Matashiya
A makon da ya gabata mun kawo wasu daga cikin jerin shahararrun
katobara da wasu suka taba yi a Dandalin Facebook, da irin tasirin da
hakan yayi ga rayuwarsu ko rayuwar wadanda suke tare da
su ko na al'umma. Kada a mance, wadannan
labarai dai fadakarwa ne. Kuma kada a mance har wa yau, labarai ne masu koya wa
mai karatu darasi kan tsarin ma'amala da kayayyaki da hanyoyin fasahar sadarwar
zamani. Muna kuma kallon samfurin rayuwa
ne daga wasu kasashe. A yau za mu ci
gaba.
Manyan Katobara a Dandalin Facebook
Daga cikin manyan katobara akwai wanda wani barawo ya taba yi. Barawo ne cikakke, wanda ke fasa gidajen
mutane yana kwashe musu kayayyaki, don holewarsa kawai. Ya taba shiga gidan wani bawan Allah mai suna
Marc Fisher, ta kofar baya, bayan ya fasa kofar. Bayan ya shiga gidan, ya kwashe duk wani abin
amfani da idonsa ya kai gare shi. Daga
kwamfuta, zuwa gwalagwalai, da kayayyakin amfani, ciki har da 'yar karamar
kwamfutar dansa mai suna Aaron. Daga nan
yayi sa'a da wasu tsaban daloli a cikin wata ma'ajiya, nan ma ya debe su. Yana gamawa kawai sai ya fice daga gidan,
hannunsa ful da haramtacciyar ganimar da ya kwashe.
Aaron, dan wannan mai gida, yana shigowa ya gane abin da ya
faru. Daga nan ya sanar da mahaifinsa,
shi kuma ya sanar da jami'an 'yan sanda.
Bayan wasu 'yan lokuta ba a gano wanda yayi wannan ta'asa ba. Rannan kawai sai Aaron ya shiga shafinsa na
Dandalin Facebook. Shigansa ke da wuya sai yayi kacibis da hoton wannan barawo
a shafinsa; wanda barawon ya dauki kansa da kwamfutar da ya sace, sadda yake
aiwatar da aika-aikansa a gidan. Ga
tsaban kudin da ya sata a hannunsa rike da su, ga fuskarsa warewake, in ji
Zage-zagi. Sannan ya sake amfani da
kwamfutar yaron, ya shiga shafinsa da ke Facebook har wa yau. Nan take ya kira 'yan sanda. Daga nan aka samu kwararru kan harkar
kwamfuta suka shiga shafin barawon, suka gano adireshinsa, har aka gano inda
yake, aka kama shi. Ashe bayan ya saci
komai, sai kawai ya kunna kwamfutar yaron a gidan, ya dauki kansa hoto, tare da
kudaden da ya sata, sannan bayan ya tafi, yayi amfani da kwamfutar yaron ya
shiga shafin yaron a Dandalin Facebook, ya loda hotunan da ya dauki kansa,
sannan ya sake shiga shafinsa da ita.
Iya karshen wauta da katobara da ganganci kenan. An yi binciken duniyan nan ba a gano shi ba,
sai ta hanyar Facebook! A yanzu da mai karatu ke karanta wannan labari, wannan
barawo na can cikin fursuna yana zaman kaso.
Cikin shekarar 2010 ne aka kaddamar da gasar kwallon kafan kofin
Stanley a kasar Kanada, wato "Stanley Cup." A lokacin wasan karshe abu bai yi wa masoya
kwallon kafan kasar dadi ba, musamman matasa.
Wannan ya haddasa zanga-zanga mai girman gaske, wanda a karshe abin ya
koma wani abu daban; masu doke-doke na yi, masu zanga-zanga na yi, masu fasa
motocin jama'a na yi, masu shaye-shaye da raye-rayi a tituna na yi. Abin dai ya tashi daga zanga-zangar kin
amincewa zuwa zanga-zangar fashe-fashe da dauke-dauke da doke-doke da
shaye-shaye. Duk motar da aka samu sai a
mata kaca-kaca, a wuntsilar da ita; kanta a kasa kafafunta a sama. Ga matasa nan birjik, galibinsu a tube, daga
su sai wanduna. Wasu rike da kwalaben
giya suna ta kurba, wasu kuma rike da makaman fasa gilasan motoci. Bayan masu wannan aika-aika, wanda ya faru a birnin
Voncouver na jihar British Columbia da ke kasar ta Kanada, a daya gefen kuma
akwai masu daukan hotuna, wadanda su ma suna cikin masu zanga-zangar. Duk abin
da ake ta yi a wurin, suna dauka, hankali kwance.
Jami'an tsaro sun kasa hana wannan ta'asa saboda yawan masu
zanga-zangar. Kuma ga shi hakan ya
haifar da hasarar dukiya mai dimbin yawa na jama'a da na hukuma. Wannan tasa dole a nemo wadanda suka yi
wannan aika-aika, in so samu ne ko fuskokinsu a gani, kamar yadda hukuma ta
shawarta. Hanya mafi sauki da za a iya
samun hakan kuwa shi ne, tunda galibin wadanda suka yi wannan ta'asa matasa ne,
ba za a rasa wani abin dauka a Dandalin Facebook ba. Daga nan hukuma ta sa aka kirkiri wani shafi
na musamman ta karkashin kasa, don tattaro hotunan da aka dauka lokacin wannan
zanga-zanga da ya haifar da hasarar dukiya da kaddarorin hukuma. Shafin da aka kirkira shi ne, "The
Voncouver Riot Photos," wato shafin
tattaro hotunan da aka dauka lokacin zanga-zangar Voncouver.
Kwamfa! Nan take sai matasa
suka yi tururuwa wajen loda hotunansu; wasu rike da kwalaben giya, wasu a saman
buraguzan motocin da suka farfasa, wasu a kwance a kasa a tube suna ta holewa,
wasu kuma suna kan aikata aika-aikarsu.
Nan take hukuma ta tara hotuna masu dimbin yawa ta wannan hanya. Daga nan aka ga fuskokin jama'a warewake,
inji Zage-zagi. Wannan ba karamin wauta
bane. Mutum ya aikata laifi, ya kuma
dauki kansa hoto sadda yake aikatawa, sannan ya mika wa wanda ke nemansa
hotunan, a sadda ake nemansa. Wannan katobara in ba a Facebook ba, babu inda za
ka samu. To me ya kaisu wannan danyen
aiki na loda hotunansu a shafin? Dalilin
dai guda daya ne, wato son birgewa, da nuna isa, wadanda ke dauke cikin dabi'un
wauta da rashin hangen nesa. Nan take
hukuma ta rairayo wadannan hotuna. Amma
kafin daukan mataki kuma sai ta samu kanta cikin tsaka mai wuya. Domin daga hotunan, akwai wadanda holewa
kawai suke yi da kwalaben giyansu, akwai kuma wadanda suke aikata
aika-aikarsu. Ta yaya za a bambancewa
tsakanin masu fashe-fashe da doke-doke, da wadanda kallo kawai suke yi? Wannan kuma aikin hukuma ne ta tuhume
su. Amma dai duk sun shiga hannu, ta
hanyar Facebook!
Daga cikin katobarar da aka taba tafkawa a Dandalin Facebook akwai
al'amarin wata baiwar Allah mai suna Nathalie.
Wannan mata dai ma'aikaciya ce a daya daga cikin kamfanonin kasar
Amurka. Tana kan aika sai ta samu
matsalar rashin lafiya mai alaka da kwakwalwa da ake kira "Clinical
Depression." Matsala ce mai alaka
da saitin tunani, kuma hakan na tasiri kan aikinta. Don haka sai likitanta ya baiwa kamfanin da
take wa aiki shawara cewa a barta ta je hutu na tsawon lokaci, don samun sakewa
da mance matsalolin da suka jefa ta cikin halin da ta samu kanta. Sannan ya shawarce ta da cewa, in so samu ne
ta yi bulaguro zuwa wasu wurare ta hole iya gwargwado. To, ka san abinka da Turawa. Sai ta dauki hutu zuwa jihar Fulorida, daya
daga cikin jihohin Amurka. A lokacin
bulaguronta ne ta dauki hotuna a bakin teku, sanye da tufafin wanka da
shakatawa a bakin teku. Ga su nan kala-kala, wadanda duk wanda ya gani, zai ce:
"kai, su wance ana holewa, ana shakatawa." A sadda take wannan bulaguro nata, sai tayi
ta loda wadannan hotuna da take daukawa a shafinta na Facebook, a cewarta:
"Don kada wadanda basu ganni ba lokaci mai tsawo su dauka wani mummunar
lamari ne ya same ni. Na kuma yi haka ne don in nuna wa jama'a cewa lallai lafiya kalau nake."
To amma tunda ba kawaye da abokananta bane kadai ke shiga shafinta
na Facebook, har da kamfanin Inshoranta, nan take sai ta shiga matsala. Ashe kamfanin Inshoranta da ke daukan nauyin
lafiyarta da kuma lura da gidanta da ta dauka bashi, yana biye da ita ta shafin
Facebook ba ta sani ba. Ganin wadannan
hotuna da loda a shafinta, sai kamfanin ya yanke tallafin da yake bata kan
lafiya, sannan ya kwace gidan da take ciki.
Meye dalili? Kamfanin yace da
ganin hotunan, ta je shakatawa ne da holewa.
Daman can lafiyarta kalau. Karya ta yi kawai tace ba ta da lafiya. Domin duk wanda ya ga hotunan, idan ba yasan
halin da take ciki bane hakikatan, babu yadda za a yi ya yarda cewa mara lafiya
ce ita. To amma ai likita ne ya ce mata
ta dan hole, saboda samun mance matsalolin da ta samu kanta a ciki. Tun cikin shekarar da ta gabata dai ake ta
tukawa da kwancewa a kotu kan wannan al'amari,
cikin wannan shekara ake sa ran yanke hukuncin karshe. Abin da ake ta kace-nace a kai dai shi ne, shin,
ya halatta a rika daukan hotunan da ke shafukan Intanet kai tsaye a yi wa mutum
hukunci da shi ba tare da neman wasu karin bayani daga gare shi ba? Duk me ya jawo wannan? Katobarar da Nathalie
ta tafka, wajen loda hotunanta don nuna wa wasu cewa lafiya take. Ga shi sun jawo mata matsala mai girma. An
kwace gidanta, sannan an janye tallafin lafiya.
Gargardi
Wadannan kadan ne daga cikin ire-iren al'amuran wauta, da sakaci,
da ganganci, da gidadanci, da tumasanci, da kauyanci da ke faruwa a Dandalin
Facebook a wasu kasashe. Shi yasa masana
ke shawartar jama'a da su shiga taitayinsu.
'Yanci ba hauka bane, sam. Graham
Cluly daya ne daga cikin manyan ma'akatan kamfanin SOPHOS, kuma shahararre ne
kan sanin hanyoyin kariyar bayanai da tsarin sadarwa a kwamfuta da
Intanet. Kamfanin SOPHOS kamfanin
sadarwa ne da ke lura da kwayoyin cutar kwamfuta (Computer Virus) da wasu ke
aikawa ta Intanet, don baiwa manyan kamfanonin sadarwa a Intanet, da hukumomi a
kasashen Turai kariya daga kamuwa da su.
Daga ofishinsu suna ganin irin kura-kuran da jama'a ke tafkawa wajen bayar
da bayanansu musamman na sirri da dai sauransu.
An tambayi Graham Cluly, kan ire-iren wadannan katobara da jama'a
ke tafkawa a Dandalin Facebook, sai yace da farko: "Facebook ba kyauta
bane, domin sun fi ka riba ma, duk da cewa kana ganin kyauta ka ke komai a
ciki, ba ka biyan kudi. To, amma ya
kamata mutane su san cewa, duk abin da ka latsa a shafin Facebook, ko ka rubuta
a shafinka ko a shafin wani, ko ka "so" (like), ko duk wani hoto da
ka loda ko bidiyo, duk kudi ne a gare su.
A takaice ma dai, kai ne hajar da masu shafin Facebook ke sayarwa." Dankari!
Ba kowa ya san haka ba, musamman matasanmu a kasashe masu tasowa. Muna ganin ai Facebook kyauta ce, inda za mu
samu abokanai da 'yan mata. Mu fadaka.
Sai Graham Cluly ya ci gaba da cewa: "Ya kamata kuma mutane su
san cewa, duk abin da ka rubuta shi a shafin Facebook, ko wani hoto da ka loda
a shafin, to, ka rasa shi kenan har abada.
Domin ba ka da wani iko a kansa. Wani na iya daukawa yayi duk abin da
yake so a kai." Zan kawo mana
misalai kan wannan batu na Cruely a gaba in Allah ya so. To, amma abin da wannan batu ke nufi shi ne,
in dai kana da wani abu da ka san sirri ne na rayuwarka; hoto ne, bayanai ne,
kasida ce, bidiyo ne, sauti ne, to kada ka loda a shafin Intanet. Domin kamar ka kai kasuwa ne ka ajiye, duk
wanda ya masa, zai iya tayawa. Shi yasa
a gaba Cluly yace: "Muddin ka san ba za ka iya zuwa tsakiyar kasuwar
garinku ka daga murya kana gaya wa jama'a sirrin rayuwarka ba, to ko kadan kada
ka rubuta ko loda su a shafin Facebook.
Duk abin da ka san ba ka son kowa ya sani, kada ka rubuta shi a shafin
Facebook." Wannan sakon a fili
yake, ba ya bukatar sharhi.
Dangane da abin da ya shafi yin amfani da shafin Facebook wajen
aikata miyagun ayyuka da laifuka kuma, Graham Cluly yace: "Dandalin
Facebook ne shafin miyagun laifuka da ayyukan yanar gizo da yafi saurin habaka
a duniya yanzu. Akwai satar bayanan
sirri, da yada kwayoyin cutar kwamfuta, da aikata miyagun ayyuka da laifuka da
ake yi a Dandalin Facebook fiye da kowane irin shafi a duniya. Idan kana son zuwa babbar matattarar 'yan
ta'addar yanar sadarwar duniya a yanzu, to ka je Facebook." Wannan bayani ne da nake da tarin sheda a
kansu, da ma wasu daga cikin hadarurruka da jama'a ke jefa kansu a ciki. A gaba za mu ci gaba in Allah Ya so!
No comments:
Post a Comment