A yau ga mu dauke da wasu daga cikin
wasikunku. Wadanda na amsa a lokacin da aka turo, na goge su. Wadanda ke nan a yanzu su ne wadanda ban samu
amsa su ba sadda masu sakonnin suka aiko. Akwai wadanda aka aiko ta akwatin
Imel, su ma wadannan duk na amsa su. Sai
kuma wadanda suka kira don neman karin bayani. Kada a mance, idan an tashi aiko
sako, a rika hadawa da adireshi. Kuma ga dukkan masu sha'awan kasidun da suka
bayyana a shafin nan cikin shekarar da ta gabata, a halin yanzu na loda su gaba
daya cikin shafukanmu da ke Intanet.
Idan kasidun Kimiyyar Sadarwa ne zalla, a je shafin da ke: http://fasahar-intanet.blogspot.com
idan kuma na sauran fannin ilmin kimiyya ne zalla, sai aje wannan
shafin: http://kimiyyah.blogspot.com Da fatan za a dace.
…………………………………………………..
Assalamu alaikum Baban Sadik, ina maka
fatan alheri tare da daukacin musulmai. Don Allah ina so kayi min bayani a kan "Hacking."
Wassalam, ka huta lafiya. Muhammad U. Bala, daga unguwar Kofar Ruwa
"B" karamar hukumar Dala, jihar Kano. 08069367793
Wa alaikumus salam Malam Muhammad, da
fatan kana lafiya. Ina godiya da addu'arka. A baya bayanai sun gabata masu
tsawo kan kalmar "Hacking" da "Hackers", wato dandatsanci
kenan, ko aikin fasakwaurin kwamfuta.
Abin da wannan kalam ke nufi shi ne tsarin amfani da kwarewar ilmin
kwamfuta wajen aiwatar da wasu ayyuka na amfani ne ko cutarwa. Kalma ce mai harshe biyu wajen ma'ana. Asali ana amfani da ita ne ga 'yan dandatsa,
matasa ko kwararru masu amfani da kwarewarsu wajen aiwatar da ta'adanci ta
hanyar kwamfuta da Intanet; ko sace bayanan sirri, ko yada kwayoyin cutar
kwamfuta, ko leken asirin abin da mutane ko ma'aikatan hukumomi ke yi. Amma da tafiya tayi nisa, sai aka canza wa
kalmar ma'ana, inda a galibi ake amfani da kalmar da manufar kwarewa wajen sarrafa
kwamfuta da aiki da ita. Duk wanda aka
kira shi da "Hacker" kuma ana daukansa a matsayin kwararre ne wanda
ya san makaman amfani da sarrafa
kwamfuta. A yayin da ake amfani
da kalmar "Cracking" ko "Crackers" wajen nufin masu aiwatar
da ta'addanci. Duk da wannan canji dai har yanzu akan yi amfani da kalmar ne
wajen nufin masu aiwatar da ta'addanci ta hanyar kwamfuta da Intanet. Da fatan ka gamsu.
Baban sadiq sannu da aiki, Allah ya kara
basira kuma ya raya mana sadik. Daga
Lauwali Ja'afar mai nema ga Allah, dan (Niger), Malali, Kaduna.
Lauwali barka dai, ina godiya matuka da
addu'arka, kaima Allah kara maka basira, ya kuma ba ka wadatuwa wajen nema ga
Allah, da'iman. Amin.
Assalamu alaikum Baban Sadiq, kuma na dauki
dogon lokaci ina karanta shafin nan naka. Ba abin da za mu ce sai dai Allah ya saka maka da alheri.
Mutane suna karuwa sosai da abin da kake
rubutawa a duk mako. Ina son yin amfani da
wannan dama don neman fahimta; me yasa idan mutum ya aika sako a daga wasu
wayoyi kamar Nokia, za ka iya zuwa wani wuri ka ga kwafin sakon da ka aika ko ka tura, amma a Tecno ba haka abin yake ba?
A huta lafiya. Suna na Usman, ina cikin Lafiyan Barebari: 08135433503
Wa alaikumus salam, ina godiya matuka da
wannan sako. Kamar yadda kace, ana dai iya kokarin wajen fadakarwa kamar yadda
ya sauwaka. Allah sa mu dace, amin.
Dangane da tambayarka, abin da ke faruwa shi ne, a Tecno din ma akwai
inda za ka je ka ga sakon, sai in ba a saita wayar a haka ba. A ka'ida, kowace waya tana taskance sakonni
na kira da sakonnin tes da ake aikawa daga gare ta zuwa wasu wayoyi ko layukan,
amma da sharadin idan an saita wayar don gudanar da wannan aiki. Don haka akwai alamar ba a saita wayar don ta
rika taskance sakonnin da aka aika daga gare ta ba shi yasa. Idan kana bukata sai ka "Menu", ka
shiga "Message", sai ka gangara "Settings," ka shiga inda
aka ce "Save Sent Messages," sai ka matsa "Yes" ko wani abu
makamancin hakan. Daga nan duk sadda ka
aika sakon tes, wayar za ta taskance masa su, don komawa gare su a duk sadda
kake so. Da fatan an gamsu.
Salamun alaikum Baban Sadik, har yanzu ban gaji da tambayarka
ba dai! Ka ba ni cikakken bayani a kan Bermuda
triangle. Dangana Musa Azare
Wa alaikumus salam, Malam Dangane, bayanai kan Tsibirin Bamuda sun
gabata a wannan shafi. Mun rubuta ko gabatar da kasidu sama da shafuka 12 kan
asali da yadda wannan tsibiri yake, da irin abubuwan da suka faru, da ra'ayoyin
masana kan haka, da kuma rubuce-rubucen da aka yi akai. Idan kana bukatar
wadannan kasidu, ko dai kaje shafinmu na Intanet da ke: http://fasahar-intanet.blogspot.com ko http://kimiyyah.blogspot.com, ko kuma ka turo adireshin Imel sai in tunkudo maka kasidar gaba
dayanta ka dabba'a don karantawa. Da
fatan ka gamsu.
Fatan alheri a gare ka. Fatana Allah ya
kara maka daukaka, da hakuri da mu. Malam Imail di na ne ya samu matsala, na
shiga sai aka ce mini: "Where Did U Meet U Spouse?" - Ali Jauro
Godiya nake da addu'a Malam Aliyu. Abin
da ke faruwa shi ne, watakila ka saba shiga akwatin Imel dinka ne ta hanyar
wata waya ta musamman, amma sai ka samu canji.
Duk sadda ka zo shiga da wata wayar daban, ko ta hanyar kwamfuta,
masarrafar za ta gane cewa ba ta hanyar da ka saba shiga bane ka shiga, ma'ana
kamar ba kai bane, wani ne ke kokarin shiga akwatin naka da karfi. Don haka sai
a nemi tantancewa, ta hanyar aiko maka da tambayar da ka amsa sadda kake bude
akwatin Imel din. Wannan shi ne abin da
ya faru. Don haka, sai ka rubutu musu
amsar da ka sa a sadda kake bude Imel din.
In kuwa ba haka kayi ba, to zai yi wahala su baka daman shiga. Da fatan ka gamsu.
Salam, don Allah ka taimaka min da hanyar
da zan gyara shafina na Facebook a Privacy kamar yadda ka gaya min,
domin na shiga amma na kasa fahintar yadda zan gyara, kuma har yanzu ana yi min
satar fage a shafin nawa. Da fatan za ka
turo min ta layi na. Na gode daga Aminu Garba Dirimin Sambo Kano
Wa alaikumus salam, Malam Aminu ka
gafarce ni, domin na riga na goge tes din da ka aiko a waya ta, sai wanda na
taskance a kwamfuta di na. Abin da nake
tunani shi ne, ko dai ka taba ba wani kalmomin izinin shiganka (Password), ko
kuma 'Yan Dandatsa, wato "Hackers" sun shiga shafin naka. Wannan ba
wani bakon abu bane. Don haka, idan ta
waya kake shiga, da zarar ka shiga shafin sai ka gangara kasa inda aka rubuta
"Settings" ka shiga, a nan za ka ga dukkan zabe-zaben da ke ciki masu
taimakawa wajen kariya. Idan damuwanka
shi ne wasu suna iya yin rubutu a shafinka, ko bangon shafinka, wato
"Wall" kenan, ina iya cewa wannan ba wata damuwa bace. Amma idan kana son hana hakan. In har wannan ne matsalarka, to a gaskiya ba
wata matsala bace kamar yadda kake riyawa.
Amma idan kana samun sauye-sauye ne a shafinka wadanda har ga Allah ka
san ba kai bane kayi su, sannan bai kamata a ce wani ya yi su ba kai ba, to, shawarar
da zan bayar kawai ita ce, ka kulle shafin (Deactivate), sannan ko bude wani
daban, sabo. Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum Baban Sadik, gaskiya
muna jin dadin wayar mana da kai da kake. Malam ina da wata mastala da take
damu na kullum. Idan zan taba rediyo sai
ta buge ni da sinadaran lantarki, ko in zan kunna na'urar DVD ma haka ne. Amma da wani zai taba ba zai samu wannan
matsala ba. Kuma ko da rediyon na aiki
da batir ne, idan na taba karfin lantarkin na iya ja na. Abin yana damuna. Meye mafita? Na gode. Daga mai son shawararka
a kullum; M. Adamu shushaina, Dikko, Jahar Naija.
Wa alaikumus salam, Malam Adamu. Ina
godiya da addu'o'inku. Allah saka da alheri, amin. Dangane da wannan matsala na jan sinadaran
maganadisun lantarki da kake samu kan duk abin da ka taba, zan so ba da
shawaran ganin likita ko wani kwararre kan harkar wutar lantarki. Musamman ganin cewa idan kai ka taba kana samun matsala, amma duk wanda ya taba ba
ya samun ja daga sinadaran maganadisun lantarki. Amma kafin nan, abin da na sani sh ne, akwai
hanyoyin gudanuwar maganadisu/wutar lantarki guda biyu. Na farko shi ne ta yin
amfani da wayoyi, don daukan wutar lantarki daga wani wuri zuwa wani, ko daga wata na'ura zuwa
wata, ko daga wani bangare zuwa wani bangare.
Wannan shi ake kira "Current Electricity." A daya bangaren kuma akwai tsarin gudanuwar
wutar lantarki sanadiyyar haduwar abubuwa biyu masu akasin dabi'a (tsakanin
mahallin namiji – Positive – da mace – Negative). Wannan yanayi shi ne wanda muhalli ke samar
da shi. Ma'ana, a duk inda dan adam ke
rayuwa ana samun wannan tsarin gudanuwar lantarki. Yana samuwa a jikin abubuwan daki, kan mota,
ko a jikin tufafi, a tsakanin kayayyakin lantarki, kamar yadda kake samu.
Bayan haka, yanayin jan wutar lantarki
sanadiyyar taba kayayyakin lantarki kamar rediyo a misali, yana samuwa ne
sanadiyyar maganadisun lantarkin da babbar masarrafar rediyo ko talabijin ke
bazawa zuwa sauran bangarorin rediyon, ko da kuwa a kashe take. Wannan babbar masarrafa ita ake kira
"Capacitor", wanda ita ce ke gudanar da wutar lantarki a tsakanin
rediyon a sadda take kunne. Da zarar an kashe, wannan yanayin lantarki ba ya
gushewa, sai a hankali. Don haka, da
zarar hannu ya taba, nan take ragowar wannan sinadaran lantarki zai tunkude shi
gefe. Abin da ke haifar da hakan kuwa
shi ne ragowar karfin lantarkin da wannan masarrafar lantarki ta taskance,
kafin ya bi iska. Hakan nan akan samu
sinadaran lantarki a jikin tufafi mai kaushi musamman, da jikin mota, ko cikin
daki, ko a tsakanin gashin kan mutum, muddin wadannan abubuwa suka yi kacibis
da wani abu da ke dauke da sinadararan lantarki da ke samuwa a muhalli. Wannan tsarin samar da sinadaran lantarki shi
ke kira "Static Electricity."
Don haka, idan a cikin daki ne, kana iya bude tagogin dakin, ko kayi
amfani da na'urar dumama daki (Heater) don kore wannan yanayi na lantarki. Da fatan ka gamsu.
Baban Sadik, Rabbi yai sakamako da aljanna. Na dade ban bude akwatin Imel di na ba, na sa
kalmar shiga (Password) sai ta aka ce mini: "Wrong password." Kuma da
shi nake shiga shafin Facebook. Abul Waraqaat
Malam Rabi'u Isa barka ka dai. Wannan ke nuna cewa lallai ka mance kalmar
shiganka ne. Don haka a kasa za ka ga
inda aka ce: "Forgot Your Password?"
ka matsa, za a kaika inda za samu bayani kan yadda za ka warware
matsalar. Da fatan an gamsu.
Salam, fatan alheri. Wallahi duk lokacin
da zan shiga Shafin Facebook, sai a ce min dole sai na sa Confirmation
Mail, kuma Gmail ya ki budewa. Ya zan
yi? Sako daga Yahuza Idris, Hotoron Arewa
Abin da wannan ke nunawa shi ne, baka
shiga shafinka ta hanyar da ka saba shiga ba, kamar yadda nayi bayanai
makamancin wannan a sama. Don haka, sai
ka nemi kalmar shigan Gmail dinka, tunda da adireshin Imel ka bude shafin ba da
lambar waya ba, ka je akwatin Imel din, akwai sako mai dauke da "Kalmar
Tantancewa" (Confirmation Code) da suke aikawa a duk sadda aka bude shafin
Facebook. Wadannan kalmomi su za ka
dauko ka saka, sai a baka damar shiga.
Da fatan an gamsu.
http://www.fnur.bu.edu.eg/
ReplyDeletehttp://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/422-2013-12-10-10-18-01
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/421-2013-12-10-09-48-39
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/419-2013-12-09-07-21-12
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/420-2013-12-10-09-48-38
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/417-2013
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/418-2013-12-09-07-17-28
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/415-2013-12-03-08-09-23
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/416-2013-12-03-08-25-21
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/413-2013-11-21-07-50-21
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/414-2013-11-25-09-38-30
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/411-2013-11-20-08-11-53
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/412-2014
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/409-2013-2014
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/410-2013-11-13-17-25-28
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/407-2013-11-09-08-51-15
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/408-2013-11-13-11-55-53
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/405-2013-11-09-08-42-05
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/406-2013-11-09-08-46-10
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/main-news/item/403-2013-11-09-08-25-
http://www.fnur.bu.edu.eg/
ReplyDeletehttp://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/departements
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/medical-surgical
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/community-health
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/nursing-administration
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/mother-health-obstetrics
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/mental-health
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/pediation-nursing
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/dean-word
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/about-faculty
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/about-faculty/tip
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/about-faculty/vision-mission
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/about-faculty/goals
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/about-faculty/faculty-administration
http://www.fnur.bu.edu.eg/fnur/index.php/about-faculty/previous-deans
Har zuwa karshen karni na 19, Hausa news da ilmin dabi'a sun kasa fahimtar tsarin da mai bacci yake ciki, da abin da ke haddasa shi bacci, a hakika. A yayin da kowannensu ya saba wa dan uwansa wajen sakamakon bincikensa, a daya bangaren kuma, duk sun dace a kan cewa a yayin da mutum ke bacci, kwakwalwarsa tana daina aiki ne gaba daba daya. Kuskuren da ke cikin wannan zance da fahimta nasu bai bayyana a fili ba sai da duniya ta shiga karni na 20
ReplyDeleteby Hausa NG
Read Hausa news now
for Hausa people in
Hausa language
Thanks for example
ReplyDelete