Assalaamu
alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya, Allah kara maka basira da hikima.
Shin, me yasa idan aka boye lamba daga wayar salula, kuma aka turo sakon tes da
ita, sai lambar ta bayyana a sakon?
- Prince Sadiq Babanni, Yola.
Wa alaikumus salam, Malam Sadik barka da warhaka. A ka'idar aiwatar
da kira da wayar salula, idan ka kira wani, za a nuna wa wanda ka kira lambarka
a wayarsa, yana gani. Amma idan kaje
sashen Tsare-tsaren wayarka, watau "Settings", ka canza wannan tsari
cewa kada ta rika nuna wa wanda ka kira lambarka, to za ta boye lambar. Wannan a kira ne kadai ya tsaya. Amma idan ka aika sakon tes dole za ta nuna. Domin babu wani tsari na boye lambar wanda ya
aiko tes a wayar salula. Dole za ta nuna. Da fatan ka gamsu.
Assalaamu
Alaikum, barka da warhaka. Yanzu don
Allah kai Abdullahi Salihu Abubakar kace yin azumi a watan Rajab ba daidai
bane? A matsayinka na Musulmi? - 08031323908
Wa alaikumus salaam, na san kana ishara ne zuwa ga bayanin da nayi
a cikin kasida ta mai taken: "Bunkasar Fasahar Sadarwar Zamani a Najeriya
– Kalubale da Hanyoyin Ci Gaba," inda nake bayani cewa jama'a su yi
hankali da sakonnin da ake turo musu ta tes musamman lokacin azumi kan falalar
ayyuka, da cewa akwai hadisan karya da ake aikowa. Idan ka fahimce ni, ban ce yin azumi a watan
Rajab ba, nace kan "…falalar yin azumin Rajab." Akwai bambanci tsakanin "yin azumi a
watan Rajab, da falalar azumin Rajab."
Akwai hadisan karya sama da talatin da aka kaga aka ce Manzon Allah ne
ya fada, masu nuna falalar watan Rajab.
A wasu kasashe bayan azumi, ana yanka dabba da ake kira
"Ateerah", ana kwana sallah a tsakiyar watan, watau "Salaatur
Ragaa'ib," ana rarraba gurasa da masa bayan an karanta musu Suratul Mulk,
duk wannan bai inganta ba daga Manzon Allah.
Mu a nan abin da muka fi yi shi ne azumi, wanda muke kira azumin
tsofaffi, da kuma sallar tsakiyar wata.
Amma yin azumin nafila cikin Rajab, kamar yadda aka saba yi a sauran
watanni, ya halatta kuma ma abin so ne. musamman azumin litinin da alhamis, da
yin azumi uku cikin kowane wata, duk sun inganta daga Manzon Allah. Amma idan
da wancan manufa ce, cewa watan Rajab na da wata falala ta musamman, ba abin da
ya inganta. Don karin bayani ka duba
littafin "Al-Fawaa'idul Majmoo'ah fil Ahaadeesil Mawdoo'ah" wanda
Shawkaani ya rubuta, lambar hadisi na 287, da 288, da 289, da 290 da kuma
291. Da fatan ka gamsu.
No comments:
Post a Comment