Matashiya
A yau ga mu dauke da amsoshin sakonninku da kuka turo cikin
kwanakin baya. Na san da yawa cikin masu
karatu sun ta neman layina basu samu ba, wasu ma sun ta turo sakonnin tes amma
abin yaki zuwa. Wannan ya faru ne saboda
tafiya da nayi zuwa wata kasa, ban dawo ba sai bayan kwanaki 40. Lokacin da na mayar da layin babu abin da ya
shigo. Amma na fahimci haka ne daga sakonnin da na samu a shafina na Facebook,
da kuma kira da wasu suka yi bayan dawowa ta.
Don haka a gafarce ni. Duk wanda ya turo sakon tes tsakanin ranakun 10
ga watan Oktoba zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba, to sakon bai iso ba. Na so in sanar kafin tafiya ta, amma sai
shaitan ya mantar da ni. Wadannan
sakonnin da na buga a yau duk wadanda aka turo ne kafin 10 ga watan Oktoba.
Bayan haka, wasu daga cikin sakonnin nan na amsa su, ko ta hanyar
Imel, ko ta hanyar sakonnin tes da aka turo su.
To amma saboda na kasa tantance wanne ne na amsa wanne ne ban amsa ba,
shi yasa na hado su duka. Akwai masu turo tambaya ko bukata su ce kada a buga,
nakan ware nasu. Da zarar na amsa nan take nake goge su don kada in cakuda da saura. Amma ta yiwu in mance ban goge ba saboda
ajizanci, idan mutum ya ga tes makamancin haka na buga, to, sai ya gafarce
ni. Bayan haka, saboda wasu matsaloli da
na samu da adireshin Imel din da nake karban sakonninku ta Intanet, na canza
wani sabo. Adireshin shi ne: fasaha2013@gmail.com.
Zan yi kokarin kankaro sakonnin da ke wancan jaka don tabbatar da cewa
na amsa wa masu su.
A karshe ina kira ga dukkan masu turo sakonnin tes ko sakonnin
tambaya ko karin bayani ta Imel, da cewa su rika rubuto sunayensu, da inda
suke, don wannan ita ce ka'ida. Don
Allah a rika rubuta sunaye da kuma inda ake.
Daga yanzu zan ci gaba da maimaita irin wannan sako zuwa wani lokaci. Duk wanda ya aiko sako ba tare da rubuta
sunansa da inda yake ba, to ba zan buga ko amsa masa ba. Sai a kiyaye.
……………………………………….
Salamun aliakum Baban sadiq, ina yi maka fatan alhairi, yaya aiki? Da
fatan Allah ya taimaka, amin. Suna na Haruna Boda Madalla.
Wa alaikumus salam Malam Haruna, na gode da gaisuwa da kuma addu'a.
Allah saka da alheri, ya kuma bamu dacewa cikin dukkan lamuranmu baki daya,
amin.
Assalamu alaikum Baban Sadiq ya ya aiki? Wai don Allah mutum zai iya aika sakon hoto
ko da wayarshi karama ce? Kuma wanda ka
tura masa zai gani rangadau? Daga Usman
Muazu Funtua
Wa alaikumus salam, Malam Mu'azu barka dai. Eh, kana iya aika sakon hoto ko da wayar
karama ce, domin galibin wayoyin salula na wannan zamani duk suna zuwa ne da
wannan ka'idar aika sakonnin hotuna mai suna MMS. Sai dai ya danganci ingancin hoton, da kuma
girma ko kankantar wayar wajen bayyana hoton. Ma'ana, idan na'urar daukan hoton
da aka yi amfani da ita wajen daukan hoton karama ce, ka ga hoton ba zai
bayyana rangadau ba. A daya bangaren
kuma, ko da babbar kyamara ce aka yi amfani da ita wajen dauka, idan wayar mai
karban sakon karama ce, mai karamar fuska, hoton ba zai bayyana rangadau
ba. Da fatan ka gamsu.
Don Allah Baban Sadik ina son karin bayani game da kyautar nan mai
suna (BBC Award Mobile Anniversary Day).
Kwanan nan an aiko mani da sakon na ci wannan kyauta ga alama gaskiya ne? An ce in tura wasu bayanai zuwa ga wannan adireshi
bbc_int@live.co.uk. Anya wannan adireshin
gaskiya ne? Daga mai kaunarka Usman
Aliyu Fatakwal.
Malam Usman, ba gaskiya bane ko kadan. Da farko tukun, ta ina suka samu lambar
wayarka, da sunanka, da kuma inda kake? Da wasu irin lambobi suka yi amfani
wajen turo maka sakon? Na tabbata
lambobin kasar Ingila ne, ba lambar kamfanin wayar MTN ba (misali: 0803). Sannan wannan adireshin Imel din da suka baka
ba na kamfanin BBC bane ko kadan. Na
'yan cuwa-cuwa ne. A takaice dai idan ka bi su a hankali, za a kai lokacin da
za a ce maka ka turo da wasu kudade ta hanyar taskar ajiyar kudi da ke Turai ko
nan Najeriya. Wannan sakon na 'yan
damfara ne, kada ma ka kasa sauraransu.
Nan gaba zan kawo bayani kan dabarun da suke amfani da su hatta a
Dandalin Facebook, don damfarar mutane a Najeriya. Idan ka dubi adireshin Imel din da ke sama,
babu ambaton BBC a ciki. Wanda hakan ya
saba wa al'adar kamfanin BBC. Duk wani
sashe da za ka yi mu'amala da shi in dai na kamfanin BBC ne, dole adireshin da
za a baka ya zama na kamfanin BBC ne.
Akwai babban yayana, shi ma ya taba fadawa irin wannan tarko. Da ya zo ya same ni, na masa bayani, saura
kadan ya tura musu kudade, sai na nusar da shi.
Sauran bayanai dai sai a kasidar "Rayuwar Matasanmu a Dandalin
Facebook (5)" in Allah ya yarda. A
takaice dai, wannan sakon bogi ne, na 'yan damfara. Sai a kiyaye.
Amincin Allah ya tabbata a gareka da kuma yardarsa. Allah ya kara maka girma da kuma basira. Ina rokon Allah ya kara maka kaifin basira a kan
wanda kake da shi a yanzu.
Amin summa amin. Ina
maka/miki fatan alheri, da addu'a makamanciyar wannan a gare ka/ki. Allah ya saka da alherinsa, amin.
Salamun alaikum, Malam Abdullahi da fatan ka wuni lafiya. Daman kiran da nayi maka taimako nake nema a game
da tsarin da zan shiga don in rika samun sakonnin tes na kyauta da kamfanin mtn
ke bayarwa. Idan Allah ya sa ka sani ka sanar
dani, domin ina son tsarin. Na gode Allah
ya kara maka girma da hakuri amin.
Abubakar Babani, Yola.
Wa alaikumus salam, Malam Abubakar da fatan kana lafiya. Idan kana bukatar sakonnin tes na kyauta da
MTN ke bayarwa, sai ka shiga tsarinsu da suke kira "MTN Pulse," duk
sadda ka sa kudi a layin, akwai adadin sakonnin tes na kyauta (Free SMS) da
suke bayarwa. Iya yawan kudin da ka sa, iya yawan sakonnin da za su ba ka. Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum Baban Sadiq, Allah ya bamu sa'a amin. Don Allah
ina son ayi mini bayani game da "PDF" da kuma "Adobe Reader."
Kuma mene ne "RAM" da "Wikipedia" da "Google" a kimiyance?
Kuma meye aikinsu? Kuma meye ban-banchin "WIFI" da "3G Service"?
Allah yasa mu dace amin. Ibrahim Muh'd. Rinji, Bauchi state. 08065750790
Wa alaikumus salam Malam Ibrahim, da fatan kana lafiya kai ma. Abin
da kalmar "PDF" ke nufi a warware shi ne: "Portable Document
Format," masarrafa ke da ake amfani
da ita wajen taskance bayanai a yanayi mai cike da kariya da kuma inganci. Sai
dai kuma dole ne sai kana da masarrafar a waya ko a kwamfutarka kafin ka iya
budo jakar bayanai da aka turo maka a wannan tsari. Sai kalmar "Adobe
Reader," wadda ita ce masarrafar da ke taimakawa wajen budo jakar bayanan
da aka taskance cikin tsarin PDF.
Dukkansu biyun, kamfanin Adobe Inc. ne ya mallake su. Don karin bayani
kana iya zuwa shafin: www.adobe.com inda za ka iya saukar da masarrafan
kyauta. Sai kalmar "RAM",
wanda ke nufin "Random Access Memory." RAM ma'adana ce daga cikin ma'adanonin
kwamfuta. Mizani mizani ce. Ita ce ma'adana ta biyu bayan ma'adanar "Hard
Disk Drive," wato babbar ma'adana kenan.
Amfaninta shi ne, a duk sadda ka budo wata manhaja ko masarrafar kwamfutar
(ko na wayar salula, don ita ma tana da ma'adanar RAM), za a dauko ta ne daga
babbar ma'adana, zuwa RAM. A nan ne za
ta bude, kayi duk abin da kake son yi da manhajar ko masarrafar. Iya girman mizanin RAM din, iya saurin
manhajar wajen mu'amala da ita. Da zarar ka gama amfani da manhajar ka rufe,
nan take za ta koma babbar ma'adana, inda take kafin ka budo ta. Kalmar "Wikipedia," kuma sunan wani
gidan yanar sadarwa ne mai dauke da babban kamus din yanar gizo, wato
"Online Encyclopedia." Duk
abin da kake nema, da zarar ka shiga ka binciko, za ka samu cikakkun bayanai
masu gamsarwa a ciki. Za ka iya samun
shafin a http://en.wikipedia.org. Haka ma kalmar
"Google", gidan yanar sadarwa ne sannan kuma masarrafar tambayar
bayanai ne, wato: "Search Engine."
Kalmar "WIFI" da "3G Service" kuma na taba amsa maka
tambaya a kansu. Don haka a yi hakuri da
abin da ya samu a baya. Da fatan ka
gamsu.
Salam, ka yi bayani a kan hanyoyin da ake samun kwayoyin cutar
wayar salula, wato "Virus," ko akwai wata hanya da za mu gane shafuka
ko hotunan da suke dauke da "Virus"?
Daga Aminu Garba Dirimin Sambo, Kano
Wa alaikumus salam, Malam Aminu lallai gane hakan abu ne mai yiwuwa
amma sai ga kwararru. Domin abu mai
matukar sarkakiya. Musamman ganin cewa
abu ne mai sauki ga kwamfuta ko wayar salula ta kamu da cuta, amma ba a iya
ganewa sai bayan lokaci mai tsawo. Bayan
haka, akwai nau'ukan kwayoyin cutar kwamfuta wadanda ba a iya ganewa; za su
shiga kwamfutar, su gudanar da duk abin da suke son gudanarwa na satar bayanai
ko leken asiri, ba tare da mai kwamfutar ya sani ba. Don haka, abin da zai tabbatar maka cewa
kwamfutarka ta kamu da cuta shi ne ya zama tana yawan saibi, tana kunnawa da
kashe kanta ba tare da ka matsa ko latsa, ko danna maballin kashewa ba, ko ka
nemi jakunkunan bayananka ka rasa, ko kuma ka gansu, amma ka kasa bude su ko
sarrafa su yadda kake so, ko kuma, a karo na karshe, ka gansu da wasu sunaye
dabam, ba sunayen da ka basu ba. Duk
wadannan alamomi ne na zahiri da ke nuna maka cewa kwamfutarka ta kamu da
cuta. Da fatan an gamsu.
Assalaamu alaikum Baban Sadiq, na kasance ma'abocin karanta rubutunka
a jaridar AMINYA. Dalilin haka yasa ina bukatar in samì ìlimi mai zurfi a kan ilimin
kwamfuta. Don Allah yaya zan yi mu hadu da kai domin ka sa ni a hanya? Daga
Mujtaba Dan Ai, Kabara Kano
Wa alaikumus salam, Malam Mujtaba kana iya kira na a lambar da ke
sama, na ba ka izini. Sai dai zai dace
ka san cewa ba a Kano nake da zama ba, ina Abuja ne da'iman. Ina sauraron
kiranka. Na gode.
Assalamu alaikum Baban Sadiq, Allah yasa ka tashi lafiya da kai da
iyalanka amin. Don Allah ina bukatan taimako da bayanai kan waya nau'in Blackberry,
ta wannan adireshin. (Bbycopshon@yahoo.com) Ko kuma a wani shafin naku zan je
na saukeshi kai tsaye? Kuma mene ne "Cookies"? Galibi ina ganin
kalmar a bangaren tsare-tsaren Intanet.
Wa alaikumus salam, na tura maka sakon. Sai ka duba jakar Imel dinka.
"Cookies" kuma wasu nau'ukan jakunkunan bayanai ne da masarrafar lilo
(Browser) ke tarawa, a yayin da kake yawo a shafukan Intanet. Amfanin yin haka shi ne, a duk sadda ka
bukaci komawa daya daga cikin shafukan da ka baro a baya, da zarar ka shigar da
adireshin, kwamfutarka za dauko maka shafuka da ta taskance a lokutan baya, ba
sai ta koma hakikanin gidan yanar sadarwar ba.
Bayan haka, "Cookies" wata hanya ce da ake amfani da ita wajen
gano zirga-zirgan mai waya ko mai kwamfuta a shafukan Intanet. Da fatan ka gamsu.
No comments:
Post a Comment