Wata Sabuwar Duniya
Idan masu karatu basu mance, a shekarar
da ta gabata ne muka kawo kasida mai shafi goma, mai teken: Dandalin
Facebook a Mahangar Binciken Ilmi. A ciki mun yi bayani filla-filla kan
asali da samuwar wannan dandali, da yadda ake rajista, da yadda ake mu'amala da
shafin, da kuma wasu daga cikin matsalolin da ke tattare da dandali a mahanga
mai fadi. A yau ga shi mun dawo ne don
kara bayani kan abin da ya shafi matasanmu, da irin rayuwar da suke yi a
dandalin, wanda hakan zai fahimtar da mu wasu abubuwa masu muhimmanci, musamman
kan mummunar tasirin wannan dandali kan tunani da fahimtar matasanmu. Kafin mu yi nisa, ina son masu karatu su
fahimci cewa wannan kasida ta fadakarwa ce kawai, ba tonon asiri tazo yi
ba. Ba zan ambaci sunan kowa ba.
A bayyane yake cewa akwai matasanmu da yawa a dandalin Facebook. Ba za ka san hakan ba sai ka shiga. Za ka ga mutane, tsakanin 'yan mata da samari
da tsofaffi da zawarawa da gagware wa tuzurai, duk sun yi rajista kuma suna
sada abin da suke kira "zumunci."
Babban abin da ya sawwake yaduwarsu a wannan dandali kuwa dalilai ne
guda biyu. Abu na farko shi ne samuwar
wayar salula a hannun jama'a, wanda ya game gari da duniya baki daya. A Najeriya akwai layukan wayar salula sama da
miliyan 90 a kididdigar shekarar da ta gabata.
A arewacin kasar akafi samun jama'a masu dauke da wayar salula. Galibin wayoyin salular wannan zamani kuwa
duk karancin kudi da araharsu, za ka samu suna dauke ne da hanyar sadarwa ta
Intanet. Wannan ya sa duk wanda ke da
wayar salula a hannunsa, to kamar yana da shafin Facebook ne, domin yin
rajista babu wahala. Karin a kan haka,
sai kamfanin Etisalat ya gina wata manhaja ta musamman na shafin Facebook, muddin
ka shiga shafin, nan take za ka iya saukar da wannan manhaja, ka yi rajistar
shafinka na facebook ba tare da wata matsala ba. Sannan, ko babu ko sisi a wayarka kana iya
shiga, in dai layin Etisalat kake amfani da shi. Abu na biyu shi ne saukin mu'amala. Shafin facebook yana da saukin mu'amala. Wannan yasa duk wanda ya shiga sau daya sau
biyu, ba ya bukatar wani darasi kuma.
Manufofi
Wadannan dalilai biyu suka taimaka wajen yaduwar matasanmu a
dandalin facebook. Kowa na son ya shigo
don ya nemi abokai ko 'yan mata, ko samari da dai sauransu. A kasidar baya mun nuna cewa daga cikin
amfanin dandalin facebook akwai sadarwa, da yin abota, da samar da sanayya mai
amfani da amfanarwa, da fahimtar rayuwa ta hanyar kallon yadda wasu ke tafiyar
da rayuwarsu a duniyar da suke. Har a
yanzu akwai wadannan amfanoni basu gushe ba a dandalin facebook. Akwai majalisu da matasanmu suka kafa, masu
amfani sosai. Akwai zaurukan tattaunawa
na musamman masu amfani su ma. Sannan
kuma wasunsu sun samu hanya mafi sauki wajen yada addini da shari'ar musulunci. Wasu sun yi abota ta Allah da Annabi. Wasu
sun yi kawance ta Allah da Annabi. Amma
galibin mu'amalarmu, ina nufin mu matasan kasar Hausa, akwai alamar tambaya
kanta.
Dandalin Abota, ko Dandalin Badakala?
Babban abin da yafi ban cikin al'amuran matasanmu a dandalin
facebook shi ne, rashin manufa takamaime a yayin da suke shawagi da shantakewa
a dandalin. Abu na farko da aka sansu da
shi shi ne yawan ruduwa da 'yan mata. Duk
wacce ka shiga shafinta a dandalin facebook in dai budurwa ce, za ka ga kashi
90 cikin abokananta maza ne. Da zarar ta
yi tari, ko "mhmm" ta rubuta a shafinta, nan take za ka ga ta'aliki
(comments) daga maza sama da hamsin kafin sa'a guda. Duk abin da tace sai an ce wani abu a
kai. balle ta loda hoto a shafin. Ba sai na gaya muku abin da zai faru ba. Su kansu 'yan matan haka suka fi so. Musamman wasu ke daukan hotuna su loda a
shafinsu, don su ji me samari za su ce.
Idan kana karanta sakonnin da matasa ke rubutawa dangane da wadannan
hotuna sai ranka ya baci. Wai duk nan
yabonta ake. Abu na biyu shi ne
yaudara. Su kansu wasu daga cikin 'yan
matan karya suke yi, hotunan wasu suke lodawa suce nasu ne. Su ma samarin suna haka. Don haka galibin
samarinmu, ba duka ba, idan ka shiga shafukansu ba abin da za ka gani sai
surutai kan 'yan mata, da wasannin kwallon kafa da hotunansu, da abubuwa marasa
kima. Wanda hakan ke nuna cewa mai
wannan shafin ya shigo ne kawai don yayi ta walagigi mara ma'ana.
Abu na gaba shi ne cin mutuncin abokin magana. Da yawa daga cikin matasa a dandalin facebook ba su da da'a, musamman dai a
majalisun da ake tattaunawa kan abubuwan da suka shafi al'umma. A daya daga
cikin manyan majalisun da ke shafin facebook na matasanmu, na sha karanta
zage-zage, da surutan cin mutuncin abokin zance; ba kunya ba tsoro. A wasu lokuta sai na sa baki al'amuran ke
sassautawa. Wannan bai dace ba. Sai kuma batun batsa da ashararanci. Wannan kuma ya kasu kashi biyu. Akwai zantuka da wasu matasanmu ke yi kan
hotunan 'yan mata da niyyar yabo, ko kokarin gamsar da 'yan matan cewa suna da
kyau. Idan ka karanta ire-iren wadannan
zantuka sai ranka ya baci. Sai kuma yaudara, wanda wannan ruwan dare ne a
dandalin facebook. Da yawa cikin mutane kan rubuta abin da ba shi bane hakikanin
rayuwarsu. Wannan tasa idan kana karanta
bayaninsu a "Profile" sai ka ga akwai tufka da warwara. Misali,
yarinya ko matashi zai ce musulmi ne shi, mai son Manzon Allah, mai kishin
musulunci, littafinsa shi ne Kur'ani da Hadisi, amma idan aka zo wajen "Hobbies"
ko "Interests", watau abin da yake sha'awa a rayuwarsa ko rayuwarta,
sai ka ga ya zayyana sunayen manyan makiyan Allah daga cikin mawakan turai, da
miyagun fina-finan da a zahiri suna cin mutuncin addini ne, ko ma wasunsu duka
cike suke da batsa da rashin tarbiyya.
Wannan tufka da warwara ne ko shakka babu. Galibin matasa idan ka shiga
"Profile" dinsu za ka ta cin karo irin wannan.
Abu na gaba shi ne yawan kankamba da fadi-ba a tambayeka ba. Akwai majalisa ta musamman da ake amsa
tambayoyi kan al'amuran addini, ma'ana majalisa ce ta fatawa dai a
takaice. Akwai wadanda aka killace
musamman don amsa tambayoyi, wanda hakan ya kamata daman. Tun da shari'ar musulunci na gudanuwa ne
cikin tsari, sannan ba kowa bane ke da kudurar amsa fatawa, domin amana
ce. Amma abin mamaki da zarar wani ya
aiko tambaya, kafin wadanda aka killace su bayar da amsa, nan take za ka mutum
yayi caraf ya fara magana, a ciki yana cewa: "…a gani na abu kaza
hukuncinsa kaza ne." Ko "…a fahimta ina ganin kaza zai zama
kaza." Sai kace an nemi shawararsa.
Ya mance cewa ilmi amana ce, kuma ba a gudanar al'amuran addini da
jahilci. A wannan majalisar har wa yau,
da zarar mace ta aiko tambaya, kafin a bayar da amsa nan take samari sama da
goma sun fara tofa albarkacin bakinsu, duk dai don neman samun shiga. Mun dauki addini abin wasa.
Abu na gaba shi ne rashin sirri.
Da yawa daga cikin matasa har yanzu sun kasa fahimtar mummunar hadarin
da ke tattare da rashin sirri. Idan kana
son fahimtar hakan kuwa sai ka shigo dandanlin facebook. Da wanda ke kwance a kan gado yana hutawa, da
wanda ke cin tuwo miyar kuka, da wanda ke zance budurwarsa, da wanda ke shan
shayi, da wanda ke kan hanyar tafiya zuwa wani garin, da wanda zai shiga wanka,
da wanda ke sanya tufafi, duk za ka gani a facebook, matasanmu sun shigar. Ba ruwansu da mai zai je ya dawo. A sauran kasashen da suka ci gaba a fannin
sadarwa, zantuka irin wadannan sun yi sanadiyyar mutuwar wasu, da hasaran
rayuka, da ta'addanci, da rasa matsayin siyasa da shugabanci, da karyewar arziki,
da mutuwar auratayya da dai sauransu. To
amma matasanmu ko a jikinsu, wai an tsikari kakkausa. Kari a kan haka har da hotuna marasa kan
gado. Wasu hotunan ma basu kamata a ce an nuna su ga duniya ba, amma a shafin
facebook duk za ka gansu.
Abu na gaba shi ne kankamba wajen latse-latse da matse-matse. A ka'idar yadda shafin facebook ke gudanuwa,
duk halin da abokanka ke ciki ana sanar da kai ne. Idan abokananka suka kalli wani hoto ko
bidiyo da Intanet ta hanyar manhajar facebook, za a sanar da kai. Matsalar ita ce, da zarar an sanar da kai,
sai kaji kaima kana son ka kalla, da zarar ka matsa shikenan, hoton ko bidiyon
ba zai bude ba, sai an kaika asalin shafin.
Ba wannan bane matsalar, galibin ire-iren wadannan hotuna da bidiyo na
batsa ne, amma kai ba za gani a fili, da
zarar ka matsa, nan take za a kai wa abokanka sanarwa cewa ka kalli hoto ko
bidiyo kaza, mai dauke da batsar, amma kai ba za ka gani ba. Ka ga a nan kai baka ga wannan hoto ba, amma
an kai wa abokanka sanarwa cewa ka gani.
Idan mai mutunci ne kai, kimarka ta zube kenan a idonsu. Matasanmu duk basu lura da wannan. Duk abin da muka ga ana yi sai kawai mu ma
muyi, ko bamu san amfaninsa ba. Wadannan
kadan ne cikin badakalar da ke faruwa a
dandalin facebook kan abin da ya
danganci matasanmu.
Kammalawa
Kafin mu karkare, biyu daga cikin manyan dalilan da ke haddasa
wadannan abubuwa kuwa su ne: samun sakakkiyar 'yanci, da kuma rashin
tarbiyya. Galibinmu idan muna dauke da
wayar salula a cikin dakunanmu sai mu ga komai ma muna iya yi. Sannan idan hakan ya hadu da rashin tarbiyya
sai lamari ya lalace. Rashin tarbiyya ya kunshi tsarin tsara lokaci kan duk
abin da muke yi. Galibi muna shiga
facebook ne kawai mu yi shashanci ba wai mu karu da wani sabon ilmi kan abin da
bamu mallaka ba. Wannan shirme ne. abu na biyu shi ne rashin manufa. Ba mu da manufa ta gari. Abin da muka ga ana yi sai kawai mu buge da
yi. Meye amfaninsa? Oho!
Wannan ya fi yawa a bangaren matasanmu maza. Wajibi ne mu rika lura da manufarmu kan abin
da muke yi a Intanet. Duk abin da ba zai
samar maka da wani alfanu ba, kayi hakuri dashi shi yafi alheri. Allah sa mu dace.
No comments:
Post a Comment