Wednesday, February 13, 2013

Tasirin Mu'amala da Wayar Salula ga Al'umma



Matashiya

A yau ina neman afuwan masu karatu, kan rashin ci gaba da silsilar da muka faro a baya kan asalin tunani tsakanin kwakwalwa da zuciyar dan adam.  Hakan ya faru ne saboda nisa da nayi da dakin bincike na.  Ayyuka sun dabaibaye ni, don haka na nemi uzuri.  Idan Allah ya kai mu mako mai zuwa za mu ci gaba.  A gafarce ni don Allah.  A yau za mu ci gaba da silsilar mu ne kan wayar salula da yadda ake mu'amala da ita. 
 
A zangon baya idan masu karatu basu mance ba, mun tsaya da bayani ne kan  Nau'ukan Matsalolin Wayar Salula.  Muna kuma kawo wadannan bayanai ne filla-filla, kamar yadda na sanar a zangon farko, don jama'a su samu gamsuwa kan abin da ya shafi wayar salula gaba dayanta.  A zangon yau ya kamata mu yi magana ne kan Amfanin Wayar Salula, to amma saboda ganin cewa mun sha tattauna wannan maudu'i a baya, za mu wuce zuwa zango na gaba, watau Tasirin Wayar Salula Ga Al'umma.  Wannan matakin bincike ya kasu kashi biyu; kashin farko ya ta'allaka ne ga dalilin yaduwar wayar salula a duniya baki daya, musamman a kasashe masu tasowa.  To amma kwanakin baya na kawo kasidar da na gabatar a taron shekara-shekara na Kungiyar Tsangayar Alheri, inda na kawo dalilan yaduwar wayar salula a duniya, kamar: saukin mu'amala, da saukin farashi, da samuwar nau'uka daban-daban, da yawaitan kamfanonin sadarwa, da zumunci tsakanin kayayyakin sadarwa, da kuma bunkasar bincike kan hanyoyin sadarwa.  Bangare na biyu da ya shafi tasirin wayar salula a al'umma shi ne abin da za mu kawo a yau.  Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare da mu.

Gamammiyar Tasiri ga Al'umma

Tasirin wayar salula da tsarin sadarwarta na da gamewa matuka, kamar yadda na san da dama daga cikinmu zasu sheda.  Akwai gamammiyar tasiri kan al'umma baki daya, da kuma kebantacciyar tasiri da ya shafi mai mu'amala da wayar.  Sanin hakan na da muhimmanci don samun fa'idar da ke tattare da wannan makamin sadarwa ba tare da cutarwa ba.  Za mu fara da gamammiyar tasiri ga al'umma:

Abu na farko shi ne ci gaban tattalin arzikin kasa. Tasirin bunkasar fannin sadarwa yana da gamewa sosai, musamman kan tattalin arzikin al'umma. Domin  hakan na saukake tsarin kasuwanci, da tsarin karantarwa, da tsarin lafiya, da sauran fannonin rayuwa baki daya. Wannan na daga cikin abin da ke kara habbaka tattalin arziki a kasa. Abu na biyu shi ne yaduwar ilmi.  Akwai sanayya da wayar salula ke samarwa ko yadawa a al'umma. Jama'a kan aiwatar da sadarwa a tsakaninsu, musamman a lokutan azumi ko sallah ko wasu bukukuwa na addini. Har wa yau akwai nau'ukan ilmi da ake yadawa ta hanyar wayar salula. A makarantu wasu dalibai kan yi amfani da wayar salula don taskance darasin malami na sauti ko na bidiyo.  Abu na gaba shi ne yaduwar akidu da al'adu.  Wannan shi yafi kowanne hadari daga cikin tasirin da wayar salula ke yi a tsakanin al'umma. Akwai al'adu na banza da wadanda suke masu kyau, da akidun addini ko wasu al'ummomi masu kyau da munana, wadanda ake yadawa ta wayar salula.  Bayan nan, ta bangaren addinin musulunci akwai hadisan karya da wasu ke turowa (watakila saboda rashin sani) kan falalan wasu ayyukan ibada (irinsu azumin watan Rajab – azumin tsofaffi – da sauransu), wadanda duk basu inganta ba a bincike na ilmi.  Sai a rika kiyayewa.  Duk wanda ya turo maka sako kan wani hadisi kuma kai baka san ingancinsa ba, kada ka tura wa wani sai ka tambayi malamai ingancinsa tukun.  Akwai sakonni da ake turowa ace idan ka samu ka tura wa wani, in baka yi haka ba za ka rasa abu kaza ko abu kaza zai same ka, duk wannan rudu ne, kuma masu yada su su ji tsoron Allah. 

Abu na gaba shi ne yawan sace-sace a tsakanin al'umma.  Tabbas yaduwar wayar salula ta 
haddasa yaduwa ko karuwar sace-sace a tsakanin al'umma musamman a manyan biranenmu.  Cikin wannan makon aka fisge wayar salular wani ma'aikacinmu, yana rike da ita yana waya.  Kawai wani ya fisge.  Ka ji karfin hali.  Duk sadda barayi suka kutso gidajen jama'a ko suka darkake su a hanya, abu na farko da suke fara yi shi ne kwace wayoyin salularsu, don tsoron kada a musu cunne ga hukuma. Haka idan aka ganka da waya mai tsada, to, ka yi hankali, musamman idan a cikin birni kake.  Babban abin da ya fi tayar da hankali shi ne yaduwar kasuwannin da ake sayar da ire-iren wadannan wayoyi na salula.  Ya kamata hukuma ta binciki masu sayar da tsofaffin wayoyin salula, ta kuma basu ka'ida da za su rika amfani da ita idan an kawo musu tsohuwar wayar salula kafin su saya.  Domin a galibin lokuta ana kawo musu wayoyin sata suna saya sannan su sayar.  Akwai wata 'yar uwa da aka sace wa wayoyinta guda biyu lokaci guda, a waje guda.  Nan take ta sanar da ni, nace to meye abin yi yanzu? Ta ce ta san inda za ta je ta gansu.  Tana zuwa inda ake sayar da tsofaffin wayoyin salula kuwa sai ga guda daya daga cikin wayoyin (watakila kafin ta zo an sayar da dayan).  Nan fa suka fara dauki-ba-dadi kan wayar, yace sam ba zai bata ba.  Ka ji karfin hali.  Abin mamaki har wajen jami'an tsaro aka je, amma a karshe mahaifinta yace mata ta bar maganar kawai; sai wata wayar aka saya mata.  A ka'ida ya kamata duk masu sayar da wayoyin salula tsofaffi su rika bincikan wanda ya kawo musu wayar sayarwa, domin akwai da yawa na sata ne. In kuwa basu yi hankali ba, to nan gaba za su samu kansu cikin rudu da tashin hankali.  Allah sawwake, amin.

Abu na gaba shi ne zamba-cikin-aminci, watau 419 kenan.  Akwai masu kiran mutane a waya 
ko su turo musu sakonnin tes cewa sun ci reful kaza, za a basu kaza da kaza, amma su turo katin MTN na dubu daya da dari biyar ko wani abu makamancin haka. Wadannan barayi ne.  Ko kuma irin sabon tsarin da 'yan mata ke bi a yau. Sai mace ta kira ka ko ta dame ka da filashin.  Idan ka kira sai ta fara kiran sunan wata, ko wani daban.  Da zarar ka ce ba shi bane, sai ta ja ka da hira: "kai a ina kake da zama?  Ya sunanka?"  Da dai zantuka makamantan haka.  Da zarar ta ga ka fara sakewa da ita, tunda mace ce, sai a rika maka filashin ko ma kira ka, kana daukawa a ce: "don Allah ka kira ni mana."  Kana kira, sai a ce ai an kira ne don a gaishe ka; an ji kwana biyu ba a gaisa ba.  A haka a haka, sai a fara bukatar ka turo katin waya, ko a fara karanto maka matsaloli.  Duk wannan zamba ne cikin aminci.  Don haka duk wanda ya kira ka idan baka sanshi ba, ko yace wani yake nema, ka ce baka sanshi ba.  Kada ka kuskura ka zama aboki da mutumin da baka san dabi'u ko yanayinsa ba.  In kuwa ba haka ba za ka sha mamaki. Wannan dabi'a ta yadu sosai.  A yau kam, ba irin daren da jemage bai gani ba; sai na mutuwarsa.  Allah dada kare mu.

Abu na gaba da yaduwar wayoyin salula ta haifar a tsakanin al'umma shi ne abin yi.  Jama'a da dama sun samu sana'ar yi sanadiyyar harkar wayar salula.  Wasu kan sayar da sababbin wayoyi ne, wasu tsofaffi, wasu kan sayar da bangarorin wayar ne, wasu kuma aikinsu shi ne gyara wayar idan ta lalace maka, wasu kuma aikinsu shi ne sanya wa masu wayar salula wakoki da hotunan bidiyo na wake-wake ko na karatuttuka, don shakatawa. Wannan, ta wani bangaren, ba karamin alfanu bane ga al'umma.  Illa dai nasiha ga masu sanya wakoki a wayar salula, su ji tsoron Allah kada su rika sayar wa jama'a abin da zai lalata musu tunaninsu ko ya cutar da imaninsu.  Amana ne a gare su, kuma sai Allah ya tambaye su ranar kiyama.

Abu na gaba shi ne ingantuwar zumunci.  Lallai an samu ingancin zumunci a tsakanin jama'a, musamman a kasar Hausa.  Yawan tafiye-tafiye don ziyara kadai sun ragu.  Domin kana iya buga waya ko ka rubuta sakon tes ka tura wa dan uwa, sai idan zama ya tsawaita ko wani tsananin bukata da ke sa a yi tafiya.  Bayan haka, hatta mutumin da baka taba ganinsa ba kana iya zumunci da shi muddin ka samu lambarsa ta hanyar da ta dace.  Kasancewarmu musulmi wannan ya dada bamu dama mai kyau kan haka.  Sai abu na karshe da nake son dakatawa a kai, watau saukin rayuwa.  Wayar salula da yaduwarta sun sawwake yadda ake tafiyar da rayuwa baki daya. Dukkan dalilan da na zayya a sama suna nuni ne zuwa ga hakan.  Kana kwance a dakinka ne, ko a tsaye kake, ko a kishingide, ko a shagonka kake, ko a harabar masallaci kake, ko a ina kake, za ka iya aiwatar da sadarwa.  Sannan kana iya mu'amala da fasahar Intanet ta wayar salularka.  Duk wannan ya dada saukake mana tsarin rayuwa musamman ta hanyar sadarwa.

Kebantattun Tasiri ga Mai Mu'amala

Bayanan da suka gabata kan tasirin wayar salula ne ga al'umma baki daya. Akwai wasu kebantattun tasiri da suka shafi daidaikun mutane da ke amfani da wayar salula.  Abu na farko shi ne tasirin wayar salula kan dabi'ar mai amfani da ita.  Amfani da wayar salula kan samar da wata sabuwar dabi'ar rayuwa ta musamman da mai yin hakan bai sani ba.  Abu na farko shi ne canza masa tsarin tunani, musamman wajen gaugawa da ci-da-zuci.  Wanda ya saba mu'amala da wayar salula gani yake kamar komai zai iya yi muddin ta hanyar sadarwa ne; da abu mai kyau da mara kyau.  Sannan  akwai sauyin tunani wajen tafiyar da rayuwa. Da dama cikin samari kan ji nakasa idan wayarsu tsohuwa ce ko ba wacce ake yayi ba ko  kuma idan ba su da wayar ma gaba daya.  Haka idan suna da waya mai tsada, sai su rika jin ai su wani ne.  Haka ma 'yan mata su ke.  Nan gaba za mu karanta bayani kan irin nau'in wayar da ta kamata mutum ya saya. 

Abu na gaba shi ne tasirin wayar salula kan lafiyar mai mu'amala da ita.  Da yawa cikin samari kan kashe dare suna waya ko suna 2go, ko BB Chat idan masu Blackberry ne; duk hakan kan yi tasiri kan lafiyar jikinsu, musamman idan dalibai ne su.  Haka kuma, yawan amfani da wayar salula musamman lokacin tuki ta hanyar karba kira ko rubuta tes, yana barazana ga rayuwa.  A kasar Kanada da Amurka an tabbatar da cewa kaso mafi yawa na dalilan da ke haddasa hadarurrukan mota a kan manyan titunan kasashen duk ta sanadiyyar mu'amala da wayar salula ne.  Sai abu na karshe, watau tasirin wayar salula kan tattalin mai mu'amala.  Da yawa cikin samari 'yan karya sukan kashe galibin kudadensu ne wajen sayen katin waya don kiran 'yan matansu ko don tura musu.  Hakan ba haramun bane a shari'ance idan mutum yayi da manufa mai kyau, amma sau tari za ka samu kundunbala ce ake yi. Sai a bar abin da ke da muhimmanci a yi wanda bai kai shi muhimmanci ba.  Har wa yau wasu sun fi son a duk lokaci a gansu da waya mai tsada ko wacce ake yayi.  Wannan ke sa dole su ci bashi ko su kure aljihunsu don ganin sun mallaki wayar da suke bukata.  Wadannan, a takaice, su ne gamammu da kebantattun tasirin da wayar salula da yaduwarta ke haddasawa a al'umma ko ga daidaikun mutane.

No comments:

Post a Comment