar da kira ta wayar salula ma ai kamar shiga gida ne. Wanda ya kira shi ne a matsayin bako mai
sallama a bakin kofa ko mai kwankwasawa.
Wanda ake kira kuma shi ne mai karban bako, mai amsa sallama kenan. Shi yasa ma galibin malamanmu na musulunci
idan ka kira wayarsu, da zarar sun dauka, sai kaji sun ce maka:
"Na'am." Kai kuma ya rage a gare ka kayi sallama sannan ka gabatar da
kanka. Tunda kai ne ka shigo
"gidansa."
A wasu lokuta muna kuskure. Idan muka kira mutum ya daga, sai kawai
mu kama gaisuwa ko gabatar da abin da muke bukata. Wannan bai dace ba. Duk sadda ka kira waya aka daga, abu na farko
da za ka yi bayan sallama, shi ne gabatar da kanka. Ka kaddara gidansa ne ka zo shiga. Idan ka gabatar da kanka, daga nan zai samu
natsuwa. Amma idan wanda ka kira ya
sanka, to a nan babu maganar gabatar da kai.
Da zarar ka gama magana, sai kayi bankwana, tunda kai ne ka kira. Bai dace da zarar ka kira mutum, ka gama
biyan bukatarka sai kawai ka kashe waya ba.
Wannan alama ce ta rashin natsuwa, ko da kuwa wanda ka kira kasa yake da
kai wajen shekaru. Yana da kyau ka yi
masa bankwana. Misali, kace masa "Sai an jima," ko "Wassalaamu
alaikum." A nan ya san cewa lallai
an gama sadarwa. Idan yana da bukata nan
take zai jawo hankalinka.
Haka mai amsa kira, bai dace da zarar ya gama bayani ya kashe wayar
ba. Domin ba shi ya kira ba. Sai ya jira sai ya ji bankwanan mai kira, ko
kuma mai kira ya kashe wayar da kansa, sannan ya ajiye. Bayan haka, wasu kanyi wani abin da bai dace
ba. Idan suka kira ka, ka daga, har kuka
gama magana, sai su maka bankwana, amma su ki kashe wayar, suna sauraron abin
da za ki ci gaba da shi na zance tare da abokan hirarka a inda kake. Wasu kanyi haka idan suna tuhumar abokin
zancensu da algushi wajen magana. To ka
ga idan kaine mai amsa kira, da aka maka bankwana, sai baka kashe wayar ba
kawai ka ajiyeta, to ana jin duk abin da kake fada. Don haka da zarar ka ji an maka bankwana, to,
alamar sadarwa tsakaninka da abokin magana ta zo karshe kenan, sai ka kashe
wayar.
Bayan haka, kasancewar kira
ta hanyar wayar salula yana jan kudin kati, wajibi ne da zarar ka kira, ka kuma
gabatar da kanka, to nan take kayi abin da ya kawo ka. Mukan shantake a kan
layi muyi ta fadin banza da wofi marasa fa'ida, wannan almubazzaranci ne. Mu kuma gode Allah, domin a wasu kasashe da
wanda yayi kira da wanda aka kira, duk sai an caje su kudin waya. To mu a nan ba mu da wannan tsarin. Duk da haka bai kamata mu bata lokacinmu a
banza ba cikin abin da ba shi da fa'ida. Idan kuma aka kira ka a waya, sai ya
zama kana da wata bukata da kake so ka tattauna da wanda ya kira ka, sai ka
nemi izninsa, ba wai kawai ka ci gaba da wasu bayanai ba. Ta yiwu babu kudi
sosai a wayarsa, kuma ba zai iya tsayar da kai ba, nan take kuna cikin magana
sai kaji wayar ta yanke. Kai ka ja. Sannan kuskure ne mutum ya kira ka ko ka kira
shi, kuna cikin magana sai ranka ya baci, ka yanke waya ba tare da ka sanar da
shi ba. Na san duk muna yin haka idan
rai ya baci, amma kuskure ne; musamman idan kai ne aka kira. Kuskure ne ka kashe wayar. Sai ka sanar da
shi, misali, sai ka ce masa: "…wane/wance, me zai hana mu bar tattaunawa
wannan al'amari, domin raina ya baci….don Allah mu bar zancen haka…in kuwa bamu
bari ba, a mini hakuri, zan ajiye wayar."
Ka ga idan ka gaya wa abokin zancenka haka, ya san ka masa adalci.
A wasu lokuta idan aka kira
mu, sai mu daga wayar, amma saboda ba mu son magana da mai kira, sai mu yi
karya; mu ce muna mitin, ko muna cikin aji, ko kuma mu ki daukar wayar da
gangan, ayi ta kira ba iyaka. Duk wannan
ba shi daga cikin tsarin amfani da wayar salula. Domin karar kiran zai ta damunka, ko wadanda
suke wurin, idan ka ki dauka. Ko kuma
karyar da kayi za a rubuta shi a littafinka.
Akwai kuma masu daukar wayar, amma sai su ba wasu da ke wurin, su gaya
musu abin da za su fada, wanda ba gaskiya bane.
Wannan kuskure ne shi ma. An taba
kiran wani mai gidana a waya, muna zaune tare muna aiki, sai yace in amsa wayar
in ce ba ya nan ya fita, alhali ga shi muna tare. Sai na roke shi, nace: "…to Oga mai zai
hana ka fita kawai daga ofishin, sai ince masa ka fita." Sai nan take ya fice daga ofishin, sai na
amsa wayar, nace ya fita. Wannan hila
ce, ma'ana dabara ce wacce shari'a bata so ba.
To amma dai ya fi da zan yanka karya ince ba ya nan alhali ga shi a
zaune ina ganinsa. Ya kamata mu rika
shirya gaskiya cikin al'amuranmu. Wannan
zai sa mu samu nutsuwa a zukatanmu kan duk wanda ya kira mu. Idan abin da yake
bukata mai yiwuwa ne, mu amsa mu bashi ko mu masa alkawari, idan ba mai yiwuwa
bane, kai tsaye mu gaya masa gaskiya.
Sakonnin Tes (SMS)
Haka
manhajar sakonnin tes, wato "SMS", tana daga cikin manhajoji masu
alfanu matuka a jikin wayar salula. Tana daga cikin masarrafan da suka kara wa
wayar salula shahara da karbuwa a duniya.
Domin ba a dukkan lokuta za ka iya samun mutum a waya har kuyi magana
ba. Ba wannan ba kadai, akwai sakonnin
da rubuta su ya fi fadinsu da baki.
Sannan akwai lokutan da masu waya kan kashe don sanyawa a caji, ko don
sun shiga wani wuri da ake bukatar kashe wayoyi a cikinsu, ko kuma sun kashe
muryar wayar; duk komai na iya faruwa. A
lokuta ko yanayi irin wannan babu yadda za a yi ka iya aiwatar da sadarwar
murya da abokin maganarka. Don haka
manhajar sakonnin tes take da amfani matuka.
Akwai da yawa daga cikin mutane wadanda sun gwammace ka aika musu sakon
tes da ka kira su, musamman Malamai masa amsa fatawa. Wannann ke nuna mana matukar mahimmancin
wannan manhaja a jikin waya. To meye
tsarin mu'amala da wannan manhaja?
Da farko dai, ba kowa da
kowa za ka rubuta masa tes ba. Ya
danganci alakar da ke tsakaninka da mutum.
Idan abokinka ne, kuma ka san ya iya rubutu da karatu, kana iya rubuta
masa tes, ta amfani da dukkan dabarun gajarta rubutu (Shorthand) da ka iya;
cikin harshen hausa ne, ko Turanci, ko Larabci, ko duk wani harshe da ka san ka
iya kuma zai fahimta. Haka idan 'yan uwa
ne, musamman iyaye. Idan al'ada ne ku yi
wa juna tes tsakaninka da mahaifanka, to, kana iya musu a duk sadda ka samu
dama ko bukata ta kama. Amma idan baku
saba ba, to yana da kyau ka nemi jin ra'ayinsu kan haka, don kada ya zama ba su
so. Idan matarka ce babu matsala kana
iya mata tes, idan ka san ta iya karatu. Haka idan akwai sako mai mahimmanci
duk kana iya aika mata ta tes. Amma duk
mutumin da ka san ba zai iya fahimta ko karanta sakonka ba, bai kamata ka
rubuta masa tes ba; barnan kudi kenan da lokaci. Amma kana iya soyar masa da abin, domin ya fi
saukin ma'amala.
Sakonnin tes kamar kira ne,
suna bukatar jawabi. Duk wanda ya rubuto maka tes, idan wani abu yake
bukata na bayani, wajibi ne ka rubuta ka aika masa, muddin kana da lokaci da
kuma kudi a wayarka. Domin zai yi ta
sauraranka ne. Haka idan sako ne na
gaisuwa, yana da kyau ka rubuta masa shi ma cewa ka samu sakonsa, kuma kana godiya. Idan sako ne irin wanda ake turowa daga
wannan zuwa wancan, wato "Chain Messages" ko "Forwarded
Messages," irin wadannan sakonni suna daukan dayan fuska uku ne; na farko
su ne sakonnin addu'o'i ko hadisai ingantattu, wadandan ana iya tura wa
kowa. Idan wani ya turo maka wadannan,
kana iya masa godiya, sannan ka tura wa wani. Domin babu suna a jikinsu, kowa
na iya karantawa.
Na biyu su ne wadanda suka
kunshi fadakarwa kamar na baya, amma ta hanyar hadisan da basu inganta ba, ko
labarun da suka kunshi wasu abubuwan da shari'a bata yarda da su ba. Irin wannan idan aka turo maka, kuma ka san
kuskuren da ke cikinsu, to ba za ka tura wa wani ba. Sai dai ka fadakar da wanda ya turo maka
kuskuren da ke cikin sakon. Watakila shi
bai sani bane, shi yasa. Ma'ana fatan
alheri yake maka. Misali, kwanakin baya
akwai sako da yayi ta yawo cewa wata mata da ba musulma ba ta yi mafarkin
Manzon Allah ya umarce ta da yin wasu abubuwa, wanda bayan ta farka, sai ta
musulunta, sannan tace manzon Allah yace dole ne kowa yayi su, duk wanda bai yi
su ba, to, zai ga tashin hankali a rayuwarsa.
Wannan sakon wani mai karatu ya turo mini, sai na fadakar da shi
kuskuren da ke ciki. Na farko dai yin
mafarkin Manzon Allah abu ne mai yiwuwa.
Amma idan a cikin mafarkin aka ce wai wanda aka gani a matsayin Manzon
Allah yace a yi wasu abubuwa wadanda suka saba wa shari'a, to a nan ba za a yi
ba. Kuma hakan ke nuna cewa lallai wanda
aka gani a mafarkin nan ba Manzon Allah bane. Domin Manzon Allah ba zai taba
umartan wani daga cikin mabiyansa da wani sabon shari'a ba, ko abin da ya saba
wa shari'a ba. Shi yasa ma Malamai suka
ce duk wanda yace yayi mafarkin Manzon Allah, to sai an tambaye shi ya sifata
shi. Idan ya sifata Manzon Allah daidai
da yadda hadisai suka nuna siffarsa, to a nan sai a yarda cewa lallai shi ya
gani. Amma idan ya siffata shi da wani
siffar da ba tasa ba, to, lallai ba Manzon Allah ya gani ba. Shedan ne kawai yake wasa da shi. Sannan dukkan Malamai sun yarda cewa ba a
amfani da mafarki wajen tabbatar da shari'a sai idan abin da mafarkin ya kunsa
yayi daidai da shari'a tabbatacciya.
Idan ya saba ba za a karba ba.
Domin Annabawa ne kadai mafarkinsu ke zama wahayi, ba gama-garin mutane
ba. Sannan duk wanda ya turo maka sako
cewa ka tura wa mutane adadi kaza, idan baka tura ba abu kaza da kaza zai same
ka. Don Allah ka tambaye shi, shin,
Allah ne ya saukar da wahayi kan haka, ko Manzon Allah? Meye hujjarsa kan haka? Domin akwai masu turo wa jama'a sakon wasu
addu'o'i su ce dole a tura wa mutane kaza, wane ya tura wa wasu, ya samu
alheri, wane bai tura ba, abu kaza mummuna ya same shi. Duk wannan shirme ne. Sai a kiyaye.
Nau'i na uku kuma shi ne
sakon tes mai dauke da shagube da cin mutuncin wani, ko wasu nau'ukan mutane ba
tare da hakki ba. Kamar shugabanni, ko wasunsu.
Wadanda kuma labaru ne kirkirarru ba gaskiya bane, ana yada su ne don
nishadi. A gaskiya sakonni irin wadannan
ba a tura wa wasu. Domin akwai giba da
cin naman wani a ciki. Mu kiyaye. Kada mu dauka abin da muka fada da baki ne
kadai Allah zai kama mu da laifinsa, a a, duk wata gabar jikinka da kayi amfani
da ita wajen yada barna ko shiga hakkin wani, to sai an kama mutum da laifi a
kan haka, sai in ya tuba Allah Ya yafe.
Yana da kyau idan ka aika
sakon tes ka tabbata sakon ya isa daga jikin wayarka, ma'ana akwai sakon
isarwa, wato "Delivery Report" mai nuna cewa sakonka ya isa. Idan yana nuna yana kan hanya, wato
"Pending" to ka san cewa akwai matsalar yanayin sadarwa. Ta yiwu sakon ya isa, ta yiwu kuma bai isa
ba. In so samu ne ka sake aikawa zai fi kwanciyar hankali. A wasu lokuta kuma tana iya yiwuwa wayar da
za ta karbi sakon a kashe take. Sannan,
iya tsawon sakonka, iya yawan kudin da za a cire. Daga layin MTN zuwa wani MTN din ana cire
Naira 5 ne, a sako madaidaici kenan.
Idan ya kai shafi biyu, za a cire naira goma ne. Idan shafuka biyar ne, naira ashirin da biyar
kenan. Amma idan daga MTN zuwa wani layi
ne daban, misali zuwa Etisalat, za a cire maka naira 10 ne a shafi daya. A shafuka biyar kuma naira 50. Haka abin yake a sauran layuka.
Daga cikin 'yan kananan
matsalolin da ake samu wajen aika sakonnin tes akwai matsalar lambar cibiyar
sadarwa, wato "Center Number."
Kowane kamfanin waya na da lambobi na musamman da ake amfani da su wajen
aiwatar da sadarwa tsakanin wata waya da wata wayar salula ta hanyar manhajar
SMS. Wadannan lambobi dai guda 13
ne. Misali, na kamfanin Etisalat su ne:
+2348090001518, na kamfanin MTN kuma: +234803000000, na kamfanin kuma su ne: +234802000009. Wadannan lambobi ana samunsu ne a bangaren
tsare-tsaren aika sakonnin SMS na jikin kowace wayar salula, wato "Message
Settings." Sai dai kuma, ba da su
wayar ke zuwa ba. Asali suna cikin katin
SIM ne. da zarar ka shigar da katin SIM
a cikin wayar da ka sayo, nan take sai wayar ta nado su, don taimaka maka
aiwatar da sadarwa cikin sauki.
Duk sadda kayi ta kokarin
aika sakonnin tes, ana ce maka ba a samu, alhali a jikin wayarka ta nuna an
aika, to, hakika akwai matsalar lambobin cibiyar aika sakonni. Ta yiwa sadda kake wasa da wayar a wasu
lokuta ko yara sun dauka suna ta tabe-tabe, har suka goge lamba ko sama da haka
daga cikin lambobi 13. Muddin basu cika 13 ba, ko kuma aka goge wani aka sa
wanda ba daidai ba, har abada ba za ka iya aika sakonnin tes ba. Sai a kiyaye.
Amma idan aka duba aka tabbatar da lambobin daidai suke, kuma ga sakonni
sun ki zuwa, to, akwai matsalar yanayin sadarwa (Network Problem), ko kuma babu
isasshen kudi a wayar. Sai a rika lura.
A karshe, yana da kyau mai
karatu ya lura cewa, sakonnin tes sun fi kira irin na murya hadari idan lalura
ta taso. Da farko, da zarar ka matsa
"Send", sakon ya tafi. Ko da
kuwa ka ga an rubuta: "Sending", watakila kace bari in tsayar, aikin
banza ne. Kai, ko da cire batirin wayar
kayi a yayin da ake aikawa, duk aikin banza ne.
Sakon ya riga ya tafi tuni. Idan
ka aika sako, ana iya ciro sakon daga kwamfutocin kamfanin wayarka a kowane
lokaci ne. Sannan ko da kuwa ka goge
sakon a wayarka, yana nan a jikin kwamfutocin kamfanin waya. Za a iya ganinsa, tare da lokacin da ka aika,
da kuma mizanin sakon, da lokacin da sakon ya dauka kafin ya isa wayar wanda
aika masa. Don haka sai a kiyaye wajen
rubuta abin da za a aika.
Cikin shekarar da ta gabata
ne aka gabatar da wani kuduri a majalisar dattawa na kasa, wadda ke neman
majalisar ta amince a rika amfani da sakonnin tes da na Imel a matsayin sheda a
kotu. Har yanzu ba a gama tattaunawa kan
wannan kuduri ko ba. Idan aka amince da
wannan kuduri, hakan zai nuna cewa sakonnin tes sun zama amintacciyar hanyar
tabbatar da hujja kenan a kotu a ko a wajen jami'an 'yan sanda.
Mu'amala da Fasahar Intanet
Daga cikin hanyoyin aiwatar
da sadarwa da samun bayanai a wayar salula musamman irin na zamani, akwai
fasahar Intanet. Wannan fasaha ce mai
tasiri matuka a duniya yanzu. Farkon
bayyanar fasahar Intanet ta ta'allaka ne
kawai da kwamfuta. Ma'ana, ta hanyar
kwamfuta kadai ake iya mu'amala da fasahar.
To amma shekaru kasa da 15 da suka gabata zuwa yau, an samu hanyoyin
ginawa da kuma bayyana shafukan Intanet ta wayar salula, cikin sauki, da kuma
inganci. Wannan hanya tana da matukar
muhimmanci sosai. Domin mai waya zai iya
karanta labarai, da taskance su, da kuma ganinsu, duk ta wayarsa. Sannan zai iya aika sakonnin Imel ta wannan
hanya, da kuma karban sakonnin, duk ta wayar salalularsa. Hakan na yiwuwa ne dangane da yanayin girma,
da fadi, da kuma ingancin wayarsa.
Kafin a iya mu'amala da
fasahar Intanet a wayar salula, dole ne ya zama tana da ka'idar sadarwar wayar
iska ta Intanet, wato "Wireless Application Protocol," ko
"WAP" a gajarce.
Wannan ka'ida
ce ke taimakawa wajen hada alaka tsakanin wayar salula da giza-gizan sadarwa na
duniya, wato: "World Wide Web."
Kana iya gane hakan idan ka je "Menu", ka gangara kasa, ka ga
"Web" ko "Internet" ko kuma "Browse." Ya danganci tsarin wayar da kamfanin da ya
kera. Da zarar ka ga tambari mai dauke
da dayan wadancan tambari guda uku, to lallai wayar za ta iya shawagi a
giza-gizan sadarwa na duniya. Daga nan
kuma sai abu na uku, wato kudin lilo da tsallake-tsallake. Ma'ana, ya zama akwai kudi a cikin
wayarka. Domin da zarar ka shiga
Intanet, nan take kamfanin waya zai fara diban nasa rabo daga abin da ke cikin
taskar ajiyarka a waya.
Abu na karshe da ake bukata
kafin iya mu'amala da fasahar Intanet a waya shi ne, tsare-tsaren kamfanin
sadarwa, wato: "Network Configuration," ko kuma "Configuration
Settings." Wannan kuma daga
kamfanin waya ne. Galibin lokuta wayar salula kan karbi wadannan tsare-tsare ne
daga kamfanin waya kai tsaye, da zarar ka shigar da katin SIM cikin wayarka a
karo na farko, ko a duk sadda ka cire ka sake mayarwa. Musamman ma katin SIM din kamfanin Etisalat. Haka ma na MTN ko Glo ko Airtel. To amma idan wayarka 'yar kasar Sin ce, wato:
"China Phone," wannan kam dole sai an sa wadannan tsare-tsare da
hannu, wato: "Manual Configuration."
Duk da cewa akwai wayoyi irin na kamfanin TECNO wadanda ke iya karbar
wadannan tsare-tsaren kamfanin waya kai tsaye.
To, amma idan aka yi rashin sa'a ba ta karba kai tsaye ba, ta kuma iya
sarrafa su ba, to dole sai an dangana da masu gyaran waya don su taimaka su
shigar da hannu.
Sannan kana bukatar
adireshin gidan yanar sadarwar da za ka shiga, muddin ta waya ne. Wannan ya danganci bukatarka. Illa dai, galibin gidajen yanar sadarwar da
ake shigansu ta wayar salula adireshinsu kan canza. Misali, idan kana son shiga shafin Dandalin
Facebook ta waya, adireshin shi ne: www.facebook.com/mobile, ko
kuma http://m.facebook.com. Amma asalin adireshin shi ne: www.facebook.com. To amma idan ka shigar da na asalin ma, nan
take ka'idar da ke lura da aiwatar da sadarwa ta wayar salula za ta fahimci
cewa ta waya kake kokarin shiga, nan take kuma za ta karkatar da kai zuwa
shafin da ya dace da fuskar wayar salula idan har gidan yanar sadarwar da kake
kokarin shiga ya tanadi shafi makamancin haka.
A Najeriya kamfanonin waya
na da gidajen yanar sadarwarsu, inda za ka iya shiga daga wayar salularka, don
mika kokenka ko kuma amfanuwa da masarrafan da suka tanada wa masu mu'amala da
katinsa. Har wa yau, wasu kamfanonin
(kamar Etisalat) sun tanadi masarrafar mu'amala da Dandalin Facebook na
musamman, don masu amfani da katinsa.
Idan kana amfani da layin Etisalat ne, da zarar ka shiga shafin www.facebook.com/mobile ko http://m.facebook.com nan
take za a ce maka, ka saukar da manhajar Facebook na musamman don mu'amala da
fasahar Intanet ba tare da ka kashe ko sisin kwabo ba. Suna yin haka ne don sawwake wa masu amfani
da waya hanyoyin ta'ammali da fasahar Intanet.
Kamar sauran ayyukan waya
masu bukatar yanayin sadarwar kamfanin waya, mu'amala da fasahar Intanet a
jumlace, ba kyauta bane. Idan ka sa kudi
a cikin katin wayanka, ka fara shiga shafukan Intanet, za a fara cire kudi ba
kakkautawa. Iya yawan shafukan bayanan
da ka budo a shafukan da ka ziyarta, iya yawan kudin da za a cire. Idan shafukan da ka shiga akwai hotona da
bidiyo, to, za a cire kudi mai dimbin yawa.
Domin hotuna da bidiyo suna wakiltar mizanin bayanai ne mai yawa,
musamman ma dai bidiyo. Haka ma
sauti. Idan ka shiga shafin BBC harshen
Hausa ka fara sauraren shirye-shiryensu, za a cire maka kudi sosai. Sai ka shirya.
Sai dai kuma ta la'akari da
ganin cewa jama'a kan so mu'amala da fasahar Intanet amma suna tsoron yawan
kudin da za a cire musu, kamfanonin waya a Najeriya sun bullo da tsare-tsare
daban-daban. Misali, kamfanin MTN kan
bayar da kyautar mizanin bayanai miliyan goma (10MB) a duk sadda ka loda katin
400 misali. Kamfanin Etisalat ya bullo
da tsarin EasyMega, inda za ka sa naira dubu daya, ka shigar, sai a baka
mizanin bayanai miliyan 500 cikin wata guda.
Ko ka sa naira 500, a baka mizanin bayanai miliyan 200 a wata guda. Haka
akwai tsarin da idan ka sa katin 200 a duk mako, kamfanin zai baka kyautar
mizanin bayanai miliyan 15 a mako guda.
Duk wadannan tsare-tsare ne da suka bullo da su don saukake mu'amala da
fasahar Intanet ta wayar salula, kuma don su ma su samu yawaitan kwastomomi
cikin sauki. Hanyar kasuwanci ce.
Sai dai ba kowace waya ce za
ka iya mu'amala da fasahar Intanet don kawai kana da kudi a katin wayarka
ba. Wayar salula nau'in BlackBerry suna bukatar
tsari ne na musamman; irin tsarin da ake kira BlackBerry Internet Service
(BIS), kamar yadda bayanai suka gabata a baya. Ma'ana, ko naira miliyan daya kake da shi a
katin wayarka ba za ka iya mu'amala da Intanet ba sai ka nemi kamfanin waya ya
dora ka kan tsarin BIS, sai ya zare kudin daga katin wayarka, sannan ya
dora ka a kan tsarin. Misali, kamfanin
Etisalat na karban naira 3,000 ne a duk wata kan tsarin BIS. Idan ka sa kudin a katin wayarka, sai ka
matsa *499*1 sai hash. Da zarar ka sa za
su zare kudin, sai su mika lambar wayar BlackBerry dinka ga kamfanin Research
In Motion (RIM), wato kamfanin da ke kera wayoyin kenan, don ya jona ka. Idan kayi rajista a wannan tsari, za ka iya
mu'amala da fasahar Intanet a kowane lokaci, na tsawon lokacin da kake so, har
na kwanaki 30, ba tare da tsangwama ba.
Babu iyaka kan mizanin bayanan da za ka yi ta'ammali da su. Da hotuna, da bidiyo, da sauti, duk kana iya
mu'amala da su, wajen gani, da saurare, da saukarwa a wayarka duk sadda ka so. Haka idan wayarka irinsu iPhone ne, kana iya
zuwa kamfanin wayarka, sai su dora ka kan wani tsari na musamman da zai sawwake
maka kudin mizanin bayanai, don ka amfana da wayar sosai.
Idan ana ta'ammali da
fasahar Intanet a wayar salula ya kamata a lura da wasu abubuwa masu
muhimmanci. Abu na farko shi ne, ba
kowane shafin Intanet ya burgeka za ka kutsa ciki ba. Akwai shafukan da ke dauke da kwayoyin cutar
wayar salula, wato "Virus."
Idan kayi rashin sa'a ka samu kanka a cikin shafi irin wannan, yana iya
gurbata maka ma'adana da masarrafar wayar salularka; ta rikice, ka kasa sarrafa
ta. Sannan ba lale bane ka san dalili. Haka za ka yi ta jele tsakanin masu gyaran
waya da masu sayar da kayayyakinta, ba kowa zai iya gano abin da ke damunta
ba. Sai ka gama kashe kudi wajen masu
gyara a karshe ace maka ai ga abin da ke damunta. Abu na biyu shi ne, ba kowane
bidiyo, ko hoto, ko kuma shafi ya burgeka za ka saukar (Downloading) a wayarka
ba. Akwai hoton da shi kanshi kwayar
cuta ce. Saukar da shi a ma'adanar
wayarka hadari ne ga rayuwarta baki daya.
Wasu cikin matasa kan saukar
da hotunan taurarin fim na kasashen waje, irin su Angelina Jolie, ko Meena ko
Solomon Khan 'yan kasar Indiya, ko Rambo da dai sauransu, zuwa wayarsu, don
kawata wayar, da nuna cewa lallai suna sonsu.
Abin da ke faruwa shi ne, galibin masu gina manhajar kwayar cutar
kwamfuta don sharri a Intanet ko don leken asiri, sukan kirkiri masarrafa na
musamman ne don yin hakan, amma kai za ga hoto ne, ba jakar bayanai irin wacce
aka saba gani a matsayin masarrafa ba.
Idan ka dauki irin wannan hoto ka loda wa wayarka, sai Allah. Sai a kiyaye.
Abu na uku, ga masu mu'amala da jama'a a Dandalin Abota musamman na
Facebook, kun dai ji irin abin da ke faruwa, musamman lamarin wata matashiya
'yar wani babban hafsan Soji da aka kashe kwanakin baya a Legas, duk ta
Facebook aka fara alakar. Ba kowane
mutum za ka yi abota ta kut-da-kut da shi ba, ko kawance na kut-da-kut da ita
ba. Ya kamata ka san waye shi ko ita tukun, kafin a kai ga matsayin
aminantaka. Matsalar matasanmu ita ce,
muna da saurin amincewa mutane, musamman mata dai. Irin wannan matsala ce mai girma. Musamman ga mutumin da baka taba gani ba,
baka taba sanin hakikaninsa ba, sannan baka gamsu da dabi'unsa ba. Ba cewa ake ka zargi duk wanda ka gani ba, a
a.
Abu na hudu shi ne, mu
kiyayi bata lokacinmu wajen rubuta zantukan da ba su da amfani a shafinmu na
Intanet ko na Facebook. Wannan bai
kamaci mai hankali ba. Ace ka bata
lokaci kana ta surutai marasa amfani gare ka da sauran jama'a. Ka sani, a lokacin da kake hakan, kana bata
lokacinka ne, wanda ba zai taba dawowa ba.
Kana bata batirin wayarka ne, wanda ba za ka kara dawo da shi ba. Kana kuma bata ingancin rayuwarka ne, wajen
salwantar da fahimtar da ta kamata a ce ka ciyar wajen ciyar da kanka ko
al'umma gaba. Sai mu kiyaye.
Mu'amala da Fasahar
Bluetooth
Daga
cikin nau'ukan hanyoyin sadar da bayanai ta wayar salula masu matukar tasiri,
akwai fasahar sadarwa ta Bluetooth.
Kusan duk mai amfani da wayar salula a Najeriya yanzu ya san fasahar
Bluetooth, ko da a baki ne. Kuma duk da
cewa muna yawan amfani da wannan fasaha wajen aika sakonni musamman lambobin
waya da sauti da kuma bidiyo, kadan daga cikinmu ne suka san asalin wannan
fasaha da tsarin mu'amala da ita. A shekarun baya mun gabatar da kasidu guda
biyu kan fasahar Bluetooth, a yau ma ga mu dauke da takaitattun bayanai kan
fasahar, da tsarin amfani ita.
A kimiyyance dai, idan aka ce “Bluetooth”, musamman ma a
wannan zamani namu, ana nufin wani tsari ne ko fasahar sadarwa da ke kunshe
cikin kayayyakin sadarwa na zamani irin su wayar salula da sauran na'urorin
sauraren wakoki da sarrafa bayanai (kamar iPod, da iPad), wanda ake iya aikawa
ko karban jakunkunan bayanai da suka shafi haruffa da sauti da murya (irin na
wakoki da karatuttuka da laccoci) ko hotuna; masu motsi (Video) ko daskararru,
a tsakanin wadannan kayayyakin sadarwa. Wannan ita ce ma’anar “Bluetooth” a
fayyace. Sadarwa a tsarin Bluetooth na
yiwuwa ne ta hanyar neman wayar salular wanda kake son aika masa, a iya tazaran
da bai wuce taku talatin ba (30ft), ko kuma nisan mita goma (10
meters). A iya wannan tazara, idan
ka kunna fasahar Bluetooth din ka, to duk wanda nasa ke kunne a iya
kadadar wannan tazara ko zango, za ka same shi da zarar ka nemo, har kuma ka
iya aika masa da sako. Wannan fasahar
sadarwa ta samo asali ne shekaru kusan 13 da suka gabata, lokacin da wasu
kamfanonin kayayyakin fasahar sadarwa guda biyar suka kafa wata kungiya na masu
sha’awar ci gaban yadawa da kuma sawwake hanyar sadarwa a tsakanin kayayyakin
sadarwa, mai suna Special Interest Group, ko SIG a takaice. Sun yi haka ne cikin shekarar 1998. Kuma a karshen shekarar 1999 ne suka cin ma
matsaya kan wannan fasahar sadarwa, inda suka zabi sunan wani sarki da yayi
zamani a karni na goma a nahiyar Turai mai suna Harold Bluetooth, suka
ba wannan sabuwar hanyar sadarwa da suka kirkira. To me ye dalilin zaban sunan wannan sarki?
Shi dai Sarki Harold Bluetooth, wani basarake ne da yayi
rawan gani a tsakanin kasashen Turai wajen iya sasanta kasashe lokacin
yaki. Rawan ganinsa na karshe shi ne
wanda ya taka wajen sasanta kasar Norway da Sweden bayan sun
dauki tsawon shekaru suna gwabza yaki a tsakaninsu. Ta la’akari da tsarin hada alaka wajen karba
da mika bayanai a tsakanin kayayyakin fasahar sadarwa, wanda kuma shi ne aikin
wannan sabuwar fasaha da kungiyar ta kirkira, sai ta zabi kiran wannan sabuwar
fasahar sadarwa da sunan wannan sarki.
Babbar ka’idar da ke lura da wannan sadarwa, a kimiyyance ita ce
ka’ida ta 802.15.1, wacce Cibiyar Injiniyoyin Lantarki ta kasar Amurka, wato IEEE
(Institute of Electrical and Electronics Engineers) ta kirkira cikin
shekarar 1994. Wannan Cibiya ita ke da
alhakin tsarawa da kuma kirkiran ka’idojin sadarwa a tsakanin kayayyakin
fasahar sadarwa na tafi-da-gidan ka (Mobile Devices) masu amfani da
tsarin sadarwar wayar-iska, wato Wireless Communication, a duk duniya.
Fasahar sadarwa ta Bluetooth ta shahara sosai a duniya, kuma babban dalili shi
ne kasancewarta a jikin wayoyin salula.
Kamar yadda bayani ya gabata a sama, wannan fasahar sadarwa an
kirkiro ta ne cikin shekarar 1998, aka kuma lakkaba mata sunan wannan sarki a
karshen shekarar 1999. Daga nan aka fara kiran wannan kungiya ta kamfanonin
sadarwa da sunan Bluetooth Special Interest Group (Bluetooth SIG), wato
kungiyar masu kebantacciyar sha’awar bunkasa fasahar Bluetooth. Mambobinta na asali guda biyar ne, amma kafin
karshen 1999, sun kai 400. A farkon
shekarar 2000 sai aka fitar da nau’in farko na wannan fasahar sadarwa, wato Bluetooth
v1.0, wanda aka fara shigarwa cikin wayoyin salula a shekarar 2001. Cikin wannan shekara ne kuma aka shigar da
fasahar cikin beran kwamfuta, wato Computer Mouse, da kwamfutar
tafi-da-gidanka, wato Laptop, da hanyar shigar da bayanai na tsarin Universal
Serial Bus (ko USB Port).
Wannan shekara ta 2001 bata karkare ba sai da aka kirkiri rediyon kunne,
wato Headset mai dauke da wannan fasaha ta Bluetooth.
Ana shiga shekarar 2002,
sai ga na’urar buga bayanai ta kwamfuta, wato Computer Printer, mai
dauke da fasahar Bluetooth, da kuma na’urar daukan hoto ta zamani, wato Digital
Camera, ita ma dauke da wannan na’ura.
A wannan shekara ne har wa yau, aka kaddamar da wannan kungiya ta Bluetooth
SIG. Da aka shiga shekarar 2003, ai sai zamani ya ci
gaba da bin fasahar Bluetooth, sau-da-kafa. Sai ga na’urar sauraran wake
ta zamani, wato MP3 Player, ita ma dauke da wannan fasaha ta Bluetooth. A wannan shekarar ne aka fitar da wani sabon
nau’in wannan fasaha, wato Bluetooth v1.2. A karshen shekara, sai aka lura cewa a duk
mako, akan fitar da kayayyakin fasahar sadarwa masu dauke da wannan fasaha a
kalla miliyan daya. Wannan ya nuna
tsananin tasirin wannan fasaha da karbuwan da ta samu.
Da aka shigo sabuwar shekarar 2004, sai kungiyar Bluetooth SIG
ta fitar da sabon nau’i mai taken Bluetooth v2.0, wanda ingancinsa wajen
sadarwa ya dara nau’ukan baya. A wannan
shekara ne aka tabbatar da cewa akwai a kalla kayayyakin fasahar sadarwa masu
dauke da wannan fasaha ta Bluetooth sama da miliyan 250, kuma a duk mako a
kalla akan fitar da sababbin kayayyakin fasahar sadarwa dauke da Bluetooth,
sama da miliyan uku. Kafin shekarar ta
kare kuma, aka kirkiri rediyon kunne irin na zamani, wato Stereo Headphones,
su ma dauke da wannan fasaha ta sadarwa. Da shekarar 2005 ta kunno kai sai aka
samu kari wajen yawan kayayyakin fasahar sadarwa da ake kerawa da fitarwa a duk
mako, daga miliyan uku a shekarar 2004, zuwa miliyan biyar. A wannan shekara ne yawan kamfanonin sadarwa
da ke kungiyar Bluetooth SIG ya cika dubu hudu, daga dari hudu da ake
dasu a karshen shekarar 1999. Har wa
yau, cikin wannan shekara ne aka kaddamar da manyan cibiyoyin wannan kungiya ta
Bluetooth SIG a manyan birane/kasashe hudu; da Washington, da Malmo,
da Sweden, da kuma Hong Kong.
Kafin shekarar ta yi wafati, sai ga kirkirarren gilashin ido, wato Sunglass,
shi ma dauke da wannan fasaha ta Bluetooth. Babban Magana, wai dan sanda ya ga gawar
soja!
Da aka shigo shekarar 2006, ai sai ga agogon hannu, shi ma dauke da
wannan fasahar sadarwa. A shekarar ne
har wa yau aka tabbatar da cewa akwai kayayyakin fasahar sadarwa a kalla
biliyan daya da ke dauke da wannan
fasaha ta Bluetooth, kuma a kalla duk mako ana kerawa da kuma fitar da
kayayyakin fasahar sadarwa miliyan goma, masu dauke da wannan fasaha. Wannan ke dada nuna mana irin karbuwa da kuma
habbaka da wannan fasahar sadarwa ke samu kuma take yi a duniya. A karshe dai, ana shiga shekarar 2007, sai
aka kirkiro akwatin talabijin mai dauke da wannan fasaha. A shekaran ne mambobin wannan kungiya ta Bluetooth
SIG suka cika dubu tara, daga dubu hudu da aka samu a shekarar 2005. An
kuma tabbatar da cewa a duk mako akan samu a kalla kayayyakin fasahar sadarwa
miliyan 800 da ake kerawa ko fitarwa kasuwa, masu dauke da wannan fasaha ta Bluetooth. Kusan kashi saba’in na wadannan kayayyakin
sadarwa, wayoyin salula (Cell phones) ne da kuma na’urar sauraron wakoki
irin na kunne, wato Headset. Cikin wannan shekara ne dai har wa yau, aka
fitar da wani sabon nau’i, wanda ya kere nau’ukan baya wajen ingancin sadar da
bayanai. Wannan nau’i shine Bluetooth V2.1, kuma tsari da kuma kimtsin
da aka yi masa na dauke ne cikin wani kundi mai shafuka 1,400 da ‘yan kai. Kuma zuwa karshen shekarar 2007 ne kungiyar
ta kaddamar da mujallarta mai suna SIGnature Magazine, wanda ke fitowa a
duk bayan watanni uku. Ta kuma yi wannan
sanarwa ne a babban taronta na shekara-shekara da take yi, wanda aka yi a
birnin Vienna, babban birnin kasar Austria.
Akwai ka’idoji masu
dama da suka shafi tsarin sadarwa ta Bluetooth, amma guda hudu kawai za
mu kawo, don su ne masu siffata mana mafi karancin tsarin da ake bukata kafin
hada alaka a tsakanin kayayyakin fasahar sadarwa masu dauke da Bluetooth. Da farko dai, wannan fasahar sadarwa na
amfani ne da tsarin aikawa da sakonni ta siginar rediyo, wato "Radio
Frequency Waves" (RFW), wanda a ilimin fasahar aikawa da sakonni ta
zamani ake wa lakabi da "Spread Spectrum." Wannan tsari na "Spread
Spectrum" shi ne tsarin da ke aikawa da sakonni ta hanyar nemo siginar
rediyon mai alaka da abokin huldansa, daga mafi karancin zango, sai ya yalwata
siginar zuwa zango mafi fadi don sawwake hanyar sadarwan. Wannan tsari na dauke da manyan ka’idoji guda
hudu da ke sawwake wannan sadarwa; akwai
"Baseband Protocol" (BP), wato ka’idar da ke haddasa samuwar
siginar rediyo (Radio Frequency Waves) don tabbatar da yanayin sadarwa a
lokacin da mai son sadarwa ke bukata.
Hakan kuma na faruwa ne daga lokacin da ka kunna na’urar Bluetooth
da ke jikin wayar salularka, don nemo abokin hulda da ke da wannan tsari a
wayarsa.
Sai ka'ida ta biyu,
wato "Link Manager Protocol" (LMP), wadda ke yin aikinta da
zarar "Baseband Protocol" ta gama nata aikin. Shi Link Manager Protocol aikinsa shi ne
haifar da sadarwa a tsakanin wayar salula da wata wayar mai dauke da Bluetooth,
don tabbatar da tsarin sadarwan. Wannan
ka’ida ce har wa yau ke tabbatar da tsaro ga jakar bayanai da ake son aikawa a
tsakanin kayayyakin fasahar sadarwan biyu.
Daga nan kuma sai ka’ida ta gaba, wato "Logical Link Control
& Adaptation Protocol" (L2CAP), wacce ke kacalcala bayanan da ake
son aikawa daga wayar da ake son aikawa da su, zuwa irin yanayin da suka dace a
aika dasu. Idan masu karatu basu mance
ba, wannan aiki shi kwamfuta ke yi a zangon Presentation Layer, kamar
yadda bayani ya gabata a kasidar Tsarin Aikawa da Sakonni a Tsakanin Kwamfutoci
(2). Za a kacalcala bayanan ne, don
sawwake tsarin aikawa dasu. Da zarar sun isa masaukinsu a daya bangaren, akwai ka’idar da za ta gyatta
su zuwa yanayinsu na asali. Har wa yau,
wannan ka’ida ce ke tabbatar da samun yanayin aikawa da sako mai inganci.
Sai kuma ka’ida ta
karshe, wato "Service Discovery Protocol" (SDP), wacce ke
zakulo maka dukkan wata wayar salula da ke dauke da fasahar Bluetooth da
zarar ka nemo, ta kuma nuna maka sunan da mai wayar ya bata ko kamfanin da ya
kirkiri fasahar ya bata. Wannan ka’ida ce ke
hada alakar idan ka zabi wacce kake son aika mata. Misali idan akwai wayoyin salula guda biyar
masu kunne da Bluetooth a yayin da kake neman abokin huldanka, za ka
gansu duka, da sunayen su, sai ka zabi wacce kake son hulda da ita. Idan ka zaba, wannan ka’ida ce ke yi maka
barbaran wacce kake nema, kai tsaye.
Wadannan, a takaice, su ne shahararrun ka’idojin aikawa da kuma karban
sakonni ta hanyar sadarwa ta Bluetooth, a kimiyyance. A yanzu ga yadda yanayin ke kasancewa, a
zahiri.
Tsarin aikawa da sako ta hanyar Fasahar
Bluetooth abu ne mai sauki. Idan kana son aikawa da sako ta Bluetooth,
abu na farko shine “neman” wayar salular da kake son aika mata da sakon. Wannan shi ake kira Searching, a turancin
fasahar sadarwa. Da zarar ka yi wannan,
ka’idar da ke lura da wannan aiki zata nemo maka wadanda ta hararo maka su, kai
tsaye. Dole ya zama suna tazarar da bai
wuce taku talatin ba (30 Feets) ko mita goma (10 Meters) daga
inda kake. In sun wuce wannan tazara, ba
za ka taba hararo su ba. Idan aka hararo
maka su, za ka samu bayanan da suke dauke dasu, ko kuma sunayen da masu su suka
basu. Da zarar ka nemo wayar da kake son
hulda da ita, sai ta sanar da mai wayar cewa ana neman sa, sai ya amince, ta
hanyar matsa “Accept”. Idan ya amince
maka, sai wayarka ta nemo ka’idojin da suka dace ta bi wajen aika sakon, ta
kuma lika wa wannan waya da ta barbaro, alamar da za ta sheda ta wajen aika
mata sakon.
Daga nan, sai kuma ta kara binciko cikin wancan
wayar, don tabbatar da dacewa da wannan alama da ta lika mata. A ka’ida, dukkan wayar salula ko kayan
fasahar sadarwar da take iya saduwa da wata ta wayar iska, na dauke ne da suna
da ke cikin rukunin lambobi, wanda ta kebanta dasu; kamar yadda kwamfuta ke
dauke da lambobin IP, wato Internet Protocol Address. To idan wayarka ta nemo sunan wannan waya da
take son saduwa da ita, ta tabbatar da sunanta, sai ta bata suna na musamman,
sannan sai ta nemo kogo (Port) mafi sauki da za ta iya aikawa da sakon,
ba tare da mishkila ba. Da zarar ta nemo, sai ta
fara barbara, don sheida wa wancan wayar salula, cewa ‘gani nan tafe’. Idan aka amsa mata, sai ta fara aikawa, kai
tsaye. Idan ta gama aikawa, sai ta rufe
wannan hanya, tare da yanayin sadarwan. Ita kuma wacce ake barbara, da zarar
sakon neman alfarma ya zo mata, sai ta taimaka wajen nemo ka’idar da za ta yi
wannan aiki na karban sako. In ta nemo, sai kuma ta zabi kogon (Port) da
zai karbi wannan sako, don shigar mata.
Gama wannan aiki ke da wuya, sai ta fara sauraron sakon. Da zarar an turo, sai ta karba kai
tsaye. Idan sakon ya shigo kogon da aka
tanada masa kafin zuwa, sai ita wannan waya da ta karba ta rufe kofofin da ta
bude da farko, don cika sadarwa. Duk
wannan na faruwa ne cikin lokacin da bai wuce dakiku ashirin ba. Illa kawai aikawa da sakon ne ya danganta da
yawan mizanin sakon; idan mai yawa ne, zai dauki lokaci. Idan kuma kadan ne, nan da nan sai a gama. Wannan tsari na aikawa, a yayin da ake aikawa
din, shi ake kira Pairing, ko kuma Point to Point Communication
(ko P2P, a lafazin ilimin aikawa da sako ta zamani.
Daga cikin alfanun da ke tattare da fasahar sadarwa ta Bluetooth
akwai saukin aikawa da sakonni ba tare da ka kashe ko sisi ba. Ko da babu taro
a wayarka kana iya aikawa da sakonni.
Abu na biyu shi ne, kana iya aikawa da lambobin waya ga wani ta hanyar
fasahar Bluetooth. A daya bangaren kuma,
fasahar Bluetooth na iya maye maka gurbin masarrafar MMS, wajen aikawa da
lambobi, ko aikawa da hotuna, ba sai lalai ta hanyar MMS ba, wanda hakan zai iya
ci maka kudi, musamman idan wanda za ka aika masa a kusa yake da kai. Har wa
yau, fasahar Bluetooth na iya hada ka mu'amala wajen musayar bayanai da wasu
kayayyaki ko na'urorin sadarwa masu dauke da fasahar, a iya tazarar da hakan
zai iya faruwa. Misali, idan kana da
wayar salula mai dauke da wakoki ko karatuttuka ko wasu jakunkunan bayanai na
sauti da kake son saurare alhali kana tuki ko kana wani abu daban da ba ya
bukatar shagala, kana iya samun lasifikar mota mai dauke da fasahar Bluetooth
sai kawai ka nemo lasifikar ta wayar, ka saurari duk abin da kake son saurare
ba tare da matsala ba. Haka idan kana
son buga wasu hotuna da kake dasu a wayarka, kana iya amfani da na'urar dab'i
mai fasahar Bluetooth (Bluetooth Printer), daga inda kake zaune, ka buga dukkan
hotunan da kake son dabba'awa, ko bugawa ba tare da matsala ba.
A duk sadda ka nemi wayar wani ta wayarka don musayar bayanai da
wayarsa, wajen karba ko aikawa, kuma ka kasa samunsa, ta yiwu bai kunna fasahar
Bluetooth dinsa bane. Idan har a kunne
take, to, watakila tazarar da ke tsakaninku ta wuce mita 10, sai a lura. Idan tazarar ba ta wuce mita 10 ko taki 30
ba, to ta yiwu akwai matsala da dayan wayoyin biyu. Sai kowannenku ya kashe fasahar Bluetooth dinsa,
ya sake kunnawa. Idan abin ya ki, a
kashe wayar a sake kunnawa. Duk yadda
aka yi sai an dace. Idan aka gano wacce
ke da matsala daga cikin wayoyin biyu; an kashe Bluetooth an sake kunnawa, bai
yi ba. An kashe wayar, an sake kunnawa,
abu bai yi ba, to, akwai matsalar da ke da alaka da babbar manhajar wayar. Don haka sai a goge tsare-tsaren wayar ta
hanyar "Resetting." A
je "Menu," a gangara "Security," sai a karaso "Factory
Settings." Idan aka matsa eh, wayar
za ta koma sabuwa kamar yadda aka siyo ta.
Duk tsare-tsaren da aka mata za su share, amma lambobi da bayanan sauti da bidiyo suna nan lafiya lau. Amma duk hoton da ka sa a fuskar wayar zai
share. Haka duk muryar da ka sa a
matsayin sautin wayar (Ringing Tone), zai share. Da haka in Allah Ya so fasahar Bluetooth din
za ta dawo yadda take, kamar yadda aka siyo wayar a farkon lokaci. A gaskiya
fasahar Bluetooth na cikin masarrafan da basu cika samun matsala ba a wayar
salula, duk yadda aka kai da amfani da su kuwa.
Sai dai idan mutum ya cika tsokale-tsokale a wayarsa. Bayan tsarin aika sakonni na SMS, fasahar
Bluetooth na biye wajen inganta karbuwar wayar salula a hannun jama'a a duniya
baki daya.
Mu'amala da Fasahar Infra-red
Kafin bayyanar fasahar sadarwa ta Bluetooth tsakanin shekarar 1998
zuwa 1999, galibin wayoyin salula na amfani ne da fasahar sadarwa ta Infra-red,
wadda ita ma mun gabatar da kasida guda tun shekaru 4 da suka gabata a wannan
shafi. Duk da cewa a yau an daina kera
wayoyin salula masu fasahar Infra-red, amma har yanzu akwai wasu da ke dauke da
masarrafar, wadanda aka kera a baya. Ko
da ma babu su, ilimi dai ba ya tsufa.
Kalmar Infra-red dai kalma ce mai tagwayen bangarori biyu da
aka kago daga harshen Latin da Turancin Ingilishi. Kalmar Infra, Latin ce, kuma tana
nufin "Kasa da…", kalmar Red kuma kamar yadda muka sani,
harshen Turanci ce da ke nufin "Launin Ja…". Abin da wannan ke nufi shi ne, Infra-red fasahar
sadarwa ce da ake amfani da ita wajen aiwatar da sadarwa ta hanyar launi kasa
da launin ja. Wannan launi kuwa na
samuwa ne a jerin launuka bakwai da ke tsarin maimaituwan haske da ake kira Electromagnetic
Wave, a harshen kimiyyar Fiziya na zamani.
An fara amfani da wannan nau’in sadarwa ne a kayayyakin fasahar
sadarwa cikin shekarar 1994, amma kafin
nan, ana amfani da ita ne wajen kera na’urar hangen nesa, da wajen magance
cututtuka da kuma daukan hotuna daga sararin samaniya. Haka ma na’urar Remote
Control da muke amfani da ita wajen sarrafa akwatin talabijinmu, duk da
makamashin Infra-red aka gina ta. A
takaice ma dai, bayanai sun nuna cewa an yi amfani da makamashin Infra-red
cikin yake-yaken da aka yi ta gwabzawa a yakin duniya na biyu. Hukumar da ta
kirkiro wannan tsari na kayan fasahar sadarwa kuma ita ce Infra-red
Development Association (IrDA). An
shigar da nau’in fasahar Infra-red cikin kayayyakin fasahar sadarwa irin su
wayar salula; kana iya aikawa da sakonnin lambobin waya da katittika daga wayarka
zuwa wayar abokinka; kana iya aikawa da hotuna, da kuma jakunkunan sauti na
wakoki ko karatuttuka da sauran bayanai.
Haka ma an shigar da wannan nau’in sadarwa cikin na’urar daukan hoto ta
zamani (Digital Camera). Bayan ka
dauki hotuna, kana iya aikawa da su ta wannan hanya; kana iya aikawa dasu cikin
kwamfutarka, ko kuma na’urar sawwara hotuna ko bayanai, wato Scanning
Machine, don ta bugo maka su waje ka gani.
Haka na’urar sawwara hotuna daga ma'adanansu ta asali zuwa bayanai na
haske, wato Scanning Machine, tana dauke da wannan fasaha, kuma kana iya
shirya alaka tsakaninta da kwamfutarka, don aika mata da hotuna ko bayanai ta
sawwara maka su nan take.
Sabanin fasahar Bluetooth, sadarwa a tsakanin kayayyakin fasahar
sadarwa masu dauke da makamashin Infra-red ya sha banban. Ba a bukatar doguwar tazarar da ta gota taku uku, ko kuma mita guda. Wannan shi yayi daidai da digiri talatin (30
Degrees). Har wa yau, fasahar Infra-red
na iya aiwatar da sadarwa ne idan ya zama babu wani shamaki komai kankantarsa
tsakanin kayayyakin sadarwa biyu. Idan
akwai shamaki, ko da na kaurin silin gashi ne, sadarwa ba ta yiwuwa.
Amma sabanin yadda muka dauka, cewa sai an hada wayar salula jiki-jiki
kafin a iya aikawa da sako ta Infra-red, ba haka abin yake ba. Idan an yi haka ba komai, amma ba ka’ida bace
cewa dole sai ta haka za a iya sadarwa. Har wa yau, fasahar sadarwa ta Infra-red ta
dara Bluetooth a wurare da dama; ba ka bukatar sai ka nemi abokin huldanka ta hanyar barbaran
wayar salularsa, a a. Da zarar ya kunna
tasa shi kenan. Amma fasahar Bluetooth dole ne ka bata lokaci wajen neman abokin
hulda da kuma barbaran wayarsa. Haka
na’urar Infra-red ta fi gaugawa wajen sadar da bayanai, wannan tasa za ka iya
aikawa da mizanin bayanai mai yawa cikin kankanin lokaci, sabanin Bluetooth
uwar saibi da nawa; duk kwaskwariman da ake ta mata shekara-shekara. Wannan ya faru ne saboda ka’idar da ke
taimaka wa Infra-red sadarwa, wato "Very Fast Infra-red Protocol"
(VIFR Protocol) ta shallake wacce ke isar ma Bluetooth, nesa ba kusa
ba.
A daya bangaren kuma, wannan bai sa Bluetoth ta gaza ba
kwata-kwata; sadarwa ta Bluetooth ba ta
bukatar dole sai masu sadarwa na tsaye cif, ba motsi. Kana iya kunna Bluetooth dinka, ka sa wayarka
cikin aljihu, ka ci gaba da harkokinka alhali wani na karban sako daga
gareka. Haka fasahar Bluetooth ba ta
saurara wa shamaki; ko da shamaki ko babu, kana iya aiwatar da sadarwa kai tsaye. Ka ga kowa da nashi ranar kenan. A cewar masana ci gaban fasahar sadarwa ta
zamani a lokutan baya, zai yi wahala wani ya doke wani daga kasuwa. Domin kowanne daga cikinsu na da nashi siffa
wacce abokin mukabalarsa ba shi da ita.
A takaice dai kowanne na da fagensa, kuma za su ci gaba da habaka
lokaci-lokaci, iya gwargwadon yadda
bincike ko mu’amala da su ya kama. To amma, ga dukkan alamu, fasahar
Bluetooth ta ci nasara kan Infra-red, domin a yanzu an daina kera wayoyin
salula masu dauke da Infra-red sai Bluetooth.
Akwai alamar dai kungiyar da ke lura da habaka fasahar Bluetooth ta fi
tasiri wajen samar da kirkire-kirkiren ci gaba a fannin sadarwa.
Mu'amala da Fasahar GPRS
Daga cikin hanyoyin aiwatar
da sadarwa wajen karba da aikawa akwai tsarin General Packet Radio Service, ko
GPRS a gajarce. Sai dai sabanin
sauran fasahohin sadarwar da suka gabata (Bluetooth da Infra-red), fasahar GPRS
ba a iya gani. Wani tsari ne ko kintsin hanyar sadarwa da ke cikin ruhin wayar
salula da aka tsofa mata, tun ran gini.
Tsarin sadarwa ta fasahar GPRS ita ce hanyar da ta kunshi aikawa
da kuma karbar sakonnin da ba na sauti ko murya ba, tsakanin wayar salula da
wata waya ‘yar uwarta. Wadannan sakonni
da ake iya aikawa ta hanyar GPRS dai
su ne rubutattun sakonnin tes (SMS) ko Imel ko mu’amala da fasahar
Intanet ta hanyar wayar salula ko kuma tsarin kira ta hanyar bidiyo (video call). Wannan tsari na sadarwa na cikin sababbin
tsare-tsaren da wayoyin salular da aka kera cikin zamani na biyu (2nd Generation Phones) suke
dauke dasu. Kuma ita ce hanya ta farko
da ta fara bayyana wacce ke sawwake sadarwar da ta shafi rubutattun sakonni da
na bidiyo da kuma mu’amala da fasahar Intanet.
Amma kafin nan, tsofaffin wayoyin salula na amfani ne da hanya kwaya
daya wajen aikawa ko karbar dukkan nau’ukan sakonni. Idan kana magana da wani, to, ko da an aiko
maka rubutacciyar sako, baza ta shigo ba sai ka gama magana sannan ta iso. Idan kana son aikawa da rubutacciyar sako
kuwa, ta hanyar aikawa da murya za ka aika, kuma da zarar ka fara aikawa, layin
zai toshe babu wanda zai iya samunka, sai lokacin da wayar ta gama aikawa
sannan za a iya samunka. Wannan ya faru
ne saboda wayoyin salula na zamanin farko (1st
Generation Phones) na amfani ne da layin sadarwa guda daya rak. Wannan tsari shi ake kira Circuit Switched Data (CSD). Karkashin wannan tsari, kamfanin
sadarwarka zai caje ka ne iya tsawon lokacin da sakonka ya dauka kafin ya isa,
wanda kuma mafi karancin lokaci shi ne dakiku talatin (3o seconds).
To, amma da tsarin sadarwa
ta wayar iska na GSM ta bayyana, sai
aka samu fasahar GPRS, wacce ke
amfani da layin aikawa da karbar rubutattun sakonni kai tsaye tsakaninta da
wata wayar. Hakan kuma na samuwa ne
musamman idan wayar na dauke da fasahar Wireless
Application Protocol, wato WAP, wacce
ita ce ka’idar da ke tsara sadarwa a tsakanin kwamfuta da wayar salula, ta
hanyar wayar iska. Karbar sakonnin text
ko Imel ko kuma mu’amala da fasahar Intanet ta hanyar GPRS shi yafi sauki da kuma sauri wajen mu’amala. Sai dai kuma wannan tsari na GPRS na cikin nau’ukan hanyar sadarwa da
kamfanin sadarwa ne ke bayar dasu, wato Network
Service. Wannan ke nufin idan
wayarka na da WAP, ko kuma tsarin
mu’amala da fasahar Intanet, to kana iya amfani da ita kai tsaye wajen shiga
Intanet. Kuma da zarar ka yi haka, kamfanin
sadarwarka zai caje ka kudin zama a kan layi.
Tsarin sadarwa ta GPRS na amfani ne da wasu hanyoyi masu
zaman kansu wajen aikawa da sakonni.
Wannan tsari shi ake kira Multiple
Access Method a harshen kimiyyar sadarwar zamani. Ta amfani da wannan tsari, wayarka na iya karban
sakonnin Imel ko tes, a yayin da kake magana da wani. Sai dai kawai ka gansu sun shigo. Kana iya karbar rubutattun sakonni fiye da
daya a lokaci guda. Hakan ya faru ne
saboda tsarin na amfani ne da hanyoyi fiye da daya wajen karba ko aikawa da
wadannan sakonni. Ba ruwansa da layin da
kake karbar sakonnin kira na sauti, sam.
Sai dai kuma, mu a nan galibi, kamfanonin sadarwarmu na amfani da ita ne
kawai don bayar da damar shiga ko mu’amala da fasahar Intanet. Idan fara
mu'amala da fasahar Intanet a wayarka, za ka an rubuta kalmar "GPRS"
a sama daga hannun dama. Idan kana
cikin lilo a duniyar Intanet sai aka kira ka, layin zai dakata, har sai ka gama
tukun. Kamfanonin sadarwar tarho dinmu duk
suna da wannan tsari na GPRS, amma kamar
yadda na zayyana a sama, idan ba wayoyin salula na musamman irinsu BlackBerry ba, ba a iya amfani da ita
sai wajen shiga Intanet kadai. Amma a
sauran kasashe ana amfani da wannan tsari wajen karba da aikawa da sakonnin tes, da sakonnin Imel da kuma yin hira da abokinka ta hanyar gajerun
sakonni, wato Instant Chat.
Dangane da nau’in wayar
salula, akwai yanayin sadarwa iri uku ta amfani da fasahar GPRS. Akwai wayoyin salula
masu karfin karbar kira na sauti ko murya da kuma karba ko aikawa da sakonnin tes, duk a lokaci guda. Ma’ana, kana magana sannan kana rubuta sakon tes, idan ka gama rubutawa, ka aika da shi nan take, ba tare da layin
da kake magana da abokinka ya yanke ba.
Wadannan wayoyin salula sune ke martaba na farko, a sahun wayoyin salula
masu amfani da fasahar GPRS, watau Class A kenan. Har wa yau su ne nau'ukan wayoyin salula masu
amfani da babbar manhajar wayar salula ta Symbian, ko Windows Phone, ko
Android, ko kuma iOS na kamfanin Apple. Su ne nau'ukan da ke iya bayar da daman
mu'amala da masarrafar waya sama da guda daya a lokaci daya, wato Multitasking
kenan.
Sai kuma wadanda ke biye
dasu, wato Class B, wadanda idan kana
amfani da fasahar GPRS, ta amfani da
Intanet ko sakonnin tes, sai kira ya shigo, to wayar za ta
tsayar da wancan layin da kake karbar sako ko kake mu’amala da Intanet, don
baiwa layin da ke karbar kira damar sadar da kai da wanda ke kiranka. Wadannan sune kusan kashi hamsin cikin dari na
ire-iren wayoyin da ake amfani dasu a yanzu.
Sai nau’i na karshe, wato Classs
C, wadanda idan kana son amfani da fasahar GPRS, to dole sai ka shiga cikin wayar, ka saita ta da kanka. Da zarar ka saita ta, to, ba wanda zai iya
samunka, sai in ka gama abinda kake yi, ka sake saita ta zuwa layin karbar kira
na sauti ko murya (Voice Call).
Wannan fasahar sadarwa ta GPRS
dai na cikin fasahohin da suka kara wa wayar salula tagomashi da kuma
karbuwa a duniya. Domin ta sawwake hanyoyin yadawa da karbar sakonni ba tare da
mushkila ba. Kana iya mu'mala da fasahar Intanet. Kana iya aikawa da sakonnin hotuna ko bidiyo
ko sauti ta tsarin Multimedia Message Service, wato MMS. Sai dai kuma a lura, duk sakon da ka
aika, za a caje ka. Haka duk lokacin da
ka shiga giza-gizan sadarwa ta duniya don yin lilo, za a caje ka. Iya dadewarka, iya yawan kudin da za a diba
daga layin wayarka. Bayan haka, har
yanzu kamfanonin waya basu gama daidaitawa ba a tsakaninsu wajen aikawa da
karbar hotuna ko sakonnin Imel ko sauti ko bidiyo ta hanyar fasahar GPRS. Ma'ana, a yanzu za ka iya aikawa da hoto
ta tsarin MMS mai amfani da fasahar GPRS daga layin MTN ne kadai
zuwa wani layin MTN din. Amma ba za ka iya aikawa zuwa layin Etisalat ko Glo ko
Airtel ba. Haka yake a sauran layukan.
Kowa ba ya iya karba daga wani, sai tsakanin layukansa.
Taskance Bayanan Sirri
Wayar salula ma'adanar sirri
ce, amma ga wanda ya iya adana, ya kuma san tsarin adanawa da taskancewa. Kowace wayar salula na iya baka damar
taskancewa (ta hanyar rubutu), da kuma adanawa (ta hanyar masarrafai) ga duk
abin da kake ganin sirri ne a gare ka.
Da farko dai, akwai tsarin kariya (Security Features) da kowace wayar
salula ke zuwa da shi. Kana iya kulle maballan wayarka, ya zama ba za a iya yin
kira ba ko ganin dukkan bayanan da ke cikin wayar ba sai da yardarka. Wannan na samuwa ta tsarin Keypad Lock, wanda
kowace wayar salula ke da shi; komai kankanta da rashin tsadarta kuwa.
Bayan haka, akwai masarrafai
na musamman da ake taskance bayanai da su, irin su Notes, da kuma Active
Notes wadanda suka shahara a wayoyin Nokia. Sannan akwai Diary kamar yadda
wasu wayoyin salula kan kira shi. A
wayoyi nau'in BlackBerry akwai Memo Pad, da Tasks, wadanda
za a iya samunsu a jakar Applications; duk kana iya taskance bayanan
sirri da su. Bayan wadannan, akwai
tsarin kariya da kowace waya ke bayarwa don kulle ma'adanar waya (Phone
Memory) da katin ma'adanar waya (Memory Card) ta yadda babu wanda
zai iya isa ga bayanan da ke cikinsu sai da kalmomin izinin shiga, wato Password.
Nau'ukan bayanan da za a iya
taskancewa da adanawa dai sun hada da adireshin Imel, da kalmomin izinin shiga,
da lambobin ajiyar banki (Bank Account Details), da adireshin wurare, da
duk wani bayani mai muhimmanci ga mai waya.
Nau'ukan bayanan ba su da iyaka; ya dangancin irin muhimmancin da suke
da shi ga mai wayar, ko irin muhimmancin da ya basu. Har wa yau kana iya taskance hotuna, da
bidiyo, da sakonnin tes da lambobi ta yadda ba mai isa gare su sai da izininka. Don haka, wayar salula kamar lalita ce. Sai dai kuma, yana da kyau mu san cewa,
kowace lalita fa, wasu lokuta tana lalata.
Don kariya daga rasa dukkan
bayanan da ka taskance sanadiyyar matsalolin da ka iya samun wayarka ba da sani
ko so ba, yana da kyau kayi tanadi. Duk
abin da ka san ka taskance shi a wayarka, to yana da kyau ka samu makwafinsa a
wani wuri. Na farko dai idan zai yiwu,
ka sake taskance su a katin SIM dinka, musamman idan lambobi ne ko sakonnin
tes. Da zarar waya ta samu matsala, kana
iya zare katin SIM dinka ka dora a wata wayar don samun makwafinsu. Idan a katin ma'adanar waya ne sai ka samu
wani katin daban, ka taskance su a ciki.
Idan kuma a masarrafar waya ne sakonnin suke taskance, irin su Notes,
ko Active Notes da dai sauransu, sai ka saukar da manhajar mu'amala
da wayar, wato Phone Suite ko Nokia Suite idan Nokia ce. Idan sabuwa ce wayar ka saya, duk kana iya
zuwa gidan yanar sadarwar kamfanin da ya kera wayar, ka saukar da manhajar da
ake mu'amala da wayar da ita. Da zarar
ka yi haka, sai ka loda manhajar a kwamfuta, sannan ka jona wayarka da
kwamfutar, ka bude manhajar, ka je masarrafar makwafin bayanai, wato Phone
Backup, ko Data Backup, ko duk wani suna da yayi kama da haka, don
taskance dukkan bayanan da ke cikin masarrafan wayarka, cikin sauki.
Mu'amala da Manhajar
Tunatarwa/Farkarwa
Wayar salula bata zo don ba
ka daman kira da amsa kira ko rubuta sakonnin tes kadai ba, har da taimaka maka
wajen samar da tsari a rayuwarka. A
matsayinka na musulmi, kana iya amfani da wayar salula wajen tunatar da kanka
duk abin da kake son yi a rayuwa; daga lokacin sallah zuwa lokacin tashi a
barci cikin dare, ko rana, ko yamma.
Akwai manhajar tunatarwa na musamman da dukkan wayoyin salula ke zuwa da
ita. Sai dai abin bakin ciki bamu cika damuwa da ire-iren wadannan abubuwa
ba. Abin mamaki, da yawa daga cikinmu na
amfani da kashi 30 cikin 100 ne na alfanun da ke tattare da wayoyinmu. Amma duk da haka da mun ga wata sabuwa, sai
muyi caraf muna neman sake saya. Shin,
kafin ka sayi wata, ka gama kure karfi da kudurar wacce kake tare da ita
ne? Shin, mai karatu ma ya taba yi wa
kansa wannan tambayar kuwa kafin ya
canza waya?
Akwai manhaja ta musamman
mai suna Reminder, ko Alarm. Ba
su kadai ba, kana iya ayyana abin da za ka yi nan da kwanaki ko watanni, ka sa
wayar ta tunatar da kai ta hanyar sauti ko bayyana rubutacciyar tunatarwa a
shafin wayarka. Da zarar lokacin ya yi
za ta tunatar da kai babu jinkiri. Kana
iya sa duk irin sautin da kake son wayar ta tunatar da kai. Har wa yau kana iya amfani da Kalandar wayar,
wato Calendar, ko kayi amfani da manhajar farkarwa, wato Alarm, don
nusar da kai abin da kake son yi; cikin dare ne ko rana, ko duk lokacin da kake
so.
Idan kana bukatar tunatarwa
cikin dare, sai ka je cikin Menu, ka shiga manhajar agogo (Clock) ko
manhajar tunatarwa/farkarwa (Alarm), ka shigar da lokacin da kake son a
farkar da kai. Idan da karfe biyu kake
son a farkar da kai, sai ka sa lokacin.
Daga nan za a tambayeka yanayin tunatarwa; shin, da sauti za a tunantar
da kai ko da gunji (Vibration)? Sai
ka zaba. In da sauti ne, za a bukaci ka zabi sautin da kake son a tunatar da
kai da shi. Sannan za a tambayeka; shin,
kana son a rika maimaita maka tunatarwar, ko a a? In kace eh, za a tambayeka tazarar lokacin da
kake son idan aka maimaita, a sake maimaitawa.
Wannan shi ake kira Snoozing. Idan
aka farkar da kai da karfe biyu, sai bacci ya rinjayeka, za a sake farkar da
kai da karshe biyu da minti biyar misali, nan ma idan baka farka ba, sai a sake
farkar da kai da karfe biyu da minti goma, har dai zuwa lokacin da ka farka.
Idan kuma tunatarwa ce kake
son a maka, don yin wani abu a wata rana ko lokaci, kana iya sa tunatarwar ta
zama da minti biyar ko goma ko ashirin, kafin lokacin abin, don ka samu
shiryawa ba tare da ka makara ba. Duk
wadannan hanyoyin tsari ne na rayuwa.
Sannan kana iya hada dukkan bayanan da ke da alaka da yin wani abu,
wadanda ka taskance su a manhajar Notes ko Active Notes misali,
wadanda kuma suka danganci wani sha'ani, misali biki, ko tafiya, ko ziyara, su
zama kamar tunatarwa. Idan kayi haka, da
zarar lokacin yayi, nan take bayanan za su bayyana a shafin wayarka, tare da sautin
tunatarwa idan ka sa. Abin da za ka
kiyaye shi ne, idan ka san kana da saurin firgita, to, kada ka sa wayarka ta
rika tunatar da kai ko farkar da kai ta hanyar gunjin waya, wato Vibrating.
Lura da Yanayin Sadarwa (Network)
Yanayin sadarwa shi ne sinadarin sadarwa baki daya. Idan babu shi, to ba a iya aiwatar da kira ko
amsa shi. Yana da matukar muhimmanci a
jikin wayar salula. Wayoyin salula na
wannan zamani suna zuwa ne da tsarin kalato yanayin sadarwa guda biyu. Na farko shi ne na kai tsaye, wanda wayar da
kanta take kokarin nemo yanayin sadarwar, don tabbatar da mai waya ya samu
damar aiwatar da kira da amsa kira ko aika sakon tes ko aiwatar da duk wani
abin da ke ta'allake da yanayin sadarwar kamfanin wayar. Wannan tsari na kai tsaye shi ake kira Automatic
Network Searching. A daya bangaren
kuma akwai tsari da neman yanayin sadarwa da hannu. Wannan shi ake kira Manual Network Searching. Idan kana son ganin kowannensu sai ka je Menu,
ka gangara Settings, ka shiga Phone Settings, sannan ka matsa
Network, nan za ka ga Automatic.
Idan ka matsa, za a bude maka shafi inda za ka iya canzawa daga
tsarin kai tsaye zuwa tsarin nemo
yanayin sadarwa da hannu, wato Manual kenan.
Akwai alama da ke nuna samuwa ko bacewar yanayin sadarwa a fuskar
kowace waya. Ita ce alamar doguwar sandar da ke tsaye a bangaren hagu, a
galibin wayoyin salula. A wasu wayoyin
kuma alamar na siffar Dala ne, a hannun dama. Musamman a wayoyi nau'ukan BlackBerry
da sauran manyan wayoyin salula na zama.
Ala ayyi halin dai, za a samu alamar ne gab da sunan kamfanin waya a
shafin wayar salula. Idan yanayin
sadarwa yayi kasa, za a ga sandan ya ragu.
Idan kuma ya karu sandan zai kara tsayi har ya daki iya tsawonsa. Amma a
wasu lokuta kuma za ga alamar a cike, amma kuma ka kasa samun layi don
kira. Duk wannan na daga cikin
kebantattun matsalolin tsarin sadarwa ta waya-iska, wato Wireless
Communication.
Duk sadda ka bukaci yin kira amma ka kasa, alhali ga alamar yanayin
sadarwa a cike, to, kana iya canza tsarin nemo yanayin sadarwa, ta hanyar shiga
Menu, zuwa Settings, a gangara Phone Settings, sai a matsa
Network. Daga nan sai a canza
daga Automatic zuwa Manual. Da
zarar an zabi Manual, nan take wayar za ta kama nemo yanayin sadarwa kai
tsaye, sai ta samu. Idan ta gama nema,
za ta budo dukkan sunayen kamfanonin wayoyin salula da ke da yanayin sadarwa a
muhallin da mai waya yake, sai ka zabi na kamfaninka. Idan aka gwada wannan dabara amma abu yaki,
to, ana iya kashe wayar, sai a sake kunnawa.
In Allah yaso za a dace. Idan hakan ma yaki, to, akwai alamar matsalar
gamammiya ce. Daga nan sai a hakura, a
ci gaba da gwadawa lokaci zuwa lokaci, har a dace.
Manhajar Wasannin Wayar Salula
Manhajar wasanni, wato Games suna daga cikin abubuwan da
wayoyin salular zamani ke zuwa da su.
Babbar dalilin samuwarsu dai ba ya wuce samar da nishadi ga mai wayar
salula. Akwai nau'ukan wasanni
daban-daban a cikin wayoyin salula. Idan kai mai sha'awar ire-iren wadannan
manhajoji ne, kana iya amfana da su sosai.
Daga cikin manyan alfanun da ke tattare dasu akwai wasa kwakwalwa, da
kuma karin ilimi da sanin mahangar rayuwa.
Amma sai dai yana da kyau mai karatu ya sani, kada ya bata lokacinsa
wajen shagala da wadannan manhajoji, musamman idan akwai wasu abubuwa masu
amfani da suke bukatar hankalinsa.
Sannan bayan haka, yawan amfani da wadannan manhajoji na wasanni suna
cinye batirin wayar salula cikin gaggawa, saboda tasirinsu wajen karin aikin
masarrafar wayar a lokaci takaitacce.
Tsarin Lura da Wayar Salula
Wayar salula kamar sauran kayayyakin amfani ne na gida ko na wajen
aiki; suna bukatar a rika lura da su, in kuwa ba haka ba, sai su rasa tagomashi
da kimarsu, ko su salwanta tun lokacin salwantarsu bai yi ba. Abin da wannan sashe zai duba ya kunshi
tsarin kunna wayar salula, da kashe wayar salula, da adanawa a yayin da mai
wayar ke yin wani abu daban, da sanya wayar a caji don tabbatar da ci gaban
karfinta wajen ba mai ita damar sarrafa ta ba tare da matsala ba. Sauran al'amuran sun shafi tsarin shigarwa da
mika bayanai, da kuma wanka da wanki, don tabbatar da tsafta da tsawon rayuwa.
Lafiya, in ji Hausawa, uwar jiki ce.
Haka lamarin yake a bangaren mu'amala da sarrafa wayar salula.
Kunnawa da Kashewa
A duk sadda mai karatu ya sayi wayar salula sabuwa kar, abu na
farko da ya kamata ya fara koyo daga gare ta shi ne yadda ake kunnawa da kashe
wayar, domin abubuwan da za su fi maimaituwa a gare shi kenan yayin mu'amala da
wayar. Bin ka'ida wajen kunnawa da kashe
waya na daga cikin abubuwan da ke kara mata dogon kwana a hannunka. Tsarin kunna waya shi ne ka matsa maballin da
ake kunna ta da shi, wanda bayanai suka tabbatar da cewa shi ne maballin da ake
kunna ta da shi. Kana iya ganin bayanan karara a cikin kundin da wayar ta zo da
shi, wato Phone Manual. Galibinmu
bamu cika damuwa da dubawa ko karanta wannan kundi ba, amma yana da
amfani. A ciki ne za ka ga yadda ake
kunnawa, da kuma maballin da ake matsawa don kunnawa. Haka idan kashewa ne, duk a ciki za ka gani.
Idan ka matsa maballin kunna wayar salula, sai ka jira har sai ta gama
kunna kanta tukun. Za ka iya gane haka
ta hanyar kulle kanta, idan ka sa mata makulli, wato Auto Lock kenan. Idan ba ka sa mata kowane irin kariya ba, za
ka iya gane ta gama kunna kanta idan dukkan tambarin manhajojin da ke fuskar
wayar suka gama bayyana. Misali,
tambarin yanayin sadarwar, da tambarin harbawan batir, da tambarin agogo, da
tambarin kamfanin sadarwa da dai sauransu.
Sai duk sun gama bayyana sannan sai ka fara amfani da wayar; idan kira
za ka yi, sai ka nemo lambar wanda kake son kira. Idan kuma ba kira za ka yi ba sai ka sa a
aljihu ko jaka, misali. Amma kafin nan,
zai dace ka tabbatar ta kulle kanta kamar yadda ta saba yi kafin ka sa a
aljihu. In kuwa ba haka ba, cikin kuskure kana iya dannawa ko matsa maballin
kira alhali tana bude, a lokacin da ka jefa cikin aljhu, kuma nan take sai ta
fara kiran wanda ka matsa lambarsa cikin kuskure, har ya dauka yayi ta halo,
halo, baka sani ba.
Idan ka tashi kashe wayar salula zai dace ka rufe dukkan masarrafai
ko manhajar da ka bude tukun. Misali,
idan ka budo masarrafan rubuta sakonnin tes ne, kada kace za ka kashe wayar
bayan baka rufe manhajar da ke bude ba.
Wannan kuskure ne. Haka idan
wakoki kake saurare, ka rufe manhajar kidin tukun, sannan kayi kokarin kashe
wayar. Idan babbar waya ce wacce ake iya
bude manhajoji sama da daya a lokaci daya, kamar wayoyin salula nau'in Smartphones,
zai dace ka je Menu, ka tabbata kowace manhaja a rufe take. Duk manhajar da ba a rufe take ba za ga alama
a saman tambarinta. Sai ka bude, ka
matsa Exit daga hannun dama, don rufewa. Sai ka tabbatar kowace manhaja
a rufe take, sannan sai ka kashe wayar, ta hanyar matsa maballin da aka tanada
don kashewa. In kuwa ba haka ba, akwai manhajojin da za su iya samun matsala a
sadda ka kashe wayar suna kunne. Haka kwamfuta ita ma, muddin kana yawan
kashewa ba tare da ka rufe masarrafan da ke bude ba, nan take suna iya samun
matsala, kuma nan gaba idan ka tashi amfani da su za ka fahimci hakan. Don haka sai a kiyaye.
Adana Wayar Salula
Adana wayar salula yana da kyau, tunda abin amfani ne kuma da kudi
aka saya. A nan ina nufin inda ya kamata
ka ajiye wayar salularka a sadda ba ka amfani da ita, ko kuma kake sauraren
wani abu daga jikin wayar. Idan a ofis
kake inda da'iman kana zaune ne a saman kujera, zai dace ka ajiye ta a saman
teburin da kake, don duk wanda ya kira za ka ji kuma za gani. Idan tafiya kake zai dace ka sa a aljihu,
muddin ba wangalallen aljihu bane, in kuwa ba haka ba, rikewa a hannu shi
yafi. Idan a kwance kake kana iya
ajiyewa a inda kake ganin ya fi dacewa.
Kada ka ajiye wayarka a inda ba ka da tabbacin tsaro, musamman idan bako
ne kai. Kada a ajiye a inda danshi zai
iya samunta. Kada ka ajiye a inda
kwazayin rana zai mata illa, ko inda raba zai iya zuba a kanta. Kada ka ajiye a inda kura zai iya shigewa
cikinta. Kada ka ajiye a inda za ta iya
zama fitina ga wasu, musamman idan mai tsada ce. Ka zama mai kaffa-kaffa da ita a duk inda
kaje ko kake. Bayan haka, idan kana
cikin jama'a ne, zai dace ka sa wayar a
yanayin da za ka iya fahimtar an kira ko tes ya shigo, ba tare da ka takura wa
wadanda kake tare da su ba.
Tsarin Cajin Wayar Salula
Abu ne sananne ga dukkan masu mu'amala da wayar salula cewa dole ne
a rika sa wayar a caji don karin tagomashi da makamashin da za a dogara gare
shi wajen aiwatar da ayyukan wayar. Idan
sabuwa ce ka siya, ana son ka sa ta a caji har sai ta cika, sannan ka kunna.
Haka aka fi so. Har wa yau, kada ka rika
sa wayarka a caji sai idan cajin yayi kasa sosai. Wannan na daga cikin abin da ke tabbatar mata
da tsawon rayuwa ta bangaren karkon batirin.
Amma na san da yawa daga cikinmu kan sa waya a caji ko da akwai caji a
ciki, musamman saboda tsoron dauke wuta.
Sai a gaskiya hakan na rage wa batirin karko. Kamar dan adam ne, bai kamata ya bukaci
abinci ba sai yunta ta kama shi. Haka
ruwan sha, sai kishi ya kama shi. Domin
a lokacin ne abincin da abin shan za su fi masa aiki a jikinsa. Saboda ya ci ko sha su a lokacin da jikinsa
ke da bukata. Don haka, yawan sanya waya
a caji ba tare da cajin ya kare ba, kuskure ne.
A bari sai caji yayi kasa, sai a sa.
A duk sadda za ka sa wayarka a caji a cikin jama'a, to, ya zama
kana kusa. Kada ka bar wayar a kunne,
tana caji, a kira ba ka kusa tayi ta damun jama'a. Wannan kuskure ne. Sannan idan ma kashewa kayi, kada ka tafi ka
bar wayar, musamman idan baka aminta da yanayin wurin ba. In kuwa ba haka ba, za ka dawo ka tarar da
na'urar caji kadai a sagale. Haka idan
za ka bayar ne a wajen masu caji, kamar yadda galibi ake yi yanzu saboda matsalar
wutar lantarki a kasar namu, to, zai dace ka kashe wayar, sannan ka bayar. Idan kuwa ba haka ba, za ayi ta kiranka
alhali ba ka kusa. Wannan na iya sa mai
cajin ya rika daga maka waya, wadanda ke kiranka kuma ba lalai bane su ji dadi,
tunda kai suke son jib a wani ba. Kada a
sa waya a caji, a bari har ta gama caji ba a cire ba. Idan kayi rashin sa a aka dauke wuta, nan
take cajin da ka yi a baya zai zuke, musamman idan wayar a kashe take. Sannan kuskure ne idan wayarka na caji, ka
amsa kira ba tare da ka cire a jikin wayar cajin ba. Akwai matsala yin hakan. Duk sadda ka san za
ka sa wayarka a caji musamman cikin dare, ta yadda ba za ka san sadda wayar za
ta cika ba, to, ka kashe sautin wayar, sai ka barta a kunne. Ko da an dauke wuta misali, hakan ba zai
cutar ba sosai. Amma idan a kashe take,
nan take cajin zai zuke. Sai a kiyaye.
Tsarin Karba da Mika Bayanai
Ta hanyar wayar salula, kamar yadda mai karatu ya sani, yana iya
karban bayanai (rubutattu, da sauti, da bidiyo, da hotuna), sannan yana iya
mika wa wasu, duk ta hanyoyin da aka killace don yin hakan. Akwai fasahar Bluetooth da Infra-red, kamar
yadda bayanai suka gabata, sannan akwai amfani da tsarin GPRS, musamman
a bangaren hotuna da mu'amala da fasahar Intanet. Abin da ake son mai waya ya kiyaye shi ne, ya
san cewa akwai kwayoyin cutar wayar salula (Virus) da ke shawagi a
wayoyin salula. Idan kayi rashin sa'a
wanda ya turo maka bayanai daga wayarsa na dauke da kwayoyin cuta, to, nan take
naka wayar za ta kamu. Idan kuwa ta kamu
ba za ka iya ganewa da wuri ba, musamman idan kadan ne, har sai sun hayayyafa,
sun fara tasiri a jikin wayar sannan za ta fara nunawa.
Daga cikin alamomin da ke nuna waya ta kamu da kwayoyin cuta kuwa
akwai yawan saibi da nawa wajen kunnawa da kashewa. Akwai matsalar taskance bayanai. Misali, idan
ka zo adana hotuna ko bidiyo a ma'adanar waya ko ma'adanar katin waya, sai a ce
maka "Memory is Full," alhali akwai sauran ma'adana a wayar ko
katin wayar; duk wannan na cikin alamomin da ke nuna akwai matsala da babbar
manhajar waya sanadiyyar kwayoyin cuta.
Har wa yau, akwai matsalar yawan sandarewa da sumewa (Hanging). Duk sadda ka ga wayarka na yawan
sandarewa ko sumewa idan kana mu'amala da ita, to, ka san akwai matsala mai
girma tare da ita. Musamman idan ya zama
ba ka iya kashewa sai ka cire batir sannan take mutuwa. Har wa yau daga cikin manyan alamu shi ne,
waya za ta rika kashe kanta tana kunna kanta.
Duk sadda ka samu haka, to, lallai akwai matsala. Abu na karshe da zan iya hararowa shi ne
hasarar bayanai daga ma'adanar waya ko ma'adanar katin waya. Ma'ana haka kawai ka nemi bayanan da ka
taskance a waya ka rasa. Wadannan su ne
kadan daga cikin matsalolin da ke samuwa idan wayar salula ta kamu da kwayoyin
cuta. Hakan kuma ya fi samuwa ta hanyar
musayar bayanai ta amfani da fasahar Bluetooth ko Infra-red ko
kuma karbar ma'adanar katin wayar wani ka sa a wayarka. Sai a rika kiyayewa.
Wanka da Wanki
Wayar salula na bukatar wanka da wanki. Amma fa ba irin wanka da wankin da Malam
Bahaushe ya sani ba. Ana nufin
tsaftacewa ta amfani da kayan wankewa da tsaftacewa. Idan kana da sinadarin Spirit, kana
iya kwance wayarka, ka wanke murafenta da burosh, sannan ka goggoge inji da
kyau, don kawar da dukkan kuran da ke ciki.
Bayan haka, kada ka bari ruwa ya rika shiga cikin wayar, za ta sume har
da sandare, in ma ba a yi sa'a ba ta haukace; sai an mata sabon zubin rai ta
hanyar filashin da kwamfuta. Idan ba za ka iya ba, ka kai wa mai gyaran waya ya
wanke maka (ko sabis, kamar yadda suke cewa), ka biya ladan aiki. Wannan na cikin abin da zai dada taimakawa
wajen kara mata kuzari da tagomashi.
Kada ka bari sai ta fara baka matsala ka nemi wurin mai gyara. Watakila ma kura ne yayi mata yawa, sabis
kawai take so, amma tunda baka sani ba, kana kaiwa sai yace ai sai an sake kaza
da kaza, kana tafiya ya mata sabis shikenan.
Ka ganta garau. Sai a kiyaye.
Wayar salula da Lafiyarka
Bayan aiwatar da kira da karban kira, da sauran amfanoni da mai
waya ke samu daga wayar salula, yana da kyau kuma a daya bangaren ya fahimci
cewa, amfani da wayar salula ba tare da ka'ida ba na haifar da cutarwa ga
lafiyar jiki. Wannan na samuwa musamman
hatta a lokutan bacci, da kuma tasirin yawan kallo da yawan sauraro na tsawon
lokaci.
Lokacin Bacci
Galibin jama'a kan bar wayoyin salularsu a kunne a lokacin da za su
kwanta, ko su sa a caji, ko su kashe, ko su kashe amon wayar, ko su sa ta a
tsarin girgiza (Vibrating). Wani yanayi
ne yafi dacewa ga mai mu'amala? Idan aka
baiwa jama'a damar tattauna wannan zance, kowa zai fadi abin da yafi sha'awa
ne, ko tsarin da ya saba da shi. Amma a
hakikanin gaskiya, idan muka yi la'akari da lafiyar jiki, kashe amon wayar shi
ne abin da yafi dacewa a lokutan bacci, ko da kuwa kai kadai kake kwanciya a
dakin. Domin idan ka barta a kunne da
amonta, a duk lokacin da aka kira ka cikin talatainin dare kana iya ji musamman
idan kai ba mai zurfin bacci bane irin Baban Sadik. To, sai dai kuma hakan na
iya firgita ka, ka tashi a firgice.
Watakila kiran ba wani mai mahimmanci bane. Haka idan kana kwanciya daki daya ne da
iyalinka, yana iya firgita ta, ko da kai ba ka tasirantuwa da sautin. Balle a ce akwai jariri ko karamin yaro ko
yara a inda kuke. Don haka, ko dai ka
kashe amon wayar ne yayin kwanciya, ko kuma ka rage ta yadda kai kadai za ka
iya ji.
Wasu kan ce ai barin amon waya cikin dare yana da amfani, domin
idan wata 'yar gagggawa ta gitta ana iya nemanka ka tashi nan take, don kawo
dauki. Sai dai kuma abin da za a lura
shi ne, sau nawa hakan ke faruwa cikin ranaku?
Bayan haka, duk wanda zai kira ka cikin dare idan ba kai bane kace ya
kira ka, ya san ba lokacin da ya dace
bane a kira mutum a cikinsa. Don
haka ko da ya ji ba a daga ba, bai kamata ya damu ba.
Har wa yau kuma duk da cewa ba a son kwana da amon waya a kunne
saboda guje wa samun firgici ga mai waya ko wanda ke dakin, haka kuma bai
kamata mutum ya rika kashe wayarsa ba gaba daya cikin dare, sai in babu caji. Domin gwamma a kira baka ji amon waya ba, da
a ce an kira wayar a kashe. Domin idan
ka farka ka ga kiran da aka maka, nan take za ka so kira; musamman idan kira ne
da ba a saba tsammanin shigowarsa cikin dare ba. Sannan, barin waya a tsarin girgiza (Vibration),
shi ma yana iya mummunar tasiri wajen firgitar da mutum, sai ga wanda ya
saba. Domin idan aka yi rashin sa'a
mutum na halin mummunar mafarki sadda wayar ke girgiza, hakan na iya mummunar
tasiri ga lafiyarsa, don a firgice zai farka.
Abu na karshe shi ne, in da hali, kafin mutum ya kwanta ya kamata ya
tabbatar akwai kudi a katin wayarsa, domin hakan zai iya taimaka masa wajen
sadar da kira cikin dare idan bukatar hakan ta taso. Bayan samuwar kudi a wayar, ya zama kuma
akwai caji. Sannan kuskure ne a sanya
waya a caji a kwanta barci. Domin idan aka yi rashin sa'a batirin da ke wayar
jabu ne ba ingantacce ba, kuma wayar ta gama caji ba a cire ta ba, tana iya
fashewa ta kama da wuta. Haka ma
kwamfutar tafi-da-gidanka. Muddin aka sa
a caji, to a rika lura, da zarar caji ya cika, a cire. Shi ne zaman lafiya. Da hasara, inji
Bahaushe, gwamma kauyanci.
Sauraro da Kallo
Wadannan dabi'un dukkan mai mu'amala da wayar salula ne, musamman a
kasashen Turai da Asiya. Galibin
kallace-kallace da sauraron kide-kide da wake-wake duk sun koma ta wayar salula
yanzu. A halin tafiya ne ko a halin
zaman gida; a wajen aiki ne ko a kan titi ne; duk inda ka dubi jama'a za ka
gansu a shagalce suke da wayoyin salularsu.
A kasashe masu tasowa irin namu, musamman da bayyanar wayoyin salula na
kasar Sin masu saukin kudi da dan karen kara. Galibin jama'a a yanzu sun samu
sauki wajen kallon abin kallo na bidiyo, da sauraron dukkan wani abin da suke
sha'awan sauraro, cikin sauki. Akwai
wadanda aikinsa kawai shi ne loda wa wayoyin salula wakoki na sauti ko na
bidiyo, musamman fina-finan Hausa da na Indiya da dai sauransu, cikin farashi
mai rahusa.
A yayin da hakan ya zama sauki, yana da kyau kuma mu fahimci
hadarinsa da tasirinsa ga lafiyar jiki.
Yawan kallon fina-finai ko abin kallo a wayoyin salula musamman masu
kananan fuska (Screen), kuma a cikin duhu ko cikin dare a inda babu haske, yana
haifar da wani irin radadi a cikin ido, da radadi a goshi, wadanda samuwarsu ke
nuna matukar gajiya irin ta kwakwalwa.
Irin wannan dabi'a na tasiri matuka wajen haddasa mantuwa musamman ga
mutumin da yake hadda. Ba kuma zai samu natsuwa ba a galibin lokutansa. Idan wannan ya zama dabi'a a gare shi, zai yi
wahala ya iya jure zama don karanta wani abu daga littafi. Saboda ya saba da kallo. Don haka kwakwalwarsa ba ta iya jure komai in
ba kallo ba. Sai a kiyaye.
Dangane da sauti mai karfi ko mai kara kuma, ya kamata mu
fadaka. Ba kowane dan adam bane dodon
kunnensa ke iya jure sauti mai karfi. Ya
danganci tsari da kintsin halittarsa, da karanci ko yawan shekarunsa. A takaice dai, duk yadda mutum ya kai da iya
jure sauti mai karfi a kunnensa, tsawon lokaci a cikin irin wannan yanayi na
iya sa masa kurumtaka na wucin gadi. Za
a wayi gari ba ya jin sautin wanda ke kusa da shi balle na nesa; sai an daga
murya sosai. Shi kanshi yawan jin
kide-kide da wake-wake mara kangado na sangartar da kwakwalwar mutum, tare da
soyar masa da yawan shantakewa. Sai a
kiyaye. Duk abin da za a yi, a rika
yinsa daidai ruwa daidai gari. Kada a wuce gona da iri.
Wasu Jita-jita
Dangane da abin da ya shafi amsa kira ta wayar salula, akwai
jita-jita da wasu ke yadawa cewa, tururin sinadaran maganadisun rediyon
lantarki (Radioactive Waves) da ke fita daga jikin wayar salula a yayin da ake
aiwatar da sadarwa, wai yana haddasa cutar sankarar kwakwalwa, wato "Brain
Cancer." Wannan magana ko kadan ba
haka take ba. An sha aiko tambayoyi kan
haka. Ganin haka yasa na leka duniyar
gizo don nemo tabbaci, amma babu abin da na samu ingantacce; sai jita-jita irin
wadda ke yaduwa a kasashenmu. Tabbas
akwai abin da ke fita daga jikin wayar salula idan mai waya na amsa kira ko
aiwatar da kira, amma babu wani tabbataccen dalili ko bayani mai nuna cewa
wannan tururi na maganadisun rediyon lantarki (Radioactive Waves) na haifar da
wata cuta mummuna kamar yadda ake riyawa. In ma akwai, to har yanzu bincike bai
gano ko ba. Sai dai, kamar yadda na sha
fada ne, duk abin da mutum zai yi a rayuwa, ba wajen mu'amala da wayar salula
kadai ba, to ya yishi daidai ruwa daidai gari.
Idan abu ne mai kyau, zai samu nishadi a yayin da yake yinsa, kuma zai
dauki tsawon lokaci yana yi bai gaji ba. Idan kuma mara kyau ne, Allah sawwake,
zai yi wahala yayi mummunar sabo da shi, balle ya kasa barinsa. Allah sa mu dace, amin.
I’m not that muсh of a onlinе reader to bе hоnest but уоur sіtes геаlly nice,
ReplyDeletekeep іt up! I'll go ahead and bookmark your website to come back later. Many thanks
My page - ohm'S Laω
Ηey! I knoω this is somewhаt
ReplyDeleteoff-topic but I had tо ask. Does buildіng a well-establiѕhed website such as youгs requiге a lot of work?
I'm brand new to writing a blog but I do write in my journal on a daily basis. I'd like
tо staгt a blog ѕо I will be аble to share my own expегіеnce and feеlings online.
Please let mе know іf you have any
ideаs or tips for branԁ new aѕpirіng blog
oωners. Aррreсiate it!
My sіte :: wire wound resistor
Hi, after rеading thіs aωesome
ReplyDeletepаrаgraρh i am toо сheerful to share
mу know-how here wіth frіends.
Here is my ωeb site ... resistor Color code
Good blog yоu've got here.. It's difficult to find hіgh-quality ωriting like yours nowadaуs.
ReplyDeleteI honestly apprecіate individuals liκe you!
Take care!!
Check out my weblog: genwiki.nl
Hello collеagues, hoω iѕ the whole thing, anԁ what уοu
ReplyDeletewant to sаy on the toρіс of this ρieсe of writing, in my
vіew its in fаct amazing in favor of me.
My ωeb pagе: Resistor Color Code Calculator
What's up, of course this paragraph is really fastidious and I have learned lot of things from it concerning blogging. thanks.
ReplyDeleteMy webpage :: Ohms law
It's a shame you don't haνe а donate button! I'd certainly donate to this outstanding blog! I guess for now i'll
ReplyDeletesettle foг book-marking anԁ аdding youг RSЅ feed to my Google aссount.
I look forward to brand new updateѕ anԁ wіll ѕhare
thiѕ blog with my Facebooκ grοup. Talk sоon!
Alsο visit my wеbpаgе :: blower motor resistor
Hoωdу! I knοw this iѕ somewhat off topic but Ӏ was wonԁeгing ωhіch blog plаtform are yοu using for thiѕ sіte?
ReplyDeleteI'm getting tired of Wordpress because I've had iѕsues ωith
haсkers and Ι'm looking at alternatives for another platform. I would be fantastic if you could point me in the direction of a good platform.
My blog post negative temperature coefficient thermistor
Thаnk уou for sharing уouг
ReplyDeletethоughtѕ. I гeally appreciаte your
еffoгts and I will be waіtіng for
уour next write ups thanκs once again.
my site ... ohm's law
At this time it sounԁѕ likе BlοgEngіne is the top bloggіng platform out there right now.
ReplyDelete(fгom whаt I've read) Is that what you're usіng on your blog?
my page: Lineary Potentiometer
I visitеd multiрle blogs but thе audiο feаture fοг audio songs present at
ReplyDeletethis web site іs truly fabulοuѕ.
my wеbρage :: rotary Potmeter
Ahaa, its fastidious diаlogue conceгnіng thiѕ рοst at thiѕ рlacе аt
ReplyDeletethis weblog, I have reaԁ all that, sο now me also
commenting hегe.
Mу ѕіte ... internal resistance
Thankѕ for one's marvelous posting! I certainly enjoyed reading it, you're а great
ReplyDeleteauthor.I ωill аlωays bookmark your blοg anԁ definitеly will come back in the foreseeable future.
I want to еncοuгagе that you continue
your great job, havе a nice evening!
Here is my web-sitе :: wiki.flisol.cl
Ӏn fact no matteг if somеone doesn't be aware of then its up to other users that they will help, so here it happens.
ReplyDeleteAlso visit my web blog :: wire-wound resistor
Whаt's up to all, as I am genuinely keen of reading this webpage'ѕ post to bе uρdated
ReplyDeletedaily. It consistѕ of niсe materіаl.
Heге is my ѕite ... varistor
Very nice pοst. I just ѕtumblеd upοn yοur weblog and ωished to ѕay that I've truly enjoyed browsing your weblog posts. In any case I will be subscribing for your rss feed and I'm hoping
ReplyDeleteyou write again veгy soon!
Feеl free to suгf to my blog post .
.. wire-wound resistor
I gο to see each dаy a few wеbsites anԁ informаtion ѕіteѕ to
ReplyDeletereaԁ postѕ, eхcept this wеb sitе offers quаlity based
contеnt.
Alsо vіsit mу page: Vegowiki.Org
For newest neωs you have to pay a quick visit woгld wide
ReplyDeleteweb аnd on intеrnet I found thiѕ wеb page
as a most excellent ωeb page for moѕt up-to-ԁate updates.
Havе a look at my hοmepage wiki.ville-Grosmorne.fr
My brothеr ѕuggested Ι mіght liκе this web site.
ReplyDeleteHe was еntirеly right. This put up truly made
my day. You can not imagіne simply hoω so much tіme I had spent fοr thіѕ infoгmation!
Τhanks!
Visit mу homepage; Http://Wiki.Edc-Samara.Ru/Index.Php/%D0%A3%D1%87%D0%B0%D1%81%D1%82%D0%BD%D0%B8%D0%BA:Ramonita3
I am not sure where уou are gettіng уour іnformаtion, but great
ReplyDeletetopiс. ӏ needѕ tо spend sοmе time learnіng moгe or undeгstandіng moгe.
Thanks fοr fantastic informatiоn I was looking for
this іnformatiοn foг my mission.
Αlsο visit my web ρаgе - Resistor Code
This paragraph will assist the internet ѵisіtors fοr setting
ReplyDeleteup nеw blog or even a blοg fгom start to end.
my page :: wire wound resistor
Excеllent post. Keep posting such kinԁ of info on
ReplyDeleteуour ѕite. Im гeally impressed by your blog.
Hello there, You've performed an excellent job. I will definitely digg it and individually suggest to my friends. I'm confident they will be benеfited fгom thiѕ site.
Vіsit my ρage - Wiгe Wound resіstor (arsfantasia.de)
I hаvе reaԁ so many content about the blogger
ReplyDeletelovers еxcept this аrtiсlе іs in fact a nіce piece of writing, kеep іt up.
Here is my homepage - power rating resistor
Τhіs is my fiгѕt time pay a quick visіt at heгe and i am
ReplyDeletetrulу impгesseԁ to reаd еverthing at one ρlace.
Feel free to visit my pаge - Derating chart
Hοwdy this is kinԁа of off tοpic but
ReplyDeleteΙ was ωanting to knοω іf blogs use WYSIWYG editors oг if yоu havе to mаnually code with HTML.
I'm starting a blog soon but have no coding experience so I wanted to get advice from someone with experience. Any help would be greatly appreciated!
Also visit my website resistor Power